← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 210

Sashe 67

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turus tayi bakin qofar ragowar sallamarta ta koma ciki,da hanzari ta juya tana mai neman fita,cikin zafin nama ya sha gabanta wanda saura kadan jikinsu ya hadu,sai ta ja baya tana dubansa,mukhtar ne sanye da dinkim shadda ruwan sararin samaniya babu hula kansa,ta masa kyau sosai saidai ramar da yayi ta bayyana,hancinta ya cika da qamshin turarensa ya dinga tuna mata baya,saboda haka da sauri tace
" matsamin na wuce"
"Babu inda zakije sumayya yau sai kince wani abu game da ni,kin yafe min ko baki yafemin ba,sumayya ya ina kike so na dora raina?,laifi ne na aikatashi na nemi afuwarki sumayya amma kinqi kice komai,kinsan kullum ya nake kwana ya nake tashi da rashin cewa komanki?,kinsan me nakeji cikin qirji na" sai kuma ya sassauta murya cikin sanyi
"Kinfi kowa sanin wane mukhtar sumayya,kinfi kowa sanin wane irin zama mukayi a baya,sumayya ki tausaya min koda ba zaki tausayamin ba ki tausayawa abdallah,abdallah ya zama marayan qarfi da yaji,abdallah na buqatar mu ni da ke a tare,idan baki tausayawa mana ba sumayya waye zaiji tausayinmu duk duniya?,taba qirjina sumayya kiji" ya fada yana fincikar hannunta zuwa qirjinsa,sosai taji zuciyarsa na bugawa,gaza cire hannunta tayi sai da taji ya ambaci wash,da sauri ta dubeshi sai taga yana dafe da kansa yana layi,batasan sanda ta riqeshi ba a rude tana cewa lafiya?,ganin yana neman gun zama ya sanya ta zaunar da shi tana masa sannu,tsahon mintina biyar sannan ya sauke numfashi ya gyara zamansa tana zaune can nesa da shi ya dubeta
"Ciwon kai nake fama da shi,amma wannan duka ba damuwata bace burina kawai ki yafemin" ya fada yana duban qwayar idanunta,a hankali ta janye idanuwanta zuciyarta na mata bitar waye mukhtar agurinta,
"Na yafe maka" ta furta murya can qasa
"Allah ya yafe mana baki daya" wani wawar ajiyar zuciya ya saki,baki daya jikinsa ya saki,wani farinciki yaji yana ratsa kowacce gaba ta jikinsa,yana so yaje ga sumayyan amma sam jikinsa babu qwari ko kadan,sai ya miqa mata hannu
"Taso sumayya kizo kusa da ni don Allah" sai ta girgiza kai ba tare data motsa ba,tilas ya tattaro duk wani ragowar qarfinsa ya kiqe ya isa gareta,kusa da ita ya zauna har tana gogar kafadarta,hakan ne ya sanyata ta janye da sauri tana hada rai
"Meye haka,don nace na yafe maka ai hakan ba yana nufin kai mijina bane ko zan sakw aurenka ba" da sauri ya sake matsawa kusa da ita babu gun matsawa a gunta don ya kaita qarshen kujerar sai ya kama hannunta ya matse cikin nashi
"Sumayya,na sake miki wani laifin don na bada sadakinki,amma bisa sharadin matsawar baki amince ba zan karbi kaya na na haqura"
Wani abu taji yana ratsa zuciyarta mai kama da farinciki,zuciyarta ta karye hawaye ya biyo kuncinta,cikin raunanniyar murya ta kwabe fuskarta
"Ni nace maka ka kai sadakina ba tare da sani na ba?,ai kuwa sai kaje ka karbi abinka don ni ban amince ba,kuma......" Bata ankara ba ya hade bakinsu waje daya wanda hakan yayi sanadiyyar katsewar maganarta,sun dauki kusan minti goma a haka sannan ya janye yana dubanta,qasa tayi da kanta kan fuskarta qaramin murmushi na fita a fuskarta
"Magana ta qare,na sanki tun ba yau ba,dukkan abinda zaki fada a yanzun nasan aji ne kawai za'a jamin ko ba haka ba" sake hade fuska tayi kamar gaske
"Nidai na fada kaje ka karbi sadakinka,bana yi"
"Ok to bari na kira ya abbakar na sanar masa" ya fada yana fiddo wayarsa daga aljihun gaban rigarsa,ganin da gaske lambar ya abbakar yake nemowa ya sanyata qwace wayar
"A'ah,ki bani mana na isar mishi da saqonki"
"Ni bance ba" ta fada a shagwabe,sai yayi jagale yana kallonta saboda tuna masa da baya da tayi ta salon yanayin maganar da tayi
"Kada ki hanani fa tafiya gida yau na kwana a nan"
"Bismillah mana ai ga guri nan" sai yayi kalar tausayi yana dubanta
"Yaushe za'a tara shaidu sumayya ki koma dakinki" idanu ta juya ta dan murguda baki
"Sai shekara iwar haka" qirjinsa ya dafe yana kallonta
"Mutuwa kike so nayi kafin lokacin sannan ko?" Rai ta hade
"Ka daina fadin haka mana ya mukhtar,ni kunya nake ji gaskiya ka bari idan ja shirya zan fada maka ka sanarwa ya abbakar" hannunta wanda ke cikin nashi ya sumbata yana fadin
"Na gode,na gode,na gode sumayya,na gode da karamcin da kika nuna min a rayuwa,na gode da kika nuna ke mai qaunata ce har yanzu" sai ya dakata yana fidda zoben azurfan dake yatsansa ya zura a nata,ya mata yawa hakan ya basu dariya baki dayansu,sai ya cire ya sanya mata a yatsan tsakiya duk da haka ya mata yawa
"Ina son zoben nan sumayy,amma sai naga yafi kyau a hannunki,ki ajiyemin zan karba"
"Idan kuma naji dadinsa bazan maida maka ba"
Dariya ya danyi sannan yace
"Babu komai,ai da kai da kaya duka mallakar wuya ne" sallamar halima ta sanya sumayya miqewa,shigowa tayi dauke da abdallah tana fadin
"Wallahi yaron nan ya koyi rigima,tunda ya tashi yaje zunduma ihu nayi tsammani ma kin jiyo shi"
"Ina zata jiyoshi ta shiga kogin qauna" mukhtar ya fada cikin salon zolaya yana miqa hannu ya amshi abdallah dake ta dokin zuwa gunsa yana kiran abba na,murmushi halima tayi tana yiwa sumayya kallon tsokana ta fice,ita kanta wani dadi taji don babu wanda yaji dadin rabuwarta da mukhtar,qafarta har qaiqayi take taje ta bawa zainab labari.

