Sashe 32
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsawon minti talatin ta dauka kan layin wayar suna qulla saqa a mugun zare,sosai taji dadi da shawarar data baga,shi yasa bata da kamarta,shawara ce mai sauqi wadda babu zuwa gun boka ko malami,hakanan babu barnar kudi,amma fa buqata zata biya,don dama babbar matsalarta yanzun duka jarinta ya karye warwas,saboda ribar da uwar kudin duka sun tafi gun 'yan tsubbu,bata kwana arba'in bata je an mata service ba,tun tana tsoron hadisin data taba tsintar wasu yaran 'yan makarantar islamiya na karantawa na cewa duk wanda yaje gun boka ko dan duba,to sallarsa ta kwana arba'in Allah bazai karbeta har tazo ta dake tama manta da hadisin baki daya bare ta tunoshi ya zame mata birki. (daya daga cikin abinda Allah ke jarabtar masu biye biyen malamai kenan,basu taba tara abun hannunsu,kullum suna kan hanyar rabawa matsubbata da 'yan duba,ko kishiya gareki mai irin wannan biye biyen ki lura da kyau,duk abinda miji zai baku sai ki nemi nata ki rasa,kullum cikin babu da bani bani take,ba zaki taba ganin burbushin abun ba ko a dakinta ko a jikinta ko a jikin yaranta,Allah ka kiyashemu ka tsare mana imaninmu).
Tana kammala wayar ta saki murmushi ita daya take magana da kanta
"Kissa ai tafi magani,ba shakka quruciyarki ta yimin rana,zan amfana da ita sosai" ta fada tana ficewa a dakin inda kai tsaye ta nufi dakin sumayya.
Tana kwance saman carfet din dakin nata tayi matashin kai da pillow,duk da ba yadda mukhtar baiyi ta dora kan nata saman cinyansa ba amma ta qiya,yana zaune dirshan gabanta da faranti a tsakiyarsu wanda ke dauke da kankana da tuffa da gwanda,ayaba yake bare mata yana miqa mata tana daga kashingide take amsa tana ci,dubansa take kawai cike da mamaki,yana son dawo mata mukhtar dinta,"Allah yasa ba yaudara bace,ya Allah kasa kada ya juyan baya"haka ta dinga fada cikin ranta tana binsa da kallo wanda shi sam bai ma kula ba,hannu ta sanya ta shafi cikinta wansa daga can qasa ta fara jin dan tudu kadan,lumshe idonta tayi tana jin qauna cakude da farinciki na ratsata,duk kwanan duniya takan shafa cikin sau babu adadi,wani lokaci takan tsaya gaban madubi ta dage rigarta tayita kallon fatar cikinta tana mamaki yau ita ke dauke da juna biyu,idanu ya zuba mata shima yana kallonta farinciki na bibiyar duk wara gaba ta jikinsa,a haka ta bude idanunta karaf cikin nashi,sai kunya taso kamata,murmushi yayi sannan yace
"Bakiyi laifi ba sumayya ki qaunaceshi yadda ya kamata,wallahi Allah a duniya ban taba jin son wani abu a rayuwata ba kamar yadda nakejin son cikin dake jikinki ba,zan iya rasa komai sabida shi,zan iya rabuwa da komai saboda shi,don Allah ki kularmin da kanki da abinda ke cikinki komai runtsi" ko bai fadi ba tasan zancan daga zuciyarsa kai tsaye yake fitowa,ita kanta bata san irin son da takewa cikin ba,kai ta sunkuyar tana murmushi tare da furta
"In sha Allah ya mukhtar".
