Sashe 50
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har ta koma saman kujera ta kwanta don bata da sha'awar cin komai taga yari yar naci gaba da kallonta idan ta lura da kyau ma kamar qwalla ce a idonta,a hankali ta miqe ta zauna tayi kiranta,yarinyar ta iso gabanta ta zauna
"Me ya faru?me ya sameki naga kamar zakiyi kuka,ko yunwa kike ji?" Sai ta girgiza kai
"To mene ne gaya min" cikin raunin murya kamar kukan zai qwace mata tace
"Anty sumayya don Allah kada kici abincin nan" sai sumayyan ta hade rai tana dubanta
"Me yasa?"
"Anty,naga amarya ta bude leda sanda kika sakami yin shara tana ta leqe sannan ta koma kitchen ta bude flask din ta debo wani yalon abu ta barbada a ciki ta juya ta rufe ta wanke hannunta" sosai taji gabanta ya fadi,saidai bata son ta bawa yaran damar da zasu dinga labe ko qoqarin dauko gulmar fa'izan suna kawo mata,saboda haka ta sake hade rai
"Ke me yasa kika labe kina kallonta?" Da sauri ta girgiza kai
"Allah ba labewa nayi ba,tsintsiyar ce ta kunce a bakin kitchen din sai na tsaya daureta shine fa na gani" shiru tayi tana jinjina zancan cikin zuciyarta,sam bata son ta baiwa kanta qofar da zata zargi fa'iza kan abinda idanunta basu gane mata ba,saboda ko ubangiji ya fadi cewa HAQIQA WANI SASHI NA ZATO ZUNUBI NE,kai kawai ta kada bayan ta koma ta kwanta
"Shikenan,bazan ci ba,amma kada ki gayawa kowa abinda kika gani kinji nana?"
"To anty" ta fada tana kada kai
"Zan tafi anty lokacin islamiyya yayi" ta amsa kana ta laluba gefanta ta dauko alawa guda uku 'yan naura biyar biyar da takan ajjiye saboda su ta miqa mata,bata fiya son basu kudi ba don kada su saba da su ta bata ma iyayensu tarbiyyar yaransu,don ba kowa keson ka yiwa yaronsa kyautar kudi ba sabida gudun kada su saba da su,randa kuma basu samu ba su nema kota halin qaqa,Allah ya kiyaye.
Sosai ta zurfafa cikin tunanin maganar da naanan ta gaya mata,sai ta kauda tunanin daga ranta ta shiga addu'a cikin zuciyarta,ALLAHUMMAK FINIHIM BIMA SHI'ITA ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta,tana fata koma mene Allah ya mata maganinsa ya sanya tsarinsa a gareta har wani baccin ya sake daukarta.
Koda ya dawo yau bai samu yin wanka ba sai bayan yayi sallar magariba,yasan cewa ba samun ruwan wankan nasa zaiyi ba saidai ya debawa kansa,hakan ne ya sanya yana shigowa ya tara ya shiga bandakin,har ya shiga ya manta da towel dinsa hakan ya sanyashi fitowa.
Da hanzarinsa ya dawo zai shige,saidai wani abu da ya fisgi zuciyarsa ya sanya shi dawowa da baya,abinda ya faru watannin baya yake ji a jikinsa tamkar zai sake maimaita kansa ne a yau,a hankali ya zarw slippers dinsa ya taka zuwa qofar kitchen din,idanunsa suka sauka kan cooler din sumayya dake bude gaban fa'iza wadda ke dauke da dafa dukan shinkafa qarshen qurewar girkin fa'iza kenan.
Cike da hanzari fata da buri take barbada garin cikin abincin,don ta fuskanci cewa sam sumayya ko bude kwanon abinci bata yi ba,amma wannan karo taci alwashi kota halin qaqa sai ta sanya ta taci ko loma daya ce kai tama yankewa kanta ko dura ce sai tayi mata.
Tana karkade hannunta cikin nishadi taji caraf an riqe hannunta,tun kafin ta fahimci wake da alhakin riqe mata hannu gabanta yayi wata mummunar faduwa,a hankali tamkar wadda ta warke daga cutar laka ta daga kai suka hada idanu da mukhtar,wani matsanancin tsoro ya shigeta wanda kadan ya rage ta saki fitsari cikin wandonta sakamakon yadda taga idanunsa sun sauya kala cikin sakannin da basu wuce biyar ba.
Wani lafiyayyen mari ya yarfa mata wanda kafin ta ankare da a wanne hali taje ciki ya sake bin fuskarta da wani,hakan ne ya tilasta mata sakin wata gigitacciyar qara saboda ji taje tamkar fuskarta na shirin tsagewa ne,wannan shi yayi silar zaburar sumayya ta miqe ta fito a razane tana tsammanin ko gobara ce ta kama gidan nasu tunda ta bar fa'iza ne cikin kitchen.
Fitowarta yayi dai dai da wurgo fa'iza da mukhtar yayi zuwa filin tsakar gidan
"Subhanallahi" sumayya ta fada da qarfi tana nufar inda fa'iza take don ta d'agata
"Kika tabata sai mun samu mummunan sabanin da bamu taba samun makamancinsa ba ni da ke,sai nayi matuqar saba miki" taji mukhtar na ambata cikin wata kakkausar murya da bata taba zata yana da ita ba.
