← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 210

Sashe 48

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai jima da fitar ba mama ta matsa mata ta shi su tafi tunda zasu gidan yahanasu,ta miqe suka yi sallama da maman ta fito.

Sai ta tadda mukhtar din da su zainab da halima ya bude musu motar suna ciki,malam kuma yana gefe da alama isowarsa shi kenan don gaisawa ma suke,ta qarasa cikin girmamawa itama tabi sahun mukhtar ta duqa ta gaidashi sannan ta gaida ya abbakar,ya shiga tsokanarta ta hanyar cewa tayi qiba ta zama lukuta me mukhtar ke dura mata ita kadai,ta kasa tanka masa sai dariya da takeyi kanta a qasa saboda kunyar malam da takeyi.

"Ai sai ku wuce ko kada dare ya muku" cewar malam yana shigewa gidan bayan sunyi sallama,mukhtar ya fidda dubu biyu ya bawa su halima yace su sayi kayan kwalliya,qin karba sukayi sai da sumayyan ta sanya baki sannan suka amsa auna godiya suka shige gidan.

Shiru ya biyo baya cikin motar,mukhtar ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
"Tarbiyyan gidanku na birgeni sumayya,naso a ce ina da wani dan uwa namiji da babu shakka sai na aura masa halima ko zainab" murmushi kawai sumayyan tayi sabida tasan koda yana da dan uwan babu ta yadfa su yaya yahanasu su yadda su sake hada zuri'a da 'yan gidansu.

Mintina qalilan suka isa gidan,ya kashe motar ya fice ta bishi a baya bakinta cike da addu'a.

Dukansu suna tsakar gida zaune kan tabarma suma saboda zafin dake dan busawa a 'yan kwanakin,ga matsalar rashin isashshiyar wutar lantarki da muke fama da ita ta kowanne bangare na qasar nan.

Da fara'ar ta ta amsa sallamar amma jin muryar sumayya yasa ta gintse 'yar fara'ar data yo tsaraba,jamila dake gefen tabarmar ta matsa ma mukhtar,yayin da sayyada taqi motsawa ko su samawa sumayya wani abun zaman,hakanne ya sanya mukhtar din dubanta fuska a hade
"Ke,tashi ki bata guri" tuni ta miqe saboda tana shakkarsa kuma tasan halinsa sarai,daki suka shige ita da jamilan baki daya.

A girmame yake gaisheta ta amsa sannan sumayya ta gaidata,sama sama ta amsa mata suka shiga hira da mukhtar din.

Jamila ta fito da ruwan pure water mai sanyi guda biyu ta cup ta ajjiye gaban mukhtar din sai ya turasu duja gaban sumayyan yana cewa
"Bude kisha,kince min kina jin qishirwa dazu" zuciyar yaya yahansu ta tunzura,ta dinga jifansu da harara tana qwafe da su,ya maida dubansa gun yaya yahanasun
"Mota na kawo miki ki gani yaya,ta iso dazun da safe" sai ta harareshi
"Au shine sai yanzu kaga damar kawo min na gani kenan sai da ka gama nunawa duniya"
"Ba haka bane,data iso din ma a gareji na wuni ana mata service,ina dawowa gida kuma nayi wanka naci abinci muka taho kawo miki"
"Sai kace makaho da baka iya tahowa kai kadai,kai Allah ya kyauta,ya warware mana wannan masifar" ta fadi cike da haushi da tsana,don ya kauda zamcan don kada yayi nisa sai ya miqe yana fadin suzo su ga motar,haka suka miqe suka fice suna hayaniyar murna,tana zaune gun burinta kawai yace ta taso su tafi,Allah ya taimaketa sayyada ta leqo tace ta fito su tafi.

Tana zaune gaban motar shima haka amma sai zuba zance yayan taje wanda ya hana musu tafiya
"To Allah ya tsare ya rabaka da sharrin masu sharri,Allah ya qara budi ya kawo masu yi maka addu'a ya rabaka da wannan matsiyacin zaman kadaicin" bai amsa ba ya ciro dubu uku ya miqa mata yana fadin
" ga wannan ku qara"hannu tasa ta karba zata sake barkewa da wani surutun ya samu yaja motar suka wuce.

