← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 210

Sashe 46

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kan sumayya ta dawo da kallonta"da sauran quruciyarki amma kin zabi nakasta rayuwarki,idan don kwanciyar aure kika zo gidan nan to kinyi babban kuskure don yadda kika zo haka zaki koma,don babu wasu 'ya'ya da za'a haifa a gidan nan sai nawa yaran,itama wadda aka haifa din don uwarta ta rigani zuwa ne,wlh da ni na rugata zuwa da bata isa ta haifeta ba,keda lukman kuwa saidai kallo"
"Ke lukman ya dama,kuma ta Allah ba taki ba,ni an bani ilimin yarda da QADDARA mai kyau ko akasinta,hikinar ubangiji kuma yawa gareta,hakanan sanin gaibu sai Allah,duk kuma nisan jifa wataran qasa zai fado,mai yiwuwa ma idan ya tashi fadowar ya dawo tsakiyar kan wanda yayi jifan"
"Ke ki iya bakinki wallahi idan baso kike kiyi kwanan gidanku ba"
"Idan kinso kina iya karbe aron numfashin ma da kika bani idan yaso nayi kwanan kabari baki daya" sumayya ta fada hankalinta kwance,don ya zuwa yanzu tana jin ta gama daukar haquri da rainin wayon kishiya,bata cuce su ba don me su zasu dinga cutar da ita,tabbaa dafi da gubar zainab har yau bata bar illata zuciya da gangar jikinta ba,don kusan ita ta zama silar data sake cillota wannan muhalli da take ganin wata rayuwa miji ke biyayya wa mata. Mamaki ya cika kariman don ta jima rabon da a mayar mata da magana haka,sai zuciyarta ta tuna mata daga inda sumayya ta fito,take gumi ya fara tsatstsafo mata,tabbas sai ta sake shiri a kanta,qwafa taja sannan ta juya tana fadin
"Da karimatu kike zancan lallai bakisan wace ni ba"bata yi nauyin bakin maida mata amsa ba don kada ma ta fita bata ji ba
"hakanan bakisan wace sumayya ba,ki zuba ido kisha kallo". Bayan fitarta muqulli sumayya ta sanyawa qofarta ta shiga toilet ta daura alwala,sam bata ji wata damuwa na barinta da angonta yayi ita daya a dakin ba,kaya ta fiddo ta sauya wadanda zata sake a cikinsu sannan ta sanya hijabi ta tada sallah,kyawawan nafiloli ta raya daren sosai da su kafin bacci ya rinjayi idanuwanta.

*asuba ta gari amaryar lukman*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

*ASSALAMU ALAIKUM*

*mas’alar saki uku cikin kalma guda*

_idan mutum ya saki matarsa saki uku_ _karkashin kalma daya ana daukan haka a matsayin saki daya ne tun asali.Haka wannan mas’alar take tun zamanin manzo S.A.W. har zamanin mulkin_ _sayyadina Abubakar.A lokacin da Khalifa Umar ya hau karagar khalifanci da shekaru biyu,sai sake-saken mata ya yawaita, don haka sai ya tsawatar da cewa; duk wanda ya sake sakin iyalinsa saki uku, to zamu dauka saki ukunne da gaske !!!_

_A mazhabarmu ta Malikiyya wadda da ita muke aiki duk macen da aka saka saki uku a kalma guda ta saku saki uku, amma akwai malaman da suke ganin za'a bar shi a saki daya, tun da haka ake hukuntawa a zamanin Annabi S.A.W. da zamanin Abubakar RA da wani bangare na_ _zamanin Umar RA, kamar yadda hadisin Ibnu Abbas ya tabbatar da hakan_
_Allah ne mafi sani._
_Mafiya yawancin malamai sun rinjayar da saki uku a kalma daya ya tabbata saki ukun ne saboda toshe qofar barna kamar yadda sayyadina umar R.A yayi,saboda a zamanin da muke ciki muna hukunci da saki ukun idan akayi ya tabbata ya muka cika balle kuma ace ukun a matsayin daya yake?_
_Allah shine mafi sani._

