← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 210

Sashe 134

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ma'aikatan suka shigo yana kwance saman kujerar yana dubansu,saidai su ba zasu iya ganinshi na sakamakon nutsewa da yayi tsakiyar kujeru runtse da hannunshi,wuqar na ajjiye saman center table dake daura da shi,to ita din ma bata lura da shi na,a nutse ta wuce taje ta shirya abincin kai dining,sannan ta sauko a hankali tana tunanin yadda zata cika roqon da umme tayi mata,ta yaya zata tasoshi kenan?,wani adon dan qullutu dake jikin kujerar da yake kwance shi ya riqe gefan hijabinta,ta waiwayo da niyyar cirewa sai ta gashi kwance,cikin dakewa da boye rudunta ta cire hijabin nata sannan ta qaraso inda yake kwancen
"Ga abinci an kawo umme tace kaa......" Sai ta gaza qarasawa sakamakon ganin irin yankar dake hannunshi,gefe kadan sharbebiyar wuqar da jini ke kwance jiki,take ta tsorata,ta sanya tafin hannunta baki daya ta rufe bakinta
"Ya salam,subhanallah,me yake faruwa?"ta ambata cikin rawar murya da tsorata,baiko motsa ba yana kwance ya zuba idanunshi a kanta,yanayim yadda ta firgita ya sanyashi ya miqe ya zauna wanda hakan ya sanyata zabura data hangin jinin da ya zubar wanda ya kwanta saman tiles
"C'mon,kada ki taramin jama'a" ya fada cikin dakiya
"Amma haka ka zauna bai da kyau fa ga lafiya zubar jini irin haka" ta fada tana kama hannun cikim rudewa ba tare da yasan ta riqe din ba,hannunshi yayi hanzarin janyewa,itama da sauri ta janye nata hannun tana zaton zafi yake ji,wannan wanme irin yanka ne daya shiga hannunshi sosai haka
"Sannu zafi ko?dame za'a tsaida jinin?"tilas ya soma gaya mata inda first aid boxs dinsu yake,sai kuma ya tuna yana dakinsa ne su'ad kuma na qulle ciki
"jeki kawai bai kusa" ya fada yana lumshe idanunshi tare da tunanin mai zai saka ya tsaida jinin,tunawa tayi dazun kamar taji qamshin na'a na'a da suka shiga kitchen dinta,da sauri ta shiga ta bude kitchen din,cikin sa'a ta sameta kuwa,ta debo a tafin hannunta ta sake dawowa inda yake din,har yanzu idonsa rufe yake,baisan me ake sawa atsaida jini ba bayan kayan aikin su na likita,a tausashe yaji an riqe tsaintsiyar hannunshi,ya bude idanuwansa ya zubesu a kanta,tana duqe bayan ta cire hannayen hijabinta ta sanya tissue da kwalinta ke saman table din ta goge jinin sannan ta shiga jera barbadata a saitin wajen ciwon,sai data kammala sannan ta tsaya na wajen minti hudu taga jinin ya tsaya sannan ta saki ajiyar zuciya ta saki hannun,miqewa tayi ta koma kitchen don dauko mopper bayan ta dauke wuqar,wadda har tashi tsigar jikinta keyi idan ta kalleta,da idanu ya bita kafin ya dauke idonsa ya dawo dashi kan hannun nashi yana duban abinda tayin kafin daga bisani ya maida idanuwan nashi ya sake lumshewa,ya akayi tasan wannan hanyar ta tsaida jini?,mopper da dettol ta dauko gyara wajen tas,baki daya zuciyarta a jagule take,ta tabbatar wannan ciwon na da nasaba da hayaniyar data ji na tashi dazun,wannan wane irin ta'addanci mata keyi?,mace mai laushi da taushin zuciya mai cike da tausayi ce ke iya aikata haka?,tabbas idan har ita ta aikata hakan ba zata saurara mata ba ballantana ta samu damar gwada hakan a kanta ba.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[2/6, 9:14 PM] Zainabu Abu💃🏽💃🏽: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣8⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

___________________________________

         Kayan ta koma maidawa kitchen,sai ya bita da kallo yana duban hannun nashi har ta shige kitchen din,a hankali ya miqe ya haura saman,a yanzun falon tsit yake da alamu ta gama haukan nata ko gajiya ce ta sata sadudar dole ganin babu wani alamu na zaya bude qofan.

