← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 210

Sashe 125

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

         Sati guda malam ya yiwa baabaa maganar ya za'a yi da jeran sumayya,ce masa yayi babu ruwanshi wannan ba huruminsa bane,murmushi kawai malan din yayi
"Ku qarata kai da 'yar taka" ya fada yana dariyaanty dije ce ta matsa kan ko daki daya abasu su saka mata kaya,tilas baabaan ya sanya aka bude daki daya dake saman aka basu shi suka saka kayan gadon da malam ya siya mata,idan baku manta ba gidan baabaan na da sashe biyu ne,ko wanne sashi akwai sassa a ciki,sashin daya barwa yaran nashi daya na wansu ne adam da matan shi,daya nasu mahomud ne da mus'ab,daya na almustapha ne,kowanne sashi yana dauke da balcony sama da qasa,sannan babban falo da dakunanan bacci manya manya wanda zasu iya cinye kayan gado set biyu,bedrooma din cikin corridor suke wanda ke hagu da daman falon,sai ka fito daga ciki zaka samu falon,sai qofar kitchen daga can gefe wanda qofa daya ce amma idan ka shiga zata tadda qofofin kitchen biyu biyu,akwai wata qofar daban da zaka fita vantilation,kusa da kitchen dining area ne,saman babban falo ne shima da dakunan bacci guda uku,daya ne makeke wanda a ciki mustaphan yake,kowanne sashe nada girma da yalwa,duk yadda ka kai ga son jin dadinka.

        Dakunan baccin duka guda biyun again dake qasa baabaa yasa aka shirya mata su ba tare da sanin kowa ba,illa ya yiwa kamfani waya ya basu adress,royal beds ne set dinsu masu azabar kyau da tsada,hakanan kitchen din aka zuba qawata shi da dukkan wani kayan qawa da kayan amfanin buqata na kitchen,falon ma ba'a barshi haka ba,sai da ya sanya aka sauya duk wani abun amfani,a taqaice dai tashin farko sashen ya sake sauyawa sosai,duk da dama sashe ne wanda ya tsaru ya qawatu tun da can,yafi kowanne sashe kyau da qyale qyale,kasancewar mai sashin mai son tsafta da gyara,yayin da matar sashen ta zama mai dagawa da son nuna iyawa da kuma qaunat ganin tafi kowa.

       Ba wai don almustapha bai da wani gida ba,yana gidan daya kusa a qalla shekara hudu ana gininshi yana narka masa kudi,har rade radi aka dinga yi a rean cewa da qyar idan ba gidan wani shugaban wata qasar vane,babu abinda bai zuba ba a cikin gidan,dai dai da cokali gidan baya buqata,hatta da kayan sangawa baki daya cupboard din gidan a cike take,wani irin tsari aka yi masa mai bala'in kyau da daukar hankali,hatta da qasashen da suka ci gaba samun irin wannan gidan sai an tona,to saidai babu wanda yasan da gidan do ba wanda ya gayawa,shi wani irin mutum ne da bai fiya son fadin abubuwan da yake yi ba,da fari yaso maida su'ad ciki,saidai irin rayuwar da yake so ya shimfida cikin gidan ba ita ta shiryawa yi ba,rayuwar soyayya da kulawa zalla tsagwaronta yakeson shimfidawa cikin gidan wanda dama ya ginashi ne don ya morewa rayuwarshi da arziqin da Allah ya mallaka masa,duk sanda ya kalli gidan yana sanyashi nishadi da walwala,ya zuba ido yana jiran yaga ranar da su'ad zatayi daidai da tsari da ra'ayinsa,ta shiryar karbar irin rayuwar da yake so,to a lokacin yake saka ran maidata gidan wanda har yanzu hakan bata samu ba,a qalla kusan watanni shida kenan da kammala komai na gidan,saidai lokaci lokaci idan yana buqatar kebewa ko hutawa yaje ya wuni ko ya kwana daya ya dawo,cikin dribobinsa ma mutum daya kacal yasan da gudan kasancewar shi ke kaishi.

  *******  *******    *******

      Duk yadda taso kauda da damuwa cikin ruhinta ko don saboda malam abun yaci tura,a yadda take yaqe da qoqarin zama cikin mutane duk da gidan nasu yanzu sun sake raguwa,daga ita sai mama,abdallah ma yaqi zama kasancewar gidan yayi shiru da yawa,ya gudu wajen yaya yahanasu don acan yake baje kolin tabararsa yayaan da su jamila na biye masa,ga yara 'yan wasa kamarshi,kana duban sumayyan kasan akwai kwantacciyar damuwa a zuciyarta,a hankali ciwon marar ke sake matsanta mata wanda ta kai ga cewa har sai ta sha paracitamol wani lokaci yake barinta tayi bacci.

