← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 210

Sashe 168

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye gadon ya hauro bai bata lokaci ba ya danneta ya aza mata nauyinshi,murya qasa qasa yace
"Baki damu da ni ba ballantana ki tsaya muyi sallama ba ko?" Qoqarin tureshi take ta miqe saidai ta kasa,cikin nishi tace
"Ba haka bane,bacci nake ji shi yasa" dagowa yayi yana duban fuskarta yayin da taqi yarda ita din ta kalleshi
"Uhummm,yaushe kika fara qarya?,ko dama can maqarayaciyar ce,idan bacci kike ji me ya hanaki yi yanzun?"
"Akwai abinda na tsaya yi ne" dagata yayi yana 'yar qaramar dariya
"Gaskiya ne,coffee nazo ki hadamin in sha kafin na kwanta" ya ambata yaba gyara wuyan rigar baccibsa wadda ke da V shape,dagowa tayi ta dubeshi
"Amman ita yafi cancanta ta dafa makan,tunda gunta kake" ta fada tana qoqarin hadiye kishin dake taso mata,eh tabbas ya sani ita zata dafa din,amma shi kansa yasan wasa ne ma,ta yaya su'ad din zata iya wani dafa mishi coffe koda ta iya bayan yasha wanka ta harde saman gado tana jiranshi?,hasalima ita ta bashi daman ya kira masu aikin gidan su dafa mishi
"Bazan samu ba kenan?" Kai ta kada tana yunqurin sauka daga kan gadon,binta yayi da kallo,kayan duk da na bacci ne amma sun amsheta sosai,ta sake kyau a idanunshi,saukowan shima yayi ya biyo bayanta,ta dora hannun saman hijabinta da niyyar sanyawa ta fice ya riqe hannun nata,dagowa tayi suka hada idanu
"Muje na rakaki kitchen din,a haka nake son ganinki" ba musu ta saki ya sanyata a gaba suka fice.

Cikin kitchen din yana tsaye jingine da freezer hannunsa harde a qirjinsa,duka motsinta da kaikawonta idanunshi na kanta,komanta a nutse a tsaftace abun burgewa,ta gama komai ta zuba cikin dogon cup wanda yake da riqe zafi ta miqa masa,hannu biyu ya sanya ya amsa yana murmushi,tun kafin yasha din kwadayi ya kamashi,qamshin ya cika masa ciki,baisan yau wanne kalar coffe tayi masa,ganyayyakin da yaga tana hadawa dabanne
"Thank you" ya furta a tausashe,har cikin zuciyarta lafazin ya sauka,sai ta samu kanta da maida masa martanin murmushinsa
"Albarka nake son ka sanyamin" ta fada a kunyace,murmushinsa ya fadada
"Qwarai albarka tafi lafazina na thank you,Allah yayi miki albarka" ya maimaita har sau uku tana amsawa da amin,gaba ya sake sanyata suka fice,sai dayaga ta shige corridor dinta sannan ya juya ya haura sama da tea din hannunshin,don a bedroom dinta na qasa tayi kwanciyarta bata ma yi sha'awar hawa na saman ba.