Yadda ya sake nufo fa'iza gadan gadan ya tsoratasu baki daya,sumayya ta janye gefe jikinta na rawa,bakinta na ambatar duk wata addu'a da tazo bakinta tare da neman agajin Allah ya kawo sauqin kowacce iriyar masifa da zata faru yau a gidan,yayin da tsoron da fa'iza taji ya sanyata sakin ihun neman agaji domin tsantsar bala'in da zata fuskanta ya fito muraran cikin idanun mukhtar tun kafin ya kai ga aiwatar da shi a kanta.
*mrs muhammad ce*
📚📚📚📚✍✍✍✍
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
3⃣4⃣
______________________________
*Bismillahir rahmnair rahim*
*tsarki ya tabbata ga Allah wanda mulki ke hannunsa kuma mai iko ne akan komai,wanda shi ya halicci rayuwa da mutuwa,ya halicci cuta da lafiya*
*haqiqa kalmomin bakina sunyi qaranci wajen nuna tsantsar godiya ta ga ubangiji bisa alfarmar samun lafiya da yayi min,bani da abun cewa face roqonsa ya bani ikon morarta ta hanyar bauta masa da yi masa biyayya*
*godiya ga iyaye na,babu shakka soyayya irin ta mahaifa babu kamarta duk fadin duniya,naga zallar ta a idanuwa da ayyukansu,ban da abin biyansu,saidai bazan gaza ba wajen yi musu addu'ar ubangiji ya musu kyautar Aljanna madaukakiya,ya musu kyakkyawan qarshe,yasa su cika da kalmar shahada,ya jiqan magabatansu,ya cika musu burikansu duniya da lahira,ya cika rayuwarsu da farinciki lafiya wadata da kwanciyar hankali*
*fans ina matuqar godiya a gareku,'yan watpadd bani data cewa sai fatan Allah ya muku kyakkyawan qarshe,'yan watsapp bazan manta karamcinku a gareni ba,ubangiji ya hadamu cikin jannatul firdausi,addu'o'in alkhairinku gareni fans ina roqa muku ninkinsa wajen ubangiji*
*_wannan shafi sadaukarwa ne a gareku_*
*mariya SB*
*aysha abubakar(maman khalipha)*
*mariya yola(mamam shuraim)*
*mommy maimuna musa*
*Allah ya saka da alheri ya qara zumunci*
______________________________
Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance cikin yake son gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin yake son gani,don rabonsa da ganinta tun randa malam ya gaya masa zancan cikin na nan a falonsa.
Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya cika,amma duk da haka da yammacin ranar ya shiga store din da ya saba siyayyar,shugaban gurin na ganinsa ya san me dame yake buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi total ya biya ya karba ya fice.
Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa,yana sanye da wani yadi mai qarancin kauri ruwan bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan bula mai turuwa,duk da sauyawar yanayinsa da rama amma hakan bai hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata masa dadi saboda a yanzun shikewa kansa komai,hakan ya sanya ya nemi wani saurayi wanda ke zuwa ya masa share share.
Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi izini ya shiga,duk da yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da,hakan baya masa dadi sam don baiga abinda su ya shiga tsakaninsu ba.
Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya amsa mata duk lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato sumayya),ba wata hira dama tun da can ke shiga tsakaninsu ba daya wuce gaisuwar,hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an gama shigo da kayan ya musu sallama ya fice.
Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron,yana da muradin ganin cikinsa gashi ko gilmawarta bai gani ba bare yaji muryarta,hakan babu wanda ya masa zancanta,jingina yayi da bangon soron hannunsa harde a qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta din,cikin ikon Allah sai ga zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da gidansu ta karbo klien zata wanke kwanukan da suka kammala abincin dare da su
"Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa" ya fada yana gyara tsaiwarsa,mamaki ya cikata,kamar tace wani abun kuma sai ta fasa ta juya ta koma ciki.
A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan rashin fitowa su gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d'anta ne,abinda ya faru kuma babu wanda ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN QADARARTA,hawaye ta soma gogewa abinda maman bata so kenan
"Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau nake"
"Na san da wannan,ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da lafiyar abinda ke cikinki ko" maman ta fadi
"Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi" tausayinta ya kamata,tana shirin yin magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda mukhtar din ya buqata
"Kin gani ai,sai kije ku gaisa" ta fada ta juya tana ficewa,hajibinta ta janyi dake rataye jikin sif ta zura sannan tayo waje.
Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallonta,sosai wannan karon cikin ya fito fiye da waccan karon,hatta tafiyarta ta soma sauyawa,kanta ma qasa din bata son hada ido da shi har ta qaraso,daga can gefe guda ta tsaya sannan tace
"Ina yini" ba tare data daga kai ta dubeshi ba
"Lafiya lau,ya jikin naki"
"Alhamdulillah" ta fada cikin sanyi,sai shiru ya biyo baya kowa da abinda ke saqawa cikin zuciyarsa,tsaiwar ta fara mata tsauri har ya lura da haka,sai ya waiwaya ya gangaro mata wani dutse da suke tokare qofa da shi ya furta
"Ga guri zauna" bata musa ba ta zauna din don tana da buqatar hakan
"Me yasa sumayya?,why?,kinga ayanzun kin zama silar da zamu raini yaronmu a mabanbanta gurare abinda ko a mafarki ban taba hasashen faruwarsa ba"ya furta wani daci na zagaya harshensa,idanuwansa na sauya launi,da sauri ta daga kai ta watsa masa fararen idanuwanta,take wani bacin rai ya soma bijiro mata,wato har yanzun zarginta yake kenan?,dama abinda yake son gaya mata kenan da har ya fiddo ta tana zaman zamanta tana lallaba rayuwarta.