*hhh,har yau fans kun kasa cankar dai dai game da abinda zai faru gaba cikin littafin kundin qaddara ta,saidai wasu kan kwatanta,so saboda haka ku bani gari kawai kuyi kurum kuci gaba da bibiya ta*
_______________________________

"Lukman na da matar aure daya da yara hudu,hakan shike nuna zaiyi riqon Allah tunda har yana da wata matar ya saba riqon macen aure,bawai zaiyi aurensa na fari bane,amma kije kiyi tunani kina da sauran lokaci har kwanaki talatin,Allah ya zaba mana abinda yafi alheri,tashi kije".

Tamkar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka take tafiya har ta isa dakin ta,kusan ranar baki daya akwance ta yita,tana jin abdallah yana qiriniyarsa har ya gama yayi bacci anan wurin.

**** ***** ***** *****

Mukhtar bai fasa zuwa ganin yaronsa ba kamar yadda abdur rahman bai fasa zuwa gidan ba,saidai baki dayansu ganinta ya musu wahala,ba wanda take yarda ya ganta saidai bacin rana,ta bangare daya lukman naci gaba da nacin sake zuwa wajenta,saidai ko sau daya taqi yarda ya kuma zuwa din,wani irin so lukmam din ke mata wanda ke bata mamaki kuma ya fara sanya mata tausayinshi,duk randa baiji muryarta ba yakan zamo kamar wani soko ko zautacce,yayi ta jera kiran kenan har sai ta gaji ta daga,hakan ya sanya sau tari takan dan sassauta masa.

Lokaci ne yaci gaba da tafiya,kwanakin da malam ya diba mata na kuma tafiya,a haka har aka cimma kwanaki talatin din cif,saidai shirun da taji malam din bai tada mata maganar ba ya sanya ta kwantar da hankali ta ta kuma sake sakankancewa abinta,har aka fara sabgar shirye shiryen auren yaya abubakar da ita.

Ranar wata juma'a da wani yammaci wanda ya tasamma kwanaki arba'in da yin maganarta da malam bayan sakkowa sallar juma'a malam din ya dawo gida yaci abinci sannan ya sanya aka kira masa ita.

Tunda taji kiransa hankalinta yayi mummunan tashi,a lokacin suna dakin mama suna shirya akwatin kayan lefan yaya abubakar da ake saka ran kaiwa satin sama.

"Ya ake ciki sumayya,kwanakin da na diba miki sun shude har da doriya ba tare da naji komai daga bakinki ba".
Cikin yanayi na daburcewa tace
" eh malam dama.....dama.."
"Unhmmm,dama mene?,kin haqura kin zabi abdur rahman dinne" da sauri ta girgiza kai
"Ok,lukman din ne?" Nan ma kai ta girgiza,sai malam din ya sauya fuska sosai sannan yace
"Ki bude baki kimin magana sosai,idan ba haka ba zan bawa abdur rahman dama ya turo,saboda daga shi har lukman din babu mai aibu a cikinsa,aure kuwa mutunci da kamala shine abu mafi muhimmanci da za'a fara nema a cikinsa" tuni hawaye ya fara wanke mata fuska
"Malam bana son sake hada zama da su abdur rahman ka yimin afuwa" karo na farko da ta fara yima malam din musu,duk sai tajita wani iri,tana jin kamar tayi ba dai dai ba
"Shikenan,a bawa lukman din dama ya fito kenan?" Shiru tayi kamar wadda ruwa ya cinye,ta yaya zata sake musa masa bayan ba al'adarta bace?,baya ga haka kuma yayi bincike halayyarsa ta yi masa me zata ce kuma?,ganin batayi magana ba ya sanya ya sake maimaita tambayar tasa saidai nan ma shiru ne ya biyo baya bata ce komai ba,a bisa ga abinda addini ya nuna shiru alamar amincewa ce da hakan malam ya dauka cewa ta amince
"Shikenan,Allah ya tabbatar da alkhairi,Allah yayi miki albarka ya albarkaci aurenku,tashi ki tafi" abinda taji malam din ya fada kenan.