***** ****** ***** ****

Misalin sha daya da rabi ne na safiyar washegari,yana tsaye kanta sanye da wani lallausan yadi ruwan qwaiduwar qwai,hannunsa zube cikin aljihun wandonshi yana dubanta sanda take shiryawa,baki daya ji take jikinta kamar ba'a jikinta yake ba,kwana sukayi jiya suna abu daya ba cikakken barci,gashi yau tunda asussuba ya tasheta wai tayi wanka tayi sallah,hakanan ta tashi ba don taso ba,ta tsani yadda yake tilasta mata tashin asubar nan,agogon hannunshi ya duba,tunda gari ya waye ba wanda ya fita a dakin shi da ita
"Ki sauri zamu je mu gaida su ummee ne kada baba ya fita" tamkar ya soka mata wuqa a qahon zuciyarta haka taji,me zata je tayi musu,magulmatan mutanen?
"Gaskiya bazan samu zuwa yanzu ba kaje kawai na shiga daga baya" take yanayin fuskarshi ya sauya,me take nufi?,a hakanne take cewa ta sauya zata dinga duk abinda yake so?,ashe ma wasu halayen ta dado?,tunda ada ko sau daya a rana takan shiga ta gaidasu sai gashi yanzun tana neman sake bijirewa
"Kada ki yadda su'ad,kada ki yarda tun ba'a je ko ina ba tafiyar nan ta sake watsewa,kada ki yarda raina ya baci kan hakan?,sai na maimaita miki abinda na fada miki jiya kenan ko?,to iyayena sunfi min kowanne mutum muhimmanci da daraja cikin duniya koda kuwa wane shi,ba'a haifi macen da zata rainamin iyaye ba wallahi ko ita din wace" ranta ya sake baci,biyayya tamkar wanda suka shanye?,tana son zaman lafiyarta hakan ya sanya ta miqe ta soma lalubar kayan da zata sanya,riga da wando ta dauko cikin kayanta ta soma qoqarin sanyawa,wani kallo ya watsa mata
"Ki nemi wasu kayan ki sauya,kin daina wannan shigar matuqar ba ni da ke bane kawai" kasa daurewa tayi tayi kicin kicin da rai
"Wai duka meye haka ne almustapha?,me ya shiga kanka ne ya canzaka haka?"
"Tunani da gayara.....dole ki sauya kamar yadda kike ganin kamar na sauya,sabida wannan shine dai dai"
"Amma meye hadin sauyina da tufafin da zan sanya" soma takawa yayi zaya fice daga dakin,ya fuskanci idan ya tsaya biye mata sai ta sanyashi ciwon kai
"Ki sauya kaya na mutunci ki sameni qasa,fine..." Ya fadi yana bude qofa ya fice daga dakin,kayan data debo din ta watsar gefe daya cikin huci,hakanan tana ji tana gani ta shiga dakinta ra dauki atamfa riga da skert ta sanya,sai yalolon mayafi data yane kanta da shi ba tare data damu da daura dankwakin ba,duk da dai sun matseta amma sunfi wadancan.

Tana cikinsu anty farida huda da amira dake falon ummee suna hirarsu tamkar sun shekara da sabawa da sumayyan,karyawa suke a qasan tiles din falon husna na saman cinyarta tana bata tea kadan kadan da cokali yayin da suke karyawa suka sauran banda ita,tun takwas ta kasa komawa bacci bayan ta farka daga dan baccin da ya kwasheta bayan sallar asuba,hakan ya sanya ta miqe ta shiga kitchen,cikin awanni biyu tayi kunun gyada da alala lafiyayye,ta diba nata ta ajjiye sannan ta samu wasu warmers masu kyau ta zubawa ummee da baba,wanka tayi ta shirya cikin shadda maroon mai adon milk doguwar riga ta yane kanta da madaidaicin milk din mayafi ta fita,taci sa'a kuwa ta tadda ummee zata wajen baban ta bata nashi bayan ta bata nata itama,tayi zamanta cikinsu farida suna hirarsu gwanin sha'awa wanda a baya basu samu wannan damar ba.

Sallamarshi ta sanya dukansu waiwayowa suna amsawa har da sumayyan,saidai ita ta dauke kanta ne taci gaba da baiwa husna tea din da takeyi,har ya qaraso idanunshi na kanta,ta iya shigar hausawa ainun,duk yayin da tayi shiga takan tuna masa da ummensa zamanin quruciyarta,bazai manta salon adonta ba,husna tayi kyau a hannunta tamkar diyarta,kujera daya suka zauna da su'ad din wadda tunda ta shigo sumayya ta tsone mata idanu,a ladabce suka gaisheshi baki daya ya amsa yana tambayar farida ina yaran tunda yaga yaran huda a hanya,tace jiya abbansu yazo ya daukesu,sunyi kaduna gidan kakanninsu za'a soma bikin qanwarshi next week,ba yabo ba fallasa suka gasheta kasancewarta matar yaya a wajensu duk da sun girme mata,ta amsa hanci a sama,don babu wanda bata jin haushinsa,tana ganin duka bakinsu daya da shawararsu aka kwaso mata abokiyar zama,sumayya ta dan waiwaya kadan ta gaidashi,sai ya amsa mata kamar sauran,cikin basarwa da dakiya,wanda hakan ya dan sosa ranta,zuciyarta tasi karyewa,ta tuno rayuwarta gidan mukhtar tsakanin fa'iza da zainab,rayuwar gidan lukman da karima,kada fa ace dare daya tak zai soma sauya mata,ya rusa dukkan wata alaqa data soma ginuwa tsakaninsu,zuciyarta ta daure ta gaida su'ad wadda bata kulata ba tunda suka shigo gun,amma itama ganin ta girmemeta yasa ta gaidata din,banza tayi da ita tamkar ba da ita take ba,falon ya dauki shiru,itakam ko a gefan takalminta,don ta saba ganin hakan wajen kishiya,tunda ta sauke nata nauyin falillahil hamdi,har sai da almustapha ya maida wayarshi aljihu ya dubeta ta gefe daya
"Ba dake ake ba?"
"Lafiya lau" ta fada a dake,zuciya ta zowa amira wuya,haushi ya tuqeta,don me ma sumayyan zata gaidata,me yasa batayi watsin tsiya da ita ba itama,shine zata zo tana ma mutane dagawa da daga kai?.