Duk yadda taso boye damuwarta amma sai da ya fuskanta,kan dole yake zuwa da ita gidan saboda yaya yahanasun dolensa ce,amma banda haka da tuni ta bar zuwan gidan,da tuni ya yanke alaqar dake tsakaninsu,kan hanya ya tsaya ya siya musu yoghourt manyan roba biyu masu sanyi da tsire mutumin sumayyan don duk ya faranta mata,a hankali ya dinga janta da hira da labarukan ban dariya,sosai ta sake sake masa jiki tana qyaqyata dariya wanda hakan shima ya masa dadi.

*~TSUGUNNE BATA QARE BA~*

Shi da ita duka suna zaune cikin falon nata da ya sake gyara mata shi,sanye suke da kayan barci saidai sai banbanta gun zama da ayyukan yi,shi yana zaune kan qaramar kujera ta zaman mutum daya dauke da computer yana aiki,yayin da ita ke kwance saman doguwar kujera tana kallo a tashar mbc inda suke hasko film din ashqui,kusan bata taba zama ta kalli film din complete ba sai yau.

Dakin ya dauki shiru kasancewar kowa ya bada muhimmanci kan abinda yakeyi,wayar mukhtar dake saman jakar laptop dinsa ta dauki tsuwwa,ya dubi wayar sai yaga baquwar lamba ce,kusan ya jima da daina daukar ire iren lambobin,to amma sunyi da wani costumer dinsa zaya kirashi kan wasu kaya da zai siya a shagonsa,sai yayi zaton shine saboda haka ya daga
"Assalamu alaikum" mukhtar din ya fada,kana yayi jim kusan daqiqa talatin sannan ya sake cewa
"Wacce zainab?,daga ina?" Ya sake yin shiru na sakan biyar sannan ya ja tsaki ya kife wayar yaci gaba da binda yakeyi.

Ba'a cika minti biyar ba wani kiran ya kuma shigowa,ya dubi wayar ba tare da yayi niyyar dagawa ba,lambar dazun ce dai sai ya sake dauke kansa yaci gaba da abinda yakeyi din ransa na quna.

Kiran da aketa maimaitawa a kai akai shi ya dami sumayya har ya ja hankalinta,tana daga kwancen ta dubeshi
"Don Allah yaya mukhtar ka daga,wallahi ta dameni" ta fada a shagwabe,bai dubeta ba yace
"Bazan daga ba,barta kawai" sai ta maida kallonta din batason ko gu daya ya wuceta.

Bai haqura ba mai kiran yaci gaba da nacin kiran har sai da sumayyan ta sake tankawa ya bata amsa irin ta dazun,sai ta tashi zaune tana gyara wuyan rigar barcinta da ya salube tare da fadin
"Shikenan,bari ni na daga maka ko a bar kunnuwanmu su huta"
"Kema ba zaki daga ba" ya fada bayan ya dago idonsa wannan karon ya dubeta,dariya ta saka tana tunanin wasa yake mata,dai dai lokacin da kiran ya sake shigowa ta sanya hannunta da sauri ta suri wayar ta daga ta kara a kunnenta tana masa gwalon taci nasara ta daga ba tare da wafce ba kamar yadda yayi niyyar yi da farko.

A hankali ta cire wayar daga kunnenta qirjinta na bugawa jin muryar macace tana gaya mata mukhtar take nema,miqa masa wayar tayi jiki a sanyaye.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣9⃣

_________________________
*Bismillahir rahmamir rahim*

*ala bi zikrillahi tad'ma innul quluub*
______________________

Mamaki fal zuciyar sumayya,kanta ya daure tamau,ta kasa furta ma komai sai kallon mukhtar da takeyi,ta tabbata ba qarya ya yiwa fa'iza ba domin ba halinsa bane,amma halayyar fa'iza har ta kai haka?.

