← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 210

Sashe 85

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Kanta a qasa qirjinta na bugawa ta dinga kutsawa cikin gidan,batasan me yasa take yawan faduwar gaba ba idan ta shigo gidan,ko don tana ganin kamar akwai banbancin matsayi tsakaninsu bai kamaci ta dinga shiga musu gida ba.

     Tazo mararrabar sashin anty maamaa data ummee sai taso ta manta wane waje ne na anty maaman don bata rarrabewa da sunayensu,a hankali ta juya idanuwanta tana canki canki,karaf idanuwanta suka sauka a kansu,zaratan samari ne ke tsaye su biyu suna magana da junansu,dukkaninsu dogaye ne saidai daya yafi daya masu matsakaicin jiki,kowannensu na sanye da t.shirt da trouser masu mabanbantan kaloli kowa da kalar nasa,farare tas da su kamar yadda ta dan fahimci haka kalar fatar masu gidan take,fuskar daya kawai taje gani bata ganin ta dayan kasancewar ya juya baya ne yana magana da dayan,da alamu kuma duk hankalinsa na kanshi,shima ya ganta,idanu ya sanya yana kallonta har waccan ya kammala fadin abinda zaice yayi gaba ya shige daya sashen.

      Rudewa tayi kamar mara gaskiya,jikinta ya soma rawa ta fara qoqarin juyawa ta koma inda ta fito ganin kamar yana takowa inda take
"Wa kike nema?" Ya tambayeta fuskarsa ba yabo ba fallasa,cikin qoqarin daidaita nutsuwarta ta hada kalmar
"Sashen anty maamaa nake nema"
"Ko gun amira kika zo?" Ya sake tambayarta yana kallon ledar hannunta,bata ma gane wace amirar ba,sai tave masa
"A'ah,saqo na kawowa anty maamaa" sai taga ya saki murmushi
"Yauwa,muje ma na rakaki,Allah yasa wannan turaren mai dadi aka kawo mata wanda tamin alqawari" ya fada yana yin gaba cikin mishadi,ta bishi a baya tana cike da mamakin sauqin kai irin nasa,batayi tsammanin haka ba.

      Falon suka shiga yana sallama cikin daga murya,wannan budurwar da take zaton ita ce amirar ta fito da sauri daga kitchen tana dariya,bata lura da sumayya dake bayansa ba,ganinsa ya sanyata tsaya tana dubansa tana qyalqyala dariya,da alama wani abu da ya faru dazun tsakaninsu taje tunawa
"Ya akayi yaya mahmoud?" Ta fada tana sake tuntsira dariya
"Zaki zo hannu ai kin sani.....yanzu ba wannan ba ga baquwa nan tazo wajen anty maamaa" dan leqowa amiran tayi inda sumayya ke tsaye,sai tayi murmushi
"Ba baquwa bace a gidansu umman khlipha take,duk da dai baquwa ce a gidan nan saboda na fuskanci bata son mutane" ta fada tana murmushi
"Ke kuma gaki da shegen kwashe kwashe ko,ki bata guri parrot tukunna,ki gayawa anty zan dawo anjima,yanzun yaa man ya aikeni ne" ya fada yana juyawa zai fice,ganin haka yasa amira daga murya
"Don Allah ya mahmoud ka siyo min na tuba" ta fada a shagwabe tana kama kunnuwanta guda biyun,harara ya watsa mata yayi ficewarsa,sai ta narke fuska kamar zata yi kuka har ya bace a falon kafin ta maida kanta wajen sumayya.

      Murmushi tayi mata sannan tace
"Ga waje zauna,amma sai kin dan jira antyn don tana wajen dan tsohon mijinta,kinsan ba'a kiranta idan ya shigo sai mutum ya jirata" ta fada cikin salon tsokana tana dariya,itama sumayyan sai ta saki murmushi,kusan haka halayyar anty dije take,take mukhtar ya fado mata,a hankali sai murmushin nata ya soma gushewa damuwa ta fara bijiro mata,take ta fada kogin tunani tana tuna wasu lokuta masu dadi daga cikin rayuwar da sukayi tare da shi.

