← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 210

Sashe 174

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

         Tsahon awa guda yana tsaka da aikinsa yaga miqewarta zumbur kamar wadda aka tsirawa allura,a gigice take neman hanyan toilet saidai ta rasa,kafin ta sake wani yunquri aman da take dannewa ya kubce mata,cikin wani irin zafin nama ya tareta sanda ta soma yunquri mai qarfi wanda yaso zubar da ita a wajen,yana riqe da ita har ta kammala aman baki daya,duk wani anu data ci daga safiyar yau zuwa dazun yafita baki daya daga cikinta
"Kai na" ta fada tana dafe da goshinta saboda yadda yake sara mata kamar zai rabe biyu,sai da ya bata ruwa ta kuskure bakinta sannan ya riqeta har zuwa bedroom din ya zaunar da ita gefan gado,bata iya zaunawa ba sai ta sulale ta kwanta,wayarshi ya ciro ya sanarwa ma'aikatan su shigo su gyara wajen ya ajjiyeta cike da damuwa ya tako inda take,gabanta ya durqusa ya riqe hannunta cikin nashi
"Me ya sameki haka?,daman baki da lafiya amma baki gayan ba?" Kai ta girgiza
"Meke miki ciwo?"
"Kaina.....da......" Sau ta kasa qarasawa duk da yadda mararta ke mutstsukarta
"Uhmmm,dame?" Ya fada yana miqewa ya dawo kusa da ita
"Marata.....Cikina" a hankali ya sakera ya miqe,kai tsaye dakin da ya ware cikin gidan tamkar qaramin asibiti na gidan ya nufa,ya duba magungunan ciwon ciki da na ciwon kai ya kawo mata,sai da ya tabbatar ta sha sannan ya umarceta ta kwanta,yana zaune gefanta hannunshi saman goshinta,addu'a yake tofa mata lokaci bayan lokaci haf wani bacci yazo ya fauceta.

         Tun yana duba agogo har ya haqura ya daina,yana ganin tilas su kwana cikin gidan don bazai iya tashin ta ba,da qyar ta tashi tayi la'asar da magariba ta koma ta sake kwanciya,wayarsa ya ciro ya lalubi lambobin su'ad,ringig biyu ta daga
"Ina ka tafi almustapha,wai me yasa baka ganin qimata ne?,bani da lafiya amma ka dauki matarka ku bar gidan tun safe har dare baka damu da halin da nake ciki ba?" Ta fada tana niyyar sakin kuka
"Yanzun ma ba yau zan dawo ba,ina tunanin sai gobe,kada ki damu din baki ga shigowata ba ki rufe sashen kiyi kwanciyarki" bau tsaya jin me zata fada ba ya katse,don ya tabbata bacin rai kawai kunnuwansa zasu jiye masa,kiran hamza ne ya shigo ta daya wayar tashi ya daga yana karawa a kunnensa
"Ya zamuyi haka dakai fisabilillahi ka ajjiyemu muna jiranka?" Banza yayi dashi kamar ba da shi yake magana ba,sai da ya mula don kansa yace
"Kada ka saka min ciwon kai malam,matar gidan tace bata buqatar naje wani guri so kowa ma dole ya haqura da ganina"
"Wace?,wai su'ad?" Ya tambaha cikin tantama,don dai itakam yasan haka bata taba faruwa ba,kuma bata isa hana almustapha ficewa ba duk sanda yaso
"Shafa kaji" ya amsa masa cikin gatse,tuni hamza ya hasaso wace ce,dadi ya lullubeshi ya dinga tuntsira dariya,amma don tsiya sai yace
"Wooo mutumina,yaushe mata suka fara juya akalarka?"
"Kasan dai halina ko hamza,zan iya biyoka har gida wallahi naci maka dama ba yau muka soma ba" bai damu ba yaci gaba da kwasarsa har sai da ya katse wayar,texs ya dinga jero masa kan ya daga suyi maganar ya daina tsokanar,da qyar yaciyo kansa ya daga suka shiga maganar da zasuyin,tuni su hamzan sunje sunga guraren sunyi,zasuyi kyau da noman audug,an gama shurya komai ma kawai ma'aikata za'a samu shikenan a shiga aiki.

