← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 210

Sashe 42

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sosai maganar ta daki qirjinta,sai ta shiga kada kai kamar qadangaruwa,da qyar ta qwaci kalmar
" haba abdur rahman,ka rufamin asiri mana,ka manta kai waye ne?,kai dan kawun mukhtar ne fa,ko ka manta mukhtar kamar yaya yake a gare ka?,baya ga haka ma so kake duniya ta zage ni?,nifa bazawara ce har da yaro na,kai kuwa matashin saurayi ne da ko auren fari baka yi ba"murmusawa yayi yadda yaga tsantsar tashin hankaki kan fuskarta kamar wadda aka ce za'a yanka,sai maganarta ta biyu data bashi dariya,dududu ita din ma nawa take,'yammata da yawa wasu masu shekaru irin nata ma ba'a fara zancan aurensu ba,wasu kuwa sai a lokacin suka isa auren ma,shekara ashirin kacal da take da su din,idan ba ita ta fada ba babu mai yadda tayi auren fari ma bare haihuwa,kai ya kada da ya tuna ita din farin shiga ce,baki daya ta rude,dole ya bita a hankali har ta sake da shi
"Dukka wadan nan basu isa hujjoji a gareni ba sumayya,jeki gida ki nutsu kiyi shawara,na baki nan da sati guda,amma kada ki manta ni din ina sonki kuma in sha Allahu sai na aureki". Har wani tsoro ta dinga ji haka taja qafafunta da sukayi sanyi tamkar an buge mata su ta fita daga motar ta rufe masa ita,sai ta kasa motsi har yaja motar ya soma fita a layin tana jin motar da idanu.

Horn din da aka danne shi ya sanya ta dawowa daga karanta wasiqar jakin data tsaya yi a qofar gida,abdallah na kafadarta duk ya bata mayafinta da nashi bakin da burbushin biscuite amma sam bata ma ankara ba,idanunta ta juya zuwa gabanta,mukhtar ne zaune cikin motarsa yana dubanta,fuskarsa a hautsine kamar wanda aka kikkifawa mari,a hanzarce ya fito daga motar ya zagayo zuwa inda take yana fidda wani huci
" waye waccan?"ya tambaya yana mata nuni da motar abdur rahman dake gab da qulewa zuwa kan babban titi,sai tabi inda yake nunin da kallo kamar bata san motar da yake nunawa din ba,mamakin tambayarsa da dalilin fusatarsa ya taru ya sake daskarar sa qwaqwalwarta,cikin qarfin hali tace masa
"Gurina yazo,sai me?", mamaki ya kamashi,shi sumayyan ke gayawa haka,zuciya ta taso masa iya wuya,hannu yasa ya fincike abdallah daga hannunta har ya dan tsorata ya tabe baki zai sa kuka,sai ya rungumeshi a aqirjinsa,yayi luf kuwa abinsa don tuni ya jima da gane shi,akwai sabo da shaquwa sosai tsakaninsu,cikin tsantsar bacin rai yace da ita
" sai me kuwa?,ba damuwata bace,saidai ki sani bashi da alaqa ya yaro na,kiyita fitowa gunsa amma badai da yaro na ba"sai ya juya ya bude motarsa ya shige ya tada ta ya bar layin.

Kuka ta saki ta shige cikin gida da gudu wanda ya ja hankalin mama dake bakin qofar madafi zaune tana gyara kwanukan abincin daren malam,tsaye ta miqe tana tambayarta lafiya
"Mama ya karbe abdallah ya tafi da shi"
"Waye?,waye ya tafi da shi" ta tambaya cikin rudewa
"Mukhtar mana" ajiyar zuciya ta saki hankakinta na kwanciya,tayi zaton wani ne ma daban,harara ta balla mata
"Sai aka ce miki saceshi yayi?,ko ce miki akayi bazai dawo da shi ba?".kai ya gyada
" bazai dawo da shi ba mama"harararta ta sake yi
"Maras kunya,idan bai dawo da shi din ba sai me,ba ubanshi bane,ke yanzu akan dan farin kika tsaya kina min kuka?,matsa ki bani guri"janye jikinta tayi ta shige daki tana ci gaba da matsar qwalla,ta yadda lallai har yau akwai sauran quruciya akan sumayyan,ko tsabar tabara ce oho.

Har maman ta gama abinda take bata iya yin shiru ba,ji take kamar ta fita ta karbo yaronta,ganin bilhaqqi da gaske kukan take ya sanya maman binta daki ta kwantar mata da hankali,ita dai jin maman take kawai,gani take bazai dawo mata sa shi ba,da qyar ta fita ta dauro alwalar sallar magariba ta dawo ta tada sallar tana kasa kunnen ta inda abdallanta zai bullo,abun sai ya hadu ya dagule mata,ga zancan abdur rahman ga kewar yaronta.