       Falon ta dawo da niyyar gabatar mai da abincin kamar yadda ummee ta roqi alfarma saidai bata taddashi ba,ta danyi jim don batasan inda zata sameshi ba,tilas ra juya ta koma dakinta ta sakaya qofar sannan ta haye kan gadon bayan ta sauya hasken dakin zuwa na bacci,baki daya bata da sha'awar cin komai,tunani ne fal zuciyarta,tana so tasan ta yaya haka ta faru a gidan nasu,dama su'ad din tana cikin gidan me koko yaya?.

        A hankali aka turo qofar dakin sanda take tsaka da tunanin,sai ta sake lamo tana son taga waye,almustapha ne,cikin takunshi na nutsuwa ya qaraso ciki a hankali,da idanu ta dinga binsa har ya isa kan doguwar kujerar dake dakin ya zauna akai tare da miqe qafafunsa,bayansa na jingine da hannun kujerar yayin da qafarsa ke tokare da daya hannun,duk tsawon kujerar ya cinyeta tsaf da nashi tsahon,hannun nashi na ajjiye saman cinyarshi,idanunsa ya maida ya lumshe yana jin yadda zugin ciwon ke ratsa ko ina ajikinsa,bai san wanne irin hukunci ne ya dace ya yankewa su'ad ba,wacce iriyar yarinya ce haka?,wadda batasan darajat rai ba,bata san darajar al'ada da mutunci ba?,wanne irin raino ta samu wacce iriyar tarbiyya ce?,iliminta me ya amfana mata da shi?,wadan nan tunanukan su suka jagoranci qwaqwalwarsa,suka hana idanunshi runtsawa,lokaci lokaci yana tashi ya sauya yanayin zaman nashi,dukka abinda ke faruwa a idanun sumayya ne,duk wani motsinsa tana lura da shi,karon farko taji tausayinsa ya kashi,wacce iriyar mace yake aure?,rashin kan gadon nata har ya kai ta sanya makami ta yanki mijinta,mijin da take ji duk duniya tafi kowa sanshi?,ita dinma kusan duka juye juye ta dinga yi saman gadon,wanda hakan yaso ankarar da shi idanuwanta biyu,a hankali ya miqe yana tsurawa inda take kwancen ido cikin duhu duhun dakin,qarasawa yayi inda makunnin dakin yake ya sanya hannunsa ya kunna qwan,take haske ya gauraye dakin wanda hakan ya sanya ta cikin hanzari ta runtse idanunta,ido ya zuba mata yana kallonta,jikinsa ya bashi idanunta biyu,cikin dakewa murya can qasa yace
"Saiki tashi ki zauna,don ba dolen yin baccin aka yi miki ba" shiru tayi ta sake yin likimo kamar mai baccin gaske,sai kawai ya qyaleta ya kashe qwan ya sake komawa inda ya taso din,kusan bacci barawo ne kawai ya fauci idanuwan kowannansu.

       Tana motsawa ya farka,sai ta tsaya sak sai data ga bai sake motsawa ba,yana kallonta ta shige bandaki,pad din jikinta ta cire ta sauya wata bayan tayi tsarki da ruwan dumi,sannan ta wanke bakinta ta daura alwala ta dawo cikin dakin,gadon ta sake komawa,saidai wannan karom maimakon ta kwanta sai ta zauna sosai ta jingina da fuskar gadon idanunta alumshe tana karanta azkar,ta riga data saba koda tana al'ada ne sai tayi wannan alwalar sannan ta karanta addu'o'inta,wannan na daya daga cikin sirrin nasararta na kubcewa kamuwar sihiri a jikinta.

