Sashe 101
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tafiya ta fara nisa,babu haihuwa wajen su'adah ba dalilinta,bata yi mamaki ba,don tuni ta jima da fara hadiyar qwayoyin tsaida haihuwa tun satin farko na aurensu,kusan tafi uwarta iya shege,don daga bisani ma zuwa tayi ita aka juyar da mahaifar,don tace bata ga me zata ci da haihuwa ba,ita da iyayenta suna da arziqin da basai ta nemi taimakon da ba,tunda dama don ya taimakeka kake haifarsa(a tunaninta),sam mustaphan bai san da wannan badaqalar ba ko kadan,ya dauka kawai Allah ne bai kawo ba,baya ga aikin da yakeyi yana kasuwanci sosai,wanda har yaso yafi baabaa prof qashin arziqi,cikin qanqanin lokaci dukiyarsa tayi haukatar ban mamaki,hakan ya sanyashi diban maqudan kudade ya zo nijeria,kowacce state din nan da muke da ita ciki harda abujan ya danqara asibiti,wanda idan da na private ne sai ka isa ma zaka iya zuwanshi,amma yace kyauta komai za'a dinga yi ciki,shi da kansa idan ya samu lokaci yazo nijerian yana zabar states din da yake ga zai iya zuwa ciki harda gombe wadda bai fashin zuwanta sabida tuna asali da tushe ya ziyarci a asibitocin,ya karbi cases masu girma da asibitin ya samu ya zauna yaga marasa lafiyan yayi musu abinda ya dace,asibitin abuja kuwa sati biyu yake yi yana ganin marasa lafiya kowanne iri matuqar lalurar ta shafi mata,hakan ne ya sanya kaf fadin najeria babu asibitoci mafiya inganci taimako da kula da marasa lafiya irin nasu asibitocin,girmamawa ta musamman gwamnati ta yi masa saboda taimako da gudun mawar da ya baiwa al'ummarsa.
Baya ga wannan ya gina gidan marayu,kano daya gombe daya abuja daya,gidan marayu mafi girma da baiwa marayu tallafi da kulawa a nijeria,shike daukar nauyi da dawainiyar komai nasu,yana daga can yana turo duk wani abun buqata nasu,ya sake samun bunqasar arziqinsa ne lokacin da ya zuba hannun jarinsa cikin wani company dake dubai wanda ke saqa nau'in dogayen riguna na maza da mata masu tsada da kuma masu matsakaitan kudi,daga bisani masu hannyen jarin kowa yaso janye nasa,shi ya biya kowa ya mallakin company,ya zauna tare da taimakon hamza,musaddiq lamin da usman suka sake yiwa companyn garambawul ya sake tashi a aiki,suka sauya masa suna wanda yake amfani da tambarin MM mustapha mukhtar,sai gashi ya zama company mai daraja ta daya dake sarrafa dogayen rigunan dai nau'i daban daban,kaloli daban daban,companyn na daya daga cikin zuciyar arziqin da ya mallaka.
Rayuwa ta yiwa su'adah dadi,sai yanzu take sake kallon irin gatan da mamanta tayi mata na maqalewa tare da naqalta mata auren mustapha,tana jin dadi tana alfahari ta juya a duniya tace itace matar MUHAMMAD EL-MUSTAPHA,wanda ya kasance cikin jerin sahun farko na matasan shahararrun masu arziqin da nijeria ta mallaka.
Rayuwa ta yi masa kyau,burikansa suna dab da cika,wannan karon yana yawan waiwayar nijeria,idan azumi ya kusa kamawa a nan zaizo yayi guda ashirin,goman qarshe su wuce umra shi da duk wanda Allah tsaga da rabonsa ko wanda baabaan shima ya biyawa,duk shekara bai dauke sunan ummensa babanshi da anty maamaa,sai autarsu sumayyatul amirah,shike biya musu,bai yadda suyi amfani da kudinsu wajen biyawa kansu ba saidai wanda suka ga dama cikin 'ya'ya dangi ko surukai,idan ta rayawa su'adah tace zata bismillah,idan kuma 'yan abun basa kusa taqi zuwa,wani lokaci da taje can ta gwammace ta siyawa kanta da qawayenta tikiti na maquden kudade su tafi kallon wani wasan a can wani shahararren gun kallon wasa duk inda yake a duniya saidai idan ba'a ginashi ba,hakanne ya sanya take matuqar qawance da qasar DUBAI,daga bisani Allah ya hukunta mustaphan aikinsa ya dawo dubai din,hakan ya masa dadi saboda yayi masa kusa da company dinsa,duk da dama bai da damuwa yana da abokai masu kama da 'yan uwa dake kula da shi,kasancewar dukkansu basu kai budin mustaphan ba,sai dubai ta sake zamewa su'ad din gida,tana iya baro karatunta ta taho dubai din takanas kallon film ko wani wasan,daga nan ta shargalle agun mustaphan idan taga dama ta wuce,hakan ya sanya karatun nata ke kwan gaba kwan baya,har yau yaqi ya qare.
