← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 210

Sashe 8

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri maman nana ta soko ma sumayyan wata hirar don ta hana kunnuwanta jin abinda suke fadin,saidai ko kadan bata cimma nasara ba saboda wani tashin hankali da taji ya ziyarceta,gudun zuciyarta ya qaru,sai ta kalli maman nana
" maman naana,qirjina bugawa yake bansan me ya sameni ba"dan murmushin kwantar da hankali tayi mata
"Kada ki damu,wannan shi ake kira kishin,kiyita ambaton hasbunallahu wa ni'imal wakeel,ni'imal maula wa ni'iman nasir" kai ta kada hawaye na silalo mata,ta sanya hannunta ta share tana mai bawa kanta qwarin gwiwa tare da hana kanta da kanta kuka.

Labule aka bankade aka shigo,fiddausi cs goye da 'yarta,ta dubi sumayyan sannan tace
"Kije dakin amarya,yaya bara'atu na son ganinki",cikin mamaki maman nana ta dubeta
" a'ah,ai ba'a haka,amaryar ai ya kamata tazo ko?"duban maman nanan tayi sai ta juya ta fice ba tare da tace komai ba.

Ko minti daya ba'a qara ba saiga yaya bara'atun ta shigo
"Baiwar Allah ke a suwa kuma,wacece ke da har zaki hanata zuwa,to bari kiji,idan ma irin masu shige da fice ne gidan kishiyoyi suna hurewa kishiya kunne wahalar da sumayya kawai zakiyi,don zama fa'iza tazo yi ta kuma hayayyafa,ba mun kawota ne don ta tafi ba,saboda haka ke sumayya ina jiranki", wani abu yazo ya tokare maman nana a wuya,tamkar zata tanka sai taga hakan bashi da wani alfanu,tayi qoqarin kai zuciyarta nesa,saboda koda ta tanka din qila qarshe abun ya juye kan sumayyan wanda bazata so hakan ba,sai abun ya mata yawa ta rasa da wanne zata ji.

Itama ta riqe hannun sumayyan cikin kalamai na qarfafa gwiwa ta mara mata baya har zuwa dakin marya,babu laifi dakin ya cinye komai nata kasancewar yana da yalwa,kuma ba wasu uban kaya suka mata ba,tunda gaba daya sun daga hankali ne anyi bikin cikin matsatstsen lokaci ba tare da sun gama shiryawa ba su kansu.

Gefe daya suka samu suka zauna,sumayyan ta gaidasu daidaikum cikinsu suka amsa,maman nana kam babu wanda ta duba cikinsu don dama darajar sumayyan ya sanyata shigowa dakin,wata 'yar tsohuwa ce dake zaune gefan amarya wadda ta lullube fuskarta da mayafi tace
" to sumayyatu,ga 'yar uwa nan mun kawo miki,abokiyar zama,Allah ya baku zaman lafiya,muna fata zaku hada kanku ku zauna lafiya"
"Kowa ya kwana lafiya ai shi yaso ato,fa'iza dai gata nan zama daram ila yaumut takunu" yaya bara'atu ta karbe zancan daga gun tsohuwar,rai bace maman nana ta daga kai ta dubi yaya bara'atu,mamaki take bata,wai 'yar yarinyar da duka duka take cikin shekaru na sha takwas take zagewa babba da ita tana yadawa wadan nan habaice habaicen da suka girmi kanta,babu lallai ma kan nata ya iya dauka,ina laifi ma ta bar yaranta masu shekara sha hudu sha biyar su gayawa sumayyan?,wata qila ace wadan nan sine dai dai da ita,amma ba ita ba wadda ta kusa linka shekarun sumayyar ba.

Ta tabbatar idan taci gaba da zama cikin dakin tabbas za'ayi batacciya da ita,bata so kuma wani abu na tsiya ya hadasu,tunda duk tsiya tafiya zasuyi ba zasu shekara ba,kuma gidan dan uwansu ta shigo sunci albarkacinsa,tunda mukhtar kowa ya shaidi halinsa,sai ta kama sumayyar ta miqar sannan ta ari bakinta ta ci mata albasa,don ta fuskanci ba zata iya magana ba kuka take qasa qasa kanta duqe
"Insha Allahu baba babu wata matsala,don sumayya bata da damuwa mu mun shaideta tun tana tatsitsiyarta muke tare da ita,zaman lpy an sameshi an gama da izinin Allah"
"To Allah ya yarda 'yar nan" cewar tsohuwar.