Dukkan wannan maganganun cikin kunnen zainab suka yisu wadda ta sawo kai don shigowa dakin
" ka nunawa kucciya baka"ta fada sannan ta shigo dakin da sallama tana sake sai saita nutsuwarta,gaban sumayya ya fadi har sai data runtse ido cikin zuciyarta tana fadin
"Allahummakh finihim bima shi'ita(Allah ka isar min da su da abinda kaso)(addu'a ce mai kyau ga wanda yaji tsoron zaluncin wasu mutane)" murmushi taje jifarsu da shi wanda shi kansa mukhtar din sai da yayi mamaki
"Ashe kana gun uwar gidanmu my mukhtar" ta fada tana zama kusa da shi,amsa mata yayi sannan ta dora
"Gwara ai ka kular mana da ita sosai musamman da take dauke da cikar muradinmu,Allah mun gode maka daka nuna mana wannan lokaci" ta fada tana maida hankalinta ga sumayya,hannunta tasa ta riqe nata hannun,ji take kamar ta kama garwashin wuta amma sai ta dake
"Sannu sumayya ya jikin naki?" Da qyar ta bude labbanta tace
"Da sauqi"
"Allah ya inganta ya qara miki lafiya kinji,na godewa Allah da zaki samarwa mukhtar sanyin idaniya,naji dadi qwarai dama ke ya cancanta ki fara samun wannan matsayin,don Allah duk abinda kike da buqata ki sanarmin kada kice zaki yiwa kanki wani abu,kada ki duba duka wasu abubuwa da suka faru a baya,sharrin shaidan ne da kuma zuciya wadda bata da qashi,in sha Allah ba zasu sake faruwa ba,sai yanzu na fahimci kyakkyawar zuciya da kuma haqurin da kike da shi,don Allah mu hada kai mu zauna lafiya kinji?" Duk da bata gama gamsuwa ba amma taji dadin maganganun zainab din,ko babu komai wake son tashin hankali?,ai babu abinda yafi zaman lafiya dadi
"Ba komai maman nafi'u,Allah ya sake hada kanmu"
"Ba amin ba,don wallahi da kai na ya hadu da na kishiya gwara na qare rayuwata kan nawa na ciwo" ta fada a zuciyarta,amma afili sai ta saki murmushi tana fadin amin.
Sake matsowa tayi ta karbi bare ayabar daga hannun mukhtar din,ita ta dinga barewa sumayyan tana miqa mata,tanayi can qasan zuciyarta na mata suya,amma fuskarta kuwa murmushi da kulawa ne kwance a cikinsu.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
2⃣7⃣
______________________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*
*wa may yattaqil laha yaj'al lahu makhraja,wa yarzuquhu min haisu la yahtasib*
_duk wanda yaji tsoron Allah to Allah zai sanya masa mafita(cikin lamuransa),ya kuma azurtashi ta inda baya zato_
*ya Allah kai mana baiwa da jin tsoronka,ka azurta mu da dukkan kyakkyawa*
___________________________________
Tana bayansa har suka qarasa inda yaya yahanasu taje zaune tana kallon ikon Allah,a mutunce sumayyan tace
"Yaya ina kwana?"
"Lafiya" ta amsa babu yabo ba fallasa,tana son ganin kyawun kyautatawar data mata idan da hali ta mata godiya amma sai ta kasa,dama sumayyan ba domin ita tayi ba,tayi ne domin girman Allah da kuma girman da zumunci ke da shi a wajen ubangiji,hakanan ko ita ba zata so ace yau yaya abbakar ya auri wata da zata rabashi da su ba,ko ita ta haifa ya auri wadda zata rabasu din,kitchen ta wuce ta soma hadawa kanta dan abinda zata iya ci,ko kafin ta kammala ta fito ma falon babu kowa da alama ta tafi,sai ta zauna ta fara kurbar ruwan shayinta.