"Ina naki abincin?" Mukhtar ya tambayeta,ta katse tunaninta ta dago ta dubeshi
"Ya d'aki"
"Ki dauko,ban amince kema. a yau kici ba,ki zuba a leda ki saka a shara a zubar,shiga kitchen ki samar mana abinda zamu ci koda indomie ce sai ki hada mana da qwai" ya fada yana kashingida gami da lumshe idanunsa,tsam ta miqe ta fice don aiwatar da abinda ya umarceta.

************************

Cikin kwanakin ta dage sosai da addu'ar neman tsari,ta san tabbas shartin mutum girma gareshi,zuwa yanzu ta kuma sallama kaidin fa'iza,ta fahimci irinsu matan da suka dauki kishi ko a mutu ko ayi rai,irinsu wadanda zash iya aikata komai saboda kishi,sosai take takatsantsan kan duk wani motsi da kai kawo nata a gidan,ba ruwanta da sabgar fa'izan bare wani abu ya shiga tsakaninsu,koda fa'izan zata shekara tana takalar tashin hankali bata bi ta kanta,don ta riga ta tabbatar cewa akwai banbancin gida da kowaccensu ta fito,bai kyautu ta biye mata su zamana kamar wadanda suka fito daga gurbi guda ba.

********************

Tun da asubahin ranar suka dinga jiyo kakarin amai a tsakar gidan nasu,sumayya ta dubi mukhtar dake gefanta wanda basu jima da kammala sallar asubahin ba kasancewar sun makara basu tashi da wuri ba
"Ya mukhtar,kamar kakarin amai nake ji fa a tsakar gida" shi din ma taji amma sam bai da muradin fita,tamkar bazai tanka ba sai ya daure yace
"Eh nima naji" yaci gaba da jan carbinsa,ganin yayi shiru ya sanya ta sake cewa
"Ya mukhtar ka duba mana,inajin kamar fa'iza ce fa" shiru ya sake mata ganin hakan ya sanya itama ta tsuke bakinta tayi shiru tana ci gaba da sauraran kakarin wanda yake fita tamkar da kayan cikinta,ya kammala azkar dinsa ya haye gado abinsa ya kashingida.

Zuciyar musulunci ya sanyata ta kasa daurewa,sai ta miqe ta fidda hijabin jikinga ta nufi qofa,sanya baki yayi ya kirata tare da tambayarta ina zata
"Zanje na duba ne,bai kyautu da mutane cikin gidan ba kuma aqi fita a dubata ba,bamu san meke damunta ba" kai ya girgiza
"Dawo tausa nake so kimin"
"Kayi haquri naje na dubata din minti biyu kawai zan dawo sai na maka tausar"
"Idan ban isa da ke ba shikenan kina iya hakan" ya fada yana maida kansa ya kwantar kan pillow,sai jikinta yayi sanyi bata son saba masa ko kadan,saboda haka ta juyo a sanyaye tahaye gadon.

A tausashe take masa tausar tana leqen fuskarsa ganin yaqi kulata,har ta soma tara qwalla bata iya jure fushinsa,sai taji kawai ya birkitota ya danneta da rabin jikinsa yana dariya qasa qasa
"Raguwa kawai sarkin kuka" ya fada yana lakuce mata hanci,dariya ta saki ya shiga mata cakulkuli daga haka suja shige duniyar ma'aurata wanda hakan shi ya hanasu fitowa da wuri.

Qarfe goma ya gama shirinsa zaya fita,a tsakar gida daga can bakin qofar dakin fa'izan suka ganta zaune dirshan a qasa,ta wani wargaje can qafa can qafa tana numfashi da qyar,da sauri sumayya ta qarasa inda take tana fadin
"Hasbunallahu lafiya fa'iza?"
"Bani da lafiya" ta fada qasa qasa da qyar,ta daga kai ta kalli mukhtar da bai qaraso gun ba,yana tsaye abunsa bakin qofar dakin sumayyan yana daura agogo
"Yaya mukhtar,ko asibiti zamu?" Baice komai ba sai hannunsa da ya sanya cikin aljihun wandonsa ya zaro naira dubu biyu ya miqa mata
"Gashi sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya" ya sanya kansa soro ya tada machine dinsa ya fice.
Chapter 48 · 0% Book details