← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 210

Sashe 20

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin dakin ya barta ya fita sallah,kasancewar tana faashin sallah sa'an nan kuma dakin nasa na hargitse don fa'iza ba kasafai take tsayawa ta gyara ba ya sanyata tsayawa tana dan kakkabe dakin haka ya dawo ya cimmata,kafin ya kai ga zama fa'iza ta fado dakin hannunta riqe a qugunta,shi ya fara cewa
"Me aka girka" ran nan nashi a hade tsaf wanda ita a nata zaton aikin da take kansa ya fara tasiri,saboda haka kanga tsaye tace
"Yau duka ma banyi girki ba wlh a gajiye nake" ta fada tana yatsina,sam ya tsaneta har yau ya kasa jinta dai dai da qwayar zarra cikin zuciyarsa,bata dameshi ba dama bisa lalura kawai yaje rabarta,qoqarin adalci ne kawai irin nasa tunda ta riga da ta rataya a wuyansa bisa alfarmar igiyoyinta uku dake hannunsa.

Hannu ya miqa mata a daqile yace
"Bani muqullan locker din kayan abinci na" ba musu ta fice don dauko masa,ya juya ya dubi sumayya
"Yau ba'ayi girki ba gida na,me kuka bawa yaya taci ita da iyalanta?" Kanta ta duqar qasa sannan tace
"Ka mance na tambayeka zani kitso?,tunda na fita ban samu na dawo ba sai bayan la'asar,dana shigo kuma nima yadda ka taddasu haka na taddasu" kai ya gyada ba tare da yace komai ba,ta dawo da muqullin ta miqa masa,kai tsaye ya danqa su ga sumayya
"Jeki ka samar mana da abinda zamuci" hannu biyu tasa ta amsa kana ta danyi jim,da kamar taqi abinda ya sata din,sai kuma taga hakan bai dace ba,idan bai isa da fa'iza ba ita ai ya isa da ita,miqewa tayi zata fice fa'iza ta saki wani mugun murmushi,ga zatonta sumayya ta shiga cakwakiya mukhtar zai soma azabtar da ita kenan,fadawa tayi saman katifar kusa da shi tana fadin
"Ammmmm......idan kin gama kizo na gaya miki me mi kuma zaki dafamin" wannan karo kasa hadiye takaicinsa yayi sai da juyo yace
"Da yake baiwar gidan ubanki ce ko,wato saboda kinga na miki shiru ne ko......hmmmmm.....ki kiyayi ranar qin dillanci wallahi,wuce kije sumayya",sai ta juya ta fice din,itakam ta ma rasa na cewa gaba daya,gaban fa'iza ya fadi,kaddai jiya i yau ne dai mukhtar din,sai ta kasa hadiye qanin zagin da yayi mata ta miqe tsaye
" wacce rana ce ranar qin dillanci,ba ranar da hajar mai gari ta bata ba?,idan ba'a ganta a gun fa'iza sai me?"ta murguda baki tana niyyar ficewa,zuciya ce ta ciyoshi ya miqe cikin zafin nama ya fincikota ya zabga mata wani lafiyayyen mari,a gigice ta dafe kuncinta don bata zaci haka ba,karo na farko da mukhtar din ya soma taba lafiyarta,ashar ta danna sannan tace
"Ni ka mara muntari,kayyasa kace yau da bala'i,wallahi baka daki bulus ba sai na rama" .

Daga hannunta tayi da niyyar kaiwa fuskarsa mari ya cafe hannun tare da murdeshi har sai ta qashin hannun ya bada wani qasss da alamu ya targadata,tsananin azaba ya sanyata sakin qara wadda ta sanya sumayya dake kitchen barin abinda take ta taho dakin cikin hanzari,dadin da taji data lura su yaya yahanasun da suka qure kallo cikin t.v dinta basu san me ake ciki ba,tun fara masa rashin kunyar duk cikin kunnenta ne saboda muryar fa'izan na sama ne sosai.