'Yar kallo sumayya ta koma sanda mukhtar suka soma wasa da abdallah,bata taba ganin d'a da uba irin haka ba,sai wajen qarfe goma ya fito zai tafi,qin tafiya yayi har sai data masa rakiya bakin mota,har ya shiga ya fito ya sake kallonta
"Ban son tafiya sumayya,banqi ace tare da ke zan tafi ba,don Allah ki taimaka ki gama shirye shiryen da duk zaki da wuri,ni na amince ma duk abinda baki qarasa ba ki qarasa shi a gida na zan baki wannan damar,ji nake kamar lokaci na qure mana" murmushi tayi tana jin maganar tasa na sauka sosai cikin zuciyarta
"Kada ka damu ya mukhtar,ka qarasa gida dare yanayi" ta fada tana taka masa,sai da yaja motar ya bar layin sannan ta koma cikin gida.

******* ******* ******

Cikin abinda bai gaza sati biyu ba mukhtar ya sabunta soyayyarsa baki daya,kullum yana tare da ita idan baizo ba kuwa ranar katin waya zaici ubanshi,har tsokanarta su halima sukeyi,wai sai kace wasu masu auren fari,ya dawo mata ya mukhtar dinta sak,sai ta samu kanta da dokanta wajen ganin ta a gidanta cikin sabuwar rayuwa ita da mukhtar dinta da yaronta.

