← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 210

Sashe 201

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Daga daya bangaren kuma tuni ummi ta gama duk wani shirinta na zuwan yaran da mamarsu,kwana biyu taji shiru hakan ne yasa ta tuntubeshi,sai yace 'yar matsala ce aka samu wajen siyan ticket,tuni ta baroshi,wanne matsala ce za'a samu wajen siyan ticket kawai?,shi kansa yasan qaryar bata hadu ba saboda ba sabonshi bace,ko kadan ne kawai baya son su tafi su barshi,baya jin zaman garin zai yiwu gareshi idan suka tafi din,shi a son ranshi duk maison zuwa cikin gidan nasu zai siya masa ticket,wanda bai da visa zai masa suzo suga yaran,sam bazaiyiwu ba ummi ta gaya masa,su a wajensu tamkar haihuwar fari ne,saboda haka dole ya kawo 'yar mutane a kula da ita sosai,sannan itama tana da yan uwa tana son zama cikinsu ai,shikam baiga wacce kulawa akeson bata ba bayan wanda take samu nan daga wajensa,yana kallonta take saka towel cikin tafasasheshen ruwa ta gasa kanta sosai,ta fito taci abinciccika masu gina jiki,ga magungunan da yasa zasuyi mata matuqar amfani a jiki da take sha,hakan ya sanya hatta da ruwan nono ta samu wadatacce,kana kallonsu zaka san kulawa kam sun sameta,daga ita har yaran kai kace sunfi kwanaki hudu da haihuwar,warshe dai haquri ya baiwa ummi yace suna tahowa.

       Sai ana ya gobe zasu cika kwanaki bakwai sannan ya siya musu ticket har da shi da su'ad zasu tafi,dakin su'ad ya fara zuwa,ya taddata zaune tana latse latsen waya,sam sumayya bata gaya mishi bata taba zuwa taga yaran ba,shima kuma bai taba kawo ba zata shiga din ba,gefanta ya samu ya zauna yana fuskantar fuskarshi a sake sosai,kai ta daga ta dubeshi,as usal bata iya sannu da zuwa ba ko gaisuwa
"Baki gajiya da danna waya?" Ya tambaya yana daukar remote ya rage saitin kidan dake tashi a tv
"Idan ban danna ba me kake so nayi?" Ta tambayeshi cikin yanayin bacin rai,idanu ya zuba mata yana karantar yanayinta,sai kuma ya hadiye ya dauke kanshi daga fuskarta yaba bata amsa
"Karatun qur'ani,istigfari da sauransu"
"K'nnnnn" ta ce a taqaice,tun daga ranar zuciyarta da shaidan suke gaya mata ta gama burge almustapha fa,yanzu ba sonta yake ba ba kuma qaunarta yake ba,yaranshi da uwarsu su kadai yake so da qauna,bayan babu wani abu da yayi mata wanda ke nuna haman,illa ma lallashinta da yake saboda yana tunanin rashin samun nata yaran na kanta ke damunta
"Gobe zamu shiga nigeria,su ummi sun matsa sai mun dawo a yi suna a can kowa yaga yara"qafafunta ta miqe ranta na baci
"wannan ku ta shafa sai kun dawo" idanunsa ya qanqance yana dubanta,wati mai hali bai fasa halinsa,duk yadda yake tattali da rarrashinta wato shi din banza ne baisan ciwon kanshi ba?
"Kamar yaya fa?" Ta tambayeta yana son qarin bayani
"Ai suma su ummin tsabar gulma ce,babu gidan uban da zani,wato nake inje aji dadin nuna ni gani ban haihu ba wata tazo bayan bayana ta haihu ko?,to bazanje ba,dama an dade ana ruwa qasa na tsotsewa,muna fukin auren ma duk ha sune sila ba sabida kai an tsaneka ba'a sonka" cikin tsananin bacin rai ya daka mata tsawa,nunata yake da yatsa cikin bacin rai
"Hey idiot.....Kar ki soma kuskuren fadin maganar banza kan mahaifana,ki kintsa bakinki kada furucinka ya jawo miki nadama......iyayena sun fiye komai da komai da na mallaka nake da shi,su din wasu abubuwane masu daraja da babu kamarsu,kudi ko qarfin iko basu isa su baka su ba.....ban gaya miki zamu nijeria ba wai don ina neman shawararki ba,umarni nake baki kaman yadda wadanda suka isa da ni suka bani umarni nabi,kema dole kibi umarni na don na isa da ke" ya miqe yana niyyar ficewa ranshi a bace
"To wallahi ba inda zani daga nan nima gidanmu zan wuce ai ina da gidan uba...." Waiwayowa yayi yana mata wani kallo daya sanyata rusuna ba tare data shirya ba
"Really?,....ok,indai haka ne idan kinje kada ki sake ki dawomin gida kinji ko?,ruwanki kije nigeria ruwanki kije ameria amma ki zauna acan,kada qafarki ta dawo gidan muhammad almustapha" yana kaiwa nan ya wuce yana mai buga qofar cikin fushi,kanta ta dafe,tabbas bata da wata mafita,zai iya aikata dukkan abinda yace din,saidai ta gama rayawa ranta abinda zatayi,zuwa gida babu fashi.