Sanda ta isa dakin ya daga hannu da niyyar sake bata wani marin,cikin hanzari ta shiga tsakiyarsu taba riqe hannunsa,cikin taushi ta langabar da kanta tana duban tsakiyar idonsa wanda hakan shi ya karya lagonsa,ya zare hannunaa daga nata,bakinta bai mutu ba sai data wurga masa kalmar
"Wallahi wallahi sai kayi dana sanin dukan fa'iza,sai ka biya farashin duka na da kayi,zaka gani,ke kuma ku zuba mu gani" sannan ta fice.

Tabbas ba don har tanzu bai cimma qudirinsa ba akanta da yau babu abinda zai hanata kwana cikin gidan ubanta,gefensa ta zauna ta sanya hannunta cikin nashi sannnan tace
"Sam hakan ba girmanka bane ya mukhtar,tunda nake ban taba gani ka daki wani ba ma bare matarka ta aure,yin hakan ba daidai bane,na roqeka don Allah kada ka sake sai ka fara bani tsoro ai" ta qarasa fada a shagwabe,sai ya dago yana dubanta da murmushi,take kaso saba'in cikin dari na bacin ransa ya zabge ga fadi sai ya dora hannunsa shima saman nata
"Banaso ki fara jin tsoro na sumy ta,idan kika fara tsoro na na zauna da wa?,bazan sake ba,kiyi haquri" kai ta girgiza tana murmushi
"Kai ya kamata nace kayi haquri yaya ka yafe mana,yau mun sanyaka cikin bacin rai" kasa magana yayi sai ua rungumeta kawai cikin jikinsa yana jin duminya,yana ganin girma da qimar wannan halitta mau tsananin hankali da biyayya a gareshi,shikam mai zai hana shi faranta nata matuqar yana da iko?,me ya isa ya hanashi sonta a duniya?,babu shi,babu shi ko mene,koda QADDARA ce baijin tana da wannan qarfin ikon,baya fata ma QADDARAR tazo masa ta wannan sigar,gwara ta kowacce siga amma banda wannan,wala'alla ya iya jurewa.

Sai da suka fara jiyo qaurin girkinta sannan ya saketa ta miqe da hanzari ta fice tana ce masa tana zuwa.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍✍✍✍
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣7⃣

________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*ma asaba min musibatun fil'ardi wala fi anfusikum illa fi kitabim min qabli an nabra'aha*
_______________________

Cikin mintuna qalilan ta kammala jallope din taliyar ta rarraba cikin coolers,mukhtar din ta fara kaiwa,tana niyyar juyawa ta fita yace da ita
"Wannan cooler din fa na waye?" Ta dubi cooler din sannan ta dubeshi
"Na fa'ixa ne a ciki"
"Ajjiye a nan" ya fada yana gwada mata inda zata ajjiye din da idonsa,bata kawo komai cikin ranta ba ta ajjiye din ta nufi dakinta.

Can ta taddasu sun baje suna kallo,duk da cewa kallo daya zaka yiwa yahanasun kasan tabbas har yau ranta a bace yake,ta dire cooler din tana cewa
"Ga abincinku yaya" wani banzan kallo ta watsa mata
"Eh zamu ci ai kuma zamu ambaci sunan Allah,in sha Allahu babu abinda zai samemu,makira,idan ma shiga kika tsakaninmu da fa'iza har take wannan tashan rashin kunyan to ni zanyi maganinku ke da iyan baki daya" kai ta kada ba tare da tace komai ba ta shige uwar dakinta,ta tube kayanta ta sauya na bacci,sai tayi zamanta gefan gado ta janyo RIYADUL JANNAH littafin addu'o'inta da malam ya bata wanda bata rabi da shi ta soma duba wasu shafuka.

Sumayyan na fita ya dauki cooler din baki daya ya fita da ita waje,wasu almajirai da rabonsu ya rantse ya samu qofar gida zazzaune ya basu,take suka karba suka rabe a tsakaninsu suna zabga godiya banza ta faadi garesu.

Yana kammala rufe gidan sukayi karo da fa'iza wadda ta dawo daga dakin sumayya ta bankade labulenta ko kallo su ya yahanasu basu isheta ba ta qwallawa sumayya tambayar ina abincinta,tana daga cikin dakin ta gaya mata yana gun yaya mukhtar.

