← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 210

Sashe 91

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Tunda ta tako daga sashen anty maaman ya zuba mata idanu,haske gidan kadai ya wadatar masa ya gane wace ita,mahmoud da ya gaji da yi masa magana ya dafa kafadarsa wanda hakan ya sanyashi daga kai da sauri yana dubansa
"Mahmoud,sumayya ta nake gani a gidanku" waiwayawa yayi zuwa inda yaga alqasim din na kalla,tabbas sumayya ce ke tahowa
"Wannan sumayyan ce sumayyarka dama?"
"Wallahi itace" alqasim ya fada a rude,dariya mahmoud ya saki
"Ai tazo gidan sauqi,amma fa ba abune mai sauqi ba shawo kanta haka na fuskanta"
"Please mahmoud" alqasim ya fada cikin damuwa yana hade hannayensa ganin sumayyan na gab da su
"Don't mind"mahmoud ya furta yana waiwayawa yadda zata iya ganinsa idan ta qaraso,sam bata lura sa su ba duk da hasken da ya wadatar da gidan tamkar raba,hanakalinta na gefe can inda wasu 'yammata ke zaune suna hira,kusan basu suka dauki hankalinta ba ma yaran dake wasansu kusa da su ne,wanda daya daga cikinsu keta kiran abbanaa da alama labarin abban nasu yake basu,tana ganin sa'o'in abdallah a ciki,cikin ranta ta raya suna cikin farinciki da gata,sabanin abdallah da take fatan zai tashi cikin farinciki saidai baisan dadin uba ba,qwalla ta taru idonta sai tayi hanzarin sadda kai da qara sauri a tafiyarta don ficewa daga gidan,tun jiya ranta a jagule yake,hakanan ta wuni da tunaninsa cikin ranta,wanda ya haddasa mata kasala da mutuwar jiki wunin baki daya,shi ya qara mata qyuyar fitowa waje
"Yi a hankali kada ki fadi" mahmoud ya fada yana dubanta,cak ta tsaya tana dubanshi tare da qaqaro murmushi
"Hala sauri ake a fice daga gidan namu"dariya ma yaso bata saidai bata yin ba sai murmushi saboda damuwar da zuciyarta ta shiga daga tuna mukhtar
" kadai camfani"
"Ko kadan,to daina saurin,ga baqo kinyi,yanata nemanki wata da watanni sai yau Allah ya qaddara haduwarku" a zabure kamar wadda ta yiwa sarki qarya ta daga kai,suka hada idanuwa da alqasim,farinciki yake ji sosai cikin ransa,takowa yayi gefanta yana dubanta
"Zakaran da Allah ya nufa da cara sumayya,mai yiwuwa Allah ya qaddara wani lamari ne mai girma tsakaninmu,shi yasa ya kado hankalina abuja gidansu abokina mahmoud,ashe rabon na ganki ne" ba shakka tana ganin girma da qimar mahmoud,tunda shi ya soma tsaidata,banda haka da tuni ta yankawa alqasim warning cikin daqiqun nan tare da kaucewa.

        Saye yake da quater zip sweater mai dogon hannu ta kamfanin armani maroon colour saboda sanyin da ya soma busawa sakamakon hadarin da ya hadu dazu bai zub da ruwa ba sai ya bada sanyi wa garin baki daya,wandon jeans baqi,sai high top sneakers,hannayensa saye cikin aljihun wandonsa ya fito zuwa harabar gidan yana duddubawa,kusan al'adarsa ce wannan a lokaci irin wannan,kafin yaje ya kwanta sai ya dudduba ko ina saboda baqin dake gidan,ya tabbatar babu yarinyar data fita yawo balle akai ga zuwan saurayi zance gidan,yace duk mai buqatar hakan ta bari idan ta koma gidansu tayi abinda taga ya mata amma ba cikin gidansu ba,tsarin ya yiwa baabaa prof saboda haka baice komai ba,a irin hakan wasu daga 'yammatan wadanda suke zaton wayewa ce garesu,iliminsu da gogewarsu ta kai wani mizani,sukan fita ciye ciye ko siyayya da samarinsu,wani lokaci sukan kai goma ko tara na dare basu dawo ba,yayin da wasu sukan maida harabar gidan filin baje kolin gayyatar saurayi suyi zance,hakan ne ya sanyashi sanya wannan doka wadda ta yiwa manyan dai dai saboda tsaron tarbiyyar kowacce yarinya har ta koma gidansu,hakanan duk wanda ke kawo ziyara gidan a irin wannan lokaci ya san da dokar,walau mace ko namiji.

