Sashe 69
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun mafarkin da taji daren jiya jikinta a mace yake,tana farkawa ta kira mukhtar din ta tabbatar da lafiyarsa,har yana zolayarta kodai ta qagu ne kawai a kawota,shi bacci ma yakw ta tasheshi,dariya tayi cikin jin kunya sukayi sallama,har zuwa wayewar garin juma'ar jikinta a mace yake,tun safe take kwance ta kasa katabus,tana jiyo koke koken abdallah da yau ya tashi da rigima amma ta kasa cewa komao,har ya shigo dakin ya gama kukansa da kawo mata qarar walida 'yar anty salma ya gaji ya fice ba tare da tace masa komai ba.
Qarfe hudu na yammacin ranar tana tsaye tana shiryawa cikin dinkin atamfa riga da zani anty salma na tsaye kusa da ita tana bata turare wayarta ta dauki kuwwa,sunan mukhtar ne ya bayyana gabanta yayi mummunan faduwar har qafafuwanta taji sunyi sanyi,sai ta koma bakin gado ta zauna tana amsa wayar cikin fargaba
"Assalamu alaiki amarya ta" muryar mukhtar ta ratsa dodon kunannata,sai ta amsa masa tana lumshe idanuwanta,cikim salon soyayya suka gaisa sannan yace
"Ina fatan kin fara shirin tahowa gidanki" dariya ya bata ta murmusa
"Yanzun haka ma shirin nake angom doki"
"Eh naji na yarda ina abdallah"
"Yana waje,yau tun safe yake ji da rigima wallahi" nemo min shi mu gaisa"
"Bai kusa fa ya mukhtar" ta fada a shagwabe,tuburewa yayi tilas ta qwalawa zainab kira ta kawo shi ta hadasu da wayar taci gaba da shiryawa,sai da ta gama sannan ta karbi wayar
"Nima ina gun masu dinki zan karbi dinkuna na,SAI KIN TAHO?"
"To ya mukhtar,ka kularmin da kanka"
"To my sumy". Ajjiye wayar tayi tana sakim ajiyar zuciya.
Bayan sallar magariba 'yan rakiyar nata sukayi mata sallama kowa ya kama gabansa,ganin har isha'i tayi shiru sai ta daura alwala tayi sallar isha'inta,sam gidan ba,gabanta ke yawaita faduwa tana ambaton hasbunallahu wa ni'imal wakil,ga abdallah na tare da mukhtar tare zasu taho da shi,ganin shirun yayi yawa sai ta miqe ta kunna saudi qur'an Allah ya taimaketa ma akwai wutar nepa ta zauna tana ci gaba da saurara zuciyarta na mata wani iri babu dadi.
Firgigit ta dawo hayyacinta tana duba agogo,goma na dare ta dubi wayarta dake ta faman ruri,sunan malam ta gani kam screen dinta,sai taji gabanta yayi mummunan faduwa har sai da ta furta hasbunallahu wa ni'imal wakil a bayyane sannan ta kara wayar a kunnenta
"sumayya kina ina?" Abinda taji malam ya fadi kenan,sai tambayar ta bata mamaki
"Ina gida na malam"
"Yauwa to maza kashe wayarki ki fito qofar gida abubakar na jiranki,yace yana ta bugu bakiji ba"sai ta amsa da to kawai tare da bin umarnin malam din kawai tana jin wani yanayi nabin fata da tsokar jikinta,hijabin data idar da sallah ta zira ta fito kai tsaye qofar gidan ba tare data rufe gidan ba.
Ya abbakar ne tsaye jikin adaidaita sahu kansa a kife,qarar bude gidan ya janyo hankalin sa,sai ya kalleta
"ya baki kulle gidan ba,malam ke son ganinki"
"To" kawai ta kuma cewa ta koma ta jajjanyo qofofin,tana fitowa ta miqawa ya abubakar wayar tata don ji tayi ta fara yi mata nauyi a hannu,kallonta kawai yayi ya sanya hannu ya amshi wayar ya sanya a aljihunsa suka shiga adaidaita sahun ya jasu suka bar qofar gidan ba tare da kowa ya sake cewa komai ba.
Cikin harabar asibitin mai adaidata ya faka ya abbakar ya biyashi suka fito,binsa kawai take a baya ba tare da tasan inda take jefa qafarta ba,tarin tambayoyi ke yawo kan kwanyarta amma ta gaza furta koda guda?,shin waye a asibiti?,me ya faru ko meke faruwa?.gab da zasu haura saman asibitin ta iya tambayarsa
"Ya abbakar,wai me yake faruwa?,waye ba lafiya?"
