← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 210

Sashe 18

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kanta cikin jiki da zuciyarta take jin salama da farinciki,dokin ganin mukhtar da son komawarta dakinta take.

Ranar kwana na biyun da maraice sai ga abdur rahman,sosai tayi mamakin ganinsa yace mata yaje gidan bai tadda ta ba,wannan sabuwar abokiyar zaman nata ta gaya masa bata nan,ta tafi kuma ba zata dawo ba,bata boyewa abdur rahman din komai ba ta gaya mishi.

Ya jima yana jinjina kansa sannan yace
"Idan zaki amince ina da buqatar muqullin dakin naki zan duba shi ko da taimakon da zan iya miki,kinsan fannin magungunan musulunci na karanta,yanzun haka ma yaya mukhtar din nazo kawowa katin gayyata zuwa bude asibiti da zamu dinga treating cututtuka da magungunan musulunci" cike da gamsuwa ba tare da haufi ba ta shiga daki ta miqa masa muqullin ya amsa ya mata sallama ya fice,a qofar gidan ha tsaya ya fidda wayarsa ya kira mukhtar ya shaida masa,take ya bashi izinin shiga,sai da yayi sallama sau biyar duka aka masa tare da dora
"Dalla a shigo an cikawa mutane kunne da wata sallama" a tunaninta yaya yahanasu ce ta mata aike,kai tsaye ya doshi dakin sumayyan ya bude ya shiga.

Cikin nutsuwa ya dinga nazarin dakin bayan wasu addu'o'i da ya dinga karantawa a bayyane,fa'iza na tsakar gida kame da qugu tana leqen dakin gabanta na faduwa,addu'arta daya kada ya zamto ya karya duk wani kafi da shiri da tasa aka yiwa dakin.

Tsawon mintina talatin ya kwashe cikin dakin yana karanta wasu ayoyi sannan ya kulle dakin ya fice,da kallo ta bishi fa'izar kamar idanunta kamar zai fado,sai da taga fitarsa sannan ta saki ajiyar zuciya tare da zama gefan rijiya.

Saidai bai wuce wasu mintina talatin din ba sai gashi ya dawo,hannunsa dauke da kaskon wuta mai garwashi sai qwarya,dakin ya sake budewa ya shiga bayan ya tari ruwa cikin qwaryan,zama yayi sosai kan daya daga cikin kujerun yayi bismillah ya fara karanta ayatur ruqya gabaki dayanta,sannan yabi kowanne lungu da saqo na dakin ya yayyafeshi tas da ruwan,komawa yayi falon ya ajjiye qwaryar ya bude wata farar leda mai dauke da 'ya'yan habbatus sauda ya watsa cikin dakin ya shiga turare dakin ciki da falo.

Kasa daurewa fa'iza tayi ganin sai da ta dangana da bakin qofar dakin sumayyan ganin hayaqi mai qauri na fitowa daga dakin,gabanta ya fadi tana tunanin wani qullin ake mata,cike da masifa tace
"Wai malam waye kai ne?,meye haka da zaka shigo gidan mutane kana wasu qananun surkulle,bana ciki da rainin hankali da iskanci zo ka fice mim daga gida tun ban tara maka mutane ba".

Dago idanunsa yayi ya watsa mata,take wani kwarjininsa ya daureta,jikinta yayi laqwas bakinta ya mutu,duk tijarar da taso yi ta koma ciki,kafeta yayi da idanu har ta saki qofar labulen ta koma dakinta,zama tayi bakin gadonta tana ta'ajjubin wanne irin mutum ne wannan yaron?,tana zaune nan har ya kammala ya kulle dakin ya fice.

