Sashe 12
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Bakaji abinda nace bane?,ceww nayi ka biyoni" kai ya shiga girgizawa cike da bacin rai
"Indai ni nake auren sumayya da fa'iza to a dakina nake buqatar ki fadi duk abinda kika zo yin shari'ar a kansa" ya fada yana juyawa zuwa dakinsa bayan yasa maqulli ya bude,basu ce komai ba ta ja hannun fa'izan suka canza akalarsu zuwa dakin mukhtar sumayya ta rufa musu baya.
Kuka take har da na qarya da munafunci,da qyar yaya yahanasu ta shawo kanta,yayin da sumayya da mukhtar ke gefe sun zubawa sarautar Allah ido,sumayya na kallon sabon shafin makirci da duniyar kishi ke dauke da shi,sabon darasi kuma sabon karatun da bata san da shi ba a duniyar aure sai yau,yayin da ran mukhtar ke tafasa,wannan har macen aure ce?,matar da cikin kwanaki uku rak! Ta fara birkita duniyarsa da zaman lafiyarsa gaba daya?,cikin kwana uku rak! Har an fara zuwa musu sasanci da shari'a,abinda iyakacin zamansa da sumayya ba'a taba samu ba cikin tarihin rayuwar aurensu.
Sai da ta kammala shawo kan nata sannan tace ta zayyane abinda aka mata,nan ta baje shafin qarya da gaskiya ta gwamutsata ta mata ado,yadda take tsara laifukan da take ikirari anyi mata kai ka rantse cewa shekara sukayi tare.
"To yanzu me kike so ke fa'iza?" Yaya yahanasu ta tambayeta
"To ni dai yaya gaskiya babban abinda yake cimin tuwo a qwarya shine,abinda aka kawoni nayi gidan nan na zube 'ya'ya mukhtar bai fa dauko turbarsa ba,don har yau bansan d'a namiji ba wlh" ta fada kanta tsaye ba tare da kunya ba,ita kanta yayanaganar ta mata nauyi,har ta danyi shiru tana nazarin ta yadda zata yiwa mukhtar magana kan hakan,amma dole ta fidda kunya,idan ba haka ba wankin hula ya kaisu dare,mukhtar shi kadai ne d'a nami acikinsu,saboda haka dole a kawo qarshen wannan tafiya,nan ta rufe ido ta dinga yayyafa masa bala'i,qasa yayi da kansa cikie da baqinciki da qunan rai har ta kammala fadanta
"Kai muntari,ashe kai ba adalin namiji bane?,to wallahi a daren yau din nan nake so a kawo qarshen komai,kada ka sake ka gama kwanakin ba tare da komai ya afku ba,kuma kada ka kuma bari ta kawomin qararka kan hakan" Ta fada tana kada yatsu,kai ya dago ya watsawa fa'izan wani matsiyacin kallo sannan ya kalli yahanasun
"In sha Allahu" ya fadi a sanyaye,sumayya dake gefe kunya duka tabi ta cikata,ga wani takaici da ya cika mata zuciya.
Sake juyawa tayi ta kalleta
"Sai kuma me?"
