Sashe 161
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bata damu tayi wanka tunda wuri ba,zani ta daura saman kayan baccinta ta zura hijabi suka fice tare da su humaida ta gaida mutanen gidan,hada hada tayi yawa a gidan kasancewar gobe daurin aure,babu abinda zasuyi cikin gidan kasancewar komai na gidan da za'a gabatar akwai ma'aikata wadanda zasuyi,qarfe goma ta koma bangaren nata,ta kintsa ko ina,saiga sallamar mai kitso da anty dije ta gaya mata zata turo mata ita,babu bata lokaci ta fara mata,'yar maiduguri ce,ba qaramin iya kitso Allah ya hore mata ba,ga sauri a wajenta,cikin awa biyu ta gaka yarfa mata shi wanda ya zauna a kanta kamar an saqa shi,baki daya jelar ta kwanta gadon bayanta,rabon da tayi kitso irin haka har ta manta,sannan kai tsaye ta wuce kitchen dinta,samun kanta tayi da tunanin me zata tana dar masa wanda zaya burgeshi,murmushi ta saki sanda ta gama wassafa mai zata dafa sannan ta hau aiki.
A wanni biyu kacal ta kammala,abinci iri biyu tayi,daya na baba ne daya na almustapha,tuwon alkama ta yiwa baban miyar karkashi wanda ya tuqo sosai yana santsi,dakinta ta koma ta sheqa wanka sannan ta fito tayi sallar azahar,tana shirin fara shiryawa ta jiyo shigowarsu amira,saukowa tayi jin amiran ma qwala mata kira
"Wallahi tunda na shigi nake jin qanshi iri daban daban,me kika girka ne haka?"
"Zaki ci?"
"Na waye?"
"Yayanki mana" ta fada tana juya ido,baki amiran ta rufe
"Wallahi duk maitata na haqura,wannan sanwa tafi qarfina" dariya sumayyan ta saka ta haura sama tana fadin ina zuwa,komawa tayi ta shirya cikin kwalliyar atamfa peach ce da adon yellow,fitted riga da skert wanda aka yi masa wata iriyar wrapper,ta zauna ta tsara daurin dankwali tamkar head din amare ya zauna dam a kanta,cas cas kayan suka mata kamar a jikinta aka dinka,ta bi jikinta da turate ta feshe shi sannan ta sauko,babu wanda bai tanka adon nata ba,har suka sanyata dariya.
Har misalin hudu da rabi na rana hira sosai suke wadda ta dauki dadi matuqa,ta sake a cikinsu ana kwasar cafta,turo qofar falon da akayi shi ya maida hankalinsu wajen,almustapha ne,sanye da straight leg da longsleeve shirt,qafanshi snickers ne baqi,idanunshi saye da glass mai haske wanda kana hango qwayan idanunshi,hannunshi soke a aljihunsa kafadarsa rataye da jaka,tuni shiru ya ratsa falon kowa ya kama bakinsa,wadanda suka cire mayafi suka fara lalubarsa suna yafawa,tunda ya shigo idanunshi na bisa kanta,cikin izza yake takowa har zuwa tsakiyan falon,baki daya suka hau gaidashi,amsawa daya kacal yayi musu baki daya ya haye saman,tsam ta miqe tana fadin
"Ina zuwa"
"A'ah madam saidai mun ganki" inji humaida tana qyaqyata dariya,harararta sumayya tayi saboda shirin bata kunya da takeyi ta juya ta haye saman.
