← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 210

Sashe 11

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da zafi tace da ita
"Me innarki ta gaya miki sanda za'a kawo miki abokiyar zama" duk sai ta rude saboda tasan cewa anty dijen ba dai zafi ba,tsab ta mareka ba komai bane idan ka bata mata,cikin tsawa ta sake maimaitawa
"Dake nake,nace me innarki ta gaya miki?" Cikin rawar murya da in ina wanda tuni idanunta ya fara tara qwalla tace
"Tace min na zauna da kowa lafiya,kada na daga hankalin kowa,kada na zalunci kowa kada na cuci kowa idan na cuci abokiyar zama na bata yafemin ba"
Kai ta jinjina ta kama hannunta tana matsawa da dan qarfi,cikin kakkausar murya ta sake ce mata
"Tace ki zauna a cuce ki?" Kai ta kada,idanunta ta zaro mata
"Ki bude bakinki kiyi magana"
"A'ah" ta fada qwalla na gangaro mata.
"Tace ki zauna a zalunceki ko a rainaki?",nan ma ta amsa
"a'ah" kai ta jinjina.
"Da kyau......me yasa kika fara bawa fa'iza qofar da zata rainaki?,me yasa kika fara nuna mata kina tsoronta" shiru tayi ta kasa bata amsa don itama bata san dalili ba.

Ganin haka ya sanya anty dije sasaauta fushin fuskarta ta sake matsowa ga sumayya
"Bamu lamunci ki zalunci kowa bama balle abokiyar zamanki,amma......bazan lamunci ki zauna ki zama bola ba,bazan lamunci ko zama raguwa matsoraciya ba,kishiyarki ba mai son zaman lafiya bace,bamu ce ki biye mata ba,bamu ce ki zama mai son tashin hankali ba,amma sam bazamu zuba ido ki zama banza ba.....kinsam wace kishiya...kishiya ma irin taki sumayya" kai ta girgiza,anty dije ta soma warware mata komai,dukkanin kunnayenta sumayya ta bata,sosai maganar ke ratsata,sai ta dinga dauko ta maman naana tana hadawa da anty dije,tabbas dukkaninsu gaskiya suke gaya mata.

"Kada ki yarda naga ba haka ba kina jina ko?" Anty dije ta fada tana kama kunnanta da kanta
"In sha Allahu" inji sumayya tana dan murmushi,dukansu suka fito any dije ta tada sallarta ita kuma ta je ta daura tata alwalar tayi sallahr sannan suka ci abinci,suna ci anty dijen na bata labaru kala kala na kishiyoyi,wani ya bata dariya wani ya bata mamaki wani ya bata al'ajabi.

Har soro ta rako anty dije sukayi sallama,tana shirin komawa ciki taki qarar machine dinsa,hakan ya sanyata dakatawa ta bude mishi qofar ya shigo tana mamakin dawowarsa yau da wuri haka bayan duka duka biyar da 'yan mintuna ne,saidai bata ce komai ba kamar yadda anty dije ta gaya mata ta koyi yawan dauke kai da yin shiru kam wasu al'amuran da ba cutarwa ne gareta ba,ko ba hiruminta bane,ko kuma bazai cutar ko ya amfaneta ba yin magana akansa duk da cewar dama can ita din ba mai shishshigi bace.

Da murmushi saman fuskarta take masa sannu da zuwa,ya kashe mata ido daya sanda suke shiga cikin gidan
"Ko ki tambayeni ma ta akai ka dawo gida da wuri ko?" Murmushi tayi tana rausayar da kai
"Ai ba laifi kayi ba,kuma mai gida da gidansa ai yana da hurumin dawowa duk sanda yaga dama"mintsinarta yayi a bayanta har sai da ta sanya dariya yace
" sarkin wayo da iya magana,ko yaushe duka kika koyi wannan wayon haka?"
"Ka manta rainonka ce?" Ta fada tana kashe masa ido daya
"Gaskiya ne" ya fada yana sanya hannunshi cikin alhjihunsa ya fiddo da kwado(key) yana fadin
"Muje kitchen ki tayani wani aiki".....