Sukan dawo daga umra ranar sallar,daga nan idan baijin gajiya zai sake hawa jirgi a washegari ya taho rano wajen kakanninsa,da shi ake hawan sallah,abun na qayatar da shi,kusan tawagarsa daban take,duk sanda zai wuce sai ya ja hankalin mutane saboda kwalliyarsu daban take,bayan ya gama hawan sallah sannan ya dawo ya koma kan ayyukanshi,haka rayuwarsa take,kusan baida wani lokaci na banza a rayuwarsa,duk daqiqa daya mai amfani ce a wajensa,yana tafiyar da ita wajen ayyukanshi,hakan bai damu su'adah na wai bata samu cikakkiyar kulawa ba,arziqi dukiya da rayuwa mai aji da tsada take buri kuma ta samu,buqata ce idan ta taso mata duk inda yake zata siyi ticket ta bishi ta fansheta ta dawo.
Hakanne yasa a hankali qannensa mata suka fara lura da irin rayuwar da yayansu yake,rayuwa ce mai kama data gauro,bai da wata mace a gefansa da zai dafa ta aduk sanda wani abu ya taso masa na gaggawa,bashi da wata mace dake tare da shi kullu yaumin da zata tsara masa lamuransa,lokutansa da rayuwarsa,ko da yaushe yana cikin aiki,aiki dai,shi yana gabas kasuwanci da aiki matarsa tana yamma karatu,sam baida wani family da zai nuna nashi kamar yadda sauran 'yan uwansa ke da shi.
Misali: babban wansu adam a yanzu haka yana da matan aure biyu,ta farko na'imah Allah bai bata haihuwa ba ya sake aure ya auri fahriyya,yanzun haka yana fa yara hudu,biyu maza biyu mata,yana aiki a legos cikin shima nashi company na qashin kansa,yana zuwa gida da su baki daya idan ya faru ko kuma daya tazo a bar daya a can,qanwarsa farida tayi aure,tana da yara uku,mai bi mata huda itama tayi aure yaranta biyu,mahmoud ya kammala karatunsa,yana juya dukiyar baabaa prof shi da dan uwansa usama,baaban baya komai sai kula da gidan gonan sulensa,har yau sule yana ranshi yana saka ran haduwarsu kafin mutuwa da ruski dayansu,gidan gonan da zuwa lokacin yayi rassa jahohi daban daban har nan abujar,duk da cewa usama akwai sauran nauyin karatu a kansa da bai kammala ba,amma daga can inda yake yana kasuwancin,thailand ne,shi da mahmoud din ke shigo da kayan su rarrabawa 'yan kasuwa,kowannensu ya fidda macen aure,lokaci kawai ake jira,sosai baabaa yaga alfanun yiwa yaran nasa sashensu,don ya zame musu tamkar mahada ko masauki duk sanda suka baro wajajensu kowa nada bangarensa da zaya sauka cikin gidan kusa da babansu,akan ga kowa a gida akai akai amma ganin mustapha yakan zama aiki,balle madam din nasa,wadda lokacin bikin sallah ne take biyoshi don ta san cewa gidan nasu kan kasance cikin baqi 'yammata da samari,takan biyoshi ne ta kasa ta tsare,abinda har yau bata sani ba kenan halayyar mijinta,itace shaida ta farko da zata fadi kan mustapha baida idanuwan kallon mata baki daya,amma ita sai take ganin hakan isarta ce tasa har yau ita kadai yake gani,ta sani cewa mustaphan nata irin mazan nan ne dake tsada,mazan da mata ke marmarin samu,ba wai saboda tsurar kyau kawai ba,a'ah,kwarjini haiba kamala da cikar zati da halitta,ita kanta ta tabbata Allah ne kawai ya kashe ya bata,tana sane da yadda ake farautar mustaphan,kama daga yammata kyawawa masu taqama da kyau da arziqi irin nata ko fiye da natan ma,zuwa manyan hajiyoyi masu juya naira,abun yakan bashi mamaki ganin yadda mata ke farautar d'a namiji,yakan jima yana jinjina lamarin,wasu na roqon aure ya hadasu,yayin da wasu ke roqo ko da harkar banza yazo suyi,son so ace yadda haduwar mustaphan take baida komai,da sun yaudareshi koda da dukiya ce,saidai kash,sai suka sameshi da arziqin da zai iya daukar nauyin danginsu ma baki daya.