Bakin qofar ta tsaya gabanta na duka,wani farinciki taji na mamayarta,cikin zumudi da son basarwa ta tura qofar dakin ta shiga,yana tsaye ya baiwa qofa baya,ko takalminsa bai cire ba bare a kai ga zama,waiwayowa yayi baki dayansa ya motsa bakinsa yana amsa sallamarta,idanunsa duka suna kanta,wani abu yaji na ratsashi,kyawun da yaga tayi masa ba mai misaltuwa bane tun daga qafafunta da yasha lalle ja da baqi ya qawata qafar ya bita da kallo ya dire a kafadarta wanda jelar kitsonta ta sauka,takowa yayi a hankali kamar mai sanda ya tsaya gan da ita,wanda tsaiwar baida maraba da runguma,tana niyyar bude baki ya rigata
"Kinsan zan dawo kika tara min wadancan?,sauka ki sallame su idan baso kike ayi abun kunya a gabansu,ke zaki ji ba dadi don na fuskanci kunyarki tayi yawa ni ko a jikina" daga kai tayi ta dubeshi,sai ya kashe mata ido daya,da sauri ta dauke kan ta ta juya da hanzarinta,a iya zamansu kadai ta soma fuskantar sa,ta soma gane sauyawar yanayiyyika tattare da shi,fargabarta daya me zata gaya musu?,zata ce su fita su bata waje?,riqota taji yayi,ta sake juyowa suka hada idanu
"Kada ki jima,kizo ki shiryani kayan jikina sun dameni" ya fada a wami shagwabe,wata bahaguwar kunya ta mamayeta,saita qara wuta zata fice kamar zata hantsila,haka ta dinga sauka har ta kai qasan.
Wayam taga falon babu kowa,wani dadi ya kamata don batasan me zata ce da su ba,abinda bata sani ba shine tana hawa saman amira ta dubesu
"To 'yammata nifa warewa zanyi wlh tunda mai gu yazo,gwara mu bashi waje tun bai koremu ba da kanshi"
"Ai naga take takenshi zai aikata kadan daga aikinsa" inji shukra
"Nikam dama wai haka yake ya man?" Inji humaira,dariya amira ta saka
"Ai yafi haka ma,sarari ne bai samu ba sai yanzu,yana auren waccen iccen ina zamu sani" dariya suka sheqe da ita sanda suke ficewa daga sashen don baki dayansu haushin su'ad suke ji,girman kanta da dagawarta sun girmeta,data tashi baya dauki dai dai ita ba,ganin babu kowa ya sanyata juyawa ta koma.
Har yau still bai yi komai ba,saidai wannan karon yana zaune ne bakin gado,qarasowa tayi tana taku cikin wani salo har ta iso gabanshi,ta duqa baki daya da zummar cire masa takalmin qafanshi tana gaidashi wanda hakan ya baiwa qirjinta damar fitowa,dif yaji tunaninsa ya dauke,yaci gaba da morewa kallonta har ta gama fidda masa takalmin da safa,ta miqe da niyyat hada masa ruwan wanka,sai ya fisgota ta dawo saman cinyarsa ta zauna,ya soma shinshinar wuyanta yana cewa
"Qarya kike wallahi,kin damen da kuka sannan na dawo ki gaza duban qwayar idanuna naga yadda kikayi missing dina,ko lacture din tamu baya zo nan ba" ya qarasa fada yana zira hannunshi cikin rigarta,muhallin da tun dazu data tsugunna ya tsone masa ido
"Uuummm" ya fada yana shinshinar jikinta,qamshinta na tafiya da tunaninsa,tsam ya hadeta da jikinsa yana magana can qasa
"Uhhmmm,tell me yaya kikayi missing dina?"
"Nima ban sani ba,bansan ha zance ba" ta furta a tausashe idanunta na lumshewa
"Kin kasa cin abinci saboda ni?ko kin dinga jinki wani iri duk saboda ni.....oya....tell me.....gaya min gaskiya kada kiyi qarya"
"Yes,duka na kasa....na kasa"
"Why,meye dalili?" Ya sake tambayarta idanunshi a lumshe cike da shauqi
"I dont know....ban sani ba"
"So ne?"