       "Ga lemo bismillah" amiran ta fada tana ajjiye tray data dora lemo da kofuna a kai,kai sumayya ta kada cikin murmushin yaqe tace
"Alhamdulillah,a qoshe nake"
"Al'adar gidan anty maamaa ne,dole kisha wani abu kafin ta fito" ta fada tana tsiyaya mata a cup,kallonta sumayya tayi tana yaba karamcin hakan,sai a sannan taga kamanni da wanda ta kira mahmoud a dazu,da alama kwai dangantaka ta jini mai qarfi tsakaninsu,hannu ta saka ta karba tana fadin
"Na gode"
"Ba komai,bari na duba girki kada ya kama"
"To" sumayyan tace,kurbe daya tayi masa ta ajjiye damuwa ke sakadarta,a haka taji an bude wata qofa dake can wani sashe daban na falon,anty maaman ce ta fito tana cewa
"Ayyah tun yaushe kika zo" murmushi tayi
"Ban jima ba,ina yini" ta gaidata amsawa tayi tana zama tare da amsar ledar humrorin,budewa tayi tana shanshanawa tare da yaba yadda sukayi bala'in qamshi,godiya tayi mata sosai tamkar ba biyanta tayi ba,miqewa tayi tana shirin tafiya
"Umhmmm,za'a gudun ne?" Amira take baro kitchen ta fada tana dan murmushi,waiwayawa tayi tana dubanta itama fuskarta qunshe da murmimushin,sam batayi zaton zata yi sauqin kai haka ba
"Na baro aiki ne a gida shi ya sa"
"Ayyah to sai yaushe?,ko sai na shigo?"
"Allah ya kawoki lafiya"
"Amin,ni sunana sumayya na gaskiya,sunan mamar babanmu ce ake kirana amira,kefa?" Murmushi ta saki
"Nima suna na kenan?" Idanu amiran ta zaro gami da rufe baki
"Kai kai,dama baabaa na kusa ya ganki,yaga mai sunan mamarshi,yana son mai sunan mamarsa wallahi,me ake ce miki to?"
"Shi ake gayan" kai ta kada sannan tace
"Gaskiya ni bazan fadi haka ba,zan dinga kiranki kema da amira,amiran umman khalipha" dariya sosai sumayya tayi
"Shikenan to" ta amsa mata sannan sukayi sallama ta juya da niyyar fita tana dariya amiran,kusan zasuyi shekaru daya da ita,saidai yanayin inda ta taso da gata sai take ganin kanta kamar qaramar yarinya,duk da aqalla zasuyi shekaru ashirin da daya.

      A bakin qofar shigowa falon taji tayi karo da abu har yana bangazar kafadarta,da sauri ta ja baya tana fadin
"Subhanallah"
"Mtsweeeeww" taji an tsaki,baya ta sake ja tare da daga kanta tana kallonta wanda ita dinma kallonta take,saidai nata kallon yasha bamban da wanda sumayyan ke mata,kallon farko ta fahimci macace mai izza da jin kanta,haka yake don sumayya bata yi qarya ba,matashiya ce dake jin duniyarta dai dai,wadda a qalla ta doshi shekara ashirin da takwas a duniya,doguwa ce sosai hakanan siririya ce,fara ce itama sosai kamar yadda sauran suke,sanye take da wani baqin hight rise slim leg jeans da v neck t.shirt mai gajeran hannu,hakan shi ya fiddo surar ta da shape dinta baki daya,kanta yane da wani dan kwali mai santsi don ba za'a kirashi mayafi ba,idanunta saye da sun glases da ya kusa cinye rabin fuskarta,wani kallo take wa sumayyan na sama da qasa cikin izgilanci kafin ta zare gilashin nata,tsaki ta ja kafin ta wuce tana taku dai dai tana duban amira
"Maamaa fa?" Ta tambayi amira kamar bata son yin magana
"Ta haura sama" ta fada tana nufo sumayya dake gab da ficewa daga falon,da sauri ta daga murya
"Kiyi haquri sumayya" amiran ta fada cikin damuwa,sai ta waiwayo tana sake mata murmushi tare da fadin
"Kada ki damu", sai da sumayyan ta fice sannan ta dawo da kallonta cikin falon ta saukesu kan wadda ta shigo din,sai ta kada kai kawai ta shige kitchen ganin ta zauna saman kujera tana jiran saukowar maamaan,ta sani sarai ba zata iya haurawa saman ba dama idan ba da wani qwaqqwaran dalili ba,shi ya sanya tayi saurin komawa kitchen don kada ma tace zata aikata.

