← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 210

Sashe 200

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

        Zaune take saman gadon sosai tana jingine da bango,murmushi ne sosai kan fuskarta wanda har sai da ya sanya haqoranta bayyana,idanunta taf da qwalla sanda almustapha yake nufota dauke da daya daga cikin jariran wadda ke nannade cikin wasu irin kayan sanyi masu azabar kyau set da abun daukansu,gabanta ya qaraso shima idanunsa cike da qwalla yana dubanta tare da duban babyn,miqa mata ita yayi sai ta dauke idanunta qwallar data cika mata idanu tana gangaro mata saidai har yau murmushin dake kan fuskarta bai bace ba,da hanzari ua sake matsarta ya kama hannunta yana matsawa cikin rauni da rawar muryar da bata taba ji daga gareshi ba yace
"Kada kice zaki ji kunya babe....karbi diyarki ki gani in dauko miki dayar....duniyarmu ce baby duniyarmu....daga ni sai ke sai su karbi ki gani", ya qarashe maganar yana dora mata yarinyar saman cinyarta,tuni ta sanya hannu ta karbeta,cikin sakanni qalilan qaunar data ke musu taji ta soma ninkuwa cikin zuciyarta,sak jinin gidan baba prof,kana dubanta ko makaho ya shafa yasan jikar mutanen gwambe ce,photocopy na almustapha,sake komawa yayi ya dauko dayar ya dawo saman gadon ya zauna sosai kusa da ita yana bude mata fuskarta
" kalli usaina baby.....ba wadda ta miki kara?"ya fafa yana sakin dariya wadda ke qunshe da zallar farinciki,jinsa yake yau kaf duniya babu dan adam din da ya kaishi farinciki,ba wanda kuma ya kaishi sa'ar zuwa duniya,itakam murmushi kawai take bakinta ya gaza furta komai,Allah kenan,buwayi gagara misali,cikin rayuwarta kaf bata taba kawowa kanta haihuwa bama bare kuma aje ga haihuwar 'yan biyu,dai gashi a yau,Allah yayi mata kyautar da bata taba hasashenta ba,haqiqa Allah mai tsananin karamci ne,sosai almustaphan ya dinga sumbatu wanda tasan na tsantsar farinciki ne tana dubanshi tana dariya,ita din ma jinta take saman wata duniya ta farinciki tana yawo,ta kasa dauke idanunta daga yaram,ba don yaranta bane,amma zata iya cewa bata taba ganin jarirai masu ban sha'awa irinsu ba,sam ya mance da ya wanu kira gida ya fada sai data tuna mishi,a sannan ne ya dauko wayarshi,ummi ce mutum ta farko da ya soma kira,danda yake gaya mata tsaye ta miqe tana kabbara,bata qarasa jin zancan ba ta rankaya falon baba,saidai kash kafin ta isa tuni anty maamaa ta rigata kai labarin,wanda ta jishi je sanda take shigowa wajen ummi,a take baban ya mata kyautar kudi masu tsoka,ta dinga ma ummi dariya tana cewa saidai a tara a gaba,itama dariyan ta dinga tace rabonki ne,duk yadda baban yaso sakaya farincikinsa abun yaci tura,haka shima ya dauki waya ya dinga kiran abokai da 'yan uwa yana sanar musu,cikin lokaci qanqani labarin haihuwar ya karade kowanne sakaye,tsakanin baba da malam sai aka rasa wanda za'a yiwa murna,amira kuwa da anty dije kukan farinciki suka sanya,ta dinga kiran almustaphan tana roqonshi zata taho yace sam,sai ta saka kuka,tana so ace cikin dangi itace mutum ta farko data fara daukan yaran,abu daya ne ya saka mata haquri hoton yaran da ya dauka ya tura mata ta email adress dinta,don shi baya watsapp.

      Da kanshi ua sallami matarshi bayan ya tabbatar da cewa komai lafiya suka kama hanya zuwa gida,yana bayan motar shi da ita,baki daya yaran na hannunshi ya hana mata ko daya,ji yake idan ya rufe idanu zaiga kamar mafarki kamar almara,ashe duk arziqinka duk dukiyarka,duk farincikin da kake taqama kana ciki bai gama kammaluwa ba matuqar baka samu diyoyin da zaka alaqanta da jininka ba,ashe zallar farincikin da zata fadeshi sai randa ka ganka dauke da zuriya taka ta kanka.

        Daidai sanda suka nufi gidan su'ad na tsaye tsakar dakinta tana amsawa wayar da suke da mahaifiyarta
"Nifa gaskiya su'ad na soma sarewa,kinga tsantsar farinciki da doki da professor yake ciki sanda ya kira mahaifinki kamar ranar aka soma haifa masa jikoki,anya kuwa su'ad ba muyi kuskure ba?,ina da yaqinin Allah kadai yasan dukiyar da zasu samu su kuma mallaka tun suna qananunsu,wanda dukkan abinda suka samu zai koma fa hannun mahaifiyarsu ne" qatuwar ajiyar zuciya ta saki
"Bama wannan ba momy,wallahi na tabbatar na shiha uku,duk wani soyayya da tattali da adalci da almustapha ke qoqarin gwadamin ina da yaqinin sai ta ragu,tun cikin bai fito duniya ba kinga abinda yake?,ina ga ya fito sannan kuma twince mommy?,shi yasa nake tunani anya ba zamu sake plan ba?,na nemi dalilin haihuwa nima ko don na sake janyo hankalinshi zuwa gareni baki daya?"
"Dqlla can rufewa mutane baki,ke ta soyayyarsa ma kadai kike,soyayyar vanza,ana miki maganar kudi abokan tafiya qare magana,so nake fa ki zama cikin jerin attajiran da duniya ke lissafinsu kaman yadda a yanzu mijin naki yake,ke kadai ce fa 'yata ke daya na mallaka,saboda haka ina so naga kinyi shaharar da ko d'a namijin da yayi shekara arba'in yana gwagwarmaya baiyita ba"
"To yanzu ya za'a yi momy?"
"Cikin satin nan kisan yadda zakiyi kizo nan mu warwareta"
"An gama" ta fada tana katse wayar saboda motsi da taji kaman ana shigowa,a hankali ta tako ta fito zuwa falon,almustapha ne riqe da baby daya,wata mace mawociyarsu 'yar asalin qasar saudiyya dauke da dayan,fuskarta a washe tana tana yaba kyawu da girman yaran cikin harshen larabci,duk da bata fahimtar me take fada amma daga yanayin matar tasan tana yabawa ne da yadda yaran suke,idanu ta zuba musu tana karantar fuskar almustapha wanda bata san da dawowarshi ba saibyanzu,tunda sukayi magana ya tambayeta sumayya tace bata sani ba bai kuma kira ba hakanan bata bi ta kanshi ha itama,iya tsahon zamanta da shi bata taba ganinshi cikin wannan hali na matsanancin farinciki ba, saidai ba wanda ya kula da ita a cikinsu saboda tana daga bayan labule ne har suka shige.

