Sashe 160
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari ummee ta danqa mata kayan fitar biki kamar yadda ta yiwa ni'ima fahariyya da su'ad,haka ummeen take,duk wani sha'ani idan ya taso sai ta yiwa jikokinta da 'ya'yanta kayan fitar biki,macace mai hannun kyauta,hakan ya sanya mutane da dama kejin dadin zama da ita,kowa takan masa dinkin ne daidai da ra'ayinsa ko abinda taga zaya dace da shi,godiya sosai ta yiwa ummeen har taso tafi wadda ni'imah ke mata,bangarenta ta koma ta dora girki,karo na farko,girki tayi musu mai shegen dadi wanda ya janyo wasu ma bangaren nata,ta diba wani da kanta ta kaiwa ummeen,ba qaramin burgeta abincin ya yiwa ummee ba,ba shakka almustapha ya dace,ya samu macen da suka jima suna masa addu'ar ya samu,godiya ta dinga mata har hakan ya bata kunya,har gidan wanda ke musu dinki yazo ya karbi dukkan dinkunansu wanda zai gama musu ne a kwana biyu kacal,abinka da kudi qare magana,shi dama haka dinkinshi yake,manya mutane yakewa dinki saidai fa babu saba alqawari,kaman qaramin kamfani ne,yana da ma'aikata,kowa da abinda yake hadawa,wani hannu,wani gaban riga,wani bayan riga,wani kalmasa haka dai da sauransu
Laila,khalipha,hafiz da minal duka sun shigo,ta rasa yaya zatayi da laila,ta addabeta,duk bayan mintina sai ta tanka ta
"Wai,wallahi ansha da mami da batazo taga yadda 'yarta ta koma ba,don Allah khalipha zaka ce anty summynmi ce wannan" da yake shima uban magana me sai ya biye mata sukayi tayi,dariya ta shata ta gode Allah,batasan sanda lailan zata daina shegen surutu ba haka,antyn dijen ce taqi shigowa,ta dinga kiran layinta tana qorafi amma saidai tayi dariya tace zata shigo,gashi ita babu damar fita tunda bata sanar masa zata fita ba,haka kuma kunya take ba zata iya kiranshi ba,
Ranar laraba mai qunshin dakewa su ummee tazo har gida,daki ne babba aka ware a can bayan gidan anan take zama idan tazo musu qunshin,ummeen da kanta tasa aka kira mata sumayya tace ta shirya za'a yi mata qunshi,qarfe hudu na yamma aka gama mata baki daya ja da baqi,kowa yasan yadda lalle ke yiwa farin mutum kyau walau ja ko baqi,kamar ka cire hannun saboda yadda ya zanu ya zauna sosai kamar dorashi aka yi,ita kanta ummen sai da tace masha Allah,ta dubi sumayyan tana cewa
"Kije kinyi baquwa,umman khalipha sai yau taga damar zuwa" farinciki ya cikata, bata iya tsayawa ta qarasa cire lallen na hannunta sai ta miqe ta nufi sashen nata,da gudu ya qarasa ta rungume anty dijem,sarkin kuka har ta soma tara qwallar
"Au ashe har yanzu baki girma ba sumayya?,inaga tare zaka daina kukan quruciya ke da abdallah da alama" sai ta saki antyn tana dariya,daki suka shige da anty dijen,farinciki fal zuciyarta,kallo daya zaka yiwa sumayyan kasan cewa kwanciyar hankali ya fara samuwa,kasa gayawa antyn komai tayi,sai take jin kunyarta,to ita din ma bata damu sai taji ba,ta dai sake jan hankalinta kawai,sun jima tare kafin antyn fa fidda wasu kayayyakin gyaran jiki ta bata
"Hajiya lami ta kawo min su,suna da tsada amma akwai kyau,wannan wata hadaddiyar dilka ce,kwana biyu kadai zakiyi amfani da ita zaki ga yadda zaki sauya,da kanki zaki nemesu nan gaba" sai wata gumbar aya ta kankana data dabino da madara,sabo dadinta da gardi tuni sumayyan ta kusan cin rabi a haka suna zaune suna hira,riqe antyn tayi sai da akayi sallar magariba sannan ta tafi,kasancewar bangaren nata babu kowa duka suna gidan amare sunje musu kamu.