"Yauwa yaya zancan bawa waccar maqullin ma'ajiyar abinci,sam ni wlh bab yarda ba a raba a bawa kowa nashi kawai" sai ta sake juyawa ga muntarin
"To kai kaji sai......." Cikin fushi da baisan ya taso masa har ya katse yaya yahanasun ba yace
"Wannan kuma bata isa ba tayi kadan,iskancin naki naga ya fara samun gindi zama,waccw iriyar shari'ace haka yaya kike?,ita daya ke da abun fada?,ita daya ke da bakin magana,to wallahi ni ba sauna bane da zan nemo abu da zafin gumi na a wulaqanta shi ba,zata iya zama idan taga zata iya zata kuma iya kama gabanta" sarai tasan halin muntarin,akwai sanin ya kamata kawaici da dauke kai,amma fa idan aka taboshi bashi da dadi,tasan cewa har yau bai son fa'iza baison auren gudun kada aje garin neman gira a rasa dukka idanuwa ya sanyata itama hayayyaqo masa cikin salo irin na nade tabarmar kunya da hauka
"Oh ni yaha,innarmu ta haifawa wata ni kuma na rainan mata,yanzu muntari har kayi riqar da zaka dinga haikemin,qwarai wannan abu yayi kyau,ko da yake baka da laifi wannan baqar jarabar da Allah ya jarabcemu da ita ne,dama ance idan bakayi wasa ba abinda ke baka tausayi wata rana shi zai koma baka tsoro,ita ba amfana ake da ita ba ma baki daya sai ita dake amfana da mutane" haka ta dinga zazzaga,abun da ya sake bata mata rai ganin yadda sumayyan tayi burus a maimakon a baya da idan tana irin hakan take zagewa tayi ta bata haquri wani lokaci har da kukanta.
Qarshe ta kama hannun fa'iza tace ta tashi suje dakinta tana son ganinta kafin ta wuce,fa'izan ta kalleta
"Yanzu na haqura kenan?"
"Fa'iza,waccar da kike gani saidai mu hadu muyita taya muntari da addu'a,don idan nayi rantsuwa ko kaffara ba zanyi ba ba cikin hayyacinsa yake ba,ke dinma inaga rabo ne ya rantse shi yasa kika shigo" ta qarasa maganar suna ficewa fa'iza na qunqunai wanda hakan ya sake bata ran mukhtar,ji yake tamkar ya shaqeta ko zayaji sauqin bacin ran dake cin zuciyarsa.
*mrs muhammad ce*
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
______________________
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*wa iy yamsaskallahu bi durrin fala khaashifa lahu illahuw,wa iy yuridka bi khairin fala raadda li fadhlih*
_____________________
0⃣9⃣
Ya rantse sai ya hukunta ta,sai ta gane bata da wayo,'yar bariki ce ita ko mai,zai nuna mata bata iya iskanci ba.
Miqewa yayi ya dauki jakarsa zai fice sumayyan ta sha gabansa
"Ya mukhtar,bai kamata ka fita cikin wannan halin da kake ba" sai ya tsura mata ido yana kallon yadda ta langabe kamar zata yi kuka,haka kawai ana son shiga tsakaninsu da farincikinsu kam wani dalili can maras tushe,kan wani abu da basu isa su yiwa kansu shi ba sai Allah ya ga dama,sai ya saki murmushi don ya kwantar mata da hankali,ya sanya hannunshi ya shafi gefan fuskarta
"Kada ki damu sumayya,ina gane komai" yayi kissing goshinta yana fadin
"Sai na dawo" ya juya ya fita a gaggauce don bai son ma yaya yahanasu ta kuma tsaidashi.
Kai ta kada sannan ta fito daga dakin ta ja ta kulle masa ta tafi da key din dakinta,cikin falonta tayi zamanta bayan ta kunna redio tana sauraran labaran rana freedom.
Tana kammala jin labaran ta shiga kitchen ta dora abincin rana,cikin kitchen din ta zauna har ta kammala saboda jallop din shinkafa ta musu,ta zuba cikin cooler ta ajjiye cikin kitchen din kana ta nufi dakin fa'izar,ita daya ta taras da alama yaya yahanasun ta tafi wanda ita sam batasan ta tafin ba
"Ga abinci can cikin kitchen na gama" ta fada ta juya ta fice ba tare da ta jira amsarta ba,bata zaci ta ci ba sai da ta shiga dora sanwar dare taga babu komai cikin cooler din tas,mamaki ya kamata saboda batayi tsammamin zata iya cinyewa duka ba,don har da yaya yahanasu ta dafa,ta kada kai ta shiga sabgar dora abincin dare.
