← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 210

Sashe 19

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanu sumayya tabi tsakar gidan nasu da shi,ko ina kaya ne na yaya yahanasun a barbaje a qasa,gaban sumayyan ya fadi,jikinta yayi sanyi,ta qarasa tsakar gidan,hannu ta sanya tana tattare kayan nasu waje daya,tsawa yaya yahanasun ta daka mata
"Kada ki sake taba mana kaya shegiya munafuka 'yar gidan malamai,to wallahi bari na gaya miki idan ma shiga tsakaninmu kikayi da fa'iza kinyi kadan,hakan da takeyi bazai tunzura zuciyata tunda nasan ba cikin hayyacinta take ba,ke sayyada maza ku hade mana kayan gefe guda mu jira shi muntarin ya dawo" sororo tayi tana dubanta
"Daina kallo na mayya,li'ilafi quraishi,ni baki isa ki cinyeni ba" sai ta kauda kai ta wuce kai tsaye dakinta ta bude ta shige.

Bata sake fitowa yayi zamanta cikin dakin,sai ta qirqiro wasu 'yan qananun ayyaukan ma cikin dakin nata don kawar da duk wani tunani da zai dameta,tana aikin tana ambatar hasbunallahu wa ni'imal wakil,allahumk finihim bima shi'ita,hakan ba qaramin taimaka mata yayi ba,sai ya tafiyar da lokacinta cikin sauqi har aka kira sallar magariba,ta miqe ta fito domin daura alwala,suna zaune gefe daya na tsakar gidan da qullin kayansu,sosai har cikin zuciyarta taji babu dadi,bai kamata mukhyar yazo ya taras da su haka ba,ko babu komai 'yan uwansa ne jininsa ne,kuma tayi imami cewa idan wani nata ne shima mukhtar din ba zaya wofantar da su haka ba,ta danne zuciyarta ta qarasa gurinsu,cikim sanyin murya tace
"Don Allah yaya ki shigi dakina,ko da ba zaki zauna din ba ki shigo idan yaso idan ya mukhtar din ya dawo sai asan yadda za'ayi din" wani kallon banza ta bita da shi
"Ke wallahi ki fita a idona,wai ke wacce iriyar mayatacciya ce ne,nace bazan shiga ba dole ne,to bari kiji,idan ma wani laqani aka baki na sai na shiga sannan zaki samu galaba a kaina to wallahi ki gayawa malaminki kunyi qarya kun kwana da yunwa" jikinta sai yayi sanyi ta kasa tafiya,zuciyarta na gaya mata basu zama masu kyautawa mukhtar ba indai yazo ya tadda jininsa a wulaqance,duk da tarin izgilu cin fuska da cin mutunci da ita yaya yahanasun ke jifanta da shi,ba ita take dubawa karamcin mukhtar take dubawa.

A haka mukhtar din ya shigo ya riskesu,tayi masa sannu da zuwa ta karbar kayan hannunsa duk da ba ranar girkinta bane,ya amsa yana duban yaya yahanasu."a'ah,yaya yanzu kuka zone na ganku a nan a zaune ku da kayanku"kai ta girgiza
"Inaaa,ai tun azahar muna gidan nan" cikin mamaki ya dubeta tare da zaro ido sai ya dubi sumayya yana jifanta da tuhuma,qas tayi da kanta don bata da ta cewa,ganin haka yasa ya dubi yaya yahanasun
"Amma kuke zaune a nan?,kada kice min nan kuka wuni?" Waiwayawa tayi ta dubi sumayya
"Sai ki bamu guri ko ko ban isa ba?" Bata ce uffan ba ta koma dakinta duk da alwala ta fito da niyyar daurawa.

Sai da taga shigarta dakin sannan ta maido dubanta ga fa'iza
"Mutuniyar tamu,wallhi lafiya lau ta karbemu,daga yi mata tambaya kan naji shiru har yanzu mun samu qaruwa ko a'ah ta shiga masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,qarshe tayo mana waje da kayanmu" sosai ransa ya baci,ya soma huci cikin fushi yace
"Fa'izar?,to da tayi muku haka gidanta ne ko nawa?,bazan lamunci wannan iskanci ba" ya fada yana juyawa zuwa ga dakinta wanda fa'izar na ciki tana jin kowa tayi lakur abinta.

