← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 210

Sashe 180

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Duk data rama hakan bai hana zuciyarta suya ba,komai zai mata ya kasance su biyu,bata son ace har gaban su'ad yana yi,haka dabi'arta take ko a gidajenta na baya,sai ta fashe da kuka maimakon ta shiga bandaki yin wanka sai ta fada saman gado tana ci gaba da rusa kuka.

       Bangaren ummi ya wuce direct zai saukewa amira,taimakon da Allah yayi mata ko layin motarsu bata gama ficewa ba ya shigo neman nata
"Sun tafi yanzun nan,lafiya?" Ummi ta tambaya tana karantarshi,fushi ne taf cike a zuciyarshi da fuskarshi,batasan me ya taboshi haka ba,tunda ita bata dauki maganan hanasu tafiyan ta kai haka ba
"Ba komai...." Ya fada yana juyawa wannan karon a sanyaye ya fice,sai ta bishi da kallo kawai ta girgiza kai tana ci gaba da yin abinda take.

        Yana shiga su'ad ta taroshi,har saman dining ya zauna tana karairaya fari da karkade karkade,babban abin takaicin sai da yace
"Bani abinci" yana lumshe ido saboda yunwa da fushi,yau duka saboda bacin rai baici komai ba,zuba masa tayi ta tura gabanshi tana debo masa labaran da sam basu shafeshi ba tana masa,idan yayi loma daya sai ya jima baiyi ta biyu ba,ga surutunta da ya soma hawa masa ka,sam labarin da take bashin sake caja mishi kai yake,labarin abokanta karatunta maza da mata,duka bata lura da hakan ba bare ta sarara,rabin hankalinsa baki daya ya karkata bangaren sumayya,yana so yaji daga gareta,haka kawai ya kasa nutsuwa,baya so kuma ya shiga haqqin su'ad ya bar ta wajen hakan bai dace ba.

        Wayarta dake daki ta soma kira tana sanar mata da sunan wanda ya kirata,qawarta ce zulee,wadda idan suka soma waya tana bata labarin bayan dawowarta nijeria har sai a qalla sun kashe kusan awa,da hanzari ta miqe tace mishi tana zuwa,kai kawai ya kada yana ci gaba da tura abincin,qoqari yake ya ture tunaninta daga zuciyarshi amma ya kasa,daga qarahe dai ya tabbatar bazai iya din ba,ture plate din gabanshi yayi wanda ya sanya abincin zubewa ya miqe,kai tsaye ya durfafi dakin.

        A kwance ya cimmata kamar dazun tana fidda hawaye,taji motsin shigowarsa amma bata motsa ba,qare mata kallo yayi sannan ya sauya akalarsa zuwa bandaki,ruwan wanka ya hada mata sannan ya dawo dakin gadon ya tsaye a kanta cikin dakiya
"Tashi ki wuce kije kiyi wanka,wannan ya zama last da zan kanki kina kuka,idan ba haka ba ranki zaiyi mummunan baci" a kasalance ta miqe tana rangaji tare da qwalla ta shige bandakin,locker dinta ya jawo ya fidda magungunanta ya ajjiye,ya shiga kitchen dinta ya fiddo plate ya juye gasashshen naman daya siyo mata da shinkafa 'yar kadan a gefe guda.

       Tana yafe da qaton towel ta fito,a sanyaye ta qaraso bakin gadon ta zauna,tura mata dan table din daya saka abincin da magani yayi a kai ya juya a hankali ya fice,yayin data bishi da kallo qwalla na taruwa a idanunta.