Sai data yi sallar sannan ta janyo kayan dilkar ta soma hadawa tana fadin bari ta gwada,ta gama rsaf ta shafe jikinta bayan awa daya ta murje ya shiga wanka,ba shakka mai kyau ce haka ta dinga fadi a ranta yadda fatarta ta sake wani santsi bayan na da,su humaida basu shigo ba sai wajen tara da rabi,har ta shirya zata kwanta ma,yau bata jin qwarin jikinta sosai,tun safe tunaninsa ya dinga kawo mata caffa,tunda ya tafi bata ji muryarsa
"Akuyar daure ta samu sake yau mun wataya wallahi wannan miskilin mijin naki bai nan" humaida ta fada tana dariya tare da tsokanar sumayya,murmushi kawai ta saki cikin kara da yakana tace
"Ai kunfi kusa" baki humaira ta rufe
"Rufamu ki saya mu,wacce kusar?,ai shi bashi da kusa,matanshi kadai za'a cewa sunfi kusa,shekara nawa amma har yau kamar bai san mu su waye dinsa ba,ku dai ku dauki mijinku kuje ku qarata"
"A'ah fa,kada kuma a wuce gona da iri" inji sumayya cikin zolaya,dariya suka sanya baki daya,kusan wannan hirar ce ta sake dauke mata hankali.
Cikin dare baccin nata ya katse,ita kadai ta dinga juyi saman gadon,tana kallon yadda su humaida ke baccinsu hankali kwance,wayarta ta janyo tana dubawa,babu wani abu sabo tattare da ita,sai ta samu kanta da lissafin awannin da suka rage gare ya waye musu zuwa ranar alhamis.
Washegari tana wajen ummee amma baki daya hankalinta bai wajen,tana yi tana duba agogo,tun la'asar ta koma sashenta,awanni suka dinga shudewa amma babu labarin dawowarsu,a haka dare ya cimmata,cikin daren ta kasa bacci,ta miqe a hankali daga dakinta ta haura sama zuwa nashi dakin,ta tura qofar ta kunna fitilar wayarta ta haska makunni ta kunna qawayayen dakin,a hankali ta qarasa bakin gadon ta zauna,da kdanu take bin ko ina na dakin da kallo,wanda dazun ta gyarashi fes,komai a killace,wani irin yanayi take ji mai kama da kewa,sai ta qudundune cikin bargo tana sakin ajiyar zuciya,qamshinsa take shaqa har cikin qwaqwalwarta,juyi ta shiga yi daga farkon gadon zuwa qarshensa,haka kawai taji zuciyarta ta karye kuka take so tayi,hawaye ne masu dumi suka fara zirya saman fuskarta,cikin haka taji wayarta na fidda sauti mai dadi,da fari ta tsorata,amma daga bisani ta tattara hankalinta ta janyo wayar,babu suna akan lambar,amma sai taji zuciyarta ta tafi kan ta daga,karata tayi a kunnenta ba tare da tace komai ba
"Baki bacci ba ko?,dama jikina ya bani hakan"tsumammiyar muryarsa ta ratsa dodon kunnenta,bai damu data amsa ba ya dora da tambayoyinsa
" me ya hanaki bacci qarfe daya saura na dare?"zuciyarta ta kuma karyewa da jin muryarshi,hawayenta ya qaru,sam batasan kukan nata ya fara fidda sauti ba sai da taji amon muryarsa ya dan qaru sabanin dazu da take kama da ta maijin bacci yana fadin
"Subhanallah?,me ya sameki?," rasa me zata ce masa tayi,sai 'yar qaramar sheshsheqa da take fitarwa,to me zata ce masa?,tace masa ta kasa bacci?,ko tace masa gidan ba dadi?,duka saboda me?,sabida shi ko saboda wani dalili na daban,idanunsa na lumshe daga can bangaren yana sauraren sheshsheqarta,cikin sanyin murya yace
"Is ok,ya isa,ya isa.....tunda ba zaki gaya min ba ni bari na gaya miki,saboda ke na kasa bacci,saboda baki a kusa da ni,tunaninki da kewarki tunda nazo banji dadin garin nan ba,ta yaya kika yiwa zuciyata ta'addanci har haka ba tare da na farga ba?"shuru tayi kukan ya dauke duf tana saurarensa,ya qware wajen watso kalaman dake taba zuciya,wai da gaske ma ita yake gayawa haka?,kodai yaudararta yake son yi?