Sati na zagayowa aka maida auren sumayya da mukhtar karo na biyu ranar jum'a bayan an sauko daga masallaci,a ranar mukhtar ya matsanta mata sai ta sanya ranar tariya,sati biyu tace ya tuburr mata kan ya masa yawa,tilas ta haqura ta maida shi sati dayan,don dama tana jiran aiken da anty dije tace zata yi mata nan da kwana goma.

******* ******** *******

Juma'a asabar lahadi litinin kwana hudu da mai da auren ran litinin mukhtar yace ta shirya da daddare zata masa rakiya zai yi siyayyar kayan da yake son sauyawa cikin gidan,mama ta sanar,Allah ya tsare sai kun dawo abinda maman tace kenan.

Tana idar da sallar magariba ta soma shiryawa,kwalliya tayi wadda rabonta da yin kwalliya irinta har ta manta,tsaf ta shirya cikin material na one million stone peach ne da adon mint green,fitted gown aka mata da shi,ya masifar yi mata kyau,zainab ke dubanta tana cewa
"Kai yaya sumayya,sai kace zaki dinner,ai kya bari sai nan da kwana hudu wannan kwalliyar,karfa ki sanya ya mukhtar yaqi maidoki" daquwa sumayya tayi mata tana cewa
"Ni sa'arki ce,naga alama kin soma rainani" dariya ta sanya
"Yi haquri yayanmu,amma dai ba hijabi zaki sanya ba ko?,naga kina da mayafi kalar kayan"
"Kyaji da shi" sumayyan ta fada tana feshe jikinta da turaruka,ita kanta tasan cewa tayi kyau,sai da tazo fitowa sai taji kunyar wuce mama a haka,da qyar ta fice kanta na sunkuye mama bayan ta barwa zainab abdallah wanda yau yayi baccin wuri.

Baki kawai mukhtar ya saki yana kallonta har sai data hure masa idanu,dariya sukayi baki daya
"Ki amince kawai yau mu wuce gida my sumy"kicin kicin tayi
" amma dai unguwa kawai kace zan raka ko?"murmushi ya saki
"Afuwa ranki shi dade,na tuna,muje" suna tafe yana tuqi amma baki daya ya wani narke mata bini bini ya kalleta har suka isa gun ya kashe motar ya zuba mata ido ba tare da ya fita ba
"Sumayya,ina jin wata sabuwar qauna taki na dasuwa cikim zuciya ta,da ace a yanzu ne wani ya aureki mutuwa zanyi wallahi,ina sonki sumayya ina fata mu kasance tare har ABADAN" murmushi ta saki tana kada kai
"Nima ina fatan haka ya mukhtar"
Sai da ya sumbaci goshinta sannan ya bude motar suka fita.

Kayayyakin amfanin gida suka siya sosai,harda kayan kitchen sai da ya siya wasu abubuwa daga ciki,motarsa ta cinye kayan a ciki aka zuba masa sannan suka fito,sake tsayawa yayi a wani gu da saida kayab qwalam da maqulashe ya sayi kaji biyu gasassu da ice cream,sai damammiyar fura ya dawo ya tada motar yana dubanta,hira suke qasa qasa duk ya wani sukurkuce,wani kallo yake jifanta da shi,sai taga ya dauke kan motar ya sauya hanya,shuru tayi ta kasa tambayarsa hakanan sai ta biye masa har suka isa qofar gidansu,gidanta ne a da wanda a yanzu ma ya sake zama mallakinta
"Bismillah muje ciki ko?"
"Ya mukhtar na bar abdallah a gida fa"
"Babu komai,minti talatin kawai ina son ganinki ne sumayya" nan ma bata ce komai ba ta fita suka shiga gidan,tayi mamakim ganin komai a tsaftace a killace,bai tsaya ko ina ba sai dakin gadonsa,ya dubeta sanda yake cirw hularsa tare da tattare hannun rigarsa
"Nasan bakiyi sallar isha'i ba ki daura alwala muyi sallah sai mu wuce ko?" Cikin shagwaba tace masa
"Wai nikam bansan gaggawar me kake ba ya mukhtar,saura kwana hudu fa na dawo gidan baki daya" murmushi kawai yayi bai amsa mata ba ya shiga bandakin.
Chapter 67 · 0% Book details