← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 210

Sashe 178

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

         Da sallama suka shiga wajen baba,yana tare da adam yayan almustapha suna hirarsu,kusan ranar sumayya zata ce ta soma ganinshi,akwai 'yar kama tsakaninsu,kana ganinshi zaka san jininsa ne,saidai almustaphan ya fishi kyau da quruciya,ran baban yayi qal ganinsu dukkansu su ukun a tare,murmushi yaqi yankewa daga fuskarshi ya tarbesu suka zauna suna gaidashi
"Sa'adatu(da yake wani lokaci hakan yake kiranta,abinda ta tsana kenan,ita aginta bata suna ne)yanzu muka gama waya da babanki"
"Allah sarki" kawai ta fadu,har ga Allah haushin tsohon take ji,gani take shine ummul Aba'isin komai ma da ya faru da ita,kanwa uwar gami,sai ya waiwaya ga sumayya wadda ta gama gaida yaya adam a mutunce
"Maman tun daga randa naci tuwo kuma sai kiyi batan dabo,inata nemanki na bada tukuici" qas tayi da kai tana wasa da yatsun hannunta kawai,ya tambayi lafiyarsu baki dayansu suka amsa mai,ganim almustapha sun soma hira da adam yasa almustapha yace suje wajen ummeen shi zaizo,su'ad ita ta fara yin gaba,sumayya na bayanta,ganin tayi wucewarta bata ko saurari bangaren anty maamaa ba ya sanyata ita shiga ta gaidata,taji dadi kuwa sosai,bangaren itama sai ita daya,dama can yaran mazan ba zama suka fiya yi ba,bare yanzu da kowa ya kama nashi gidan,don su a waje suke zaune,saidai kowanne yace idan yana sha'awa zasu zo suyi kwana biyu cikin gidan tunda suna fa wajensu,sosai taji dadi suka dan taba hira atsaitsaye ta wuce zuwa sashen ummee,tana gab da shiga su'ad ta fito tana hura hanci,ganin tana yunqurin bangazarta ya sanyata ja gefe,wani kallo su'ad din ta watsa mata sannan cikin harshen turanci tace
"Banza" murmushi ta jefeta da shi,cikin salon nuna qwarewa itama ta karya nata harshen da salon data koya a uk
"Banzayen ai suna da yawa ba daya bace,suna da yawa,bansan wacce daga ciki kike nufi ba"cewar sumayya sannan ta juya hankali kwance tayi shigewarta.

        Cikin kulawa suka gaisa ta samu gefan ummin ta zauna,bakin kowanme yayi nauyi,sumayya ya kunyar ummin ita kuma yau ummin surukuta ce ta motsa,saidai duk motsin sumayya tana lura da ita,sai take ganin ta soma sauyawa baki dayanta,jefi jefi suka dinga hira da ita har almustaphan ta shigo ya taddasu,baiyi zaton zai sameta har tsawon lokacin a nan ba,a sannan ummi ta shiga kitchen tana hanyar fitowa ta jiyoshi yace
"Baki gaji da zama ba?,akwai magungunan da zaki sha fa?"
"Me ya sameta?" Ta fada tana fitowa akitchen din tana fatan jin abinda zuciyarta keta faman raya mata,kanshi ya shafa yana jin nauyin ummin
"Ciwom ciki ne,kuma tana shan magani yanzu haka yana samun sauqi" ta san zurfin cikinshi qwarai,sai ta zauna tana cewa
"Allah ya sawwaqe,lallai kam ki kula da shan magani"ta miqawa sumayya wani dan bowl na plastic mai garai garai wanda akayi wrapping dinshi,maganar tata sai ya jita kamar a baibai,gaba yayi cikin jin nauyi yana cewa ta taso su tafi,ummi ta bita da kallo sanda ta miqe tayi mata sallama,sai taji tamkar ra tsaidata taji ainihin meke damunta,saidai kuma koma meye tasan indai da gasken ne abinda take zato to nan da wani dan lokaci qanqani zata fasu,suna ficewa ta samu kanta da yin sujuddushshukur,duk da bata tabbatar da cewa hakan bane,wani farinciki data jima bata ji irinsa ba yana ratsata,tamkar bata taba riqe jika ba.