Sirrin samuwar nasararsa ta ta'allaqa ne ga biyayya da tsananin kyautatawa iyaye,bai iya tsallake umarninsu,uwa uba kuma tausayi da taimako.
Wannan shine familyn baabaa prof.
TOFA ADDU'RKU TACI,YAUMA NA KUMA KO?
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[1/20, 10:03 AM] +234 807 885 3729: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
6⃣6⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*Allah s w t yana cewa*
*HAQIQA SAI NA CIKA JAHANNAMA DA MUTANE DA ALJANU BAKI DAYA*
*Ya Allah ka yi mana tsari,ka suturta mu*
__________________________________
"Wannan shine cikakken tarihin familyn baabaa sumayya,na tabbata zuwa yanzu kin fahimci komai" murmushi sumayyan keyi tana gyada kai,sosai labarin asalin zuriyyar ya burgeta ya qayatar da ita,very interesting,ta tsinci darussan masu yawa a ciki,sunyi gadon karamci mutunci da halacci,qasan ranta take raya amma shi kam bata san inda ya tsinto nashi halayyar ba,tana masa duban mutumin da bai girmama mutuntaka ta dan adam,mutum mara saurin fahimta da dogon tsinkaye da bada hanzari
"Wa kenan"ta tsinci muryar anty dije na tambayarta
"Na'am"sumayya ta waiwayo da hanzari tana tambayarta,don bata tsammaci da ita take ba
"Idan na canka dai dai mustapha kike wa wannan yankan hanzarin ko?" Da sauri ta kada kai
"Ko kadan,me kika ji nace?" Murmushi antyn tayi ganin tana son musanta mata,cikin sigar tsokana tace
"Kiyi dai a hankali,kada kema ki fada tarkonshi,naga ba wuya 'yammata sun zurma cikin komarsa" wata matsananciyar faduwa gabanta yayi,kai ta soma kadawa
"Allah ya sawwaqe anty,ya rufamin asiri duniya da lahira,yanzu kyamin wannan fatan haba anty?,na kai su'adah ina,baya ga haka ma wallahi baiyimin ba ko kadan,banga abun burgewar ba anan wajen" dariya antyn tayi sosai har su laila dake sit din gaba suka waiwayo suna dubanta sai data ce su juya
"Dukka yadda akayi kallon tsoro kika yi masa,kece mutum ta farko da naji kin ambaci haka,ko minal dake da qarancin shekaru cemin take,mami uncle man yana da kyau kamar na 'yan india,ta yaya ma zaki gane shi bayan kallon mukhtar kika yi masa ba ainihin kamarsa kika gani ba,kuma ma meye na saurin rantsuwar baiyi miki ba?,kika san inda rana zata fadi?"
"A inda ta saba faduwa mana anty,komai kyansa bazan gane ba anty daga kan mukhtar an gama namiji" ta qarashe zancan fuskarta na nuna rauni da karaya da zuciyarta tayi,hakan ya sanya antyn yin shiru,yayin da itama tayi shirun tana maida numfashi tare da hadiye yawu da qyar.
Kai ta girgiza bayan ta gama wassafa ta yaya zata zauna zaman aure da wani bayan mukhtar din,sam,ji take ba zata iya ba,babu wannan mafarkin cikin rayuwarta,kamar soyayyar da take nuna masa bata cika ba kenan.