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

______________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wa ufawwidu amri ilallah,innallaha basirun bil'ibaad*
____________________

0⃣8⃣

"Wanne irin aiki kuma,daga dawowar taka?" Ta fada tana duban fuskarsa da maqullin dake hannunsa,girarsa ya dage mata yana fadin
"Muje mana,idan muka je ai kya gani" ya fada yana nufar kitchen din,bata sake cewa komai ba tabi bayansa.

Kayan abincin dake jifge gefe daya na kitchen din ya nufa ya fara daukarsu daya bayan daya yaba zuba cikin locker din sumayya,sai daya gama kwashesu tsaf tana gefe tana kallonshi,ya bude kwadon yana shirin
"Me kenan?" Sumayya ta tambaya,waiwayo wa yayi yaba dubanta
"A nan nake son kayan abinci na su zauna,zan baki dan muqulli daya,kada ki soma bawa fa'iza muqullina sai ranar girkinta"
"Amma ya mukhtar gani nake wannan ba shine dai dai ba,ka raba ka bawa kowa nasa yafi maslaha,idan yaso......."
"Haka nake da buqata" ya fada yana mai katseta ba tare da ya barta ta gama fadar abinda tayi niyya ba,bata sake cewa komai ba har ya gama rufewa ya cire muqullin guda daya ya miqa mata ya zuba sauran cikin aljihunsa.

Tana gaban mudubi bayan sallar magariba gab da isha'i tana shafa mai kasancewar yau bata samu tayi wanka da wuri ba,saboda tunda fa'iza ta fahimci wanka zata shiga tayi shigewarta bandakin,bata fito ba sai da aka kammala sallar magariba sannan ta bata gu.

Wayarta dake kusa da ita taga na haske alamar kira na shigowa,ta miqa hannu ta dauka ganin sunan mukhtar
"Kizo daki na ki sameni" taji yace
"To" ta amsa masa sannan a gaggauce ta kammala kwalliyarta,ta shirya cikin doguwar rigar atamfa fitted gown mai dogon hannu,ta geshe jikinta da turare bayan tayi daurinta wanda ta kafa shi gaban goshi.

A dakin ta tadda su yana kan kujera yana rubuce rubuce ita kuma na gefan gadon zaune,ta musu sallama mukhtar ya amsa ta samu gefansa ta zauna,cikin karyar da murya tace
"Sannu da aiki yallabai" tilaa salon da ta masa maganar da shi ya sanyashi daga kai ya dubeta,a nan yaci karo da kwalliyar ta wadda ta burgeshi
"Masha Allah,yauwa my sumy" wani mugun tsaki suka ji an ja,dukansu suka dubeta,mukhtar yace
"Kina da matsala ne?" Idanunta na kan sumy tana kafa mata harara wanda hakan bao sanya sumayyan itama kafeta da ido ba duk da cewa ba hararar ita take aika mata ba
"Na fuskanci fa wasa wasa ana neman rainani da take min haqaina cikin gidan nan,idan banda haka ya za'ayi mace ba girkinta ba komai ba zaka wani daga waya kayi kiranta,tun yanzu ma ina cikin kwanakin amarci na kenan?,to wallahi sam bazan lamunta ba idan hakan yaci gaba wallahi zan kao gaba ne inda za'a qwatar min haqqina ehe" ta qare maganar idanunta na kan mukhtar
"Inda kinsan yadda kike da rashin matsayi a zuciyar wanda kike mawa da baki aikata hakan ba ma wlh"sumayya ta fada cikin zuciyarta amma a sarari sai ta saki wata siririyar dariya tana rausayar da kanta tare da janye qwayar idanunta daga kan fa'izan wanda hakan ya sake qular da ita,saidai kan ta kai ga cewa wani abu mukhtar ya tari numfashinta
" ba wannan shirmen ya sanya na taraku ba.....na taraku ne saboda almubazzaranci da na lura an fara min da abincin da nake nemowa da gumi na wanda duk cikinku ko wace na lura ke hakan zan taka mata burki ne,dalili kuwa shine duk wani almubazzari dan uwan shaidan ne,saboda haka bazan yarda a dinga shaidanci da abinda nake nemowa da gumina ba kuma na siyo da halali na,ni ban barawon gwamnati bane bare ace bansan ciwon kudi ko zafin nema ba,ni dan kasuwa ne dake nema cikin inuwa da rana,sanyi da zafi,hakanne yasa na yanke hukuncin adana kayan abincina ta yadda ya dace"ya dan sarara yana maida numfashi yayin da fa'iza wadda ta cika tayi fam take jira taji qarshen zancan,don gaba daya ta sarrafa maganganun nashi ta aunasu a mizani ta dorasu kacokam a kanta.