Dubansa tayi"ina abinci na?"banza ya bawa ajiyarta yayi wucewarsa,sai ta bishi da kallo,bata haqura ba tabi bayansa tana sake tambayarsa,wani wawan birki yaci wanda sai da ya sanyata ja da baya
"Baki daku ba kenan ko?,tare muka hada muka siyo abincin?,ko kinzo da bayi ne daga gidanku?,uban wani ne ya hanaki dafawa kici,ki fice min daga nan tun kafin na hasala na sake kikkifa miki mari" tana qunquni ta juya ta fice ranta qunci fal,ga uwar yunwar dake sakadarta,abinka da mutum mai shegen ci ta riga da ta saba.

A tsakar gida taci karo da jamila na wanke hannunta,da gayya ta bangajeta tayi taga taga ta fadi,sai ta miqe kuwa ta lailayawa fa'izar ashar abinka da itama tana ji da tata rashin kunyar,ai kuwa fa'izan tayo kanta zata huce bisa kan nata,dai dai sanda yaya yahanasu ta qaraso tayi hanzarin riqeta ta gabza mata mari dama tana ciki da ita ne,tana waiwayowa kuwa ta cakumi wuyan yaya yahanasun take jamila ta shigarwa uwarta nan fada ya kaure tsakanin su ukun.

Sumayya ce ta fara fitowa,cikin tashin hankali taje dubansu idanunta a waje,dambe da yaya yahanasu?,tab,lallai fa'iza ta kai,dakin mukhtar ta nufa da hanzari tana mamakin me ya hanashi fitowa,ga mamakinta yana tsaye bakin window yana kallonsu,saidai idanun nan sun kada sunyi jazur,a hankali ya juyo ya zuba mata su,itama sai jikinta yayi sanyi,tausayinta ya kamashi,babu shakka wata jarrabawa ce ta fado rayuwarsu,idanunta suka cika taf da qwalla ta tausayin mijin nata,sai kawai ya saki labulen ya taka a hankali ya fita tsakar gidan,wata gigitacciyar tsawa ya sakarwa fa'iza dake tsakiyarsu tana cin na jaki wadda tsawar sai data sanya hanjin sumayya hadewa ya cure guri guda,ta runtse idanunta tana jin ruguginta na ratsa kunnanta.

Nuni kawai ya yiwa fa'iza da hanyar dakinta yana mata wani irin kallo mai cike da tsana,ba musu ta wuce jikinta na rawa,ya juya ya dubi yaya yahanasu sai kawai ya kamata yayi dakin sumayya da ita.

Bakin rijiya ta zauna,sai ta kasa daurewa idanunta ya shiga fidda qwalla,wannan wacce iriyar masifa ce lokaci guda,duk wani farinciki da zaman lafiya na gidansu yayi qaura lokaci daya?,tana share hawayen idanunta tana tausayin mukhtar dinta.

Tana zaune a nan mukhtar din ya fito ya shige dakin fa'iza,a nan ne ta jiyo tashin muryarsa saidai nan din ma bata ji duka abinda yake fadi ba,daga bisani ne ya fito,ta miqe tsaye ta isa gabansa tana kallonsa,tabbas taso ace yau ranar girkinta ne,ta lallashi mukhtar din,saidai sam bata da wannan damar,karyar da kai tayi murya a tausashe tace
"Kayi haquri don Allah yaya mukhtat,komai na duniya mai wucewa ne,jarrabawa ce daga Allah" murmushin qarfin hali ya saki ya shafi gefan fuskarta
"Babu komai my sumy,kije ki kwanta,kuma ban lamunce ki sanya abun cikin ranki ba,ki kwanta kiyi bacci sosai" ya sanya bakinsa yayi kissing goshinta,sai ya bata kunya har ta dan murmusa,yana tsaye har ta wuce dakinta sannan ya juya nashi.

Ko da ta isa dakin tuni ta taras da su sun rarrashe kan gadonta,sai yaya yahanasu dake zaune gefan gadon tana huci,abinda take da buqata ta dauka zata fice taji sakin qwafar da yaya yahanasu tayi,ranar kan doguwar kujerar falo ta kwana,saidai tayi qoqari kamar yadda mukhtar ya buqace ta tayi bacci ta qoqarta tayi na 'yan awowi.

*******************
Chapter 20 · 0% Book details