← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 210

Sashe 45

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Basu jima da kammala tsifar ba anty dijen ta dawo hannunya dauke da baqar leda,ta cillar kan cinyar sumayya
"Da baki iya zuwa gaida mutane ba gashinan haj bilkisu tace na kawo miki kiyi fitar biki,ta yaba da zabin leshin ki wai kin iya zabar kala,ashe tare kuka shiga shagon da mansur din". Baki ta saki sanda ta fiddo leshin taga daya daga cikin wadanda suka siya dinne
"Anty kinsan kuwa nawa ne farashinsa duk guda daya?". Dariya anty dijen tayi
"Hmmmmm,bakisan mutan gidan bane sumayya,kinga ku tashi ku shirya ku wuce wankin kan nan kada dare yayi muku hanya"ta furta tana miqewa ta nufi kitchen.

****** ******* *******

Sanda suka isa kwanaki biyu sukayi saura a daura aure don babu wani event da sumayyan ta tsara yi,yaya abubakar ne kawai zaiyi walima bayan an gama daura aure.

Kusa awa guda kenan da shigowarta gidan amma bata ga wulgawar abdallah ba,tun tana kawaici bata tambaya ba har sai data magantu
"wai nikam ina abdallah ne?" Maimakon maman ta amsa mata sai tace da ita
"Kije malam nason magana da ke" hakanan taji jikinta bai bata ba,ta miqe ta zura hijabinta ta fice.

A ladabce ta gaisheshi ya amsa yana tsokanarta abuja ta karbeta,sai ya bata kunya ta sunkui da kai tana murmushi yayin da tausayinta kuma ya darsu a zuciyar malam din
"Sumayya maganar da zamuyi da ke nasan ba zata miki dadi ba,domin raba da da uwa sai Allah,saidai babu yadda muka iya,bayan tafiyarki mukhtar yazo ya karbi yaronsa...." A firgice ta dago ta dubeshi muryarta na rawa idanunta na fidda ruwan hawaye
"Amma malam me yasa zaimin haka,rabamu ken......."kaaa qarasawa tayi tayi qas da kanta
" kiyi haquri sumayya,shi ya fiki a haqqu da shi,sannan ya riga da yace baiso yaron yayi zaman a golanci gidan wani kamar yadda shima yayi,kiyu haquri nasan ba wai ya rabaku bane na har abada saboda yadda yazo mana bada nuna isa ko qarfa qarfa bane,abinda na lura shine bazai iya jurar rashin ganin yaron bane,tunda idan har kika tafi da shi bashi yiwuwa ya dinga binki gidan mijinki da sunan yazk ganin dansa,kiyi haquri babu komai ai kuna tare,na tabbata za'a dinga kai miki shi"malam ya fada cikin tausasawa. Haka malam din ya dinga lallashinta yana bata kalamai har ta samu ta danji sauqin zugin zuciyarta,saidai abinda take ji na game da kewar yaron har yau bai sauya ba.

Data koma daki taga sauran kayayyakinsa kasa ci gaba da daurewar tayi,ba shakka raba da da uwa ba qaramin abu bane,shi yasa aka ce ko mutuwa tana shakkar idon uwa,yaya wadanda suka rabu da 'ya'yayensu suke ji rabuwa ta har abada?,ashe da sauqi ita tunda yana nan cikin duniyarta kusa da ita amma duk da haka ta gaza daurewa,kuka tayi mai yawan gaske wanda shi ya haifar mata da zazzabin da ciwon kai mai tsanani har ranar da aka daura auren,haka nan aka tattarata aka kaita dakinta tana mai ci gaba da kuka mai qunshe da abubuwa iri daban daban

**** *9:30 pm* *****

Lukman Bashir shine asalin sunansa,haifaffen garin kano cikin qaramar hukumar kano municipal,yayi karatunsa iya N.C.E sai ya fada kasuwanci gadan gadan,mahaifiyarsa hajiya kubra shi kadai tallin tal ta haifa,hakan ya sanya ta dauki so da qauna da kulawa ta dora masa,wannan shine dalilin da ya sanya duk lokacin da yayi aure ta fuskanci yana mutuwar son matar take rabasu don wai ba zata bari a mallake mata yaro ba tana kallo,kasancewar gidansu daya part guda yayi mata da ya tashi ginin gidansa,a haka a haka ta sanya lukman ya rabu da mata kusan hudu kenan duk da cewa yana dacen matan aure masu matuqar haquri da biyayya saidai ita sam bata gani,haquri da biyayyar da sukewa lukman din ita ke jawo musu qauna gunsa,amma ita gani taje tsabar asiri ne matan suke yi,sam matan basu da sukuni,hatta zanin daurawa idan zai musu ita ke karbar kudin ta siyo ta bada adinka musu ita kuwa sai wanda ta zaba zata sanya,hakanan duk cikin matan da yake aurowa mutum daya ce ta haihu da shi don na wani dadewa take bari suyi ba,ita din ma a gidansu ta haife sai da ta yaye hajiyan tasa aka karbota,'ya mace ta haifa wadda ake kira da nuwaira.

