Sashe 190
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun daga nesa ta hango tahowar motar 'yan sandan amma sai ta dauke kai saboda tasan bata da wata alaqa da su,ga mamakinta gabanta suka tsaya,a wulaqance ta daga kai tana dubansu zata soma zazzage musu ruwan masifan sunzo gabanta sun tsaya sun tada mata qura,fitowar daya daga cikin 'yan sandan ya tsaya qiqam gabanta shi ya katse mata masifar data so yi
"Malam lafiya?" Hannunshi ya saka a aljihun gaban rugarshi ya fito da ID card dinsa ya nuna mata yana cewa
"Suna na inspector uba labaran,ina fata kece Aisha jamil?" Kai take gyadawa
"Eh yes nice,ya akayi kazo gabana kamin wani qiqam?"
"Akwai qorafi a kanka wajen yunqurin aikata laifi,sabida haka muna gayyatarki zuwa ofishinsu ki riqe bayananki duka kya yisu a can" miqewa tayi cikin masifa
"Me kake nufi malam,wannan wanne irin iskanci ne,rashin mutuncin naku na 'yan sanda haf ya kai haka,kawai kazo ka sameni kace wai ana tuhumata,waye yake tuhumar tawa?,wai tsaya ma malam kasan wace ni kuwa?"
"Eh mun sani,wanda kuma ke tuhumar taki ya fiki shi yasa muka zo tafiya da ke" wata gajeriyar baqar mace dake sanye da unifoarm ta fada tana qarasowa gefan eeshan,kallo daya zaka mata kasan fuskarta babu rahama
"Lallai kunyi kuskure,baru na kira mahaifina qila watan rasa aikinkune ya kama" ta fada tana yunqurin fiddo da wayarta daga jaka,damqe jakar matar tayi ta karbeta daga hannunta tana fito da ankwa daga aljihunta tana duban eeshan
"Ko ki wuce salin alin mu tafi,ko kuma ta qarfin tsiya mu saka miki wannan sannan mu tafi da ke" wanu gagarumin baqinciki ya rufe eesha,ta tabbatar matuqar tayi gardamar matar haka zata aikata mata din,bugu da qari kuma ga mutane sun soma cika a wajen,yawancinsu sun santa,sun san dagawa da daga kai irin nata da taka duk uban wanda taga dama,bata ragawa kowa,kada ma dai a ce babanka ba wani bane
"Kawai ki wuce ku tafi sister eesha kada su qaqaba miki wannan qarfen ki kafa tarihi" cewar titi kenan hatsabibiyar yarinyar da suke takun saqa da eesha kaman suna ganin hanjin juna,saboda kowa na taqama da kudin ubanshi,sauran 'yan jam'iyyarta suka sheqe da dariya,ba yadda zata yi,da wani tozarcin ya sameta a nan gwara ta bisu koma mene sa qareta a can,haka ta taka matar ta bude mata motar ta shige suka rufe suka ja suka bar wajen.
Cikin motar ta kallesu tace
"Ni bansan me nayi ba,amma ko mene ku bude jakata akwai kudi nasan su kuke nema zasu isheku ku raba" wani kallo matar ta watsa mata,tuntuni ta fuskanci yarinyar tana da dagawa da izgilanci
"Ko nawa ne jakarki wanda ya turo mu idan su muke buqata zai iya linka mana su" haushi ya tuqeta,cikin tsiwa da masifa tace
"Ni dinma zan iya,akwai atm cikin jakar,ku dauka ku ciri ko nawa kuke so a ciki,nasan dai kudin ciki duka sun muku yawa"
"Munce miki bama so ki rufe mana baki,laifi kikayi kuma dole mu kamaki"
"Mtsweew,ai matsiyaci ko a tandun mai ka sanyashi ka tsamoshi qamas zai fito,kada Allah yasa kuso,labari ya kai kunnen babana zakuyi biyu babu ne,ba kudin ga kuma asarar aikinku da zakuyi"dariya matar tayi,tabbas ba dan yace kada su taba lafiyarta ba da sai ta bawa wannan fuskar da rake taqama da ita lafiyayyun marin da har ta mutu ba zata taba mantawa da su ba
"ina jin baban naki ne ma idan baiyi wasa ba zai rasa hanyar cin abincinsa,dom wannan mutumin lallai an taboshi,ban taba ji yasa an kama wani saboda kan kanshi ba,kuma wallahi kika sake mana magana ko rashin kunya sai na magutsa bakinki a nan na sauya miki kamannin fuskarki" ba shakka eesha naji da fuskarta,ganin yadda matar ta soma huci tana fito da jajayen qananun idanunta ya sanya eeshan yin laqwas,ranta da zuciyarta na tafasa,so take kawai tasan waye yayi mata wannan tozarcin da tunda tazo duniya ba'a taba yi mata irinsa ba,lallai bata da maqiyi kamarshi ko waye.