      Tana hanya tana tuna irin kallon da ta yi mata,a qa'ida ita ta bigeta,ranta yaao baci amma sai ta dorama kanta laifin,ko ba komai ita tazo musu gida,tana isa gidan ta bawa anty dije labarin amiran,
"Amira kam akwai son mutane ai haka take ita da mahmoud ai mutane na ne"
"Eh kam na ganshi shine ma ya rakani wajen anty maamaa,yana da kirki sosai"
"Shine d'a na uku a wajen ummee"
"To ita amiran 'yar waye ne anty,yau tana can gobe tana nan"
"Itama d'iyar ummee din ce"
"Ita ummin bata da yara ne?" Hararta tayi tana cewa
"Yau kin zama 'yar jarida,to ban sani ba,ai baki son jama'a ne,banda haka watanki nawa a gidan nan yaci ace kin gama saninsu,tunda alhamdulillah mutane ne masu kirki karamci da son jama'a" dariya sumayyan tayi tana kame bakinta da yatsunta
"Ni dama amiran nake son na san 'yar ina ce kuma an gayan" sai suka yi dariya anty dije na qorafin qib sakin jiki na sumayyan.

       Da daddare dukkansu suna zaune a qasa suna cin abincin dare har da mai gidan,sumayya ce kawai ke zaune can gefe tana cin nata,babu yadda anty dije da uncle farouq baiyi ta dinga cin abinci cikinsu ba amma ta kasa,kunya gareta,bata da sabo sosai idan ba wajen yara qananu ko mutanen gidansu da suka taso tare ba,tun suna qorafi har suka suka haqura suka zuba ido a haka suka saba saboda sun lura halittarta ce ba zata sauya ba.

         Sai da suka kammala baki dayansu sannan hafiz yace cikin doki
"Abba,wanne albishir ne da kace sai mun gama cin abinci zaka yi mana?"idanu ya zaro yana murmushi yana duban hafiz din
" ummm,wannan zumudi haka?"
"Eh wallahi abba nima na qagu ya rigani fada ne kawai a baki" juyawa yayi yana kallon lailan,wannan karon dariya ce ta subuce masa
"Au kema?"
"Eh abba" ta fada itama tana dariyar,sai ya dubi anty dije
"Kefa madam?" Murmushi tayi tana gyara zama
"Ai yara sun gama magana,nima na zaqu inji wanne albishir ne?" Dariya ya sake yi
"Uhmmm,shine kenan to tunda bakinku yazo daya" ya fada yana gyara zamanshi,sumayya na gefe tana satar kallonsu,yanayin rayuwarsu tana burgeta,soyayya dake tsakanin uncle farouq da anty dije kullum kamar wasu sabbin aure,waiwayawa yayi ya fito sumayyan da hannu
"Taso kema ya shafeki" sai tayi qasa da kanta sannan ta miqe ta qaraso tana murmushi,gefan laila ta samu ta zauna,duk sukayi shiru suna sauraronsa.
Chapter 85 · 0% Book details