Kamar daga sama zainab din ta fito tana banbamin masifa kamar zata ci baki mukhtar na biye da ita yana son shan gabanta amma ya gaza cimmata,qerere tayi a kan sumayya wadda ko mutuncin kallonta bata samu ba
"Uban wa ya saki ki tabamin turaren wuta na?" Sosai abun ya bata mamaki,har tana iya bude baki tayi cigiyar kayan data tabbatar ba na Allah bane?,qare matsota tayi tana huci ta kuma maimaita tambayar tata,ganin zainab din na qoqarin kai hannunta jikinta ya sanya sumayyan dubanta
"Kada ki soma,don fankan fankan bata kilishi wallahi kika dakeni bazan dubi girmanki ba tsaf zan rama" idanu ta zaro tana nuna qirjinta
"Ni zaki daka don ubanki,to dokeni din"
"Wai meye haka ne zainab ba tun cikin daki nake miki magana ba?,ke sumayya tashi ki koma dakinki" wani kallo ta watsa masa sannan ta dakata da shan tea dinta
"Kayi haquri amma bata isa ba wlh don yanzu na fito ban kuma kammala uziri na ba,kana iya janye matarka idan na gama na tafi ita ta fito" ta fada tana ci gaba da kurbar shayinta duk da wata iriyar tafasa da zuciyarta ke mata,jinta take dai~dai sa su baki dayansu,banda daraja da girman sa da take gani babu abinda zai hana ta yayyaba masa baqaqen maganganu masu zafi
"Muje nace zan biyaki kudin ko?" Sai ta sauke ajiyar zuciya,dama abinda yafi damunta kenan,don sake samun wani maganin wannan da sauqi
"Allah ya ceceki" ta fada tana huci sannan ta juya tabi mukhtar din,cak shayin ya tsaya mata a wuya,ambaton sunan Allah ta dinga yi don ya kawo mata dauki,tabbas sai yau ta tabbatar mukhtar dinta ba cikin hayyacinsa yake ba,kayan karin da bata gama ci ba kenan.
**** **** *****
Wani nannauyan bacci ne ya dauketa tun bayan kammala sallar asuba,hakan ya sanya bata tashi ba sai wajen sha daya saura na rana saboda zafin rana da ya fara hudo labule.
Da wata mahaukaciyar yunwa ta farka,saboda haka bandaki kawai ta shiga ta wanko bakinta ta shiga kitchen don samarwa kanta abinda zata ci,don bata sa aka ba tasan ba samun abun kari zata yi ba,haka ne yake faruwa duk ranar girkin zainab din,shi kansa mai gidan wani lokaci sai dai ya fita haka.
Sam bata lura da meke faruwa ba sai data shiga cikin kitchen din sosai,nafi'u ne yaron zainab tsaye dare dare kan stool yana sauke dukkan farantanta na tangaran dake jere cikin glass drower dinta yana sakinsu qasa daya bayab daya suna tarwatsewa.
Da sauri ta qarasa ciki tana kiran sunansa cikin tsawa,ko gezau baiyi ba bare ya fasa aikata abinda yakeyi din,hannunshi ta riqe gam kana ta saukeshi daga kan stool din tana dubansa ransa a bace
"Baka da hankali?,ko bakasan me kake yi ba?,ko bakasan abin amfani kake lalatawa ba?",cikin rashin kunya yace mata
"na sani mana"abun sai ya bata haushi ta kama kunnansa ba tare da ta murde ba tace
" wato tsabar rashin ji ne kenan ko?"
"Sakarmin kunnena ai kema bake kika siya ba,kuma Allah ya isa na da tabamin kunne da kikayi" sosai yaron ya bata haushi da mamaki,ta sanya tafin hannunta ta buge masa baki,wata qara ya saki kamar wanda aka sanya wuqa aka yanke masa maqogaro yana fadin "wayyo bakina wayyo mama ta fasamin baki".
A hautsine ta fado kitchen din dama tasan hakan na iya faruwa,don ita ta sanyashi,saboda har yau bata huce takaicin asarara maganinta da sumayyan ta jawo mata ba,duk da mukhtar din sai da ya biya ninkin kudinsa,da sauri ta qarasa inda suke tsaye ta ture sumayya tana fadin
"me kika yi masa?,me tayi maka nafs(da yake haka take kiransa)"
"Bakina ta dakarmin mama duba ki gani"hannunsa ta sauke tana duba bakin,babu wani abu da yayi tunda duka duka dukan data masa ba wani mai zafi bane,waiwayawa tayi ta dubi sumayya dake tsaye rungume da hannu tana dubansu
" dukarmin yaro kikayi saboda bakisan ciwon haihuwa ba ko?,to wallahi sai na rama masa"sai kuwa tayo kan sumayyan gadan gadan.