Sashe 33
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko alama bata motsa ba har ta qaraso inda take,ta daga hannu da niyyar zuba mata mari caraf ta kama hannun nata ta yarfar da shi gefe,sannan cikin bacin rai tace mata
"Bansan ke din wace iriyar uwa bace,ban kuma san irin tarbiyyar da kika bama yaronki ba,amma bari na gaya miki,matuqar irin wannan tarbiyyar ita kika bashi to ba shakka kin cuci kanki,abu na gaba duk iya zaluncin da zaki aikata cikin gidan nan kiyi,Allah na sane da ke,amma kada ki soma gigin daukar hannu kice zaki dake ni,don baki haifeni ba,ba kuma kisan ciwo na ba kamar yadda kika ce bansan ciwon haihuwa ba,kuma kema ba Allah kika yiwa fadanci ba ya baki,ganin........".ihun da zainab din ta qwalla gami da dora hannu bisa ka ya dakatar da ita daga maganar da takeyi,sai tayi sororo tana dubanta tare da tunanin ko zainab din nada ciwon hauka ne dake tashi lokaci bayan lokaci?.
Sam bata fahimci tarko bane ta dana mata sai data ga shigowar mukhtar cikin kitchen din a rude,ashe tuni taga giftawar inuwarsa ita zainab din,binsa tayi da kallo sanda ya nufi zainab,ta manta kwana nawa rabon da ta sanyashi cikin idanunta,ranar qarshe kawai zata iya tunawa da bata kuma ganinsa ba sai yau,itace randa ya rufeta da fada tamkar zaya daketa,sabida tayi dan wake abincin dare,ita kuma zainab tace sam bazata ci ba ai dan wake ba abinci bane,ya umarceta ta shiga kitchen ta yiwa zainab din shinkafa da miya qarfe goma na dare,umarnin ya yi mata tsauri saboda haka bata ko tanka ba ta wuce dakinta tayi kwanciyarta bayan ta kulle qofarta,don tana da yaqinin zaya iya biyota,ilai kuwa ya biyo sahun nata,yayi bugun duniya taqi ta bude masa,hakan ya sake harzuqa shi,haka ya koma tare da ci mata alwashin sai ya sabar mata,to tun daga ranar rabon data karbi girki ma cikin gidan,saidai idan sun kammala a barshi a kitchen,idan tana da sha'awarci ta diba,idan bata ga dama ba ma ko kallo bai isheta ba.
"Wato ke kin zama 'yar iska mara mutunci ko?" Ya fada yana nufota cikin huci bayan zainab ta gama tsara masa qarya kan abinda ya faru,hannu tasa ta toshe bakinta saboda yadda taji kanta ya mata dummm,kalmar ta yiwa qwaqwalwarta tsauri haka nan ta yiwa kanta nauyi,ita mukhtar ke kira da 'yar iska?,kalmar da babu wani mahaluqi da ya taba jifarta da ita?,da sauri ta juya ta fita daga kitchen din cikin sassarfa saboda kukan dake shirin qwace mata ba wai don mukhtar din dake nufota ba.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
2⃣8⃣
_________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*
*lillahi mulkus samawati wal'ard,yakhluqu ma yashaa,yahabu limay yasha'u inasan wayahabu limay yasha'uz zukur,au yuzawwijihum zukranaw wa inasaa,wa yaj'alu may yasha'u aqima*
_mulkin sammai da qassai lallai na Allah ne,yana halittar abinda yaso,ya bawa wanda yaso kyautar(d'a) 'ya'ya mata ya bawa wanda yaso kyautar 'ya'ya maza,ko kuma ya cudanya musu maza da mata,ya sanya kuma wanda yaga dama ya zamo bakarara(wanda baya haihuwa)_
*ya Allah ka azurtamu da managartan zuriyya shiryayyu saboda annabinka S A W*
__________________________
Yau babu tantama abinda ke mata kaikawo a zuciya ya tabbata,mukhtar ya daina sonta ya daina mararin ganinta,wannan wacce iriyar rayuwa ce?,haka mata keji duk sanda suka samu juya baya daga wajen mazajensu ba tare da haqqinsu ba?,me yakai wannan zunubi shiga tsakanin ma'aurata?,shiga tsakanin masoya?,masoyan da suka gina zuciyoyinsu da qaunar juna,tsaftatacciyar qauna ta fisabilillahi. Wani mugun amai mai zafi taji yana taso mata,da qyar ta samu ta isa bandaki,ta dinga kakarin aman tamkar hanjin cikinta zai fito,saidai banda wahala da yunquri babu abinda abinda ya fita din saboda babu komai cikin cikin nata,don a yanzu ba kowanne lokaci take yarda da abincin zainab ba. Haka ta gama wahalarta sai yawu kawai data fitar ta sakarwa kanta shower tana wanka tana kuka har ta kammala sannan ta dawo cikin dakin iska na dibarta ta zabi doguwar riga ta sanya ta koma saman gadonta tayi dai dai,jinta take wani iri daban,zazzabi taji na son rufeta,haka ta yunqura ta sha paracetamol ta dawo ta kuma kwanciya,tunani ta shiga mai zurfi lokaci lokaci tana dauke hawayen dake bin kuncinta.