        A hankali ta motsa tana bude idanunta,baki daya a yanzu wasai take ji bata jin komai,idanunsa a kanta yayi mata sannu,shi ya taimaka mata ta miqe duk sa bata jin komai
"Kiyi wanka sannan kici abinci,me zaki ci?"dan shiru tayi sannan a hankali kamar mai tsoron fada tace
"nama"
"Irin na dazu?"kai ta gyada masa,miqewa yayi ya fice falo din bada oder ita kuma ta shige bandaki,a gaba ya sanyata bayan ta fito wanka ta shirya cikin kayan bacci,tana cin naman yana kallonta suna zaune a dandagaryar,dukkan alamu sun nuna tana jin dadinshi sosai,sai data kammala tace
" ba gida zamu wuce ba?"kai ta kada
"Noo,a nan zamu kwana,baki jin dadi sosai har yanzu ko baki fada ba na sani" kai ta mirgina,don bata son su kwana din hakan ya dasa wani abu a zuciyar su'ad
"Am feeling better,zamu iya tafiya"
"Am not feeling better ni kuma...." Ya fada yana jifanta da wani kallo hannunsa nade a qirji,hannunshi ya miqa ya jawota,ya ware qafafunshi ya sanyata a tsakiya habarshi saman kafadarta saitin kunnenta,cikin yin qasa da murya yace
"Tunda muka zo gidan nan babu abinda kika bani ko qwaqwqwaran kiss ban samu ba,sai amai sai bacci.....you know gidan nan na love ne,shi yasa na kawoki.....me zan samu ne?" Kunyarshi ta kamata,ta sake kafewa a qirjinsa kanta na qasa
"Wai ma na tambayeki......meke damunki?"
"Dazu ciwon kai ne,amma yanzun ba komai"
"Haka akeso......zan samu wani abun to?" Ya fada yana juyo da ita suna fuskantar juna,idanunta ta saka a nashi,sai ya kashe mata ido yana sake tausa murya
"Pleeeeaaaase......ko kadan ne" a kunyace ta daga masa kai,ya miqe da hanzari yana dariya tare da dagata suka wuce babbar headquater.

