← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 210

Sashe 84

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farar mace wadda a qalla za'a kira da mai matsakaitan shekaru wanda hutu da tsabta suka kwakwashe shekarunta suka boye,a zahiri ta tasamma shekara hamsin da uku amma kai baka ce haka ba,fara ce tas kamar yadda nace a baya wanda har wani yellow takeyi,kallon farko zaka san cewa zamanin quruciya an kasa maza da yawa a kanta,akwai kyau da kansa zaune a fuskarta,duk da shekarun da take da su amma basu ci nasarar boye kyawun nata ba wanda hakan ke nuna na asali ne ko kuma ace na gado ne,tana da matsakaicin tsaho yayin da jikinta ke a murje,sam babu rama ko qiba tattare da ita,fuskarta a sake take saukowa daga saman tana sanye da jar atamfa da ta haskata dinkin riga da plain zani
"Ummee ina kwana" murmushi ta saki har sai da fararen haqoranta suka bayyana
"Ina kwana ko ina wuni khalipha sarkin shirme,ku zauna mana sai mu gaisa ko?,baquwa mukayi" an aosa masa inda ke masa qaiqayi
"Eh yayarmu ce muka taho da ita ummee,itama ta dawo nan ta zama 'yar gidanmu" dariya sosai ya bawa ummeen duk da kasancewarta mara son hayaniya,gu ta samu ta zauna,hakan ya sanya sumayya dake qame gu daya ta qaraso a hankali kanta a qasa ta samu gefan kujera ta zauna,hakanan take jin matar ta mata wani kwarjini da girma
"A'ah tashi baquwa ki koma saman kujera... Me sunanta khalipha?"
"Anty sumayya"
"Tashi sumayya ki koma sama" kai ta girgiza don ta qagu ta koma gida
"Yanzu zamu koma laila muka zo dubawa anty taji shiru" ta fada sannan ta soma gaidata,amsawa tayi tana cewa
"Na tsammaci ai ta koma tun dazun data kawomin aiken ta fita,amma ba mamaki suna wajen maamaa bilkisu,don nayi hayaniyan yaran gunta"
"To sai anjima" ta fada tana miqewa
"Yauwa rakata khalipha wajen maaamaanku,ki yiwa khadijan godiya naga sautu sunyi kyau"
"To zataji" ta fada suna nufar qofar fita daga bangaren nata,saidai kafin sukai ta shigo,budurwar rannan ce sanye take da gown mara nauyi wadda take armless bata da hannu,sai siririn mayafi data yane tulin tsefaffen gashin kanta da shi ,kumatunta duka biyun da hannunta jagale suke da wani abu kamar butter,sallama tayi tana dariya idanunta a kan ummee dake dubanta itama,harara ta watsa mata
"Da kyau,sannu shugabar masu shiririta,shine kika dora mishi girki sannan kika tafi kika tara yara kuna wani birthday din shirme,to sai ki wuce ki duba Allah yasa ya qone,wallahi ya shigo kada ma ki dosheni don baxan qwaceki ba a hannunshi" idanuwa ta qwalalo cike da tsoro,sannan ta kwashi sauri ta nufi hanyar kitchen din fuska a kwabe kamar zatayi kuka tana cewa
"Wayyo ummee na banu don Allah kada kicemin girkin ya qone"
"Ke kika sani" ummin ta fada.

Shikam khalipha fuska ya bata bayan sun fito
"Ina ga yau bithday din siddiqa shi yasa ma anty laila taqi dawowa gida tunda aka aiketa,tunda naga anty amira ma nasam da qyar idan ba yau bane,dama tun kafin mu tafi kano anty amira tace an kusa,wayyo mami duk ita ta hanamu zuwa" ya qarashe kamar zaiyi kuka,itakam sumayya bata ce komai ba,duban hanya take ganin sun nufi wani sashen na daban.