         Sati guda cif da daura aurensu malam baice mata komai ba,itama bata tambaya ba bata ma damu taji komai ba,addu'a ma take Allah yasa tayi zamanta a haka,kan me zata damu?,ta damu da mijin da batasan haqiqaninshi ko wani abu nashi ba?,da zaiyita zama bai nemeta ba ma ita haka take so,ko banza sunanta matar aure ba za'a matsanta mata kan aure ba tunda akwai igiyar wani a kanta.

      Ranar da suka cika kwana takwas ranar litinin abdur rahman zaizo daukar tashi amaryar,tun rana halima ke faman shiri duk da cewa jikinta a sanyaye yake,kusan sumayya ce qarfin shirin duk da ciwon marar dake tsunkulinta haka ta dinga shirya ta tana mata hira da gaya mata abubuwa masu amfani duk don ta saki jikinta,zuwa sanda aka idar da sallaf magariba ta kammala shiryata tsaf sai tashi qamshi take mai sanyi wamda duka cikin taskar hadaddiyar humrar sumayyan ce,sumayyan ce ta raka haliman har zuwa falon malam,gabanshi suja zauna kan haliman a duqe,a hankali malam din ya dinga yi maya nasiha mai narjar da zuciya wadda kusan dasu yake baki daya,hatta da sumayyan sai data yi qwalla,ta sake taqinin duniya ba'a bakin komai take ba,hakanan mace bata da wata riba a rayuwa indai bata yi biyayya wa mijinta ba,ta ina zaki ci rina bayan aljannarsa na qasan qafarki idan kika saaba masa ya take fa?,da qyar halima ta iya roqon gafarar baabaa sabida kukan da yaci qarfinta,tashi sumayya tayi ta basu waje jin baabaa na yiwa abdur rahman izinin shigowa wanda ta tabbatar shina nasihan baabaa zaiyi masa,fuskarsa sai qyalli da annuri take,yana sanye da wata danyar shadda fara qal dinkin 'yar ciki da babbar ruga,kana kallonshi kaga ango sak,dakinta ta shigi ta samu gefan gado ta zauna tana fidda hawaye bayan taji tafiyarsu,shikenan,kowa ya fashe ya barta,kowa ya tafi wajen nashi masoyin,saura ita,ko ya zata qare?(nidai huguma nace Allah A'alamu).

      Babban dakin taron wanda ke cikin qasaitaccen kamfanin na MM dauke yake da ma'aikata wanda a qalla sun doshi su arba'in,manyan ma'aikata daga qasashe daban daban wanda ya qunshi naijeria,pakistan,china,gahana da india,kowanne zaune cikin tsari kan tashi kujeran wanda suke a jere hagu da dama,tsakiya kuma dogon tabureni wanda kana kallonshi kasan cewa kamfanin da suka qerashi ba qaramjn fasaha garesu ba,shine teburin wadan nan kujerun da ma'aikatan ke kak,gaban kowanne dauke da ruwa da lemo,saidai baki dayansu ba wannan ne gabansu ba,sun tattara hankalinsu ne kan ogansu wanda ke hakimce a kujefa qwaya daya tal dake tsakiyar teburin,sanye kowa cikinsu yake da suit baqi da fari sabanin shi dake sanye da tashi tsumammiyar suit din ruwan sea blue mai dan turuwa,ta sake fidda sigar kyawunsa da zatinsa,wadda kana kallon suit din kasan tasha banban data duk wani mahaluqi dake dakin taron,jikinsa na jingine ne da  makarin kujerar yaja juyawa kadan kadan hagu da dama tamkar mai hutawa abinsa,saidai ina,bayani yake cikin gamsarwa da hikima da fasaha ta iyawa da qwarewa a kasuwanci,kusan sun gama tattauna komai conclusion yake musu,tafi kowannensu ya sanya bayan ya gama yana rufewa da idan akwai mai tambaya yayi,minti uku ya bada babu wanda yace komai kasancewar ya gama hadiye komai cikin jawabansa,ya duba agogon fata na kamfanin gucci dake daure tsintsiyar hannunshi,awa biyu ya rage jirgin fly emirate da zaibi zuwa nijeria,hakan ya sanyashi miqewa,wanda ke tsaye kusa da shi cikin baqin kaya da baqin glass ya soma tattare dukkan wasu files da takardu ya dauka masa yayin da ya bishi a baya zuwa office dinsa.
Chapter 125 · 0% Book details