← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 210

Sashe 176

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gyara mata kwanciya yayi ya rage mata kayan jikinta sannan ya sumbaceta a goshi
"Ki kwanta ki huta,banson ko qwaqwqwarar magana ki sake yi,zan kawo miki maganin tsaida amai.....zanje nayi wanka yanzun"
"Na gode" ta furta a tausashe,murmushi ya saki yana shafa saman kanta,ji yake tamkar ya maidata jikinsa su koma abu daya
"Shshshshsh......nine da godiya,kin manta cewa babban gift kika bani wanda ba wanda ya taba bani kwatankwacinshi?"murmushi ta sake masa,ya sake sumbatar labbanta masu taushi dake burgeshi sannan ya soma takawa da baya da baya ya fice,ido ta rufe bayan fitarshin,tabbas so shike iya juya mutum ya sauya masa halayya komai girma isa da qasaitarsa.

Saura kadan yaci karo da ita sanda yake fita don bai tsammaceta a wajen ba,dauke idonshi yayi yayi gaba tabiyoshi a baya tana sauri don ta cimmasa,daidai sanda daya daga cikin ma'aikatan dake shirya abincin dare a kitchen ta fiti,da hanzari ta koma da baya zata koma kitchen din ganin tahowar almustaphan
"ki qarasa bakin qofan can ki gyara wajen ya baci da amai"
"To yallabai" ta furta kanta. aqasa cikin ladabi
"Amma girki take mana,ya za'ayi ta je ta taba qazan......"harara ya watsa mata wadda ta hanata qarasa fadin abinda take da niyyar fada,yayi gaba ta sake bin bayansa.

Yana tsaye yana ragw kayan jikinsa yayin da take tsaye bayanshi tana lissafo qorafe qorafanta daya bayan daya,tie dinshi ya cire ya wurgar saman gadon,cikin zafin nama ya fincikota sandan take tsaye bayanshi ya zaunar da ita bakin gadon da yake tsaye,ba waramin tsorata tayi ba da ganin yanayinshi,cikin kakkausar murya ya soma magana
"Wace irin macace ke da bakisan komai ba sai qorafi da tashin hankali?,wace iriyar macace ke da komai na mijinki bai dameki ba,lalurarki da buqatar ki itace gaba akan ta kowa,a haka kike so na kyautata miki?, ahaka kike so naji dadin zama da ke,bakisan komai nawa ba,bakisan duk wani abu da ya shafeni ba,na dauka laifi nane da fari na zaunar dake na karanta miki komai da yadda nakeson komai ya zama amma a banza,shin wai sai yaushe zaki sauya ne?,sai yaushe?,dame na rageki da shi na dukka haqqinki da Allah ya dora min?me kike so nayi miki?"ya qarashe maganar yana jin zafi har cikin zuciyarshi,idanu ta zuba masa tana dubanshi,idanunsa ya lumshe yana komawa da baya ya zauna,qoqarin cooling temper dinsa yake,baiso wani abu ya bata zallar farincikin da yake ciki a yau.

Kuyi manage da wannan,ba lallai gobe wani ya samu banyi alqawari ba,naso yau na barshi sai gobe na hada na turo muku mai yawa amma nasan zaku fison a baku ko kadan ne.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣5⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYUL AZIM*
___________________________________

      Zuba masa ido kawai tayi tana jin wani zallar bacin rai na ratsata,hawaye na bin kuncinta,ji take a duniya ya gama tozar tata,ya gama wulaqantata,a dacan ba haka ai ta sanshi ba,ta ina zata fara debo irin rayuwar da yake da muradi,sam ko daya ita ba zata iya ba
"Yanzu na sake tabbatarwa cewa baka qaunata almustapha,kanka tsaye kake gayan wadan nan maganganun?" Ta furta tana nuna qirjinta da yatsa,a nutse ya daga idanunshi ya zuba mata su,wato wanda yayi nisa baijin kira,barin hali sai mutuwa?,duk yadda ya kai ga dorata a hanya kenan qaryarshi ta sha qarya,bazata taba fahimta ba,ya fuskanci duk abinda yake gaya mata ashe bata bakinsa yake,kwanaki biyun da yayi dakinta ya bata lokuta sosai yana nusasheshe da ita abubuwa da dama,ta kuma kwantar da kai ta nuna tana dauka,ashe duka busa yake mata cikin kunnuwanta ba magana ba.