Tun kafin su shiga ta tabbatar akwai banbanci tsakanin waccen sashen da wannan,tun a qofa ta fara jiyo hayaniya da ifce ifcen yara,da banbancin kam,don wannan falon cike yake da yara sun kusa su goma sha biyu,qananu da matsakaita,baki dayansu sanye suke da gown suma mara hannu,dukkan rigunan irin daya ne,hatta safunan qafafunsu(socks)iri daya ne,yaran sunyi kyau gwanin sha'awa,tsakiyar falon qaton cake ne wanda suka dora kan center suna ta wadaqarsu da shi,da alamu shi ya bata jikin budurwar data gani dazu,kusan ba wanda yaji sallamarsu sai wata mata dake tsaye daura da su tana kallonsu idan zasuyi ba dai dai ba ta gyara musu,ita ta juyo murmushi dauke a fuskarta tana amsa musu sallamar idanuwanta kan sumayya,gaidata tayi tana duban laila da ta nufo gun saboda taga shigowarsu
"Wuce muje" sumayya ta fada tana mai juyawa tare da cewa sai anjima tasa laila a gaba.

Daf da zasu fice taji matar na fadi cikin daga murya
"kuyi maza ku kwashe kayayyakinku zansa a gyara gurin kada uncle ya shigo ya tadda wajen haka...." Bata qarasa jin me suke cewa ba don sun fice.

Suna gab da fita daga gidan baba halliru cikin gaggawa ya budewa motar wadda aketa faman danna horn kamar za'a tashi unguwar,baqar motace wadda ke dauke da baqaqen glass baqi wanda har baka iya hango wanda ke ciki ta danno cikin gidan a guje wanda badan grass carfet dake harabar gidan ba da anga tashin qura
"Hmmm,gata nan ta dawo Allah yasa an tashi ma" laila ta fada tana hararar motar sanda suke qoqarin fita
"Anty su'ad ko?" Inji khalipha ya tambaya yana kallon laila tare da tabe bakinsa
"Itace mana,nifa shi yasa idan tana garin bana son shiga gidan baabaa wallahi anty sumayya" ta fadi tana duban sumayya tana son bata labari,saidai hararar ta sumayyan tayi
"Ke kam laila ke da khalipha bansan wanda yafi wani surutu ba wallahi"
"Wallahi ya fini" inji laila tana dariya,take musu ya sarqe tsakaninsu da khaliphan har suka qarasa cikin gidan.

Shigarta ta tadda wayar gidan nata faman ruri anty dije na kuma saukowa da alama fitowarta kenan daga wankan
"Qarar wayar nan ce ta isheni,tunda kika fita aka dinga kira,hafiz ya daga akace ke nema ya gaya musu baki kusa amma basu daina kira ba,don Allah jeki daga ko kunnuwanmu sa huta" bata fuska tayi ranta na baci,jikinta ya bata mai kiran jiya ne wanda ya kira kansa da alqasim
"Ni wa na sani anty da zai kirani da lambar wayar gidanku,na gaya musu bani bace amma anqi daina kira"
"To amma ya akayi haka?,shikenan....bari na daga na musu bayani" antyn ta fada tana nufar kitchen,sai sumayyan tayi saurin barin falon ta shige dakinta haushinsa na kamata,haka kawai don musiba yana son ya zame mata jarfa,ta bar kanon amma don ta samu hutu ta nutsu amma bata samu nutsuwar ba,ina dalili,su qarke qalau da anty dijen.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[1/8, 8:18 AM] ‪+234 807 885 3729‬: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wallahi tallahi billahil azim duk wanda baibi Allah ba ya shiga uku,duk wanda baiji tsoron Allah ba ya kade,duk wanda tsoron Allah bai hanashi bin son zuciyarsa ba yana cikin babbar musiba,dan adam ba kowa bane hakanan ba komai bane shi,kaji tsoron ubangijinka kayi biyayya a gareshi KAJI TSORON AZABARSA KAYI KWADAYIN RAHAMARSA sai ka samu rabauta,ka guji duk wani abu mara kyau,kayi riqo da kyawawan ayyuka, 'YAR UWA,KI KARANTA YADDA UBANGIJI DA MA'AIKI SUKA WASSAFA MANA JAHANNAMA,ALLAH KAYI MANA TSARI DA ITA BADON HALAYENMU BA,KADA KA NUNA MANA ITA KO NA QIFTAWAR IDO NE,KA BAMU IKON YIN BIYAYYA A GAREKA,KA KADE MANA ZUKATANMU DAGA TUNANI KO AIKATA DUK WANI SABO KO ZALUNCI*