Suna isa station din suka karbi duka kayanta,sannan aka bude wani daki wanda ba kowa suka saka ta ciki suka maida qofa suka rufe,kukan baqinciki ne ya qwace mata ta soma maganganu tana zage zage,ba wanda ya kulata sai data gaji don kanta tayi shiru,dakin ta fara bi da kallo kusurwa kusurwa,banda duhu da wari ba abinda ke tashi ciki,ga kukan sauro tun yanzu da ranar Allah,ina ga dare yayi,tsaiwa tayi taqi zama sabida qyanqyamin wajen da takeyi,sai daga bisani da taga ba sarki sai Allah qafafunta na neman sandarewa tilas ta tsugunna tana hawaye,addu'a kawai take Allah ya kawo babanta,ba shakka dukka 'yan sandan sai ta sanya an koresu daga bakin aiki.
Qarfe biyu da rabi na rana ya sauka a filin sauka da tashi na jiragen sama dake abuja,a masallacin dake cikin filin ya sallaci azahar,zuwa sannan drivanshi na nan abujan ya iso da daya daga cikin motocinsa na hawa ba bata lokaci suka dauki hanyar gida.
Suna zaune ita da ummi da sajida ne kawai,ummi da sajida na saman kujera,yayin da sumayya ke zaune qasan carfet sajida na ware mata kalabar da amira tayi mata guda takwas sanda tazo dubata,wadanda jelarsu ta sauka a bayanta,hira suke kadan kadan suna tuna haujar amira sanda taji abinda eesha tayi,cewa tayi wallah har gida zata Allah ne kadai take tunanin zai rabasu da eesha,zagi kuwa ranan babu wanda eesha bata shashi ba,sanda ummi taji ta hanata zuwa amira harda qwallar takaici,ita sam bata damu da ko yaron cikin dake jikinta ba,so take kawai taje su casheta,ta rasa ita da amira wa yafi wani quruciya ne.
Shirt ce ajikinta mai shirt sleeve irin ta mata fara qal wadda aka yiwa adon pink,sai A line skert shima pink ne kaman adon pink dake jikin rigar,mayafin da ta dan yane kafadunta da shi fari saboda nauyin ummi da take ji duk da ita ba ruwanta ita tace ta dinga saka su tana shan iska,kalbar an tsafe biyar bata taje ba saura uku.
A nutse ya sanya hannunshi ya turo qofar falon tare da sallama kan labbansa duk da bai bude muryarshi sosai ba,fararen idanunta ta daga suka sauka cikin nashi sanda yake takowa cikin falon ummi na masa duban mamakin zuwan ba zata,sosai ta dauki hankalinshi tayi wani fresh ta qara kyau kaman zane,amma sai miskilancin ya motsa,haushin abinda tayi masa ya taso masa,sai ya janye idanunshi daga kanta ya maida kan ummi fyskarshi kadaran kadaham
"Lafiya dai ko almustapha wannan zuwan ba zata?"
"Lafiya qalau..." Ya fadi sanda yake zaman saman daya daga cikin kujerun falon idanunshi kan qafar sumayya dake miqe saman filo,wani abu ya tokareshi,wato abun har ya kai a nade mata qafa haka?,cikin ladabi yake gaida ummin tana amsawa,ta lura da yanda qafar sumayyan ke jan hankalinsa sai tace
"Kaga tsautsayin da ya faru ko?"