Cikin izza da ginshira yake takowa tsakiyar harabar gidan yana qarewa kowacce kusurwa ta gidan kallo da idanunshi,tuni hayaniyar wajen ta soma raguwa kowa ya soma shiga taitayinsa,wasunsu suka shagala da kallonsa,masu gulmarsa qasa qasa nayi.

Kamar ta sanya kuka haka sumayyan keji,yayin da alqasim kuma ya dage wajen ganin komai ya daidaita kafin barinta wajen,idanunsa ya sake wurgawa wani sashen,a can saka masa kamu,maca ce tsaye da hijabinta har qasa da wani saurayi tsaye a gabanta,sai wani saga gefanta,ranshi ya matuqar baci,ya tsani ya sanya doka a karya masa,a ganinshi wannan daya ne daga cikin alamun raini,idanu ya zuba sosai sai ya dinga hango kamar mahmoud ne dayan dake gefe,cikin bacin rai ya soma takawa idanuwansa na wajen,sam mahmoud bai ankara da fitowarsa ba shakka da tuni ya sallameta,ya riga da yasan halinsa sarai mutum ne mai doka da qa'ida,bazai karya dokar wani ba so shima kada a karya tasa shine zaman lafiyar mutum.

"Mahmoud" ya ambaci sunanshi bayan isowarshi gun,wani abu taji ya caketa tun daga tsakiyar kanta zuwa tafin qafarta da taji muryar mukhtar gab da ita,kuma a bayanta,kamar mai ciwon wuya haka ta dinga waiwayawa a hankali har ta kammala juyawa baki daya,tsaye yake harde da hannayensa yana yiwa mahmoud da alqasim magaba cikin bacin rai,idanuwansa na kansu,wanda sam bata iya jin abinda yake gaya musu illa bakinsa da take gani yana motsawa,muryar ce taci gaba da yi mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,a hankali ya dinga juye mata zuwa mukhtar dinta,sannu sannu jikinta ya soma rawa tamkar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi,bata ankare ba taga yana qoqarin juyawa ya bar gurin,batasan lokacin da ta daga murya cikin qaraji daya sabbaba har wadanda ke daura da su jin sautinta ta ambaci
"Mukhtar!" Cak ya tsaya tare da waiwayowa yana dubanta,kallonsa take tana takowa zuwa gurinsa a hankali,tsayawa kawai yayi yana dubanta,tun dazun haushi ya tsaye masa a wuya,tunda ya tsaya gun ya lura da yadda ta zuba masa udanuwa,abinda ya tsana kenan cikin kafatanin halayen 'yammatan wannan qarnin,kallon tsiyawa d'a namiji,babu wata kunya tattare da su
"Mukhtar kai ne?,kaine mukhtar!,dama kana nan,dama baka mutu ba?" Cikin bacin rai da yi mata kallon mai tabin hankali ya dubi mahmoud
"After All ma ashe da mai lalurar tabin hankali kuke tsaye?,sai kuzo kusan yadda zaku fidda ta tun kafin ta soma yiwa mutane barna"
"Mukhtar nice fa,sumayyarka ce mukhtar,nike da tabin hankali?" Har yanzu bai gasgata mai hankali bace,amma sai ya nutsu tsaf ya dubeta,babu alamu na hauka tattare da ita,ayyanawa yayi kawai tsabar rainin wayo ne da son samun guri,wanda ba tun yau ba ya gama haddace kissa ta son samun guri na 'yammata masu cusa kai kala daban daban,wani tsaki ya ja,sannan cikin dakakkiyar muryarsa wadda ta sake taimakawa wajen sawwara mata surarsa zuwa ta mukhtar yace
"Ban ciki da hauka da gidadanci kinji ko,ki kama kanki tun bai gudu ya barki ba,kama hanyarki ki koma inda kika fito" ya juya yana yunqurin barin wajen,a zabure ta bishi har ta samu nasarar riqo dantsensa,cikin tsananin bacin rai ya juyo yana dubanta cikin ido,wani kallo ya jefe ta da shi wanda tabbas da cikin hayyacinta take tuni ta sake shi saidai sam ko a jikinta
"Sake tafiya zakayi ka barni?"
"Sakeni!" Ya daka mata tsawa
"Bazan sake ka ba" itama ta fada cikin tsawa da bacin rau,take zuciya tanzuroshi,marinta yaso yi amma yaga rashin dacewar hakan,maiyiwuwa akwai tabin qwaqwalwar da batasan tana da shi ba,yaga kuma alama matuqar yaci gaba da tsaiwa zata iya ma rungumeshi kaban wadan nan yaran ta zubda masa mutunci,saboda haka sai ya fincike hannunshi tare da tunkudata yayi gaba,wani irin zafi yake ji da haushinta,baya tayi cikin rashin qwarin jiki,sun tsammaci zata turje ta tsaya sai kawai suka ga ta sulale ta zube baki daya,cikin firgici da tashin hankali mahmoud ya soma qwalawa amira kira don babu damar taba ta wadda fitowarta kenan shan iska batasan ma meke faruwa ba,ganin sumayyan kwance ya daga hankalinta ta koma ciki a sukwane,nan sukayi kacibus da anty farida mamar husna ta kamo hannunta suka yo wajen.