          Da sallama bakinsa ya shiga dakin sanda take gaban sif tana fidda kayansu tana shiryawa cikin akwati,yaran na kwance cikin gadonsu suna bacci hankalinsu kwance,cukin tsafta da qamshi,a qunshe suke cikin kayan baby masu taushi pink,yanayin muryarshi kawai taji ta saki abinda take ta waiwayo tana dubanshi,duk sanda taji muryarshi haka tasan ranshi a bace yake koda yayi yu qurin boye mata,bai dubeta ba har ya isa gaban gadon yaran ya bude dan net din dake matsayin qofa ya zura kanshi,kissing kowannesu yayi yana lumshe idanunshi,qamshinsu da kyan da suka yi suna ratsashi,kaso hamsin cikin dari na bacin ranshi take ya kwaranye,sai da ya gama duddubasu sannan ya sake rufesu,ya waiwayo suka hada idanu da sumayya,kusan tare suka sakarwa juna murmushi,qare mata kallo yake yana takowa inda take tsaye,rigar jikinta ta kamata ta fidda surarta qarara,ga na shanunta fa suka cika sun zauna das jikinta har wani qyalli suke,hankalinshu bai kwanta ba sai da yasanyata cikin jikinsa ya dora hannayenshi saman qirjinta yana yawo da shi yana lumshe ido
"Me kike a tsaye...ke da na gaya miki bacci nakeso kiyi?" A tausashe tace
"Na gaji noor,kuma gobe zamu wuce kaga dole na hada mana kayan da zamuyi amfani da su ko?" Kai ya kada
"noo,kada mi wahalar da kanki,babu wani abu da zaku dauka a nan,akwai komai can an tanada" mamaki ya kasheta,kada dai ya gaya mata ya sake wata siyayyar ne bayan wadda yayi a nan,bakinta ta bude da niyyar magana,saidai ba bata dama ba ya hade bakin nasu waje daya ya soma aika mata da saqo.

