← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 210

Sashe 47

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakin katifa ta zauna tana sauke ajiyat zuciya,kafin qwaqwalwarta takai ga tuno wani abu wayarta ta fara tsuwwa,ta sanya hannunta ta dagota ta duba mai kiran,sai taga anty dije ce,ji tayi kamar an mata rahama,tun kafin ta kai ga dagawa zuciyarta ta karye,da dake ta amsa kiran nata,bayan sun gaisa anty dijen tace
"Ance min kina nan kina ta kuka saboda zaki sake aure ko?,ince dai ba mukhtar kikewa kukan ba?" Girgiza kai tayi kamar tana gabanta ta rasa me zata ce mata don ita kanta bata san me takewa kukan ba
"A'ah anty"
"To baki son angon ne?"
"Nima ban sani ba anty" ta fada da gaskiyarta,shuru anty dijen tayi tana nazari,tana tunanin har yau zuciyar sumayya a kulle take,babu mamaki har yanzu batasan soyayya ko qiyayya ba duk da tayi zaman aure na wasu shekaru
"Indai har baki sani din ba ina son ki kwantar da hankalinki,mai yiwuwa ki koyi yadda zaki soshin tunda baki tantance mai kike ji a kansa ba,banason ki dinga daga hankalinki sumayya kinji,kiyi addu'a kibi komai a sanni,duk abinda kika ya zowa bawa ya dauka hakan MUQADDARI ne daga ubangijinsa"
"To anty in sha Allah" ta fada tana jin qaunar anty dijen na ratsata,duk cikin 'ya'yan 'yan uwa anty dijen tafi sonta,haka nan Allah ya hada jininsu tana jin sumayyan ne kamar diyarta saboda irin halayyar da take sa ita wadda ta banbanta da ta sauran
"Maman ta gaya min sati na sama za'a kawo lefe,sati biyu masu zuwa zq'a fara biki har da na abubakar ko?"
"Eh" ta amsa a sanyaye
"To shikenan babu damuwa,cikin satin nan kamar naji hajiya bilkisu matar professor zata aiko direbansu kano zai mata siyayyar wasu kaya,zan tambayi hajiyan idan zai iya qarasowa nan sai ya daukoki ya kawomin ke,idan yaso satim bikin sai mu taho baki daya ko?" Duk da bata sha'awar zuwa abujan amma bai kamata taqi ba sai ta amsa mata
"To anty na gode a gaida min da minar dita(amina ne sunan kakarsu ce ake ce mata minal sumayya ke tsokanarta da minar)" dariya anty dije tayi tana cewa
"Zataji,nasan babu zama indai taji kina zuwa abuja" itama sai ta dan yi murmushi saboda tana son qiriniyar yarinyar.

***** ****** *******

Qarfe goma na safiya dai dai kamar yadda anty dije ta gaya mata direban ya iso,da qyar lukman ya bar tafiya dan dai yaji anty dije ce amma cewa yayi baiso ta masa nisa,ta bari next week sati daya saura bikinsu zashi abujan shima kaiwa wasu abokansa katin daurin aure sai su tafi tare tayi kwana biyu gidan anty dijen ya dawo da ita,tilas ya haqura da yaji antin ce.

Tana tsaye gaban motar wadda saboda azabar kyau tana ganin kanta a jikin motar,yaya abubakar da direban na sanya mata akwatinta a bayan motar,bayan sun gama shigarwa ne sukayi sallama direban ya bude mata bayan motar ta shiga a hankali ta rufe murfin motar tana kallon su halima ta gilashin motar mai duhu wanda ya nuna su basa ganinta har suka fice daga layin,wani sanyin ac da qamshi ya ziyarceta lokaci guda,ta dan lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya,sanyin har yaso ya dan mata yawa amma hijabin dake jikinta ya taqaita haihawar sanyin
"idan ba damuwa zan dan tsaya a kwari bakin wani shago zan karbawa hajiya saqon wasu kaya"
"Babu komai" sumayyan ta fada a hankali,ni da za'a yiwa alfarma ma sai an nemi shawara ta ta fada cikin zuciyarta.