       Cikin dare ya kasa bacci,ji yake kamar yaje ya roqeta ta bishi amma wani sashe na zuciyarshi na hanashi,a hankali ya sauka daga saman gadon,ya zura slippers dinsa ya fice bayan ya dauki wayarshi,qofar ya tura a hankali,dakin lullube yake da duhu,ya ci gaba da takawa har ciki bayan ya kunna fitilar wayarshi,har lokacin itama bacci bai dauketa ba,wani iri take ji cikin jiki da zuciyarta,tana jin shigowarshi tayi hanzari rufr idanunta tare da qara yin luf tamkar mai yin bacci,ragowar hawayen dake maqale a fuskarta ya tona asirin baccin qarya take,ya dauki wajen minti biyar yana duban kyakkyaar fuskarshi,fuskar dake sanyaya mishi rai,fuskar da duk duniya ayanzun bayan ta umminsa yana jin yafi qaunarta,don me zata guje mishi a sanda yake tsaka da tsananin buqatarta ita da abinda yake cikinta,kada dai ace har yau bata sonshi?,har yau bai cimma nasarar zama wani sashe na rayuwarta ba?,sai ya juya a hankali zuwa inda ya ajjiye mata abincin,yasa hannunshi ya bude,ba abinda ta taba aciki,ya duba magungunan ta balla ta sha duka,hankalinshi yaji ya tashi ranshi ya dugunzuma,sai ya kunna wutar dakin baki daya
"Wakeup" ya fada a taqaice,shiru tayi ita adole bacci take
"Ki tashi nace miki!", ya fada a dan tsawace,cikin hanzari ta miqe,daukan abincin yayi ya isa gabanta ya zauna suna fuskantar juna,cokali ya sanya mata ya mata alama da ido kan ta dauka taci,hannunta har rawa yake saboda yunwa,hakan ya sanya ya amshe cokalin ya soma bata a tausashe duk da fukarshi a dinke take,a hankali ta soma karba,tana ci tana satan kallonshi,saidai ko kadan yaqi ya kalleta,
"Abu abdallah"ta kirashi tana kallonshi,yana son sunan qwarai amma wannan karon sai yaqi dubanta,hakan ya karya mata zuciya ta kuma sakin kuka harda 'yar shashsheqa,sai ya ajjiye cokalin yana hade yatsunshi waje daya tare da zuba mata ido,kukanta na ratsa zuciyarshi tamkar ana yankar tsokar zuciyarshi,tsahon minti biyar sannan ya motsa bakinsa
"yanzu fisabilillahi ni me nayi miki?me ke damunki?" Ya fada murya can qasa a tausashe,wanda hakan ke nuna raunin dake cikin zuciyarshi
"Kain....ne" ta fada cikin sheshsheqa,ci gaba yayi da dubanta kafin yace
"Saboda Allah a dakeni a hanani kuka?,saboda ni ban da bakin kukan?,kinsan zafin da nakeji a qirjina?,ina tunanin har yau baki gama yarda da wacece ke cikin rayuwata ba shi yasa kike son aikata min haka,amma babu komai....Allah ne ya jarabceni kuma ina fatan ya yayemin,tunda baida amfani sanya mutum cikin zuciya,da can da ban sanya ba kinga rayuwata lafiya lau..." Bata ji dadin furucinsa ba,sai ta sake sakin kuka
"Kayi haquri don Allah"
"Zan haqura ne kadai idan kika shaidawa ummi zaki bini,ke kadai zaki fada mata ta yarda" kai ta girgiza,ba zata iya watsawa ummin qasa a ido ba,tace mata meye?,kafadanshi ya daga sannan ya miqa mata ruwa,tare da tsareta da ido,tilas ta sha ya kauda kayan ya ja mata bargo zuwa saman cinyanta ya gyara mata filo,bai sake sauraran komai ba ya kashe qwan ya ja mata qofar ya fice.

Washegari yaje kaima baba qara,saidai duka bakinsu daya da ummi,hakan ya sake jagula lissafinshi,haka ya fice jikinsa ba qwari,baki daya sai yaqi zaman gidan,ya wuni waje,yayin data wuni begen ganinshi,amma bata ga gilmawarsa ba,wuni tayi bata leqa ko ina ba tana daki akwance abinta.

Randa ta amshi girki ya rage saura kwana biyu su tafi abida ta haihu,su'ad anata rawar kai tare da shirin tafiya,jifa jifa idan sun hadu a falo tana yadawa sumayya habaicin zasu tafi banda ita,ita tana tsammamin uban tafiyar ne yace ba zata je ba,sabida tana laulayi,ko kallonta batayi bare tasan tana yi,ita ayanzun fushin almustaphan yafi komai daga mata hankali,kaf ta laluba walwalarta ta rasa,ji take kamar taje ta cewa ummin zata bishi,saidai hakan ba mai yiwuwa bane,kawai kunya mai tsanani tattare da hakan.