Da sauri yaya yahanasun ta dakatar da shi
"Kaga muntari bana son hauka fa,laifi muka yi mata mu mika bata mata rai,nasan kuma zata huce,don haka bance kaje ka sake bata mata rai ba,kadai lallabata har ta yarda mu zauna taren" jagale yayi tare da juyiwa yana duban yayar tasa,take kuma ya tuna sunfi kusa fa ita da fa'izan,ya ma kamata a yau din ya qyaleta taga halin fa'izan taga wace ita ra'ayil ain wato ganin ido,saboda haka sai ya saki murmushi cikin salon canza shawarar da yayi farat daya,gyada kai yayi
"Shikenan,muje to a lallabatan" da sauri suka miqe yaya yahanasun tana cewa
"To,to ai kaga hakan yafi" tabi bayansa.

Tana miqe daga kan gadonta tana taunar chewing gum dai dai,zama sukayi kan kujerarta dake fuskantar gadon,yayin da mukhtar ya qarasa gefan gadon ya tsaya,duk da cewa ransa a matuqar bace yake,ji yake kamar ya janyo fa'izan ya yi mata dan banzan duka ya watsar amma sai ya dake
"Fa'iza,me yasa ba zaki bar yaya ta zauna dakinki ba,ai ina ganin bai kamata ba" hura hanci take tana tunanin ko yanzu mukhtar ya soma tsoronta,inko haka ne kowa tasa ta qare,tabbas sai kowa ma yaci ubansa cikin gidan
"Mukhtar banga dama bane,bari kaji" ta fada tana miqewa zaune kan gadon
"Na farko bansan sa ido gaskiya kuma na fuskanci su sun fara koyar wannan halayyar,na biyu na fuskanci ni aka rainawa wayo,ga mai daki ciki da falo can ba'a dosheta ba saini mai daki daya kamar zuciyar talaka" ba qaramin dukansa maganar tayi a zuciya ba amma ya hadiye don so yake ya jata aje gun ta dora da
"Saboda haka su nemi gurin kwana don ni bazan zauna da wadan nan qattan a daki na ba" wani qullutun abu ne ya tokare masa wuya qanda ya hanashi sake magana,sai yaya yahanasu da tace
"Haba ke kuwa fa'iza,kwana nawa ne duka duka mun koma gidanmu,ai ban zaci ko wani na turo gidan nan ki masa sauki a dakinki ba zaki kasa,kada fa ki manta nice silar zuwanki gidan nan" zabura tayi tana dakatar da ita
"Kinga kada ki sake kice zaki mun gori,don ke kika kawoni gidan ai bake kike aure na ba,buqatar maje haji sallah kuma da taku buqatar ai ba haka siddan kika kawoni ba,sabida haka kuje ni don Allah kada ku cikan kunne,tunda kun nace sai kun zauna a dakin kuje zanyi tunani,ko kwana daya ne kuyi kafin ku koma inda kuka fito".

Ba qaramin daurewa kan yaya yahanasun yayi ba da kalaman fa'iza,duk yadda fadima ke gaya mata sai yau ta sake tabbatarwa da lamba daya ce ita wajen rashin mutunci tsiya da tsiyataku
" fa'iza ni kike gayawa haka"kanga tsaye babu kunya tace
"Na fada din,ke kike aurena ne nace wai kawai da zaki takuran,wannan fa kamar kina lissafin sau nawa nake kwanciya da mijina ne"tuni maganar ta sake dora yaya yahanasun kan dokin zuciya
" ke qaramar mara kunya,ko bani nake aurenki ba kinsan ina da power din da zan sa ungulu ta koma gidanta na tsamiya ko?"
"Bismillah,sai mu gani " ta fada tana murguda baki gami da turo daurinta gaban goshinta ta dage kanta idanunta na kallon ceiling din daki.

tabbas tana jin yau idan bata nunawa fa'iza isar da take da ita a wajen mukhtar ba bata huce takaici ba,idanunta taf da bacin rai ta dubeshi
"Mukhtar,ina so a yau yau din nan ka sawwaqewa fa'iza,yanzun nan" ta qarashe cikin daga murya.