Sau biyu suna kacibus da fa'izan na fitowa a kitchen din sanda take tsaka da girkin,tuwon semo tayi miyar kuka wadda ta wadata da man shanu da nama,ta kammala ta jere komai cikin kitchen sannan ta nufi famfo ta tara ruwan wanka tana jira botikin ya cika.
Da sauri taga ta fito daga dakinta ta suri silifas ta fada bandakin ta bame qofa,sai ta bita da ido kana ta dauke kai,tana tsammamin matsuwa fa'izan tayi har haka?,ta kashe fanfon ta koma gefan rijiya ta zauna tana tsumayin fitowarta.
Wasa wasa har ba fa'iza ba alamunta,abun har ya dan bawa sumayyan tsoro,sai ta miqe ta isa ga bakin bandakin ta qwanqwasa qofar,gyaran muryar da taji tayi mata ya tabbatar mata komai lafiya,sai ta koma bakin riniyar ta zauna tana ci gaba da dakon fitowarta.
Ba ita ta fito ba sai da taji shigowar mukhtar gidan,a qalla awa daya kenan ta kwashe cikin makewayin,sumayyan ta miqe tana masa sannu da zhwa tare da jin nauyin zuwa ya taddata babu kwalliya saboda ta riga da ta saba al'adarta ce daya dawo ya sameta tsaf.
Ta miqa hannu zata karbi ledar hannunta taji anyi wuf an karbe,da mamaki ta waiwayo fa'iza ce wadda batasan sanda ta fito daga bayin ba ke tsaye tana ta faman doka masa murmushi tare da yi masa sannu da zuwa,a dake yake sa mata,sai sumayyan ta koma ta dauki botikinta zata shige wankan
"Ai wlh ni da ke ne cikin gidan nan,indai ina nan an daina wannan karuwar kwalliyar daren" ta fada bayan da taga mukhtar ya shige dakinsa,waiwayowa tayi ta dubeta sai ta saki murmushi sannan tace
"Ko?"cikin qufula da ganin yadda maganar bata da da ta da qasa yadda taso ba tace
" eh,ko kina musu ne?"kai ta gyada sannan a taqaice tace mata
"Zamu gani" ta shige bandakin abinta,yatsa ta ciza takaici ya kamata,wai dama can yarinyar ba tsoronta take ba basaja take mata ko kuma zugata aka soma yi?,qwafa ta ja domin bata da amsa ta shige dakin angon nata.
Ga mamakinsu suna shirin soma cin abincin dare sai ga fa'izan,tana wani murmushi ta raba gefan mukhtar din ta zauna
"Naga ya kamata nima adinga cin abincin da ni don qara donqon zumunci ko?" Ta fada tana wani kashe masa ido,ha fuskanci yau sai wani rawar kai take,amma idan batasan kan garin ba shi zai mata kyakkyawan kwatance,babu wanda ya tankata iyaka aka tura mata kulolin ta debi yadda taga zata iya.
Ita da sumayyan kusan tare kowannensu ya sanya lomar farko a bakinsa,idanu sumayya ta zaro sakamakon wani dan banzan gishiri da ya cika harshenta har zhwa kwanyarta,take qwaqwalwar tata ta tafi tunanin ta yadda akayi hakan ya faru?,a iya saninta lafiyar Allah ta kammala komai ta gyatta shi,amma me ya kawo wannan sauyin?,ko dai harshenta ke shirin samun matsala?,.
"Qundun uban nan" abinda fa'iza ta fada kenan wanda shi ya tsinke zaren tunanin sumayya,kallon mukhtar suke dukkansu kowanne da tasa manufar a zuciya,zaquwar mukhtar yayi magana ta samu filin baje hajarta da kuma mamakin yadda yaqi maida hankali ga kalamanta takeyi,cikinsu babu wadda ya kalla saici gaba da sambada lomarsa yake,yayin da sumayya tayi qas da kanta ta daure duk wani abu da take ji kan harshenta itama taci gaba da kai lomarta tamkar babu wata matsala dake waka na.