Hausawa suka ce alhaki kwikuyo ne,a irin haka ne Allah ya hada lukman da KARIMA gogaggiya mai idanu a tsakiyar kaa wadda ita ta haifa masa yara uku dukka mata zaitun marwa da radiya,da fari kariman lumbu lumbu ta yiwa hajiyan har ta saki jiki da ita,sannan daga bisani ta sanya gaba daya daga lukman din har hajiyan aka sanya su qarqashin ikonta,daga lukman din har hajiyan umarni suke karba daga wajenta,babu wanda ya isa ya tsallake abinda ta shimfida masa,sai a bayan idonta su yita takaici da jimami amma a gaban idonta ko tari ba wanda ya isa yayi,mutane da yawa sunyi murna sunyi shewa da wannan sauyi domin ya zamewa hajiya kubra izina.

Tun bayan da ya auri karima bai kuma gigin qara wani auren ba sai a yanzu da yake KUNDIN QADDARArsa na rubuce da auren sumayya,sanda yake gaya mata zai qara aure a tsorace yake,ita kanta tayi matuqar mamaki,a fusace ta shiga dakinta ta kira wayar malaminta ta sanar masa,wayar tace ya kashe zaiyi bincike nan da awa guda zai nemeta,ya kuwa nemetan ya sanar mata wannan aure ba makawa sai an yishi saboda yarinyar nada addu'a hakazalika 'yar gidan malamai ce,wannan kalma ta sake tunzura karima ta sanya aka sake sabunta aiki mai kyau akan hajiya da lukman don kada sumayyan ta samu kafar rusa mata shirinta wanda ta riga ta qudurceshi cikin ranta,haqura tayi saidai duk wani harkar biki kama daga lefe da sauransu ita tayi su,komai sai data ninka kudinsa sannan kuma ta zuba abinda ranta yaga dama,sauqin daya gidansu sumayyan gida ne na dattako babu wanda ya damu dabtsada ko yawan abinda aka zuba cikin lefen.

Qarfe tara da rabi na daren bayan an kaita gun hajiya an gabatar da ita yayin da ita kuwa hajiyan ke fadin tabi karima wanda ya baiwa kowa mamaki sannan aka dawo da ita dakinta wanda falo ne guda daya makeke sai dakunan bacci na kowacce mace da bandaki a cikinsa,sai dakin yara da mai gida kitchen da bandaki duk cikin babban falon,cikin falon dai ya kira sumayya don dama ita karima na zaune a falon tun kan a kawo sumayyan har kowa ya watse
"To sumayya wannan itace uwar gida na uwar 'ya'ya na,idan kika bita kamar kin bini ne,na auroki ne ba don bana sonta ba,bana so kuma ki raina min ita,hatta hajiya farincikinta shine farincikin karima da fatan kin gane" kanta ta cira a hankali tana dubansu baki daya,cikin zuciyarta ta furta
"Ikon Allah,yau kuma da wacce kalar Allah ya hadani?".
Miqewa kariman tayi cikin izza tana yatsina
" idan ka gama ka sameni a daki,kada ka wuce minti biyar"
"To....to to" ya amsa cikin inda inda tare da binta da kallo har ta wuce dakinta,da sauri ya dubi sumayya
"Amarya ta muje na rakaki daki kinji" ya fada cikin kwantar da murya,ba musu ta miqe tayi gaba mamaki na kasheta,wai dama haka lukman din yake?me yake shirin faruwa ne?.

Bakin gado ya zaunar da ita yana duba agogo don kada yayi laifi
"Zauna bari naje,in Allah ya yarda zanyi qoqarin dawowa,ga kaxarki nan idan kina jin yunwa kici kafin na dawo" ya fada yana juyawa ya fice da sauri,binsa tayi dakallo baki daya qimarsa da mutuncinsa da take dan gani a da suna ficewa fit daga ranta,hawaye suka soma fita daga kuncinta data tuna rayuwar gidan mukhtar makamanciyar wannan,saidai sam da alamu bata kai qazancewar wannan ba,ita kuma nata salon QADDARAR kenan?. Juyawa tayi ta kwanta tana faman zubar da hawaye.

Har bacci ya soma fusgarta taji yana ambaton sunanta sama sama,ta bude idanunta tana dubansa,murmushi yake yana kallonta shima tare da duba bakin qofar dakin kamar wani ya biyoshi,ganin ta tashi ta zauna ya sanyashi maida qofar dakin ya murza key,kamar wanda ke sauri jirgi zai tashi ya barshi yake magana
"Tashi maza ki dauro alwala,ina fatan dai kinci abincin ko?.....kinyi sallar isha'i?.....dauro alwala sumayya babu lokaci...."ya fadi yana satar kallon qofar dakin
Cikin mamaki take dubanshi duk ya wani firgice,lokaci kada ya qure kamar yaya take tambayar kanta
" don Allah tashi mana sumayya kada ta....."bai qarasa fada ba aka fara dukan qofar kamar za'a ballata
"Innalillahi wa inna aihi raji'un" ya fada yana dafe kansa.
"Zaka bude ko sai na sassaba maka,maci amana" inji mai buga qofar,jiki ba qwari ya nufi qofar ya bude mai bugun ta fado dakin tana raba idanuwa,kubra ce sai data qarewa dakin kallo ta fuskanci babu abinda ya faru sannan ta kalleshi
"Ni zaka ci amana ka karya alqawarin daka yimun?,to wallahi ko kwana a dakin baka yi butulu kawai,maye,tunda ni ban isar maka ba,wuce muje nace ka tsaya ka kafeni da idanuwa" sai ya waiwaya yana duban sumayyan har sai data ingiza qeyarsa sannan ya fice yana waiwaye.
Chapter 45 · 0% Book details