Duk da cewa ranshi ya kai qololuwa wajen baci kan abinda fa'izq ta yiwa yaya yahanasun amma sai ya danne komai tamkar bai b'aci ba,ai dama duk wanda ya sai rariya yasan zata zub da ruwa,to ya kamata yaya yahanasun taga yadda tata rariyar ke zubar da nata ruwan,ruwan kuma da baiyi qasa a gwiwar malalowa ya jiqata sharkaf ba,kai ya kada sannan yace
"Kan me zan saki fa'iza yaya,ni babu abinda ta yimin,hasalima fa'iza ai zabinki ce,kinga bai kamaci na wofantar da ita ba,zan riqeta hannu bibbiyu kamar yadda kika umarceni" tsawa ta daka masa
"Mukhtar,kai makaho ne?,ko kuwa kai kurma ne,baka ganin abinda ta yimin ne,ni na umarceka nace ka saketa kamar yadda na umarceka ka aureta a baya" kai ya sake kadawa tare da yin tattaki don barin dakin yana cewa
"Ki gafarceni yaya,amma yanzu na fara zama da fa'iza,don ni bata aikata min komai ba" sai ya fice abinsa ya barsu ana kallon kallo.

Kira ya qwalawa sajida ya sanyata suka dinga jidar kayayyakinsu yana tayasu suna kaiwa dakin sumayya wadda ke zaune kurum tana ji da ganin sarautar Allah,sai da suka kammala tsaf yaya yahansun na dakin fa'iza suna cecekuce,ganin abun na sake qamari ya sanyashi shiga dakin ya janyeta yana fadin
"Kiyi haquri yaya yahanasu,kizo ku zauna dakin sumayya tunda itan da kuke so ta qiya" sai ta waiwayo ta bishi da ido galala tana kallonsa,mukhtar din da baison bacin ranta?,mukhtar din da baiso a tabata amma yau an mata cin kashin data jima rabon ta da irinsa amma ya kasa cewa uffan,kardai mallaka fa'iza tayi masa wadda baya iya qetare umarninta?,ranta ya shiga suya ta shiga fatar cewa Allah yasa ba haka bane,bata da wani zabi a yanzun illa ta bishi,idan yaso daga bisani tayi tunanin mafita a tsanake.

Bayan sun shiga dakin ta zauna sannan ya kira sumayya ya fice zuwa dakinsa.

Zaune ta tadda shi dafe da kansa,a hankali cikin kasala ta zauna gefansa,ta sanya tafin hannunta tana shafar bayansa a hankali,tasan fushin mukhtar din,saboda haka ta tabbatar ransa na a bace ne,kusan minti goma baice komai ba kafin daga bisani ya dago ya dubeta
"Sumayya" ya kira sunanta,a tausashe ta amsa sannan ya dora
"Gasu yaya yahanasu nan zasu zauna dakinki,kinsanta sarai ita da yaranta baki daya,baki buqatar muraja'a kansu,na shaideki da haquri wannan halinki ne,to amma don Allah ki nunka haqurinki,baqunta zasu mana na wani d'an lokaci,insha Allah zanyi qoqari na kammala musu gyaransu cikin qanqanin lokaci,idan da na kammala ma gini na sabon gida na can zan ara musu su zauna gudun fitina,kiyi haquri da su don Allah ki sake ninka kawaicinki" kai ta girgiza
"Haba ya mukhtar,ai ba roqona zaka yi ba,umarni kadai zaka bada,da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne,nima yaya take agurina,insha Allahu babu wata matsala ko damuwa"
"Na gode,Allah yayi miki albarka"
"Amin yaya" ta fada tana sakin qayataccen murmushinta wanda har sai da ya sanyashi tsura mata idanu,hannu ta turo sautin idanunsa kamar zata tsone masa yaja baya suka saki dariya baki dayansu.
Chapter 19 · 0% Book details