Sai da suka iso bakin kwarin ma sannan ta lura saboda sam hankalinta bai kan titin bugu da qari kuma lafiyayyar motace da bakajin kwaram kwaram din titi,bayan ya kashe motar har ya juya zai fita sai ya juyo
"Hajiya ko zaki taimaka min muje ki zaba musu kala sabida gaskiya ni bansan kalar mata ba,gashi hajiya ta jadda da min na zaba musu mai kyau ta riga da ta biya kudaden". Dan jim tayi tana nazari,ita da bata sansu ba ta yaya zata san kalolin da suka dace da su?,amma duk da hakan bata musa ba ta amsa masa da to ta fito tabi bayansa.

Wani lafiyayyen shago ne da kana kallonsa kasan na qananun kaya suke saidawa ba,kai tsaye mansir dire ba ya nufi inda manajan gun ke zaune wanda tun daga nesa da ya hangoshi ya fara washe baki,hannu ya miqa masa suka gaisa yana tambayarsa su hajiyan yace kowa lafiya qalau sannan ya masa jagora zuwa inda lesukan suke.

Kallo daya zaka musu kasan ba kowa ke iya siyansu ba,inda suke a ajjiye ma na daban ne,a nan manajan ya juya ya barsu don su zabi wadanda sukayi musu,ta kai mintuna wajen biyar kafin ta juya ta dubi mansir
" guda nawa za'a zaba?"ta tambayeshi
"Guda shida ne" ya bata amsa,cikin hikima da dabara ta dinga zaben kaloli masu dauke da pattern mai kyau har ta kammala,washe baki mansir yayi yana yaba kalolin data zaba din duk da bata ce komai ba,suna shirin barin wajen idanunta ya qyallaro mata farashinsu,tayi mamakin yawan kudin amma daga bisani mamakin nata ya ragu duba da irin kyansu.

Cikin mintinan da basu gaza arba'in ba suka saitu sosai kan hanya,tafiya ce mai dadi saboda yadda na cikin motar baijin rana ko gajiyar zama balle ya jigata,suna tamburawa wayar direban ta dauki tsuwwa,a hankali ya gangara gefen titi saboda ganin mai kiran nasa sannan ya daga,cikin tsantsar ladabi ya fara gaida mai kiran nasa ,waya sukayi na 'yan mintuna yana mai amsawa sa to to yallabai cikin ladabi sannan ya kashe kana waiwayo baya inda sumayya ke zaune
"Hajiya yallabai ya katse mana hanzarinmu ya sake maida mu baya,sai mun koma zoo road mun karbo dinkunan madam,kiyi haquri bansan zamu karbo su ba sai yanzu yake sanar mini" agogon wayarta ta duba,a qalla sun kashe kusan awa biyu da rabi kenan daga fitowarsu daga gida amma basu dau hanya ba sai yanzu,yanzun kuma gashu zasu sake komawa cikin gari,duk da ta danji babu dadi amma ba yadda ta iya tunda 'yar alfarma ce,
"Kiyi haquri fa" direban ya sake fada yana juya kan motar"
"A'ah babu komai ai" . sai kusan qarfe daya da rabi sannan suka dauki hanya sosai.