"Babu komai muje kawai"
Tun daga farkon barandar ta fara cin karo da mutane,yaya yahanasu,malam,kawu mahaifin abdur rahman da hajiya mahaifiyarsa,jamila yarinyar yaya yahanasu,sai mamanta da wasu mutane uku da batasan su waye ba,tunda taga yaya yahanasu mukhtar ko abdallah ne suka fado ranta,jikinta ya fara rawa sai ta fara qoqarin faduwa sanda suka had ido da yaya yahanasu taga ta saki kuka,da sauri hajiyan abdur rahman ta qaraso ta tareta ta zaunar da ita kan kujera tana fadin
"Yi a hankali sumayya,babu komai in sha Allah Allah zai bashi lafiya,kiyi masa addu'a"
"Waye hajiya me ya sameshi" malam ne ya qaraso yayi mata bayani,hatsari mukhtar din ya samu yana hanyar tahowa gida shida abdallah gab da sallar magariba,yanzu haka mukhtar din na tare da likitoci amma sunce yanzu zasu fito da shi saidai ICU zasu kaishi,wani irin tauri taji zuciyarta tayi
"La haula wala quwwata illa billah" ta dinga maimaitawa,jin jikinta take kamar ba nata ba.
Bata ce komai ba har zuwa sanda aka bude qofar wani daki aka turo gadon,mukhtar ne kwance tamkar gawa,babu abinda ke aiki a jikinsa sai numfashinsa dake fusga duk bayan wasu daqiqu,kansa nannade da bandeji fari wanda jinin da ya ci gaba da ratsowa ke barazanar sauya masa kala,a haka ma sun gyarashi sun dan gogeshi,wani kalar tashin hankali ya ruftowa sumayya,sai ta miqe tsaye har suka wuce da shi intensive care unit din,kukan yaya yahansu na haduwa da nata tashin hankalin yana yamutsa qwaqwalwarta,qunshe bakinta tayi cikin hijabi ta saki wani irin kuka qasa qasa ta soma furtawa
"Ya ubangiji na,na roqeka kada ka sanya wannan ya zama cikin KUNDIN QADDARA ta,Allah na tuba,na tuba ubangiji na" abinda ta dinga maimaitawa kenan qasa qasa,hajiyan abdur rahman ita ta dinga lallashinta,saidai babu abinda ke qara mata sai tashin hankali ahaka sha biyu na dare ya cimmasu dai dai lokacin da likitocin suka fito,bayani suka yi masu kan dakin bai buqatar shigar mutane ciki,haka nan mutum daya suke da buqata wanda zai zauna da mara lafiya
"Don Allah don annabi malam ku qyaleni na kwana,wallahi bazan iya tafiya gida ba" sumayya ta fada tana fashewa da kuka,babu wanda tausayinta bai kama ba anan,ganin babu yadfa za'ayi a barta ita daya kawu da ya abbakar zasu kwana cikin asibitin,ita kuma ta kwana gun mukhtar din.
A hankali ta dinga takawa har gaban gadon da mukhtar din ke kwance,ko ina na'ura ce ke aiki a jikinsa,baki daya fuskarsa ta sauya kamar ba mukhtar ba,kallo daya zaka masa kasan lallai ya bugu sosai a kansa don tuni har ya kumbura kan nasa,kujera ta ajjiye bakin gadon tana qoqarin danne zuciyarta tare da tuna nasihar da malam yayi kata kafin su tafi
"Kuka baya maganin komai,addu'a ita ke magani" abinda ya gaya mata na qarshe kenan,kanta ta girgiza tana sake baiwa kanta qwarin gwiwa,sai ta kama tafin hannunsa ta sanya cikin nata,a hankali murya can qasa mai cike da rauni ta soma karanto ayoyin qur'ani wadanda su suka dinga debe mata kewa tsawon daren,saidai abinda ke daga mata hankali dai dai da second daya babu wani abu da taga ya motsa daga jikinsa,wanda likitocin sunce ta kula ko yaya taga ya motsa ta sanar musu,duk da lokaci bayan lokaci suna shigowa suna sake dubashi.