Ita dai bata san yadda aka yi ta kai kanta dakinta ba,sai tsintar kanta tayi saman katifarta tana malelekuwa hawaye na malala daga idanunta
"Shikenan,shikenan lukman cikin KUNDIN QADDARATA?," abinda ta dinga nanatawa kanta kenan,kuka tayi na fitar rai a ranar,sai ta dinga jin wani banbarakwai wai yau ita zata sake auren wani?,su zauna suyi rayuwar aure da shi.

Washe gari lukman ya kirata,murna kamar ya taka rawa cikin waya,daga qarshe yace mata jibi yana tafe in sha Allah bayan masu kawo kudi sun tafi.

Washe garin kuwa iyayen lukman suka iso,naira dubu dari suka kawo kudin har da kudin sa rana,sannan suka ce sati na sama za'a kawo lefe,duk yadda malam ya dakatar da bidi'ar da ya lura suna shirin yi amma sunqi,ganin cewa ko aurenta na fari bai karbi kudin aurenta har haka ba bare yanzu,sunce angon keson hakan tilas ya haqura.

Qarfe takwas ya kira wayarta ya shaida mata ya iso,ba wani abu da ta sanya ko ta sauya,kayan dake jikinta da hijabinta duka da su ta fita,fuskarnan duka a kode saboda kuka,mama na lura da ita amma sai ta alaqanta hakan da cewa wata qila tsananin sabo da rayuwar da sukayi da mukhtar ya sanyata take jin duka ba dadi zata sauya sheqa,ita dai da addu'a take binta tare da fatan alheri.

Yana zaune cikin motarsa sanye da shadda cream colour sai maiqo take,ta masa cas tare da yi masa kyau ta kuma haska kwantacciyar fatarsa kalar choculet,fuskarsa kawai zaka kalla kasan cike yake da farinciki da annashuwa,murmushi ne zallah kan fuskar tasa kadan kadan,lukman na cikin sahun tsaka tsaki na kyawawan maza,waqa ce ke tashi a motar tasa wadda aka ragewa sauti sautinta can qasa,wanda kalaman soyayya me kawai zalla cikin baitukan waqar.

A jikin motar ta tsaya hannayenta harde a qirjinta,wani banbarakwai take jin ta baki daya,bai lura da tsaiwar tata ba sai da ya daga kai da nufin ganin ko ta fito saboda yadda ya zaqu yaga abar qaunar tasa,da hanzari ya fito daga cikin motar ya rufe sannan ya zagayo zuwa inda take
"Ranki ya dade da kin shigo ai saboda kada ki gaji da tsaiwar"
"A'ah na gode,nan ma ya isa" ta fada tana gyara tsaiwarta,gaisheshi tayi don gajarta maganar,ya amsa a tausashe
"Naji dadi qwarai da gaake da kika aminta da ni a matsayin mijin da zaki aura,ina fata Allah ya sanya alkhairi a tsakaninmu amin,kuma ina mai miki albishir da cewa da yardar Allah zan baki dukkan wata kulawa data dace,Allah ya tabbatar mana da dukkan alkhairinsa"
"Amin " ta amsa can qasa,haka ya dinga janta da hira tana saurarensa,ba shakka ya iya kalamai na soyayya da jan hankalk,ta kasa kunnuwa tana saurarensa saidai duk yadda yaso bata farinciki ta kasa jin farincikin dai dai da qwayar zarra,a haka suka shafe mintina talatin kafin wayaraa tayi tsuwwa ya daga ya kara a kunnensa
"Allah ya taimakeki gani nan zuwa" ya fada yana maida wayar aljihunsa,sai ta lura kamar duka hankalinsa yayi gaba ya dubeta
"Uwar gida tayi kira ni zan koma sai wajen jibi haka" bata damu ba ko kadan tace
"Allah ya kaimu" duk yadda yaso ta karbi kudin da ya mata kyautarsu taqi karba haka ta juya ta shige gida.
Chapter 46 · 0% Book details