← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 210

Sashe 5

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To shikenan,haka ake so,inaga zan duba wajen sati na gaba ko wajejen satin sama,zan aiko abubakar(yayanta ne shine na fari a gidansu,amma baiyi aure ba karatu yake)zaizo. A fidda kayan gadonki da kujerunki a sauya miki wasu" farinciki ya cikata,duk da cewa wadan nan natan ma babu abinda sukayi,don sanda sukayi shekara hudu da aure mukhtar ya fitar da na aurenta na ainihi ya sauya mata su.

"Na gode,na gode qwarai malam Allah ya saka da alkhairi,ya qara lafiya da nisan kwana mai amfani,Allah ya qara budi da rufin asiri"
"Amin ya Allah,amma abinda zaki biyani da shi kawai kici gaba da zaman aure cikin gidanki"
"Da yardar Allah malam" ta amsa masa daga haka sukayi sallama.

Sosai malam yake aon sumayya,don tun tana mitsitsiyarta halayyarta daban take,tana da tarin haquri kawaici da zurfin ciki,shi yasa duk cikin yaransa yafi sonta,duk da cewar dukan yaran nasa maman sumayyan ce ta haifesu,ko a lokacin da suka aura mata mukhtar ma ce mata kawai yayi ga miji yayi mata kuma aure zaiyi mata,bata ce komai ba don ba wayo gareta ba,duk da haka dama kunya gareta,gudu tayi ma ta bar gurin sanda malam din ke gaya mata,ita ce yarinya mace ta farko a gurinsa sai qannenta su hudu.

Mukhtar zamu iya cewa rako wani abokinsa yayi gurin malam din kasancewar malam din yana bada karatu tsakanin sallar magariba da isha'i wa matasa da dattijan unguwa,gani daya ya yiwa sumayya yaji tayi masa kasancewarsa mutum wanda sam baya da sha'awar auren macen da tayi zurfi a karatu,tunda yayi universty shima yaga irin qazamar rayuwar da mafi yawancin 'yammatan keyi duk da ba duka aka taru aka zama daya ba.

To sara ne yazo kan gaba shima malam ba mai son yaransa suyi bokon bane,saboda haka yana bincike kan mukhtar ya tabbatar da nagartar halayyarsa ya basu auren sumayyan.

Da fari 'yan uwansa sun so su turje kan mai zai sa ya auri yarinyar da rainonta kawai zaiyi,musamman yaya yahanasu wadda ita ta riqe mukhtar din,saboda bai wuce shekara biyar a duniya ba Allah ya yiwa mahaifiyarsu rasuwa wanda dama tun mukhtar na da watanni a duniya mahaifinsu ya rasu,to amma daga bisani suka haqura kasancewar sun lura mukhtar din bashi da niyyar fasa aurensa.

Da fari sun karbi sumayyan a matsayin 'ya kuma qanwa,amma daga lokacin da suka lura da gatan da mukhtar ke mata hassada ta soma aiki,duk da ba zaka kirashi mai kudi ba amma mai arziqi ne,iyalansa sunfi qarfin yin kukan rashin wani abu cikin gidansa,shekara uku tayi ta cika shekara sha shida,a lokacin ta zama mace saboda Allah ya mata halitta da jiki mai kyau,sai suka juya akalar hassadarsu kuma zuwa sa mata idon yaushe zata samu ciki?,yaushe zata haihu?,wanda har yau suna bisa wannan bigire basu sauka daga kai ba

Wannan kenan.....

Sati hudu suka sanya lokacin aurensu,sunata budirinsu suna shirye shiryensu ango ko oho,kayan lefe ne yace zaiyi kuma bai fasa yi din ba.

A falonta ta tadda shi yana amsa waya bayan ta gama soya masa wainar fulawa da yace yana sha'awa har tana ta masa dariya qai qwalama ce kawai ta dameshi,mai ya hadashi da abincin mata,ya sauke wayar daga kunnensa yana janyo plate din tare da budewa yana fadin
"Yauwa amaryata kuma uwargida na" qeya ta juya masa tana turo baki
"Um_um,barni a uwar gidan dai,amaren na nan tafe" cikin sigar tsokana ya dan talle mata qeyar data turo masa
"Ka jini da yarinyar nan wai itama ta iya kishi?" Duk da tasan wasa yake sai ta juyo tana dubansa zuciyarta na raunana amma ta dake
"Don me bazanyi kishinka ba ya mukhtar?" Bai so maganar tayi tsayi don bata masa rai maganar take balle ita saboda haka yace
"Haka ne" a taqaice sannan ya hau qirqiro santin waina duk da cewa a zahiri tayi dadin,biye masa tayi tana masa dariya tare da kara masa filo a bayansa.

Sai da yaci kusan rabi sannan tace da shi
"Nikam yaya mukhtar banga kana shiri ba" cikin son samun qarin bayani yace
"Wanne irin shiri?,name?"
"Banga wani sauyi ba agidan nan?"
"Kamar wanne iri fa" ya sake tambayarta
"Gani nayi kace na kwashe shirgin dake cikin dakin shirgin can nan amarya zata zauna,nace maka ka hada mata da naka dakin itama ta samu falle biyu ka qiya,to a barshi a hakan,amma ya kamata ace daga dakin nata zuwa tsakar gida ko shafen farar qasa ka yi masa don ya haska ko,tunda nawa dakin ba'a jima da yi masa fenti mai tsada ba fes yake kamar yau akayi".

Banza yayi da ita kamar bai ji ba har sai da ta qosa tace masa
" kana jina kuwa ya mukhtar?"
"Ina jinki kuma bazan yi ba,ke wallahil azim kika sake yimin magana makamanciyar haka sai ranki ya baci,idan zata zo ta zauna haka ta zauna,idan ba zata zauna ba ta qara gaba dama ba ni na gayyatota ba,haba,dame kike so naji?".sai ya miqe a fusace ya fice zuwa dakinsa ya barta da sauran wainarta.