Da sauri ta janye hannun sumayyan suka fice saboda ta soma ganin bakinsu yana motsi suna shirin fara qananun maganganu,sai data tabbatar sumayyan ta samu nutsuwa kana tayi mata sallama ta tafi,zuwa lokacin suma 'yan kawo amaryar suna qofar gida suna shirin tafiya.

Sha daya na dare agogon falon nata ya nuna mata,gidan yayi shiru kowacce na dakinta,sauqinta daya akwai wutar nepa da ta haskake ko ina cikin gidan,ta sauke ajiyar zuciya tana ci gaba da jan hasbunallahu wa ni'imal wakil,har zuwa lokacin da taji an turo qofar gidan an shigo,sai ta miqe tsam a tsorace kasancewar basu taba barin qofar gidan nasu haka ba.

Tana ji aka rufe qofa ta biyu hakan ya alamta mata cewa mai gidan ne,ta aauke ajiyar zuciya duk da cewa tana tsayen bata zauna ba.

Da sallama ya daga labulen dakin idanunsa ya sauka a kanta,ta kowa yayi a hankali ya shigo dakin yana dubanta yadda tayi carko a tsaye,cikin sanyin murya yace
"me kikeyi a tsaye haka kamar wadda taga wani abun tsoro" ta saki ajiyar zuciya,muryarta a sanyaye tace
"Ji nayi ana taba qofa ne",murmushi yayi yana ajjiye ledojin hannunsa
" ke kam farar kura ce sumy"sai tayi murmushin yaqe tana kawar da kai,ta qarasa inda yake tana masa sannu da zuwa ya amsa yana zama kan daya daga cikin kujerun falon
"Hada min ruwan wanka sumayya" ta danyi sororo kamar tace wani abu sai kuma ta fasa tace to.

Wanka yayi sannan ya sauya kayansa,falon ya dawo ya zauna yana maida numfashi cike da gajiya,shiru ne ya ratsa tsakaninsu kowa ya rasa abinda zaya cewa dan uwansa har kusan sha daya da rabi.

Motsi suka dinga jiyowa a tsakar gida,kallo juna suke suna sauraron motsin ba tare da kowa ya cewa kowa komai ba,sumayya ce ta fara fahimtar amarya ce,sai ta dubi mukhtar
"Ya mukhtar bacci nakeji"
"Hala ma korata kike da dabara ko?"kai ta kada zuciyarta a cunkushe
" a'ah ya mukhtar ba haka bane"shiru yayi har kusan mintina goma wanda motsin da suke ji na qara qarfi kadan kadan.

Miqewa yayi ya dauki leda biyu cikin ledojin da ya shigo da su ya tura mata daya sannan yace
"Tashi muje ki rakani" daga kai tayi kawai ta dubeshi,tamkar tace ba zata ba amma sam bata iya rashin kunya da gardama ba,kuma ba zata fara a kan ya mukhtar din ba da take ganin qimarsa.

Mayafinta ta janyo ta yafa sannan ta miqe,tare suka jero har zuwa qofar dakin.

A tsaye suka sameta a bakin qofar dakin,tana ganinsu tayi hanzarin komawa kan kujerar ta zauna,saidai kallo daya zaka mata ka fuskanci ko kadan babu walwala saman fuskarta.