      Yana fitowa daga dakin ya lura da ita,fuskarshi sake yake dubanta,bacin rai da take dannewa ya taso yafi qarfinta,sai kawai kuka ya qwace mata,sai ta juya da gudu gudu ta koma ciki,tausayinta ne ya sauko masa lokaci guda,yana tunanin rashin samun tata haihuwar shi ya motsa mata,wanda hakan zai iya faruwa ga kowacce mace,kowanne lokaci kuma yanayin kan iya motsuwa cikin zuciyarki har ki kasa controlling din kanki,sai ya rufa mata baya,samunta yayi kuwa zaune saman kujera tana buge buge da hannunta,dama ace dama ace ce fal cikin zuciyarta,zata so a ce itace ta samu wannan yaran ba sumayya ba,wai shin me ya hanata tsayawa ko guda daya ta samu ne?,ba shakka tana ji a jikinta lokaci yayi da zata tashi ta dawowa da kanta dama ta samun haihuwa a gareta,a tausashe ya zauna gefanta yana riqeta,baison idan wani abu ya sameta ta dinga irin wannan acting din dake nuna zallar rashin yarda da qaddara,cikin taushi ya soma ce mata
"Am sorry dear....ba kuka zakiyi ba,addu'a zakiyi Allah ya kawo mana,komai a duniya yana da lokaci sannan komai yai farko yana da qarshe banda ikon Allah,matuqar kina da rabo ta babu makawa sai kin haifa kema"
"Ko bani da rabo wallahi sai na yishi,sai na haihu nima" tsauri maganar tayi masa,haqiqa ba qaramin illa da tasiri dabi'un yahudawa marasa tauhidi suka yiwa su'ad din ha,saidai yana da burin sosai wajen ganin ta daidaitu,duk da hakan ma alhamdulillah,ya rabata da shigar banza ya sata tsaida sallah,koda kuwa zata yita ne bayan wucewar lokacinta
"Subhanallah,kiyi istigfari,babu bawan da yafi qarfin QADDARA,saidai addu'a na maida MUMMUNAR QADDARA ta koma zuwa KYAKKYAWA,ki roqi Allah sai ya kawo komai a sauqaqe,ba wayonki ko dabararki ba,ita kanta ada can an taba kiranta juya,an fidda mata rai zata haihu,amma a yanzu gashi ke ya faru?" Cikin hikima yake gaya kata kalaman kwantar da hankali,saidai jinsu take kaman busat sarewq,abu daya ne ya dan kwantar mata da hankali,kasancewa da yayi tare da ita duk da ba ranarta bace,da kuma yadda yake lallashinta,saidai ba shakka cikin satin nan zata san yadda zata wuce america don bazata juri rasa cika burin data qudurtawa ranta ba.

      Maqota biyu da suke da su wadanda ba yarenta ba saidai 'yan uwantaka ta muslunci da tsananin kirki da suke da shi,wanda batasan suna da shi ba sai yanzun da haihuwar 'yan biyu dake da farinjini suka sa tasan hakan,suna kula da ita sosai,akai akai suke leqota da kalar abinci da kulawa da sukewa maijego,akwai mai tayata zama guda daya daya samu wanda ta kasance mutuwar qasar ghana ce,zaman sana'a yasa take zaune a qasar,sai ta kasancewa sumayya tamkar yar uwa,sosai matar ke kula da ita,tana da qoqari da zafin nama qwarai,babu abinda sumayyan ta nema ta rasa,hatta da shi mai gayya mai aikin idan ya fita sha daya,biyat na yammaci ya dawo gida,koda yashe burinsa ya ganshi tare da su,a haka ma idanun su'ad yasa ya dan rage wasu abubuwa tare da danne daukinsa,don har ga Allah tausayinta yake ji,yasan cewa rashin haihuwa babbar damuwa ce dakan iya zamewa wasu matan ciwo cikin zukatansu,abinda bai sani ba shine ta soma girbar abinda ta shuka ne ba tare da shi karan kanshi ya sani ba,wani tsananin son hauhuwa ne ya mata mugun kamu cikin kwanakin da basu haza hudu ba,sosai walwala da kuzarinta ya ragu,kishin yaran da uwarsu baki daya ya gallabeta,ko sau daya tak bata taba kusantar dakin sumayya ba bare tace zata ga yaran,wani abu ke tokare mata wuya duk sanda taji sautin kukansu,ji take kaman ta kaudasu ko ta samu hutu.
Chapter 200 · 0% Book details