______________________________________

       Kwanaki nata tafiya,tun tana a takure da zaman garin har tazo ta fara sakin jiki,abu daya ke damunta kewar abdallah,tausayinsa take hakanam tausayinsa ya ninku a zuciyarta tun daga randa ya rasa mahaifinsa,kullum takan kira a bata shi su gaisa susha hirarsu,abinda ya sake kwantar mata da hankali a nan ba inda take zuwa bare ta gamu da wani yace mata yana sonta,hakanan kiran waya ma da ake ana nemanta tun ranar da anty dije tayi magana aka samu sauqim kiran,sai jifa jifa shi din ma ba dagawa take ba,abdur rahman ne kadai ke kiranta su sha hirarsu har ta riga da ta saba,babu wata rana da zata fito ta fadi bai kirata ba,ta sake sosai don bai qara yi mata wata magana daban ba banda ta zumunci,anty dije tayi ta mata tsiyar batasan muguwar kifin rijiya bace ita sai yanzu,bata son zuwa ko ina,ko gidan baabaa prof shigarta biyu kwata kwata shima da dalili na farkon kiran laila da taje,na biyu kuma da sumayyan tayi dambu gidan ba yara ta sata ta kaiwa anty maamaa da yake ita mai son dambu ce,kota shiga din ma bata wuce minti biyar ko goma ta fito,hakan ya sanya anty dije ta bada sautun kayan turare da humra aka kawowa sumayyan ta soma yi a nan,cikin designers kwalabe take zubawa,nan take kuwa ta soma ciniki,duk da wani gu ake kaiwa,'yan unguwar ne kawai ki zuwa siya cikin gida.

      Yau ma kamar kullum babu yara a gidan suna makaranta,gab suke da fara jarabawa ayi musu hutu saboda gabatowar wata mai alfarma na azumin watan ramadan,suna zaune da anty dije a kitchen tana anty dijen ke girki yau sumayya na ganin yadda take yi din don bata iya irinsa ba,iya zamanta da anty dijen ta qaru da abubuwa da dama ta fannin zamantakewar gida,girki iri iri,gyaran jiki da kuma uwa uba iya gayu,wayarta anty dijen ta daga wadda ta fara ruri ta kara a kunne,ganin haka sumayya ta karbi yankan cabbage din da takeyi taci gaba,sai data gama sannan ta dubi sumayyan
"Sumayya,inaga fa ke zaki miqawa anty maamaa humrar nan,kaya take hadawa kuma kinga yaran basu dawo ba" kasaqe tayi,sarai anty dijen ta gane bata son zuwa ne,bata san me yasa bata qaunar shiga gidan ba amma sai ta shareta,ta gane mai anty dijen ke nufi tilas ta miqe tace to,dakinta ta shiga ta sanya dogon hijabinta har qasa sannan ta jawo ledar data jera humrorin wadda anty maamaa ta bata tayi mata,saboda umrar azumi da zasu tafi ita da maigidan da kuma ummee,sai babban yaron gidan shi da matansa biyu sai qaninsa da tashi matar,sai manyan jikokin gidan su biyar duk da basu wuce shekara sha hudu zuwa qasa ba,duk laila aku(sunan da idan taso take kiranta da shi kenan kusamman idan tayi hali ) ke bata wannan labarin tunda ita ba shiga take ba ballantana ta sani.

       Kamar kullum a hankali ta dinga ratsa gidan bayan sun gaisa da mai gadin dake gadin wannan qofar sa suke shigowa da yake akwai wata qofar ta baya,mutumin ya haifeta shi yasa take ganin girmansa,mutum me mai faran faran da son jama'a,duk da ganinsa da sumayyan baifi uku ba amma yana yabawa hankalinta yadda take rusunawa ta gaidashi,duk da yasan iyalan gidan alhj umar farouq ba baya bane wajen tarbiyya.
Chapter 84 · 0% Book details