"Na gani" ya fadi kawai yana duban qafar,yanayin yadda ya amsa din kaman yasan komai sai ya bata mamaki,ita dai tasan bata gaya masa ba haka ma sumayya,sai tayi shiru ba tare data idasa bayanin ba,miqewa ummin tayi don son basu waje tana cewa
"Me za'a kawo maka?"
"Ruwa....ruwa ma ya isa"
"To....taso sajida ki kawo masa" badon babu ma'aikatan da zasu kawo masa din ba don ta basu waje nw ta fada tana yin gaba.
Har suka bace a falon idanunshi na zube qur a kanta,baki daya wani nauyinshi take ji ya koma mata wani baqo,tunda suka soma jituwa basu taba nesa da juna haka ba,ribbom ta janyo tana qoqarin tattara gashinta waje guda
"Barka da zuwa,an iso lafiya?"ta ambata tana kunyar kallonshi,bai amsa ba kaman yadda bai bai dauke ido daga kallonta ba,a nutse ya miqe tsam daga inda yake ya tako a hankali zuwa gabanta,durqusawa yayi saman qafafunshi,ya sanya hannunshi ya daga qafar tata dake miqe saman filo ya soma warware nadin da aka yiwa qafar,idanu ta zaro sannan cikin sauri tace
"yau zaya zo ya cire da kanshi tunda....."wani kallo ya watsa mata da idanunshi da ke cike taf da bacin rai,da sauri ta janye idanunshi shi kuma ya maida kai yaci gaba da warwarewar,bai dakata ba sai da ya gama tas sannan ya yar da tsumman gefe cikin tsantsami,duk da cewa ba wani abu yayi ba fes yake,miqewa yayi tsaye ya miqa mata hannunshi alaman ta taso,fargabar tashin take da kuma fargabar taka qafar,gashi lokaci guda ya sauya mata,babu annuri ko kadan kan fuskarshi,ba yadda ta iya haka ta zira hannunta cikin nashi ya dagata ta miqe tana rintse ido.
Baki daya tayi luu zuwa cikin jikinshi saboda ragowar radadin da qafarta take mata,qirjinsa ta fada tana riqe da shi,kusan lokaci guda suka saki ajiyar zuciya,duk yadda yaso boye tasa sai data bayyana sabanin tata da tayita a boye,abinda ke cunkushe cikin zuciyarshi yaji ya soma sauqi,nauyin da qirjinsa yayi ya soma raguwa,wani wawan shauqi kewa da qauna ke ratsashi,take wani abu ya soma kai kawo cikin jikkunansu.
Sajida ce ta fito dauke da cups da gorar ruwa,zata koma da baya almustapha ya dakatar da ita
"jeki dauko mata hijabi cikin kayanta"
"To" ta amsa tana dire cup din sannan ta juya ta haye sama da gudu,dan janyewa tayi daga jikinsa tana dubanshi,so take ta tambayeshi ina zasu bayan mai gyaran zaizo duba qafarta amma ta kasa,yayi mata kwarjini da yawa,daure fuskarshi ya hanata katabus,har sajida ta sauko ta miqa mata hijabin ta sanya ya dubi sajidan
"Ina ummi?"
"Wanka ta shiga"
"Idan ta fito kice mata mun tafi"
"To,a dawo lafiya" cewar sajida tana juyawa ciki,da idanu ya mata alaman su tafi,saidai ta kasa yin gaba,ji tayi kawai yayi sama da ita ko a jikinshi ya soma takawa da ita ya fice daga falonsatar kallon idanunshi take,wadanda tayi kewarsu matuqa da gaske,bata sake yarda da abinda take ji tattare da shi ba sai yanzu da suke tare da juna,hada ido sukayi sai ya dauke kai yana ci gaba da takawa zuwa ma'ajiyar motoci,kunya ta cikata,ganin jifa jifa ma'aikatan gidan na giftawa,saidai duk wanda ya sako kai ya gansu sai ya koma baya ya lafe yana jiran wucewarsu,ko a jikinsa shi kam,sabida tun asali duk abinda zaiyi yanayinsa ne kai tsaye matuqar ya dace da ra'ayinsa ya kuma yi masa dai dai,bai direta ko ina ba sai cikin mota sit din baya,shima ya shiga ya baiwa driva umarnin yaja suje.