Kamar daga sama ta dinga jiyo sallamar zainab qanwarta,daurewa tayi ta miqe ta dawo bakin qofar dakinta don ta sanar mata tana ciki kada zainab tayi qaryar bata nan,sai data tabbata zainab din taji sannan ta koma bakin gadonta ta zauna har ta shigo. Kallo daya ta yiwa sumayyan tace
"Lafiya kike kuwa anty" qoqarin qaqalo murmushi tayi sannan ta dan ja tsaki
"Qalau nake,yau ne kinga na tashi bana jin dadin jikina da bakina gaba daya"
"Yaya kamar fa kuka naga kinyi" sai ta basar ta hanyar fadin
"Barni kawai,nida mukhtar ne ya matsan sai da nasha magani,ni kuma kinsan bana son qwayoyi" sai zainab din ta gamsu da maganarta ta zauna tana fadin
"Kamar kuwa mamanmu ta sani kinga tace sai na tsaya tayi dambu mutuminki na kawo miki",ba jira kuwa ta sanya hannu ta janyo flask din ta bude ta soma ci. Sosai taji dadinsa cikin bakinta,sai data ci fiye da rabi sannan ta ajjiye.
Bata sake fitowa daga dakin ba ranar,kusan yini sukayi ita da zainab tana mata 'yan gyare gyare cikin dakin,koda ta yunqura don sama mata abinci sai tace azumi ma takeyi,a nan take gaya mata mama tace taje ta yiwa anty dije sallama zasu koma abuja ita da mai gidanta,gwamnatin tarayya ta qara masa matsayi,duk sai jikinta yayi sanyi,bata son rabuwa da anty dijen,idan ta tafi bata da gun wanda zata je su shawarta matsalarta kenan,anty dije zata tafi ta barta a sanda alamu ke nuna matsalolinta qara qarfi suke. Sai taji zuciyarta na neman raurawa amma sai ta aro dakiya da juriya ta yafa wa kanta gudun kada zainab din ta fahimci wani abu.
Sai yamma lis zainab ta tafi ko banza ta debe mata kewa sosai kuwa,a ranar ta sanar da mukhtar tana so taje wajen anty dijen washegari,saboda jibi zasu tafi,Allah ya dorata a kansa ranar tambotsan nasa da sauqi,don a dakinsa ma ta kwana duk da zaman kurame sukeyi.
**** **** ****
Tun goma na safe ta kammala shirinta tsaf cikin shadd ja wadda aka yiwa adon stone work baqi,ita kanta sai data tsaya ta kalli kanta,duk damuwar da take ciki amma sai taga ramarta bata fito kamar baya ba,mamakin yadda ta qara haske da cika takeyi,haka ta yafa baqin mayafi a kanta ta saqala baqar jaka ta fito.