Ana ya gobe zasu tafi suka je yima abida barka,ta samu santalelen danta namiji tubarkallah da shi,babyn ya burge su su duka,sai taji kwadayin son ta haihu ya sake kamata,ta shafi cikinta ta cikin mayafi tana ddu'a cikin ranta,tana son taga ta tara yara da yawa,wanda ta fuskanci ra'ayin almustaphan ma kenan,su'ad kam dama bai mata tayin zuwa ba,don ko yayi mata dama bata zuwa,don ba shirin arziqi tsakaninta da abida,ta raina ajawalin abida yayin da ita kuma abidan bata daukan raini sam,bata roqa komai daga gareka ba don haka kada ka raina mutincinta,kowa ya tsaya matsayinshi,ya dauki sumayyan bayan sun biya wani katafaren shago sun mata siyayyan kayan barka masu yawa kyau tsada da kuma quality,har ita abidan sai da ya saya mata kayan fitan suna masu kyau bawai don hamza ya gaza ko bai da shi ba,kawai ya wuce komai a wajensa,ya dora musu kudin dinki dubu dari a saman kayan,tun jiya take dubanshi,duk abinda yake kawai gashinan ne babu karsashi sam tattare da shi,tana jin hamza na kwasarsa kan me ya sanyashi laushi amma yayi masa shiru bai ce masa uffan ba,shi ya tuqasu hakan ya sanya su biyu kenan suka fita,a parking space ya tsaida motar ya kasheta,sai ta kasa fita tana dubanshi kawai,bai dubeta ba ya dage gilasan motar,ya kwantar da kujerar ya miqar da bayanshi a kai,hakan ya nuna bai da niyyar fita kenan,ta jima tana dubanshi kafin tace
"Kayi haquri don Allah" ya jima shiru kafin ya bude idanunsa da suka kada
"Da kikayi me?"
"Na rashin tafiyarmu tare" ta fada tana murza yatsunta
"Ba abun damuwa bane ai tunda bake kadai bace" maganar ta soketa,ranta ya baci,kishi ya soma cinta
"Haka ne" ta fada tana dora hannunta kan mabudin motar ta bude ta fice,ta gefan ido ya bita da kallo,ya rasa yadda zaiyi controlling kanshi,bai taba damuwa da wani abu haka ba,sonta ba qaramin mamaya ya yiwa zuciyarsa ba,yana son ya daure kan rashin tafiyar tasu tare ko don abinda ke jikinta amma ya kasa,tun yanzun kewarta ke damunshi,nan yaci gaba da kwanciya,baison ya shiga ya taddata cikin rashin walwala ko kuka,hakan na tabashi,bashi ya shiga ciki ba sai sha daya na dare.

A falon qasa ya tadda su'ad sanye da kayan bacci,tsaye bakin t.v tana shan ruwa cikin gora,dubanshi tayi tana sakin murmushi,wani dadi ke ratsata a kwanakin nan,ta fuskanci kamar akwai wata a qasa tsakanin sumayyan da almustapha,bugu da qari kuma ga tafiyar da zasuyi daga ita sai shi
"Welcome" ta fada tana murmushi
"Yauwa....baki bacci ba?" Fari tayi da idanu tana cewa
"Wlh ban kammala shirina bane"dubanta yayi cikin mamaki,don bai taba ganinta cikin zumudi haka ba irin wannan lokacin,don ko tafiya ta kamasu tare wano lokaci idan tana wata sabgar saidai su raba flight ita ta biyoshi
"Ya kamata kam ki gama da wuri,don tafiyar safe ce"
"Ba damuwa ai" ta sake fadi tana faari
"Sai da safe" ya fada yana ci gaba da takawa,binsa tayi da kallo kafin tace
"Ok goodnight" ba haka taso ba,so tayi ta bata masa lokaci a nan,har sumayya ta gaji da jira taga bai shigo da wuri ba,koma tazo ta samesu tare.

Sanda ya shiga tana gaban mudubi sanye itama da kayan bacci tana gyara gashinta,kaya ne da bata taba sanyasu ba cikin kayanta,sun bala'in karbar fatarta,abinka da mai yaron ciki,ga wani kyau na musamman data ajiye,kanshi ya dauke ranshi na suya idan ya tuno gobe warhaka basa tare?,har ta kammala shirinta ta kwanta bai gama nashi ba,bacci ya soma rinjayar idanunta,cikin baccin taji ya janyota cikin jikinsa ya rungumeta tsam,shiru tayi ba tare data yi qwaqwqwaran motsi ba,saqonni ya fara aika mata kafin daga bisani su shiga babbar headquater.
Chapter 180 · 0% Book details