"kema haka ne a zuciyarki uhmmm?" Ya ambata cikin salon rada wanda ya sake hautsinata,baki ta turo kaman yana gabanta
"Umm ummm.nifa ba haka bane"
"To meye?" Ya fada dariya na qwace masa wadda baisan ta fito ba,jin shiru bata ce komai ba sai ya dora
"tunda ba haka bane sai na bari sai wani satin na dawo,dama aiki ne ya tsare mu yau din bamu dawo ba na gama komai kenan a hankali na taho daga baya ko?koda zuwa satin sama ne"shiru tayi qirjinta na bugawa
"shikenan.....sai da safe tunda ba wani abu sabo"
"Nifa bance ba....." Tayi hanzarin fada tana tsoron kada ya kashe wayar,abun ya bashi dariya ya kuma burgeshi tare da tabashi,hakan dama yakeson ya ji ko ya gani,reaction dinta kawai ya wadatar da shi
"To me kika ce?"
"Ba komai" ta fada a shagwabe
"Uhm,to shikenan,muna hanya tomorrow in sha Allah" sai ya datse wayar daga haka,wani sanyi taji yana ratsata wanda batasan dalili ba,murmushi ya kubce mata,sai ta soma goge ragowar hawayen fuskarta tana jin kunyar kanta kuma daga baya,ya ta bari har ya ganota?,oho itama bata sani ba ta baiwa kanta amsa,sosai ta kwanta saman gadon tana 'yan tunane tunane,zuciyarta fes,quncin da take ji ya ragu,da haka bacci yayi awon gaba da ita nan cikin dakinshi saman gadonsa.
*ko wanne namiji ya banbanta da wani,wani abunda ke burgeshi shike bawa wani haushi,so ya kamata mata mu kula mu lura musa nutsuwa,mu banbance meke burgesu duk qanqatarshi,da kuma meke basu haushi duk girmansa,ba lallai abinda waccan tayi ya burge mijinta ba ke in kinyi ya burge naki,qasaitacciyar mace na zuba ido tasa nutsuwa ta karanci yanayin mijinta ,Allah yasa mu dace.*
*ina masoyan SU'AD,to fa ku shirya ku hada qarfinku waje guda,a next page jarumar taku zata iso gidan baba prof,to ko ya zata kaya Allah masani,sai kawo mata gudun mawa,lol*😜😜🤪😂
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
8⃣8⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*wa qadimna ila ma amilu min amalin faja'alnahu haba'an mansura*
*YAN UWA MU YAWAITA KARANTA WANNAN AYA,ALLAH YAYI MANA MAGANIN MACUTA AZZALUMAN SHUGABANNI,WADANDA SUKA TASAMMA KASSARAMU SU KUMA KASSARA QASARMU,ALLAH YA FIMU SANIN NUFIN KOWA DA ABINDA KE QULLACE A ZUCIYAR BAYINSA,ALLAH KAYI MANA MAGANINSU KO SU WAYE,KODA CIKIN GIDAJANMU SUKE,MATUQAR ZASU ZAMA BALA'I GA AL'UMMAR MUSULMI BAMU DA QARFI BAMU DA MADOGARA SAI KAI YA ALLAH,KAJI QANMU KO DON QANANUN YARA DAKE RAYUWA A TSAKANINMU*
______________________________________
Sallar asuba ce ta farkar da iya,sai data kammala sallar sannan ta sauko qasa ta dawo wajensu humaida,tsokanarta suka dinga yi kan ina ta gudu?,bayan sunsan oga baya nan,murmushi kawai tayi tana tuna abinda ya faru daren jiyan,mamakin kanta ta dinga yi,batasan me ya sameta haka ba.