A harabar gidan sukayi clashing da su kasancewar harabar ba mai girma bace,tilas idan zata wuce din su ganta,yana zaune cikin mota zainab na tsaye riqe da murfim mota,kudade ta yanka masa zai bata shine ta biyoshi amsa,tana karba ta juya tayi ciki abinta,zuwa lokacin sumayyan ma har takai ga ficewa daga gidan.
A hankali yake bin bayanta,sosai ya rage gudun motar yana tafiya a hankali don baison ya wuceta,tafiya take cikin nutsuwa,idan ka kalleta sai ka rantse da Allah bata taba aure ba,sosai shaddar ta haska jar fatarta,ga komai nata yayi mata cif a jikinta duk da da shigarta babu inda ta bayyana tsiraici,a haka har suka kai bakin titi,yana so yace ta shigo ya kaita amma kamar an masa shamaki da ita haka yakeji,haka ya karya kan motarsa ya wuceta ya hau kwalta sosai. Itakam sai a lokacin ne ma ta lura da shi,da idanu ta rakashi sannan daga bisani ta dauke kanta tana hadiye wani abu mai d'aci.
Sosai ta lula tunani tsaye a bakin titin wanda hakan ya sanya ta kasa ankara da horn din da yake ta zabga mata,murmushi tayi ta qaraso gaban motar bayan ya sauke glass din
"Wa nake gani kamar abdur rahman cikin mota?"ta fada tana duban motar samfurin *vibe* fara qal da ita,sosai motar ta mata kyau
Murmushi yayi yana fadin
"Eh mana,ya son ranki?" Cikin dariya tace
"Fes wallahi"
"Ina zuwa haka da safe?"
"Zani gidan anty dije ne zamuyi sallama suna shirin bar mana kano su gudu abuja"
"Shigo ciki ma qarasa maganar ai hanya ta ce indai gidan da take har yanzu shine" ya fada yana bude mata mazaunin gaba
"Rufan asiri nan ai na qanwata ne,nan ma ya isa" ta fada tana shiga baya
"Yayarki dai,kina nufin nidin ban girme miki da wajen shekara uku ko hudu ba?"
"Jimin mutum da shegen son girma,shekara hudu kakar wata shekara arba'in,kai uku ne ma"
"Ko second daya ne dai na fiki ko?" Ya fada yana dariya,don sun saba da wannan caftar indai shi da sumayyan ne,itama dariya ta saki sannan suka shiga gaisawa a mutunce,ta tambayeshi mutanan gidan da kawunsa wanda qani ne ga mahaifin mukhtar.
"Kinsan tun ranar nan naso kawowa yaya mukhtar mota ta ya gani da kuma takardar zanen filin da zamu fara gina islamic clinic to ban samu dama ba"
"Da kyau masha Allah abdhr rahman,Allah ya sanya alkhairi ya kade fitina,kace yanzu sai bude asibiti"
"In sha Allah duk da aikin ginin ba qaramin abu bane,har kwantarwa nake sa ran zamu dinga yi,zamuyi amfani da likitancin musulunci da kuma na'urorin bature"
"Kace mun kusa fara kiranka alhaji abdur rahman"
"Da ba alhajin bane?,mijinki zaki cewa haka,gashi har yau ya kasa zuwa ko ina,ya zama sai a hankali wallahi" sai ta danyi shiru tana sauke boyayyar ajiyar zuciya don ha taba mata inda yake mata qaiqayi
"Ina fata kina ci gaba da addh'o'inki ko?"
"Babu abinda na fasa abdur rahman,sauqin ne sai a hankali"
"Haka ne,kada ki gaji,kinsan ita cuta farad daya take shiga sauqi kuma samuwarsa sai a hankali,Allah ya yaye ma dukkan musulmi baki daya"
"Amin abdur rahman,na gode" haka suka ci gaba da hira jifa jifa yana kwasarta da tsokana,har qofar gidan anty dije ya sauketa sanna ya mata kyautar dubu uku,da fari taqi karba sai da ya bata rai sannan ta amsa tayi godiya tare da bashi saaon gaisuwa gun qanwarsa bahijja da mamarsu.