← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 210

Sashe 139

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

        Duk da yadda ta gaji bata kwanta ba sai data gama shirya dukkanin kayanta,haka kawai ta tsinci kanta da sauya yanayin kayanta baki daya,hijabi biyu kawai ta dauka madaidaita saboda sallah,ita kanta batasan manufar yin hakan ba batasan me yasa tayi haka ba,wanka tayi bata huta ba ta shiga kitchen,tana son gabatar da duk abinda ummen ta sanar mata,tukunya ta dora bayan ta zuba ruwa,ta duba inda suke ajiyar kayan hade haden shayin su tayi wani hadi na musamman wanda ya bada qamshin shayin wata qasa,cikin qanqanin lokaci ta juye cikin cup mai plate ta sake dorawa kan wani plate din tayi shahada ta haura sama,motsin ruwa data ji a toilet ya sanyata ajjiyewa ta sauka qasa bayan taja qofar tana fatan ya sha kada ya barshi kamar yadda yake barin sauran kayan abincin,tunda ya fito a bandakin ya dinga neman inda yake jin wannan qamshin shayin,qamshin da ya san a dubai kadai yake samunshi,sai da ya gama komai na kwanciya sannan ya qarasa gadon,a lokacin ya lura da shi sanda yake qoqarin kashe fitilar gefan gado,a hankali ya sanya hannunshi ya dauka,kamar wanda ke tsoron kurba haka yakai bakinsa ya kurba,idonsanya lumshe na tsawon mintuna dadin shayin na ratsashi,sai ya jishi ya koma qasar dubai,kadan kadan sai gashi ya tashi da cup din,saidai bai gamsar da shi ba,hakan ya sanya ya soma qoqarin sauka daga gadon don ya samo qari.

       Da dan sassarfa ya sauko qasan ya nufi kitchen kai tsaye,babu komai cikin tukunyar da alama kai da kai aka dafa,sai ya bude locker bayan ya kunna gas ya maida tukunyar cike da karambani don bai taba yi ba,canke canken ganyayyakin ya dinga yi,haka ya hadasu ya zuba suka tafasa ya juye,kurba daya yayi fatali da cup din ya furzar da na bakinsa yana yamutsa fuska,tilas ya wanke bakinshi ya fice daga kitchen din ya koma saman,zuciyarsa na son yasha amma baijin zai iya sanyata ta sake mishi.

To masu karatu,ga Almustapha ga sumayya zuwa wata qasa,koya zaman zai kasance.

*SADAUKARWAR WANNAN SHAFIN GA ZAMA NA AMANA GROUP DAKE FACEBOOK,ina godiya da fatan alkhairi ga dukkan wani member dake group din,haqiqa comment dinku na qayatar da ni,Allah ya qara zumunci,LOVE YOU ALL*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[2/8, 8:41 PM] Zainabu Abu💃🏽💃🏽: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣0⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

Wannan page sadaukarwa ne ga

HUGUMA CONVERSATION GROUP

HUGUMA NOVELS GROUP

ZAUREN BIEBIE ISAH ZBI

MAMAN HANEEF NOVELS

MAMAN AYSHA NOVELS

INSPIRING STORIES

HASKE WRITERS FANS GROUP

KUNDIN HASKE GROUP

KUNDIN QADDARA NOVEL GROUP

DA KUMA IYAYEN GAYYAR

HASKE WRITERS ASSO

DA KUMA

FOLLOWERS DINA NA WATTPAD MUSAMMAN MASU KANKARO MUTUNCI(LOL) DA COMMENTS DINSU

ALLAH YA QARA ZUMUNCI,INA GANIN COMMENTS INA GODIYA,SOMETIMES ZAKUGA NA AMSA WASU WASU BAN AMSA BA SABODA YAWAN MUTANEN,SAIDAI GASKIYA ALQALAMINA BAI IYA TSALLAKE KYAWAWAN ADDU'O'INKU NA FATAN GAMAWA DA DUNIYA LAFIYA DA KUMA SAMUN ZURI'A DAYYIBA,INA GODIYA.