        Tsam kawai ya miqe ya ci gaba da rage kayan jikinshin,ya daura towel ya shiga toilet,yana tsaye riqe da qugunshi yana tarawa kanshi ruwan wanka ta turo qofat,hankalinshi kaf bai wajen,ya kasu gida biyu,wani na wajen sumayya yana tunanin tayi bacci kuwa?,yayin da daya ke kai kawo kan halaye da dabi'un su'ad
"Kana nufin kai maisheni banza da baka da lokacinta kenan?,amma ita waccar ai kana da nata lokacin ko?,har kana iya kamata bayan qazantar data futar,wanda iyakar sanina da kai kana da qyanqyamin da bansan lokacin daka zama haka ba" shiru yayi mata baice mata kanzil ba,iya tsahin rayuwarshi mutum ne da baya son hayaniya,tubewa yayi ya shige bathtube abinshi ya barta tsaye,sai ta fashe da kukan baqinciki ta juya ta fice zuwa uwar dakin.

          A nutse yayi wankanshi,ranshi na sake fari da haske a duk sanda ya tuna cewa nan da wasu watanni shima zai zama baba,nan da wasu watanni zai dinga gajin gilmawar yaro ko yarinua cikin gidanshi,yaron da za'a kirashi da d'anshi,mallakinshi,jininshi,murmushin farinciki ne ya subuce masa sannan ya miqe ya fito.

        Kwance rub da ciki ya tadda ta tana rusgar kuka,ya bude ma'ajiyar kayanshi ya fitar da shirt da trouser ya sanya,ya shirya tsaf abinshi ya fice ya sauka qasa,dining ya wuce yayi serving kanshi yaci abinci ya qoshi sannan ya wuce zuwa sashen ummee.

         A kwance ya taddata tana kallon news a al-akhbar,sallamarshi ta sanyata miqewa ta zauna tana amsawa,suna ranta shi da sunayyan tun jiya da bataji motsim daya daga cikinsu ba,ya qaraso wajenta fuskarshi dauke da murmushi ya zauna gefanta suka soma gaisawa
"Ya sumayyan take?"ummin ta tambayeshi ba tare data tambayi su'ad ba,rabonta data shigo ta gaidasu tun shekaran jiya da suka shigo tare da shi,amma ita hakan ba damuwarta bace tunda dama ba zamansu take ba zaman mijinta take,indai kuma suna zaune lafiya lau to da sauqi
"Lafiya.....na barota tana bacci"
"To masha Allah" hira suka shiga yi irin ta da da uwa,cikin daqiqu kadan ta fuskanci yaron nata na cikin farinciki da annashuwa qwarai,sai ta danganta hakan da cewa tsantsar farinciki kulawa da walwalar da yake samu ne daga wajen abokiyar zamanshi,ya jima gurin ummeen sosai sunyi hirar da suka jima basuyi irinta ba,bai bar wajen har bayan sallar magariba,sai da aka kirashi a waya ya qarasa baqin get wajen masu gadi da kanshi ya amshi saqon da ya bayar ayi masa order.

          Sanda ta farka taji dadin jikinta sosai,hakan ya sanya ta shiga toileta ta hada ruwan wanka mai dumi ta wanke jikinta,ta dawo gaban madubi daure da towel ta janyo kujera ta zauna kai,don kasala take ji ba zata tsaiyawa ba,haka kawai take jin wani farinciki da annashuwa tana ratsata,ta dinga kallon kanta a madubi tana sakin murmushi,lokaci lokaci tana shafa cikin nata wanda yake a dame da hannunta,itakam ciki na zuwa mata a bazata,tun yanzun Allah ya dasa mata so da qaunar abinda take so tamkar yadda taso abdallah tun kafin ta haifeshi,gababta ya yanke ya fadi sanda ta tuna irin gwagwarmayar da tasha hannun zainab,tsantsar makirci zalla da kuma wuyar da tasha kafin abdallah ua kai labari,ambaton sunan Allah ta dinga yi tana nemawa kanta da abinda ke cikinta tsari tun daga lokacin,bata fatan makamancin abinda ya faru da ita wancan karon ya sake maimaituwa da ita, akasalance ta dinga shafa man gabanta na faduwa ta wani bangaren.

        A nutse ya turo qofan dakin wanda sam bata ji ba saboda yadda hankalinta yayi gaba,takowa yake amma idanunshi na kanta yaja qarewa halittar Allah kallo,saboda banda qirjinta zuwa mazaunanta ba inda yake a rufe,dogon wuyanta da santala santalan cinyoyinta a bayyane suke,fatarta data sake kyau sai sheqi take yi,wani qaunarta da shauqinta na fusgarshi,a haka ya qarasa ya sanya hannayenta ya rufe idanunta,taushi da sanyin hannunshi kadai sun isa gaya mata waye?,ballantana da zuwa yanzun koda bata ganshi ba matuqar yana muhallin da take sai jikinta ya bata,matuqar tasiri yayi cikin rayuwarta,ya mallaki duk wani tunaninta,shiga da fitar numfashinta na tattare da nashi,bata son ta fiya zaqewa ne da yawa kawai,tunda ta sani cewa ba ita daya bace ta mallakeshi.
Chapter 176 · 0% Book details