Gidan ya koma ya riski sallar magariba tare da malam sannan daga bisani ya nemi kebewa da shi,cikin falonsa dake zauren gidan suka shiga,bayan sun sake gaisawa abdur rahman din ya gabatarwa da malam maganar sannan ya dora
" a abinda na fuskanta malam ba qaramin mugun nufi aka nufi sumayya da shi ba,saidai koma mene Allah ya taqaita darajar addu'a ya rage kaifin QADDARAR TATA,naje gidan kuma na aiwatar daga cikin abinda Allah ya horemin na sani kan irin wadan nan mashaakilat din,kuma in sha Allahu komai yazo qarshe babu abinda zai sake samunta da izinin Allah"gyara zamansa malam din yayi sannan yace
"Hakane,tunaninmu yazo daya abdur rahman,mun gide qwarai da gaske daka nuna kulawarka kan lamarin,Allah yayi albarka,kuma in sha Allahu zamu ci gaba da addu'ar,Allah ya tsare gaba"
"Amin amin malam" ya amsa a ladabce sannan daga bisani sukayi sallama ya bawa malam muqullin dakin shi ya wuce.

Qarfe takwas na dare suna tafe kan babur dinsa bayan ya daukota,wani farinciki ke ratsa zukatansu,jinsa yake tamkar wani sabon aure.

Murtala suya spot ya zarce ya siya musu kaza da damammiyar fura sannan suka qarasa gida.

A tsakar gida suka taddata tana ta faman safa da marwa,tunda ya sheqa wanka ya fice da magariba ta kasa samun sukuni,far gabarta qara daduwa take duk bayan wata daqiqa,qofar gida kuwa ta leqata yafi sau a qirga tana addu'ar ganinsa ya dawo shi kadai,sallama sumayyan tayi hannunta dauke da leda kanta tsaye ta doshi dakinta,sai da ta tsaya bakin qofar dakin tayi addu'a sosai sannan ta shiga,cikin ikon Allah abinda ta zaci zata ji bata jishi ba,dakin gadonta ta wuce ranta qal tamkar babu wani abu da ya taba faruwa da ita,tabbas babu shakka addu'a takobin mumini ce.

Sai da ya kulle gidan sannan ya tako zuwa tsakar gidan,ya ganta amma ya dauke kai tamkar bai ganta ba yana shirim wucewa,sam har yau ya kasa sonta,ya kasa jinta a jikinsa ko zuciyarsa ko da qanqani je,baisan dalili ba kwata kwata ya tsaneta bata burgeshi.

Ganin da gaske wucetan zaiyi ga wani dan banzan kishi na sakadarta ya sanya ta saurin shan gabansa
"Wai me kake nufi ne?,wallahi babu inda zaka,daga dawowarta yau shine saboda rashinvadalci zaka debi kwana ka kai maga,ai sai ka bari sai gobe ko" wani banzan kallo ya jefeta da shi,yau din cikin farinciki yake kuma baya buqatar abinda zai tarwatsa masa farincikin da yake sa ran samu a yau,cikin kakkausar murya yace
"Ki matsa daga gabana,umarni ne ba shawara ba" ya fada a tsawace,taji tsoro amma taurin kai ya sanya ta shanye,ta bude baki zata sake magana ya sanya hannu ya janyeta gefe daya ya wancakalar yayi wucewarsa.

Wani kukan baqinciki da takaici ta saka,wankin hula na neman kaita dare,duka magungunan da yaya yahanasu ta amshi kudadenta ta kawo mata tana zuzuta mata aikinsu sam ba haka ta gani ba,haka kawai sun hadata da diyar malamai tana ta faman wahala da ita,wahalar ma ya banza,eh ta banza mana tunda ko hankalin mukhtr din ma da akeyi don shi har yau ta kasa janyoshi gareta,kullum kwanan duniya kamarvsake sabunta qaunar sumayyan ake cikin ruhinsa ba qoqarin fidda ta cikin zuciyarsa ba?,abu goma da ashirin kenan,sam wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa.

A fusace ta shiga dakinta ta lalubi wayarta,lambar yaya yahanasu ta kira da niyyar yi mata wankin babban bargo saidai kash ta daki gurbi wayar tata a kashe take,da sauri ta sauya akalar kiran nata zuwa ga fadima,cikin sa'a ta sameta,tun kafin fadiman tace wani abu fa'iza ta soma sauke mata kwandon rashin mutunci,zagi na tsamar nama ta dinga luluqa mata tare da laqaba musu sunan macuta,sai da ta tabbatar ta rage farashin baqincikin da take ciki sannan ta datse layin tana huci tare da cin alwashin gobe har gida zata yi tattaki taje ga yahanasun ayita ta qare,don ba zata dauki asara ba sai ta biyata kudinta,tunda ai ba ita daya ke da buri ba suma suna da buri don me zasu dinga cutarta suna wankarta ana amfani da kudinta kadai?.