Ba amira da anty farida ba,hatta mahmoud da alqasim hankalinsu tashi yayi,kowa mamaki yake,meke faruwa ne haka,abu kamar dramer cikin sakanni qalilan,tana ta faman kiran mukhtar shi kuma wannan ALMUSTPHA ne abinda suke tunani kenan,cikin hanzari anty farida ta soma yunqurin dagata da taimakon amira,idan ka dubi fuskar wasu dai daikun 'yammatan dake gun jimami da tausayi ne bisa fuskrsu,addu'a suke mata kan Allah yasa ba qoshin wahalar da suka afka bane itama ta afka cikinsa,yayin da wasu dadi ya rufesu kamar su taka rawa,ko banza basu zama su kadai ba cikin wadanda suka rasa wannan damar.

A hankali ta ja numfashi tana ambaton sunan Allah,idanunta ta bude,jinta take kamar wadda ta tashi daga bacci,idanuwanta ta sake lumshewa take abun ya sake fado mata,kalamansa da muryarsa suka fara yi mata amsa kuwwa cikin kunne,take idanuwanta suka tara hawaye masu dumin gaske suka soma bin gefen kunnenta,sake rintse idanuwanta tayi,kamanninsa suka fara dawo mata ganin farko data yi masa kafin idanuwanta su rudeta,da sauri ta bude idanuwanab tana girgiza kai,tabbas ba mukhtar bane,babu kamannin mukhtar ma tattare da shi idan ka dauke murya,me ya shiga kanta ta aikata haka sai kace wadda jinnu suka juyawa tunani?.

Saitin fuskarta taga an turo screen din waya,idanuwanta ta bude kan screen din,shine,shine wanda ta gani dazun,sanye yake da qananun kaya kyakkyawar fuskarshi qunshe da murmushi,hotonsa ya cika fuskar wayar baki daya,a yanzun ta sake tabbatarwa bata ga kama tsakaninsa da mukhtar dinta ba,sai ta waiwaya don taga wanda ke haska mata hoton,amira ce zaune gefanta,idanuwa suka hada sai ta janye wayar tata ta kasheta tana duban sumayya
"Wannan yaya nane,mama da baabaanmu daya,ummee ita ta haifemu,sunanshi MUSTAPHA ko ALMUSTAPHA duk daya ne,anty dije ta bani labarin waye mukhtar a gunki,matuqar suna kama da mukhtar kuma yayi miki na miki alqawarin zaki zama mallakinsa,duk da nasan babban aiki na daukawa kaina saboda sanin waye YAYA MAN,amma abinda yayi miki ya bata min rai,ina jin tamkar ni aka yiwa,ko don saboda wannan indai kina sonshi amiran umman khalipha na miki alqawarin aurensa".

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*SHIN ko kunsan RUWAN DAN WUTA,RUWAN MUGUNYA NE(KAMAR RUWAN CIWO QURJI)TAFASASHSHE MAI AZABAR ZAFI DA TURURI,A DUK LOKACIN DA YA BUQACI SHAN WANI ABUN SHA SABODA TSANANIN QISHIRWAR DA YAKE JI SHI ZA'A BASHI YA SHA,YAYIN DA YAKE SHA DIN SABODA TSABAR ZAFI DA TAFASA HAKA ZAI DINGA YAYYANKA DA TSITSTSINKA MASA HANJINSA,YANA ZAGWANYEWA*

*Subhanallah,muji tsoron azabar Allah 'yan uwa*

____________________________________
Chapter 91 · 0% Book details