"Nooooooo" ta fada tana jan kalmar cikim jin kunya tare da tura kanta a wuyanshi
"Nace kada kimin qarya fa,tashi ki gayan" ya fadi yana qoqarin hade fuskarsu waje daya,goshinsu ya hade kamar yadda tsinin hancinsu ya hade,suka fara musayar numfashi,muryarta a sanyaye tace
"Kace kaima baka iya komai,kaima so ne?"
"Yeah,feeling ne dake yawo cikin zuciyata da ban taba jin mamakamancinsa ba,so that na yarda so ne,sone unexpected....."nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,abu guda suke ji a cikin zukatansu lokaci guda,indai ko haka ne ita din ma son ne?,amma ta yaya zuciya daya ke iya son mutum biyu,taso mukhtar yanzu kuma almustapha?saidai idan tayi rantsuwa ko kaffara ba zata yi ba,abinda take ji a yanzu bata taba jinsa kan wata halitta ba,ba mamaki dalili kenan da ya sanya ta gaza gane meke damunta
"Why you keep silence?" Kai ta girgiza duk da fuskarsu na hade waje daya tana kuma sauke numfashi
"Babu komai"
"Akwai....na sani bazanji irin wannan abun ni kadai ba at the first time in my life,idan baki sani ba lissafo min me da me kike ji,ko yaya...konyaya inason naji wani abu mai dadi,lafazi mai dadi kamar yadda sauran maza keji" a hankali ta soma lissafa masa kamar mai koyon magana
"Tsoro....kunya.....nauyi....tausayi...kewa son ganinka....damuwa....faduwar gaba......" Sai tayi shiru tana jan numfashi wanda ke cakude da nashi mumfashin da qamshin lallausan turarensa,yana mata kwarjinin da bazata iya kammala fada masa ba,murmushi ke fita daga fuskanshi,dukka wadan nan sun tabbatar masa akwai wani abu mai girma dake son wanzuwa cikin zuciyarta dangane da shi,don kada ya matsanta mata da yawa sai janye fuskarshi daga tata
"Is ok,hakan ma ya gamsar da ni,hadamin ruwan wanka kafin a kawo min abincin da nayi order" sai ta kwabe baki tana dubanshi
"Abinci na jiranka,no need sai ka yi order" ta fada taba niyyat shigewa toilet din,murmushi ya sake kube masa,binta yayi da kallo har ta shige,ba shakka akwai banbanci,akwai banbanci wanda kullum sai yaga wani sabon abu,tunda suke da su'ad bata taba jera abinci yana jiransa ba,duk da orser yake amma ganda take kafin ya fito ta fidda komai daga park dinshi ta ajjiye masa inda ya dace.
Yana shiga wanka tayi hanzarin ficewa ta dauki abincin baba ta kaiwa anty maamaa kan ta bashi sannan ta juyo ta dawo,saidai tayi nawaa,saboda tana tura dakin ta ganshi har ya fiti,qugunshi daure da towel yana shirin soma shafa mai,sai ta dauke idonta
"Ina kika je?"
"Naje gaida baba ne"
"Amma dai kin gani gidan a cike yake har da maza ko?" Sai ya danja tsaki
"Banjin gidan nan zaya zaunu,ki shirya zamu basu waje" idanu ta fidda tana son tambayarsa inda zasu,saidai taja bakinta tayi shiru,ta qarasa inda yake zaune gefan gadon ta lakato man ta soma shafa masa,daya daga cikin lacture din da yayi mata,duk inda ta motsa binta kawai yake da kallo,baki daya ta kashe masa jiki,sai ya miqa hannu ya karbi man yana cewa
"Barshi kawai,kasala kike saka min,jeki shirya,bana so magariba tayi mana a nan",bata jima da yin wanka ba amma ta fuskanci mai muradin haka ne,shi ya sanya ta juya ta koma bayi,ta cika turaren wanka a ruwan ta sake wani wankan,sanda ta fito bai saman,tuni ya sauka qasan,bai iya jira ba yayi sarving kansa ya fara cika tumbinsa,dadin abincin ya dinha zagayawa wata duniyar da shi.