"Na siyi muqulli na kullesu suna kantar sumayya,hakanan muqullin na gurinta,duk wadda ke da girki ta karba ta bude ta debi gwargwadon abinda zaya wadaci kowa yaci ba tare da barna ko almubazzaranci ba...." Yana dire zancan fa'izan ta miqe ta dubesu kana ta ja qwafa ta fice fuuuu kamar wadda guguwa ke binta.

Sumayya ta bita da kallo yayin da shi kuma ya shareta tamkar baiga abinda tayi din ba ya dinga jan sumayyansa tasa da hira,qarshe ma ya janyota cikin jikinsa yana fadin yayi missing dinta,sai data masa wayo sannan ta samu ta gudu dakinta,batasan ya suka kwashe da fa'iza ba.

Washe gari sun kammala break fast kamar yadda suka saba yi tare ba tare da fa'iza ba,ta rakoshi tsakar gida kenan aka turo qofar gidan tare da kwado sallama aka shigo,sai da gaban sumayya yayi wata mummunar faduwa,yaya yahanasu ce,ta qaraso tsakar gidan tana binsu da kallo daya da daya
"Sannu da zuwa" sumayya ta ambata cikin gayyato dakiya da juriya
"Sannu da zuwa yaya" mukhtar ya ambata yana shirin juyawa zuwa falon sumayyan
"Dakata ba shiga zanyi ba" ta fada tana daga masa hannu alamar dakatarwa,sai ya tsaya din ya waiwayo yana dubanta
"Ina fa'izar na ganku ku daya a tsakar gidan kuna ta warkajaminku?" Ta fada tana yamutsa fuska,kafin daya daga cikinsu ya bata amsa ta bude qofar dakin nata ta fito.

Fashewa tayi da kuka da sauri ta taho gun yaya yahanasun ta fada kafadarta tana fadin
"Wallahi yaaya na gaji,na gaji da zaman gidan nan,cikin kwana uku kawai amma baki ga irin wulaqancin da na fuskanta ba,gwara kawai a yita ta qare don ni gaji,tunda nazo ban samu kwanciyar hankali ba,matarsa ta gama da shi sai abinda tace,a haka kuma kuke so na zauna da shi na haifa muku 'ya'yan?har yau fa ban sanshi a da namiji ba fa,randa aka kawomi kwana nayi muna artabu da shi kan hakan"kafadarta yaya yahanasun ke bubbuga wa,cikin murya mai nuna iso ga wanda ake da iko da shi take fadin
" yi shiru fa'iza,kwantar da hankalinki,ai tunda nazo zance ya qare,ko da baqar jaba take asiri wallahi sai na karya shi......kai muntari muje......kema kuma shegiya munafuka muje"ta fada tana dosar dakin fa'izan jaye da hannunta,sai data kai gab da shiga ta waiwayo ta dubi mukhtar wanda ke tsaye idanu jajur saboda bacin rai,sai taga ma sam bai daura aniyar binta ba bare sumayya da taja gefe daya,ta riga ta qudurci indai a dakin fa'izan za'ayi shari'ar saidai yaya yahanasun tace ta mata rashin kunya amma babu inda zata je.
Chapter 11 · 0% Book details