← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 199 OF 210

Sashe 199

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

        Ba wanda ta amsa sallamarsa a cikinsu,hakan ya sanya sumayya tayi wucewarta ba tare data sake cewa komai ba.

        Satinsu biyu dai dai a kano suka koma dubai,bayan sun ziyarci gidan maimmartaba sarkin rano,mahaifin ummi,tsoho mai ran qarfe,karon farko kenan da sumayya ta kai ziyara,tsantsar soyayyar da tsohon kewa almustaphan ta shafi sumayya,kowa haba haba yake da su yana neman wajen ajjiuesu,taga kara taga karamci,ba qaramin dadi zuwan yayi mata ba,duk da bata samu zuwa gidajen sauran 'yan uwa ba,amma tayi alqawarin duk sanda tazo kano toba shakka zata sake zuwa musu,kyautar girma tsohon yayi musu shida matanshi,duk da mahaifiyar ummi ta rasu,amma matan baban nata sun daukeata tamkar diyarsu,suna farinciki da juna suka rabu,tun a sannan ummi taso riqe sumayya har sai ta haihu amma almustapha ya shafawa idonshi kwalli yace ba yanzu ba zai kawota idan lokacin yayi,yayin da cikin zuciyarshi ma sam ba haka bane,don baida niyyar kawota din,yana ganin meye amfaninsa a matsayinsa na likita kenan.

      A hankali kwanaki suka ci gaba da wucewa,ba abinda ta daga qafa ko ta sauya game da kyautatawar da takewa almustaphan,dukkan wani abu data sani cewa yana so takan sanyashi gaba da komai nata,lamarin su'ad kam sam baya damunta,duk wani iskancinta da tambotsanta basa gabanta,sai taga dama ma zata ganta bare wani sabga ya hadasu,abu daya take qoqari a kai shine tausar almustapha a duk sanda ta kunnoshi,sam bazata so ace su'ad din tabar gidan na,kullum fatanta shine Allah ya shiryata ta gane illar abinda take yi,ta tabbatar da cewa duk duniya bata da wata mafita matsawar almustapha ya sawwaqewa su'ad tofa za'a ce itace sila,bayan duk wanda zaiyi alqalancin baisan meke wakana game da zamantakewar auren su'ad din cikin gidan ba,saidai hasashe dai kawai.

       A haka cikinta ya shiga watanni tara har ya soma yunqirin shiga na goma,kallo daya zaka mata ba zaka so sake dubanta ba sabida tausayi,sosai cikin yayi wani girma har wani lokaci sai ta tallafeshi idan tana tafiya saboda girmansa da yadda ya sauko qasa,ta sauya kamanni sosai kamar ba sumayyan ba,munin da tayi a da nafila ne,har bata son kallon kanta a mudubi,sau tari idan taga almustapha na kallonta sai ta kau da kai tana tunanin munin da tayi yake kallp,saidai shi sam ba haka bane cikin zuciyarshi,tsananin tausayinta ke damunshi,ba don kada yayi riga malam masallaci ba da tuni ya yankata ya cire mata cikin ta huta,yakan tallafo fuskarta ya saki murmushi
"Ki daina boyen fuskarki,a hakan kinmin kyan da ban taba ganin kin yimin irinsa ba,kinsan me?" Sai ta kada kai cikin murmushi
"Da zaki sake zama haka nan da wata takwas ma bayan kin haife wannan cikin ina so,da nafi kowa murna"
"Kayimin addu'a Allah ya rabani da wannan ma lafiya"
"Yadda zuqar numfashina ya zamemin dole haka wannan addu'ar ta zamemin dole" ya fada yana karata da jikinsa tare da shafa bayanta a hankali yana ci gaba da yi mata addu'a cikin ranshi.

       Semina ce ta kamashi ta sati guda wadda za'a yi a china ta 'yan kasuwa,sam yace ba zashi ba,ita ta tausashi da qyar tace ba'a jiran haihuwa sai sanda Allah ya kawota,ko kadan baison tafiya don ko fita ya rage,tausayi take ji matuqa,hatta tashi sai tayi da gaske take iya yinsa ko shi ya dagata,ita ta tayashi hada kayanshi tana yi tana tsokanarshi wai ya zama rago,jawota yayi jikinsa yana dan mintsinarta yadda ba zata ji zafi ba yana murmushi
"Laifin wa?uhmmm babe,bake kika maidani haka ba?" Dariya ta saki,ta jawo hannunsa ta dora saman cikinta
"Laifin wannan ne ba nawa ba"sake matseta yayi a jikinsa yana sakin murmushi,tasan duka hanyar da zata sashi nishadi.

       Sai da ya hadata da babban asibitin dake qasar wanda anan yake musu aiki lokaci lokaci,ya basu lambarta lambar gidan da adress,sannan itama ya bata number dinsu,sannan ya karba mata nurse guda daya wanda suka tanada saboda jinyar marasa lafiya wadda zata dinga zuwa tana kwana da ita,sam bai fadawa ummi ba don ya tabbatar cewa zatayi ya turota nigeria,shikuwa baison ko daya abinda zai rabashi da ita dai dai da minti daya

       Tattaki ta masa har zuwa cikin falonta,kasancewar ranar girkinta ne,ya jawota kusa da shi ya riqe dukkanin hannayenta cikin nashi yana duban qwayar idanunta
"Kimin alqawari zaki kulamin da kanki har na dawo,ba tunani ba damuwa,kinyi alqawari?" Murmushi ta sakar masa mai kwantar da zuciya ta gyada kai
"Nayi maka noor,Allah ya tsaremin kai ya dawo min da kai lafiya"
"Amiiin baby na" ya furta yana lumshe idanunsa sannan ya matso da ita gab da shi yayi kissing goshinta zuwa wuyanta.