*******     ******    *********

      Bai taba riskar kansa cikin farinciki ba irin na wadan nan kwanakin,bai taba tunanin haka samun d'a yake dadi ba sai wannan karon,ashe daa baki daya hasashene kawai yake yi,sumayya kam na fama da laulayi sosai,saidai Allah ya bata wata juriya da qwarin gwiwa,tana matuqar qoqari wajen boye ma almustapha,saboda kullum kwanan duniya tunaninshi na kanta ita da abinda ke jikinta,bai da sukuni yana gida koko baya gida,dawainiya yake da ita bilhaqqi,idan da yana da iko numfashi ma shi zaya yi mata,bata taba cin karo da soyayya kwatankwacin wannan ba,bata taba zaton ita din sumayya abar soce har haka ba,bangaren su'ad kuwa gani take Allah ya sita da bata taba gwada daukan ciki ba,musamman duk randa amai ciwon kai ko zazzabi ya make sumayyan,da yake sautari yanzun tana yawaita zaman falo,haka kawai sai taji bata sin zaman dakinta,a falo kawai take jin dadi,idan zata kwana tana amai ba abinda ya shalli su'ad,saidai ta watsa mata baqar magana
"waya kaiki da zaki cikawa mutane kunne da kakari?"ba yau ta soma gani ba balle ya dameta,saidai idan taga dama ta rama wani lokaci kuwa tayi banza da ita,abu daya ke damun su'ad shine yadda wani lokacin take vcin karo da zallar kulawa da sumayya ke samu daga wajen almustapha,tarairaya da damuwa,kalar wanda taci burin yayi mata koma fiye da haka,abu daya kawai ta sani shine indai sai ta dauki wannan kayan wahalar to kuwa ba zata samu wannan abun na,jira kawai take sumayya tayi nauyi kota haife,ta tabbatar a sannan duk wata gayya zata watse.

       Ko daya sumayya bata bari laulayinta ya hanata yin duk abinda ya dace ba,saidai abinda ba'a rasa ba wanda dole ka gaza saboda sauyawar yanayi,a hakan ma takan faki idanun almustapha ne ko,idan baya nan,idan kuwa ya dawo kaman yayi kuka,takan sanya dariya tace
"amman dai kai likita ne,ku kuke bawa matan mutane shawara su dinga motsa jiki sanda suke da juna biyu ko?"cafkota yake ya hukuntata son ranshi,ba hukunci na duka ko zagi ba hukunci ne zallar qauna.

       Ummi taso daurewa amma ganin dukkansu ba wanda ke da niyyar sanar mata komai bayan raga dukka wasu canje canje da suka wajaba ga mai ciki,randa ta gaji ta tsare sumayyan tazo gaidata da safe,kunya ta kamata,ta sumkuyar da kai,kamar zata nutse haka take ji,murmushin farinciki ummu ta saki tana furta alhamdulillah a fili kafin tace
"shine kika biye masa amiran umman khalipha zaku boye mana?,kyaci gidanku"itakam kunya take ji,don ko anty dije ta kasa gaya mata,da yake kwana biyu basanan sunyi tafiya ita da yara da mai gidan baki daya bikin 'yar qanin babanshi dake bauchi,kuma sun dan jima a can shi yasa ko rashin lpyr bata sani ba,zaunar da ita ummi tayi ta dinga zayyano mata dukkan wasu dabaru na kula da kai da ciki,ta kuwa qaru sosai,ummi tamkar ta jawo dare yayi haka takeji don wannan kyakkyawan labari ya isa ga kunnen baba prof.