Mazauni kowanne ya yiwa kansa,shiru ya dan ratsa,sumayya ta gyara zama tayi qoqarin cewa
"Sannu amarya"
"Uhmmm" kawai ta fadi,shirun suka sakeyi,sai da ta mula don kanta wai ita an mata laifi kana ta gaida mukhtar din,ya amsa sannan ya fara magana,daki daki daga bisani ya gangaro ga rufewa
"Daga qarshe ban auroki don ki raina min mata ba,ban auroki saboda sumayya ta gaza ta kowanni fanni ba,ina son mata ta matata tana sona,bana son tashin hankali cikin gidana,na riga da nasan halin sumayya tun tana mitsitsiyarta,saboda haka ku hada kanku ku zauna lafiya.....haka kema sumayya duk da nasan ki tun ba yau ba baki da matsala,inaso ki dore kan halayenki kada kice zaki sauya,saboda bazan lamunci rashin gaskiya ba......akwai wani sauran mai magana?".

Jin shiru ya sanya duka suka gane ba zata yi magana ba,sai cika da take tana batsewa,hakan ya sanya sumayya cewa
"In sha Allah ba zaka samemu da matsala ba,zamu zauna lafiya da junanmu,Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu"
"Amin amin" miqewa sumayyan tayi sai shima ya miqe
"Muje na rakaki ko" duk da suyar da ranta yakeyi amma sai da yasa ta dan murmusa,ina dakin fa'izan ina dakinta.

A tsakiyar falon suka tsaitsaya suna kallon juna,hannayenta ya kama a sanyaye yace
"Kiyi addu'a ki kulle qofar dakin,kiyi bacci sosai kada ki sa damuwa a ranki,mukhtar naki ne kinji ko" kai ta gyada
"Sai da safe" ya fada yana juyawa a sanyaye.

Duk yadda taso danne qwallar data cika mata ido abun ya faskara,duk yadda taso jurewa ta kasa,ashe kishi gaskiya ne haka yake?,ada idan ana zancan shi dariyarta take tuntsirawa abunta,sai ta cafko hannunsa ya waiwayo yana dubanta
"Ya mukhtar,ka zama mai adalci tsakaninmu,don Allah kada ka wofantar da ni" kai ya gyada ya janyota jikinsa ya rungumeta yana share mata hawaye yana fadin
"In sha Allah" sai da ya tabbata ta hau gadonta ta kwanta sannan ya fice ya rufe mata qofar.

Ta rufe idanunta a hankali tana fata bacci ya dauketa,karo na farko kuma rana ta farko a shekarun aurenta da zata fara kwana ita daya cikin dakinsu kan gadon su.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*rabbana afrig alaina sabran watawaffana muslimin*

0⃣6⃣

Idonta ta runtse tana jin qarar rufe maga qofar da yayi,ta gefe daya ta kwanta ta sake mirginawa daya gefan,gaba daya take jin gadon yayi mata fadi.

Ganin tana neman cinhe daren idanu biyu ya sanyata runtse idonta,ta damqe filon da take kai tana fadin
"Ya rabb,afrig li sabra" tayi ta maimaitawa babu qaqqautawa,Allah maji roqon bawansa,bata san lokacin da wani bacci ya sadado ya sace ta ba.

Qarfe shida ta farka firgigit tana ambaton sunan Allah,tayi mamakin yadda tayi bacci mai nauyi irin haka,cikin mutuwar jiki ta sauko daga kan gadon ta fito.

A hankali ta murda qofar dakin nata kana ta tura ta ta bude,tashin farko idanunta suka sauka kan qofar dakin fa'iza amarya,qofar dakin na kulle gam da alamu ba'a bude ta ba tunda aka rufe,sai taji wani qunci na ziyartar zuciyarta,ta kau da kai tana jan tsaki kana ta wuce bakin fanfo,ta taro ruwa ta shige bandaki ta kama ruwa sannan ta fito ta daura alwala.

Har qarfe takwas na safiya tana saman abun sallar,ta kalli agogo sannan ta janyo rediyonta data kunna wadda ita ta tayata zama ta kashe,ta miqe ta zare hijabin jikinta ta ajjiye ta fito zuwa tsakar gidan,ta saba tun tuni da kammala ayyukanta da wuri saboda ya mukhtar bai wuce goma a gida.

Idanunta suka sake sauka kan qofar dakin karo na biyu,sabanin dazu yanzu an sassauta rufin qofar da alama an budeta ne,sake dauke kanta tayi sannan ta shiga ayyukanta kamar yadda ta saba.
Chapter 8 · 0% Book details