_tofa masu karatu,nasan yanzu zamu fara raba team,ga team ABDUR RAHMAN,ga MUKHTAR ga kuma wata sabuwa LUKMAN_

*MRS MUHAMMAD CE*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣8⃣

____________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*wala taqulanna li shai'in inni faa'ilun zalika gada,illa ay yasha Allah,wazkur rabbaka iza nasit*

_kada kace ni zan aikata wani abu gobe,face sai ubangijinka yaso,ka tuna ubangijinka idan ka manta_

______________________________

Wani abu ne ya tokare masa wuya yana jin wani irin bacin rai na taso masa,sai yayi qoqarin dannewa ta hanyar daukar abdallah da ya nufo gunsa kai tsaye yana fadin daddy daddy,motsawa sumayya tayi don shigewa cikin gidan cikin hanzari ya sha gabanta
"Me abdur rahman ke zuwa yi gunki?" Idanunta ta dora a kansa kanta tsaye tace
"Alheri"
"Alheri wanne iri?,kada kice min gonata yake son shigowa?"wani irin kallo ta masa
"Yaushe ka fara noma?,dama kana da gona ne?,alheri kuma duka alheri ne babu wani banbanci" ta fada tana rabeshi zata wuceshi ranta a bace,baisan ya riqo gefen hijabinta ba hakan ya sanyata waiwayowa tana dubansa a mamakance
"Me yasa kike cutar da ni haka sumayya me na miki a rayuwa da zafi?" Ya fada zuciyarsa na zafi yayin rauni ya bayyana qarara a fuskarsa
"Cutarwa?,ni nake cutar da kai ma mukhtar!" Ta fada tana nuna qirjinta da yatsa cikin mamaki,sai ta juyo baki daya tana dubansa sosai
"Bance ka cutar da ni ba mukhtar ni da ka saka saki uku ina kwance?,bance ka cutar da ni ba ni da ka yanke min hukunci kan zato da zargi,ka yanken hukunci ba tare da kayi bincike ba?...."
"Wanne bincike sumayya bayan ba labari aka bani ba,na gani da ido na,sannan bincike na likita ya sake tabbatar min da kinsha din wanne bincike kike da buqata nayi bayan wannan" a kaikaice takw dubansa sannan tace
"Ok ko?,to shikenan,yayi kyau hakan ai,amma shawara zan baka ka fita daga dukkan harkoki na,ko da maza dari zaka ganni da su wannan ba damuwarka bane,tunda dai a yanzu ba qarqashin ikonka nake ba,gashin kaina nake ci sai ka shafamin lafiya" tana gama maganar ta juya tayi shigewarta cikin gida ta barshi da abdallah.

Binta yayi da kallo,taushe sunayya ta koma haka,yaushe bakinta ya bude da magana haka?,saidai batayi laifi ba yana ganin baiken kansa,tabbas ba shakka gaskiya ta fadi yanzun ita din ba huruminsa bace,baisan me ya sanya ya shishshigewa lamarin rayuwarta har haka ba,jiki ba qwari ya koma mota ya dauko siyayyar abdallah ya riqoshi har bakin qofar da zata sadaka da tsakar gidan ya ajjiyeshi ya wuce,cikin mota yana tuqi yana tunanin yadda zai raba kansa da shiga lamuranta,don bisa gaskiyarta take,wani sarawa kansa yayi wanda hakan ya sanyashi yin parking motaraa gefan titi ba shiri,ya dauki a qalla sama da mintuna talatin kafin yaci gaba da tafiya.

***** ***** *****

Duk yadda taso abdur rahman ya fahimci abinda take nufi yaqi fahimta,sai ta tattarashi ta janye masa jiki,sau tari takan qi dawowa daga makaranta akan kari,tana kuma dawowar lokacin sallar magariba ne,daga nan kuma suna zama karatu da malam wanda ya sanya musu wasu litattafan addini wanda suke hadda ce wasu abubuwa a ciki,sam ta daina bada wani gaf ko wata dama da zasu kadaice har suyi magana,idan ana tare cikin jama'a zasu yi magana da shi kamar kowa.

Ta bangare daya kuwa luqman shima ya matsa lamba,tilas ta bashi dama yazo gidan sau daya,a ranar malam ya dawo ya ganshi suka gaisa,saidai malam din baice mata komai ba kamar yadda ta zata,hakanne ya sanya ta saki jiki har ta sake bashi wasu damammakin yazo wai koda hakan zai sanya abdur rahman ya janye daga qudirinsa,saidai duk da hakan babu abinda ya girgiza shi,har mamaki abun ke bata,cikin lokaci qarami ya sanyata ta saki jikinta da shi,mutum ne mai barkwanci da yawan bada labarai,ko bata son magana sai ya sanyata dariya.
Chapter 42 · 0% Book details