        Yana zaune baban yana shan fura,jifa jifa yakan daga kai ya dubi ummi dake zaune gabanshi,ba don ya qoshi ba ya ajjiye mazubin yana dubanta
"Fadi kawai abinda ke bakinki....ummin su adam yau tunda na shigo naga bakinki nata motsi,tunda naga hakan nasan akwai magana sarauniyar miskilanci yau zan sha labari" murmushi ta saki,har yau baba bai daina tsokanarta ba,bai daina tuno mata gamonsu ba akaron farko wanda shi ya zama silar wanzuwar alaqar mai albarka dake tsakaninsu a yanzu
"Babban albishir ne wannan,bai kamata na baka shi haka ta sauqi ba me zan samu" murmushi yayi ya maida bayansa jikin kujera
"A'a a'ah,bazan fada ba sai naji girman albishir din tukunna"
"Kasan girmansa kuwa?"
"Har yakai na ganin sule na?"
"Yana da alaqa ai da sulen naka" jin ta ambaci sulensa ya sanya shi gyara zamanshi
"Wanne irin albishir ne haka zuwairiyya gaya min"
"Mun samu qaruwa fa agidan nan?" Dubanta yayi
"Ke ko maamaa?" Dariya ta saki yana toshe bakinta
"Kai.....haba prof..rufamana asiri don Allah,muna haihuwa surukai nayi....mamanka ke da juna biyu?"
"Maman tawa biyu ce ai wacce?"
"Mai dakin almustapha" daukewa wutar baba tayi kafin yace
"Allahu akhbar!,Allahu akhbar!!,kilishi.....da gaske kike ko da wasa,kada fa ki sani nayi abun kunya" dariya sosai ta dinga yi masa ganin yadda ya diriri ce
"Ta bakinsu nima naji,dama na jima ina zaton haka"kabbara hamdala da hailala baban ya dinga saki,tammat burikansa sun cika a rayuwa,Allah yayi masa baiwa ba shakka,a take ya daura alwala yayi sallah raka'a biyu ta godiya wa ubangiji,kallonshi kawai ummi take,gani take kamar yama fita jin dadi qwarai nesa ba kusa ba.

Daga daya bangaren sumayya ke fitowa daga bandaki bayan tayi wanka saboda kwanciya,wankan da bata samu yi ba sai a lokacin,ta hada har da kanta ta wanke,saboda sam ta tsani zuwa salloon,tunda almustapha ya taba gyara mata a gida taji tafi son nashi,yana zaune saman gado yana aiki kan system,fitowarta ya ja hankalinshi,ya daga kai yana dubanta,tayi kyau cikin rigar bacci,tana gaban mudubi tana daukan mayuka da hand drayer dinta ta zo dab da gadon ta jona ta sannan ta miqe,ta daga kai suka hada ido da shi,kusan ta saba da irin wannan kallon daga wajen almustapha,abun mamakin kuma idan suka fita sai ki wuceshi baima san dake ba,hakanan bai fiya gane mata ba,amma batasan ya akai ya koyi irin wannan kallon haka a kanta ita daya ba,iska ta hura masa a fuska suka saki murmushi tare
"baka sanni bane?"
"Kullum sabuwa kike koma min,daga zuciyata har idanuna,i dont know why?,ko kin iya sihiri ne?" Murmushi ta saki tana juya ido
"Yessss....tunda har na iya sihirce zuciyarka" kai yake gyadawa yana qaramar dariya
"Na yarda kam,tunda gashi kin hana mu koma wajen aiki....amma in sha Allah next week zamu wuce dubai baki daya,kinga...sai munfi sakewa ko?,saboda ina buqatar kulawa sama da haka gaskiya" fara'ar fuskarta ce ta ragu,baki daya taji baga qaunar sake komawa garin,duk da taji yana maganan gidanshi zasu wuce,amma tana ganin gwara kawai ita ya barta nan ya wuce da su'ad ita taji da kanta,system din ya ture ya amshi drayer din daga hannunta ya zaunar da ita a gabanshi ya soma busar mata da kan
"Nikam ko?,ina ganin kawai da zaka wuce da su'ad ni ka barni nafi son nan" wani abu ya taba zuciyanshi,tana zaton zasu iya raba gari shi da ita?,kwana biyun ma da yake ba tare da ita ba shi daya yasan me yake ji
"Ba haka na tsara ba" ya fada a taqaice,don bai son ta sake cewa komai
"Amma ko don yanayin jikina wai ko?"
"Na fiki sanin hakan ai"
"ina son cikina ya sake......."
"Shut up sumayya,kada ki gayan abinda kike ganin ya dace mana...."ya fada a kausashe.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣6⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*
Chapter 178 · 0% Book details