Shigowar ummee falon ya sanya su miqewa,ummee ce ta tsaida sumayyan saura suka shige ciki,a ladabce cikin qauna da kulawa ya gaidata,ta amsa fuskarta fadade da fara'a,su'ad itama ra gaidata kadaran kadaham,duk da tana jin ba don almustapha dake wajen ba wallahi ba zata gaidata haka ba
"Ya kika baro su khaulat din" sai data raya,munafuka kamar gaske cikin zuciyarta sannan ta amsa da
"Lafiya lau"
"To masha Allahu"
"Inaga sai kayi hanzarin zuwa ka tadda baban naka,don ina tunanin zai fita,na barshi yana karyawa"
"To ummee"
"Me za'a kawo maka me zaka ci?"ta tambayeshi tana dubanshi,kunya ta kama sumayya ta sadda kanta qasa,tana ganin kamar ummee zata ga ita din ma ta gaza tunda gashi yana shirin komawa 'yar gidan jiya cin abinci wajenta,saidai ita ummeen tuni ta fahimci cewa yau ba kwananta bane,indai kuwa hakanne kamar yadda take zato ba shakka bazaya samu abin kari ba saidai yaci a waje
"me kuka dafa?"
"Akwai tea,akwai chips,sai farfesun kayan ciki da amira tayi,sai kuma amiran umman khalipha data kawo alala da kunun gyada" satar kallonta yayi sanda ita kuma taje duban wani waje,duk da sarai taji alamun yana kallonta din,yaushe rabon shi da yaga kunun gyada ko alala ya mance tsahon lokacin,yaushe har ta tashi ta gama dukkan wadan nan ayyukan har ta shirya ta fito
"A kawomin abinda ya samu" duban su'd dake hakimce ummee tayi
"Su'ada shiga kitchen zaki ga kayan jere,ki deba masa abinda zai iya cinyewa" dauke kan da ummeen tayi ya sanya bata lura da sauyawar fuskar tata ba,gani take da gayya ummeen tayi mata haka,ita waccar baqauyar me ya hana ta aiketa sai ita,wanzuwar almustapha a wajen shi ya takawa abinda ta taka burki,miqewa tayi cikin bacin rai ta nufi kitchen din.

A qalla sai data bata wasu mintuna masu dama kafin ta fito dauke da farantai kamar wadda ta dauko duniya,ba zata iya tuna ranan data shiga kitchen tayi wani aiki kamar haka ba,tana isowa ta saki tray din har da suka tsorata saboda yadda ta soma yarfe hannu tana kiran Allah,hanzarin kama hannun yayi yana dubawa,tsammani yake ko qonewa tayi,saidai ba haka bane,daukan kwanukan da tayi takewa haka,tsam ummee ta miqe saboda takaici
"Idan ka gama ina saman" ta fada tana niyyar haurawa,sai sumayyan itama ta miqe ta rufa ma ummeen baya,binta yayi da kallo kamar ya dakatar da ita,domin ko gaisuwar da sukayi bata yi masa ba,ji yake kamar ya shekara ne bai ganta ba,amma sai ya dake ya maida kallonsa ga su'ad,hararar wasa ya jefa mata
"Raguwa,sai kace wadda ta qone,oya....yi serving dina" tamkar wadda tayi aikin shekara haka ta dinga zuba abincin,wani bakin kwanukan duka ya baci.
Chapter 168 · 0% Book details