Sai da suka saitu sosai kan hanya sannan mama tace
"Ina abdallah" tofa,sai lokacin hankalin kowa ya dawo jikinsa,duk cikinsu babu mai amsar tambayar,don hatta jama'ar da suka ceci mukhtar dim babu wanda yace yaga yaro,take wani sabon tashin hankalin ya samesu,mama kam kasa daurewa tayi saboda tsananin tausayin sumayya sai kawai ta sanya kuka,kai tsaye malam ya nemi alfarmar mai abun hawar ya canja akalarsa zuwa policestation wanda tafi kusa da inda al'amarin ya faru don si shigar da report cike da matsanancin tashin hankali.
Kiran sallar asubar fari sanyi ya fara busowa,sam bata lura ba tana gyara zamanta,tana daga kai suka hada idanu,ya bude idanuwansa tar yana kallonta,wani farinciki ya dinga zagaya ta,ga mamakinta taji sai taji ya kita sunanta,cikin matsanancin farinciki ta amsa
"Qarfe nawa?"
"An kusa sallar asuba"
"Daura min alwala sumayya banyi sallar magariba da isha ba" girgiza kai tayi
"Ya mukhtar jikinka duka kayan aiki ne,ka bari likita yazo sai ayi maka" tubure mata yayi hakan ya sanya ta lallaba ta shashshafa masa ruwan iya inda zai yiwu,yana daga kwancen ya dinga halarto da sallar yana yi har ya kammala baki daya tana zaune tana kallonsa,yana sallamar qarshe kansa saitinta ne sai ya zuba mata idanu,murmushi tayi tace
"Sannu ya mukhtar" kai ya kada mata sannan yace
"Ina abdallah" abdallah,ta dinga nanatawa,idan kunnuwanta basuyi mata qarya ba ance tare suke da abdallah,to ina yake ina yayi?
"Ina fata lafiya yake babu abinda ya sameshi" tabbas lafiya yake idan da ba lafiya ba da sun gaya mata
"Lafiya yake ya mukhtar" ta fada cikin salon son kwantar da hankalinsa
"Alhamdulillah" taji ya fada sai ya maida kansa,cikin farinciki da tada sallah itama.
Shaquwa taji ya soma yi wadda kan ta idar da sallar ta qara yawa,tana sallamewa tayi kansa tana masa sannu,da hanzari ta dauko ruwan roba ta bude ta fara bashi a hankali,sosai ya sha ruwan kuwa sannan ta cire roban daga bakinsa ta qulle tana masa sannu,minti biyar tsakani shaquwar ta dawo,ta sake matsawa gunsa tana riqe da hannunsa tana masa sannu cikin tashin hankali ganin yadda qirjinsa ke dagawa wannan karon
"Bari na qara maka ruwan" ta fadi tana shirin juyawa inda gorar ruwan take,sai taji ya damqe hannunta,juyowa tayi tare da tsayawa cak kamar an kafeta,idanuwansa taga sun fara juyewa,jikinta ya hau rawa ta qanqame hannunsa tana fadi a fili
"La'ilaha ilallah,muhammadur rasulullah" abinda ta dinga maimaitawa kenan a fili babu qaqqautawa,a hankali taji ya kama yana maimaitawa,kusan minti biyu yana fada shima cikin fusgar numfashi sai taga idanunsa na lumshewa,riqon da ya yiwa hannunta tsaurinsa ya sassauta
(Abinda ake so ga kowanne majinyaci kenan,mutuwa na da sa gigita da daga hankali,amma gata ake so ka yiwa mamaci wanda shine qarshen qaunar da zaka nuna masa,a yayin daka fuskanci wasu alamu na fitar ruhi daga gangar jikin majinyaci,bakinka ya dinga ambaton la'ilaha ilallahu muhammadur rasulullah ko za'a dace mamaci ya kama,ba cewa ake fadi abinda na fada ba,ko kuma cene la'ilaha ilallah,a'a ka dinga fadi yadda kunnuwansa zasu iya ji,idan Allah ya qaddara bawansa ne na gari sai ya kama ya kuma cika da ita,Allah kasa mu cika da wannan kalma mu da daukacin musulmi baki daya,amin).
Hannunta ta zare qirjinta na fat fat fat,hawaye ne ke bin kuncinta,wasi wasi ya cika zuciyarta,fata take ba abinda take zato bane,wannan tunani ya sanyata fita da gudu tayi ofishin likitan.
*mrs muhammad ce*