Gab da zasu shiga garin zaria wayarta ta dauki burari,sai da gabanta ya fadi hakanan da taga sunan abdur rahman,kasa dagawa tayi har sai da ya kirata kusan sau biyu ana ukun ta daga
"Sumayya har abun yayi zafi haka?,ba wani abu bane kiranki nayi na miki sallama,naje gida ban sameki ba ance kin tafi abuja wajen anty dije,koba komai ai akwai kyakkyawar alaqa tsakaninmu ko sanarmin kyayi,kin yaye abdallah ma duka ban sani ba sumayya haka rayuwa take?,cewa da nayi ina sonki ban sameki ba bashi zai bata zumuncinmu ba" muryarta a matuqar sanyaye tace
"Kayi haquri don Allah,duka banyi hakan bane da wata manufa,kawai bansan da fuskar da zan kalleka bane"
"Da fuskar da kike kallona sumayya,ni na yarda da QADDARA na yarda cewa hakan na cikin KUNDIN QADDARARMU ba wai don baki qauna ta ba duk da bansan zahirin zuciyarki ba"
"Haka ne abdur rahman,bana qinka wallahi har ga Allah,kawai QADDARA ta riga fata ne,bansan dalilin da yasanya zan auri lukman ba,amma nasan cewa QADDARATA ce ta rubuta hakan kuma sai ya faru"
"Na fahimceki sumayya,Allah yayi mana zabi mafi alkhairi a dukka rayuwarmu shine fatanmu,na kiraki na sanar miki in sha Allah jibi zan koma inda na fito,tunda ban samu cikar buri ba,nasan kafin na sake waiwayowa najeria kin jima a dakinki,ina miki fatan kyakkyawar rayuwa,na bar miki saqo a hannun halima"
"Na gode qwarai da gaske,haqiqa ka jima kana bada gudun mawa a rayuwata tun ba yau ba abdur rahman,ina maka fatan kyakkyawar rayuwa fiye da tawa fiye da wadda ka roqamin,ina roqa maka alkhairin ubangiji a duk wani motsi na rayuwarka,Allah ya haskaka rayuwarka karatunka da duk wasu harkokinka,na gode na gode"
"Nima na gode sumayya,saduwar alkhairi" ya fada yana katse layin,sauke wayar tayi daga kunnenta tana bin wayar da kallo,sai kuka ya kufce mata tayi azamar rufe bakinta saboda tuna a inda take,kanta ta kifa saman cinyarta tana tunanin mai ya hanata zabar abdur rahman?mutumin da babu abinda ya rasa na nagarta da kyawawan halaye saboda wasu dalilai dake gefe guda?.
QADDARA CE babu shakka qaddara ce tana kuma fata wannan karo tazo mata da kyakkyawan sakamako,kifan kan da tayi bata sake dagowa ba bacci ya kwasheta bata kuma farka ba sai da suka tsaya bakin qofar gidan anty dije cikin kyakkyawar unguwar tasu.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣1⃣

*innal laha ma'assabirin*

Cikin qanqanin lokaci yayi wankan ya shirya cikin shadda sea grean,sosai tayi masa kyau,itama sabuwa ce cikin sabbin dinkunan da yayi shima,ya kulle gidan suka fito.

Sai daya bude mata gidan gaba ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga daya bangaran yana duban ta,yadda fuskarta ta cika da farinciki tana masa addh'a,sosai yaji dadi cikin zuciyarsa shima,yayi bismillah ya tada motar suka fice daga layin a hankali.

Suna tafe suna hirarsu cikin nishadi da walwala har suka iso qofar gidansu sumayyan,cikin zumudi ta bude ta fice mukhtar ya bita da kallo yana murmushi,tamkar yau ne ta fara zuwa gidan sai murna take.

A tsakar gida ta tadda maman zaune saman tabarma sai fitilar qwai dake kunne a gefanta kasancewar babu wutar nepa,ba kowa tsakar gidan sai ita kadai
"A'ah,sumayya da kece haka da daren nan?" Mama ta fada tana sake bude tabarmar da take kai,gefanta ta qaraso ta zauna bakinta yaqi rufuwa
"Wallahi mama nice,ke kadai ce?"
"Eh duka sun tafi makarantar dare,amma gab suke da dawowa"
"Malam fa?"
"Sun tafi dubiya asibitin murtala shi da abubkar,maqwafcin mu malam sule ba lafiya"
"Ayyah baba sule,Allah ya sawwaqe......bari na yiwa yaya mukhtar din magana to ya shigo ku gaisa"
"Au tare ashe kuke......maza shigo da shi" inji mama tana janyo hijabinta dake gefanta ta zura.

Cikin girmama juna suja gaisa sannan ya fada mata motarsa ya kawo su sa mata albarka,tayi kuwa addu'a sosai don babu damar ta leqa malam din baya nan,nan ya fice qofar gida ya barsu.
Chapter 47 · 0% Book details