       A hankali ya miqe ganin ana gab da sallame sallar asubahin ya nufi qofa ya fice a dakin,kai tsaye ya sake nufar saman,ya sanya muqulli ya bude dakin,kallo daya zaka yiwa dakin ka rabbatarwa kanka an masa barna ba kadan ba,don kusan duk wani abu da zai iya fasuwa an sauya mishi kamanni,a hankali yake takawa saboda kwalaben dake dakin dai dai ko ina,wanda idan baka kula ba kana iya takata,zaune take dirshan a can lungun gadon ta hade kanta da gwiwa da alama a haka ta kwana,baki daya gashin dokin dake kanta ya wargatse kai kace anyi barin shinkafa bisa kwalta,bakin gadon ya qarasa ya zura takalman da yake amfani da su idan yana cikin bedroom ya nufi toilet,a bakin toilet din ya cire wannan ya saka na shiga bandaki ya murda qofar ya shige,wanda warar bude qofar shi ya farkar da ita daga baccin da ya saceta,da hanzari ta duro daga gadon wanda hakan yayi sanadiyyar yankewarta da kwalbar dake tsakar dakin,bata damu ba ta isa bakin toilet din ta tsaya yana kiran fitowarsa,wanda badon shakkar kada ya aikata mata wani mummunan abu ba afkawa kawai zatayi.

       Ruwa ya hada mai dumi yayi wanka sannan ya daura alwala,ya zira rigar towel ta wanka ya fito,bai kula da ita ba har sai data ce
"Almustapha!" Wani kallo ya juyo ya watsa mata wanda ya sanya ta nemi iskancin data tsara yi masa ta rasa,bai sake waiwayarta ba sai ya wuce ma'ajiyar kayansa ya bude,bin bayansa tayi ta tsaya tana qoqarin bawa kanta qwarin gwiwar yi masa wata tijarar,fidda jallabiya ruwan madara yayi ya sanya da hular tashi ka fiya naci bayan ya feshe jikinsa da turare,sannan ya dauki darduma yana niyyar wucewa,gabansa ta sha cikin gunjin kuka
"Almustapha ni zaka wulaqanta?,wallahi wallahi nafi qarfin wulaqancin namiji,kuma wallahi yau sai na tashin hankalin kowa a gidan nan"hannu ya sanya janyeta gefe guda ya wuve,don ya tabbata matuqar yaci gaba da saurarenta hannunshi zai kai ga tumurmusata cikin fasassun kwalaben dake dakin.

      A guje ta fito daga bangaren nasu ba tare data damu da suturar dake jikinta ba ko ciwukan data ji ba,kai tsaye bangaren baabaa ta nufa wanda gab da zata shiga suka kusa karo,da sauri ya ja da baya a tsorace yana ambatar
"Subhanallahi waye haka?" Kuka ta saki iya qarfinta wanda duk mutumin dake daura da su zai iya jiyota
"Baabaa kun jawo min masifa da bala'i ina zaman zamana,me nayi muku haka kuka bibiyeni da irin wannan sharrin?" Sam bai ma fuskanci me take fadi ba,don sai da ya gyara gilashin idanunsa sosai ya iya gane wace,duk da hasken ya fara gauraye garin,kasancewar babu wanda yasan da dawowar tata
"Wuce ciki muje kada ki tara jama'a da sassafen nan" cewar baaban yana mai juyawa zuwa ciki lura da irin shigar dake jikinta,ba zaya so ma'aikatan gidan maza su fito su ganta haka ba,dole ta bi bayansa tana jin kamar ta danna masa ashar,dole tabi a sannu don ta sha kansa ya sanya mustapha ya saki wannan auren.
Chapter 134 · 0% Book details