      Da qyar ta qwaci kanta gajin yana yunqurin wuce makadi da rawa tana maida numfashi,da baya ta soma ja ya dinga binta idanunsa kafe a nata yana dariya
"Me na tsorata haka babe?"Kai ta langabe
"jego fa nake noor...ni wallahi na yafewa anty su'ad kai ka manta yadda mukayi da kai jiya?"
"Don kin yafe kata kuma sai ki haramtamin romancing dinki?,baki isa ba wallahi,wannan tamkar rai da numfashi ne kinga babu mai rabawa ko?"
"Haba noor ka tausaya min mana" ta fada kaman zatayi kuka sanda ya cimmata,kamata yayi sosai yana duban qwayar idanunta
"Toni cewa nayi zanyi wani abu?,kawai dai a barni na dinga hutawa,kuma Allah idan kika yarda kika wani zauna zaman me ake cewa zaki gani shayi ruwa ne,ko an miki tayi kice kawai ni zaki biyo,sati daya kawai zamuyi mu dawo,if not kuwa wallahi takanas zan baro dubai na taho nigeria suburbudarki in koma abina" sosai kalmar ta bata dariya har tana toshe bakinta,yayin da shima ya saki qaramar dariyar yana rage zafi,motsin farkawar usaina ya sanyashi sakinta
"Kina da zabi kan sunayen yaran nan?" Kai ta kada tana kallonshi
"Bani da zani,duk abinda ka yanke dai dai ne" murmushi ya saki,ko yaushe tana maida shi yana jin kansa tamkar wani sarki,komai yayi da rayuwarta bata da zabi dai dai ne,hakan ke qara mata qima a idanunshi
"Amatullah da amatur rahman" idanunta ta juya tana murmushi,sunayen sun mata,sunaye ne masu kyau da ma'ana,bai bi iyayi ko dadin suna a baki ba
"Allah ya musu albakarka,ya sanya ma'anar sunayen ta bisu"
"Amin ya rahman ya rahim"shi yaje ya daukota ya kawo mata ita,har yau bai taba ganin tana shayar da su ba quru quru,hakan ya sanya yau ya titsiyeta,ganin ta tsaya nuqu nuqu ya sanyashi zura hannunshi da kanshi ya dauko mata ya sa mata a baki sannan ya sake daidaita mata riqonta yadda isaka ba zata shiga bakin yarinyar ba sanda take shan nono,dubansu yake cikin shauqi qauna soyayya da burgewa,har sai da tayi kaman zata tsole masa ido tace
"Kada ka cinye mu mana ha'an?" Qawataccen murmushi ya saki,ya jawota jikina yana cewa
"Da zai yiwu hadiyekun zanyi na huta wallahi baki daya,saboda bansan ya zan fassara miki yadda nake jinku cikin zuciyata ba" lumshe idanu tayi,kalamansa na ratsata,tana godewa Allah tare da qarawa kanta qwarin gwiwar yadda zata ci gaba da yi masa biyayya don ta mallaki zuciyarsa fiye da yadda ta mallaka a yanzu,saboda sau da yawa kyautatawa itace ke mai da d'a ya zama bawa,to itakam kyautatawar da take masa ta sanyashi ya zama tamkar bawa a gareta.

   ******     ******    *******

       Cikin cikakkiyar kama da kamala take sanye cikin atamfa riga da zani da wadataccen mayafi,haka almustapha ke sanye da wani yadi irin na sarakai da aka yiwa aikin gidan sarauta,takalmi zuwa hular kanshi duka irin na gidan sarauta ne,sunyi kyau sosai,zallar farinciki qauna da girmamawa juna ta bayyana a tsakaninsu,su'ad ma na sanye da doguwar riga ta gown,saidai a sake take bata kama wani sashe na jikinta ba,almustapha ke dauke da hassana ita kuma na dauke da usaina,karon farko data fara daukar yaran,wanda ganin idanun almustapha yasa ta daukesu,tana son tayi wani abu da zai barta zuwa gida,saidai tana ji kaman tayi jifa da yarinyar,kamar wadda ke dauke da garwashin wuta haka take jinta,tun daga harabar gidan ya isa ya sanar maka akwai baqi a gidan,hakan kuwa yake,anty farida da yaranta,huda da yaranta,oga amira,anty ni'imah wadda ta taho da hibba da hibban sun bar biyu a gida legos tare da mamarsu sai ana ya gobe suna zasu iso.

      Ashe baki daya suna daga gefe suna jiran qarasowarsu ciki,take kowa yayi tsaye bakin motar fuskarshi qunshe da murmushi,ba don shakkar ya man din ma da suke ba da babu shakka tuni sun ruge bakin motar suna rigengeniyar daukarsu,amma duk da tsare gidanshi hakan bai hana amira saurin amshe usaina dake hannun su'ad ba,tunu ta sakar mata dama neman mai dauka take,a rayuwarta kusan zata iya irga sau nawa ta dauki jariri,ko da can ita ba mai son yara bace,balle ma ina ta gansu,anty maamaa ita ta karbi hassana,take waje ya kacame da murna,hayaniyarau ta soma tashi,suna mata sannu tare da nuna tsantsar farinciki da kyautar da Allah ya yiwa ahalin nasu na 'yan biyu,wanda wannan ne karon farkonda suka samesu,hakan ya sanya shi janye sumayya zuwa sashen ummi wadda alkunya ta sanyata bata fito ba tun basu saka shi ciwon kai ba.
Chapter 201 · 0% Book details