___________________________________

Sha daya ne na safe,tana zaune cikin girmamawa a gaban baabaa,sanye da daya daga cikin baqar abaya wadda aka yiwa adon fari,tun daga zare kama duwatsu,tayi rolling da mayafinta wanda ya fidda shape din fuskarta da sirrin kyawunta,hill shoes ta sanya fari qal da 'yar madaidaiciyar jaka wadda mariqinta bai wuce ka saqala shi a gwiwar hannu ba,tsintsiyar hannunta daure take da farin agogo na fata mai baqar fuska,qamshi jikinta ke fiddawa mai sanya nutsuwa da kwantar da hankali,gama shirinta na tafiya kenan tayi burki a bangaren baban,nasiha baban yake mata mai ratsa jiki,wadda tabi kowacce gaba ta jikinta,yana sake tunasar da ita haqqin daya rataya a wuyanta,cike da gamsuwa cikin sanyin jiki ta soma yi masa godiya,a daidai sanda uban tafiyar ya shigo,cikin shigarsa tako yaushe ta suite,baiyi tsammanin zai tadda ta a nan ba,sallama yayi dai dai lokacin da baban yake cewa
"Goge hawayen,duka abun bana kuka bane ai" ta gefan idanu ya kalleta,karon farko da irin wannan shigar ta soma burgeshi,kwata kwata ba shigar su'ad bace wannan,bai taba ganinta sanye da abaya ire iren wadan nan ba,a hankali ya kau da kanshi yana maidawa kan baban,ya isa gabanshi nesa da ita ya duqa yana masa sallama,sanda ta yunqura zata tashi don basu wuri baban ya dakatar da ita
"Almustapha ga amanar sumayya nan na danqa maka,kada ka cutar da ita don kana ganin kunyi nesa da gida,kasan muhimmanci amana,ko ban gaya maka ba aure amana ce ta mace da ake danqawa namiji,wanda duk kuma yaci amana Allah bazai qyaleshi ba,na tabbata diyata bata da matsala,idan naga wata matsala to daga kaine,ka kuma kuka da kanka don bazan taba daga maka qafa ko baka uziri ba,ki kiyaye" kowa amana dai amana duk saboda ita?,abinda ummee ta gama gaya masa kenan yanzun daya fito,tana jaddada masa cewa ko rama taga tayi to shi zata tuhuma
"Insha Allahu zan kiyaye,Allah ya qara girma,ya qara lafiya da nisan kwana"
"Ameen summa ameen,Allah yayi muku albarka"inji baban,sannan yaja musu addu'a suka shafa.

Su biyu ne zaune bayan motan sai driver a maxauninshi,hawaye ya ziraro mata sanda suke gifta gidan anty dije,ta tuno sallamarsu ta jiya,ita kanta antyn wannan karan ta kasa daurewa sai da tayi qwalla,gefe tayi da kanta tana damqe littafin da antyn ta bata wanda har yanzu bata kai ga budewa ba
"kowa amana yake bani,ni me yasa ba'a bada tawa amanar ba?"kunnuwanta suka jiyo mata shi yana fada cikin mafi soyuwar sauti a wajenta,kamar zata juya kuma sai ta fasa,taci gaba da barin kanta a inda yake,ya motsa bakinshi kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya ciro wayarsa dake ruri,yanayin yadda taji yayi sallamar kawai tasan hamza ne,bisa dukkan alamu shima bai wuce wannan satin zaya koma,wayar bata qare ba har suka isa airphort din wanda hakan ya sanya bai samu damar qarashe maganar da zaiyi ba.

A baya take biye da shi cikin nutsuwa,yau airphort din ba laifi akwai yawaitar jama'a,hakan bai rasa nasaba qila da yawan matafiya masu sauka da masu tashi a safiyar yau din,sai taga ya fara rage saurinsa har ta cimmasa,da idanu yayi mata nuni kan tayi gaba,wucewar tayi kamar yadda ya umarcetan suka ci gaba da tafiya a hakan,idanunshi ne biye da ita duk inda ta taka qafarta tamkar mai qididdige adadin takun nata,a jikinta takejin akwai idanuwa a kanta baya ga idanun jama'ar dake kai kawo wajen,hakan shi ya sanyata ta fara jin rudewa,tun baya can mutum ce da aka raineta cikin tsaftataccen yanayin da bata iya cudanya da ajnabiyyanta ba,bata sakewa da kowa a lokacin idan ba malam ko yaya abubakar ba,koda wani taro ne na dangin mama matuqar ya hada da maza kamar daurin aure da sauransu bata sakewa,hakan na daya daga cikin dalilan da suka ja ko bikin amira da qyar ra iya sakewa(gareku iyaye mata,wannan dabi'a ce mai kyau,ana son a dasawa diya mace dabi'a ta rashin yarda da sakewa,dari dari da takatsantsan da duk wani jinsin d'aa namiji,wannan dabi'ar na taimakawa qwarai da gaske wajen dakusar da sharrin mai sharri cikin jinsin maza,misali masu baata yara da sauransu,ko da yayye gareta ko qanne maza ki nuna mata yadda zata dinga kamewa a cikinsu,to balle wani d'aa namijin a wajen,idan yayanta ne namiji ki nuna mata girmama shi zata dinga yi,bawai su dinga wasu wasa don tana qanwarshi ba,ko zama a jikinsa kada ki yarda ta yawaita yi don yana wanta,wannan dalili ne yasa ma'aiki yace mu rabawa yaranmu maza da mata wajen kwanciya da zarar sun fara wayo,idan qannenta ne kuma ki koya mata kama girmanta,bata shiga suyita wasu wasanni ba,koya mata sanya hijabi kallabi,saka sutura mai rufe jiki,kada kiyi tunanin ai yarinya ce babu komai,a'ah,ita rai dabi'antar da ita ake akan abu,ta yadda komai tsahon zamani zata dawwama a kan wannan dabi'ar).
Chapter 139 · 0% Book details