*****   ******   *****    ******

      A safiyar ranar yana tsaye yana shiryawa gaban mirrow,yayin da itama taje tsaye gabanshi suna fuskantar juna,sanye take da da wata gown mai dogon hannu,wadda tsahonta bai qarasa idon sahu ba,mai roba ce rigar saboda haka tayi cif a jikinta tare da fitar da duk wani tudu na jikinta,baqa ce sai touches na fari,ta yane kanta da wani farin dan kwali mai tsaho don bai kai mizanin mayafi ba,sabuwa ce batasan da itaba cikin gidan da safen ya dauko ya bareta ya bata yace ta sanya tunda basu zo da shirin kwana ba,hannunta dauke da suit dinshi mai three pieces,neck tie,vest da safarshi,tana miqa masa da dai dai yana amsa yana sanya kowanne a muhallinsa a jikinsa,kusan hakan ta sabar masa,ita ke kiqa masa komai shi kuma yana shiryawa,babu magana tsakaninsu saidai salon kallon da kowanne kewa dan uwansa yana sadar da saqo kai tsaye zuwa gareshi ba tare da ya magantu ba,wani yare suka dinga amfani da shi a tsakaninsu dake wanzuwa tsakanin zuciya da zuciya,lokaci lokaci zaga daya daga cikinsu ya saki murmushi,a haka har ya kammala komai tsaf,yayi kyau cikin black nd white suit,ya kammala sanya safanshi ya dago,sai ya janyota jikinsa cikin ba zata,ta baya ya rungumeta ya dora hannayenshi a qugunta,sam taga ma kaman bai da niyyan maidata gida a yau din,a hankali ya ware tafin hannunshi ya soma shafo har saman damammen cikinta,sau da yawa yana mamakin yadda wai a haka har ta haihu amma har yau cikinta a dame yake,darensu na jiya kawai yake tunowa,irin jarumtar data nuna,shi kansa sai da yaji cewa kada ya cutar da ita fa
"Yau zamu wuce gida ko?" Kai ya girgiza
"Ba yau ba,saikin warke" narkewa tayi tare da rage fara'ar fuskarta duk da bai iya gajin fuskar baki daya sai gefanta
"Amman anty su'ad fa yau girkinta ne"
"I know babe,think dai sai magariba sannan aka shiga time dinta ko?,so sai na dawo tukunna,zan fita just one hour zan dawo,ya kamata na dinga hutawa hakanan" shiru ta danyi na wani lokaci
"kin gaji da ni kenan ko?gwara mu koma gida?"baki ta bude tare da waiwayowa tana dubanshi,kai ta girgiza alaman a'ah,sai ya saki qaramin murmushi wanda ya sanyata sake juya masa baya itama tana dariya qasa qasa,mamaki wani lokaci yake bata,wai wannan almustaphan ne ya koma haka?
"Me ya saki ciwon mara ne jiya?ina fatan ba irin na wancan karon bane"ya sauya akalar maganar
"Nima ban sani ba" ta fada a shagwabe,sai ya sanya hannunshi saman mararta ya danna
"Wash" ta fada saboda dan zafin da ta ji,cikin hanzari ya juyo da ita suna fuskantar juna,idanunsa cikin nata a rikice yace
"Yaushe rabonki da al'ada?" Idanunta ta juya alamun tunani,idan zata iya tunawa tun sanda ya daukota ya taho da ita daga kano ba tare data shirya ba,idanu ya zuba mata yana ci gaba da kallonta,sai kuma ya kama tafin hannunta yana kalla kamar mai neman wani abu,wani irin riqo yayi mata
"Please when last kika ga period dinki....tell me" sai ta tsorata ta fara zaro idanu ganin yadda ya rude lokaci daya,cikin rawar murya tace
"Tun.....tun sanda muka taho daga kano....sanda nayi ciwon mara" riqeta yayi ya ajjiyeta bakin gado,binsa tayi da kallo sanda ya juya ya fice,dakin nan mai kama da qaramin clinic ya shiga,ya dauko syringe ya dawo ya sameta zaune,yana daga tsaye ya farke,idanu ta fiddo,idan akwai abinda ta tsana a duniya allura ce,rabinta da ita kuwa tun haihuwar abdallah,qarasowa gabanta yayi ua duqa,ya riqe hannunta ya janye hannun rigan yana duban cikin idanunta,tayi wani kicin kicin,qwalla kwance can qasan idanunta,ya gama fuskanta sarai tsoron allura take,sai ya basar ya daura farar robar da zata bashi daman ganin jijiya,ta runtse ido sanda allurar ta ratsata,ya zuqi iya jinin da yake so sannan ya warware mata robar ya zare syringe din ya miqe
"Ina zuwa" ya fada yana nannade syringe din da tushu ya fice da sassarfa,binsa tayi da kallo sai da ya fice sannan ta janye idanunta,da baya ta koma ta kwanta cikin ranta tana tunanin me zaiyi da jininta kuma?,sai tsoro ya dinga shigarta,kada dai ace wata cutar ya gano a jikinta,gabanta ya fadi,sai ta gaza kwanciyar ta zauna daram samam gadon tana ambatar sunan Allah
"Ya ilahi,kada dai a ce har yau ban gama bitar SHAFUKAN KUNDIN QADDARA TA BA" ta ambata a ranta hawaye na qwace mata tsoro na dabaibayeta,yanzu ina zata saka ranta ina ta nufa idan wani abu ya hango tattare da ita?,ta ina zata soma rayuwa bayan tuni ya riga data haqiqance wani qaqqarfan abu wanda idan har akwai abinda yafi so qarfi to ba shakka ya kama zuciyarta dangane da shi,ya riga da ya dasa shaquwa qauna shauqi da bege mai zurfi fadi da girma cikim qirjinta,tsoka da jininta
"Ya rabbi ka kula da ni" ta fada wata qwallar na bin wata.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukakin sarkin yana cewa*

*CENE DA SU HARAM DA HALAL BAZAI DAIDAI BA,KODA KUWA YAWAN HARAM DIN NAN YA QAYATAR DA KAI(KO YA BAKA MAMAKI),KUJI TSORON ALLAH YA MA'ABOTA HANKULA DON KU RABAUTA*
_______________________________________
Chapter 174 · 0% Book details