Jikinta ne yayi sanyi,tayi da na sanin yi masa maganar,sai data bashi kusan awa guda sannan ta gyara gurin ta shirya zuwa shigar barci tabi bayansa don ta lallashe shi.

Bata sake masa maganar ba kuwa,sai ranar asabar ranar 'yan yaranta duka suna gida saboda ba ranar karatu bace,ta aika nana tayi mata kiran wani dan saurayi dake maqotansu,tace ya duba mata don Allah farar qasa kwano nawa zai isa dakin zuwa tsakar gidansu ya gaya mata yadda yake zaton zata isa,cikin kudin da take adanawa ta qirgo ta bashi har da kudin mota,cikin minti talatin ya dawo,tasa ya jiqa mata sannan ya tafi ta masa godiya ta bashi dari tace yasha ruwa.

Yaranta ta kalla wadanda sun kai su takwas,akwai bilkisu,fatima,hauwa'u,khadija,aisha,ummi,asma'u sai nana ta gurinta
" maza kowa yaje gida ya cire kayan jikinsa ya saka marasa kyau zamuyi fenti"cikin zumudi kuwa har suna rige rige suka fice suna murna.

Kafin su dawo itama har ta sauya nata kayan,saiga yaran kuwa,nan suka zage suka dinga shafen farar qasar,abinka da ba aikinsu bane tun safe har bayan la'asar,nan ta musu girki suka ci,idan sun huta su dora.

Cikin haka sai ga maman nana ta shigo,salati ta saka tare da kama habarta ganin sumayya saman tsani,duk sunyi face face da farar qasa
"Ni salma,ai nayi zaton qarya nana take da tace fenti zakuyi ashe da gaske take",dariya ta qyalqyale da ita tana saukowa daga kan tsanin
" to ya zanyi maman naana,ya mukhtar yaqi yarda yayi fenti,shi yasa na siyo da kaina mukeyi ni da 'ya'ya na"(da yake ita kadai ta gayawa zancan,saboda yadda take mata tamkar mamanta,tafi shaquwa da ita fiye da sauran iyayen yaran.

kai maman naana ta dafe tana cewa
"Lallai sumayya quruciya na damunki,yanzu kishiya kike yiwa fenti da kudinki da jikinki,Allah ya shiryeku" ta fada tana dariya
"To sauko hakanan na kira muku jamilu(babban danta) ya qarasa muku,tunda kun rantse sai kunyi" murmushi tayi tana kakkabe jikinta tare da fadin
"Ai kuwa mun gode" da kanta maman naanan ta leqa ga nemo jamilun,cikin 'yan qananun mintina ya qarasa musu inda basu qarasa din ba.

"Magana ba zata yiwu yau ba sumayya na dawo gobe,tunda yau kun zama 'yan qwadago yinin fenti kukayi" ta fada tana miqa mata ledar data shigo da ita,tana dariya ta amsa tana dubawa,ko bata ce mata komai ba ta fahimci meta kawo mata,magunguna ne masu kyau ingantattu na 'ya'yan itatuwa data saba bata.

Sanda mukhtar ya dawo yaga aikin da sukayi cak ya tsaya,sai kuma yayi gaba ba tare da yace komai ba,qaunarta ke saka ratshi,uwa uba kuma tausayi don yasan har yau da zallar quruciya tattare da ita,inda yasan zata yi da tun sanda yace ba zaiyi ba da tuni ya hada da yimata hannunka mai sanda don kada ma tace zata yi din.

Kamar yadda abba malam ya alqawarta mata,sati biyu da yin maganarsu kuwa saiga motar kaya,irin kayan da sam sumayya bata zata ba,kaya ne 'yan italy masu kyau da tsada har kujerun wanda ko a aurenta ba'a yi mata irinsu ba,har da qarin labulaye masu kyau da door mat,mamam naana da maman ummi ne tare da uaran gidanta suka tayata jerawa,saiga dakinta ya fito fes tamkar ma ita ce amaryar,mukhtar baiyi qasa a gwiwa ba yace har gida yiwa abba godiya,hakanan shima ba'a barshi a baya ba,kayan kitchen baki daya ya sauya mata,kasancewar yanzun an maida kitchen din bangare biyu,hannun hagu da hannun dama,kowacce anyi mata kantarta da drowers dinta,hakanan ya sauya maya plasma wadda tafi waccar girma harda qarin home thierther,sai ta dinga mamaki da yace bashi da kudi da bazaiyi lefe da fenti ba,bata ce masa komai ba tunda ta fuskanci dama ce bai gani ba,godiya ta dinga zuba masa sosai kamar yadda yake al'adarta.

Mamanta ita ta sauya mata showglass da kayan cikinta baki daya,farinciki duk ya cika sumayyan,ta fuskanci ita 'yar gata ce sosai,batasan duk sunyi haka bane don kwantar mata da hankali da sake sa mata nutsuwa,ba qaramin kyau dakinta ya sake yi ba sai ka rantse amarya ce.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

__________________________

_bismilla hir rahmanir rahim_

_iza qada amran fa innama yaqulu lahu kun fa yakun_
________________________

0⃣4⃣

Sati guda da kammala gyara gidan ranar wata litinin mukhtar ke gaya mata ran laraba masu kafin amarya zasu zo,sai da taji wata faduwar gaba da bata san ta mece ba
"Allah ya kawo su" ta fada kawai kana tayi shiru tana dubansa yana rubuta lissafin kasuwa cikin wani qaramin excercise book.
Chapter 5 · 0% Book details