Kwanan baqinciki tayi tare da kusan qarar da daren nata wajen zirga zirga tsakanin dakinta da window din sumayya,su kam suna ca wata duniya basu san ma me takeyi ba,kwanan farinciki qauna bege da faranta ran juna sukayi,yayin da tayi kwanan gadi da safa da marwar da babu lada.

*tabbas duk wanda ya saki Allah yana tare da tarin wahala maras qarewa*

_wannan kenan muje zuwa masu karatu,har yanzu da sauran qaddarori wa sumayyan taku_

*zuku ji shiru gobe in sha Allah sakamakon uzirin dake gareni,idan kuma ya samu to amma kada ku sanya rai,na gode.*

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍✍✍✍
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣5⃣
___________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wama tadri nafsun maza taksibu gada*
_____________________

Kwanaki biyun da yayi a dakin sumayyan shi kansa ji yake ya zama tamkar ango,zuciyoyin su fes,duk wani buduri da fa'izan keyi basu san da shi ba,soyayyarsu kawai ta ishesu rayuwa.

Cikin kwanakin da suka biyo baya damina ta shigo,wanda hakan shi yayi sanadiyyar zubewar ginin maqotan yaya yahanasu ya fadowa gidansu har ya janyo rushewar wani bangare na gidan,hakan ya sanya mukhtar yace su baro gidansh su dawo gidansa don a samu sararin gyaran gidan nasu,ko bayan rasuwar mai gidan anty yahanasu kusan shine jigo dake d'awainiya wa su yaya yahanasun.

Qarfe biyu na azahar suka iso gidan tare da yaranta biyu jamila da sayyada,sumayya na tsakar gida a lokacin tana wankin kayanta,da fara'arta ta taso tana musu sannu da zuwa tare da qoqarin karbar jakar hannun yaya yahansun bayan yara sun gama shigewa da sauran kayayyakin nasu d'akin fa'iza,kaucewa tayi gami da jifanta sa wani kallo tana fadin
"Kada ki kuskura ki taba min jaka,matsa da Allah ki bawa mutane guri" ta fada tana wuceta sauran yaran suka mara mata baya,a salube ta koma kan wankinta taci gaba da yi har ta kammala tana jiyo shewarsu cikin dakin fa'izan kai kace yaya yahanasun sa'arta ce,ya tabbatar cewa da ita ke shewa haka da yaya yahanasun sai ace bata da mutunci bata da kunya,amma ga fa'iza na faman shewa da qyaqyatawa gabanta,matar da ko sau daya sumayyan bata iya hada idanu da ita,biyayya take mata tamkar uwar mijinta haka ta dauketa sakamakon ganin irin girman matsayin da take da shi gun mukhtar.

Tana kammala shanya kayan ta shige wanka saboda tana so taje kitso sakamakon ita ke da girki gobe,har ta fito ta gama shiryawa ko alamun dora abinci babu gun fa'iza,itama bata damu ba sai ta hada shayi kawai ta sha tayi ficewarta ta barsu.

Qarfe biyar ta dawo gidan saboda layi da ta taras a gidan kitson,tun daga qofar gida ta soma jin muryar fa'iza cikin balbalin bala'i,ta kutsa kai cikin gidan cikin mamakin ita da wa,dai dai lokacin da fa'izar ke fadin
"Yo da kika damen da zancan ciki laifin uban waye mayun 'ya'ya?,qanin naki yayi min cikin mana ya gani idan ban dauka ba,wata uwar yake yimin idan kwana na ne banda kwanciya da zaki uzzura min,to wallahi babu ma mai kwanarmin cikin daki balle ya sanya min ido,dama daki ba daki ba ya zuciyar talaka,sai ku nemi gun kwana" ta fada tana komawa cikin dakin tare da banko labulenta.
Chapter 18 · 0% Book details