       Tare da su'ad suka rakoshi har bakin mota,sai da driver ya ja suka fice sannan kowacce ta juya zuwa ciki,wani kallon banza take jifar sumayyan da shi gami da jan dogon tsaki,bata kulata ba don idan da sabo ta saba,tayi wucewarta ciki abinta.

   *******    ****   ********

     Bayan kwanaki biyar da tafiyarshi ne inda suke saka ran dawowarshi jibi,tun safe take jin ciwon mara kadan kadan,saidai bata gayawa ko nurse dinta ba saboda tunda cikinta ya shiga wata na goma take fama da irin hakan kadan kadan lokaci zuwa lokaci,yanzun ma fitsari ne ya tasheta,sai data dauki a qalla minti biyar ta iya yunqurawa ta miqe,mararta ta amsa sai data ce wash sannan ta iya miqewa a daddafe ta qarasa bandakin mararta na ciwo sosai,koda taje fitsarin kadan tayi sai ciwon da ya dadu,dawowa tayi cikin dakin ta soma kai kawo a tsakar dakin,a jikinta take ji tabbas naquda take,bata da maraba da abinda take ji lokacin haihuwar abdallah.

      Tsahon awa daya tana gumurzu babu sassauci,hakan ya sanya ta fito falo a daddafe,ta dauki waya ta kira lambar nurse din,cikin sakanni kadan ta iso ta dubata ta tabbatar haihuwa ce,saidai akwai saura,asibitin ta sanarwa,babu jimawa saiga mota sun aiko da ita suka daukesu suka wuce,su'ad taji motsinsu,ta dauka wasu ne ta leqo da taga sune ta koma tayi kwanciyarta abinta.

      Daki ne na musamman suka bata,dauke da na'urori kala daban daban bayan ta sauya riga zuwa ta asibiti,tun tana daure ciwon har abun ya soma wuce tunaninta,naquda take haiqan saidai haihuwa tawi zuwa,tun biyu na dare har gari ya waye haihuwa bata zo ba,daga gefan almustaphan ya kira wayarta yafi a qirga saidai ba amsa,saboda sun baro wayar a gida,ya kira su'ad tace bata sani ba,bata gama bashi cikakkiyar amsa ba ma ta kashe wayarta,yayita kira switchoff,take hankalinsa ya tashi,sai sannan yayi dana sanin me yasa ko baba uwani baisa an kawo ba?,kai tsaye ya kira asibitin nan suka shaida masa tana nan tun daren jiya,ranshi ya baci hankalinsa ya tashi,fada ya hauyi kan me yasa basu shaida masa ba?,sannan ya za'ayi su barta tun jiya har yanzu wayewar gari tana naquda har ta kusa cinye awanni da aqa'idar likitoci ba'a so ta gama su bata haihu ba,haquri suka shiga bashi,bai sauraresu ba ya katse layin ya soma tattara ya nasa ya nasa ba tare da ya kammala abinda ya kaishi ba,hankalinsa gaba daya yayo dubai,jinsa yake kaman yayi tsuntsuwa ya ganshi a can.

        Qarfe hudu na yamma ya iso dubai,kai tsaye ya yiwa drivan umarni ya wuce da shi asibitin,kai tsaye ya wuce dakin da take,kwance take saman gadon,kallo daya zaka mata kasan cewa ta jigata qwarai,duk sanyin dake dakin bai hanata gumi ba,muryarshi kawai taji ta daga kanta taba dubanshi,tuni ya ajjiye jakar dake hannunsa ya qarasa inda take,nurses din dake dakin suka fice daya bayan daya,tafin hannunta ya laluba ya sanya nashi hannun ciki,hannunsa saman kanta yana shafawa a hankali,baki daya zuciyarsa ta karye
"Baby......sannu baby" ya fada idanunsa cikin nata,ga mamakinsa murmushi ta sakar masa a wahalce
"Ka dawo?"
"Eh...." Maganar tasa ta katse sanda ta furta
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Cikin madaukakin sauti ta soma murqususu cikin matsanancin ciwon da ya taso gadan gadan,tamkar dama jiran zuwan almustaphan yake,yanayin yadda yaga tanayi ya sanyashi sake dubata da kanshi,nan ya tabbatar haihuwar ce,nurses din da suka fita ya kirawo don su taimaka masa,din bashi da qwarin gwiwar da zai iya karbar haihuwar shi kadai,yana riqe da ita yana gaya mata addu'o'i tana maimaitawa cikin wahala,a qalla mintuna goma kafin jaririyar ta samu isowa duniya,kukanta ya karade ilahirin dakin baki daya har zuwa waje,basu gama tantance komai ba ta sake wani yunqurin,wani sabon kukan ya sake karade dakin suka hadu suka cika ilahirin dakin zuwa harabar dakunan da kukansu,nurses din ne suka dauke yaran yayin da baki daya hankalinsa ya raja'a a kanta,gumin da ya mata sharkaf ya soma goge mata yana jero mata sannu babu qaqqautawa,dubanshi take yadda ya rude baki daya,kukan yaran na yawo cikin kwanyarta,tasbihi take wa ubangijin talikai,yau gata a karo na biyu ta sake samun diyoyi,diyoyin da suka fito daga tsatsonta,kasa dauke idanunata tayi daga shiyyar da yaran suke sankda nurses suka gama rabasu,kukansu suke sosai suna wutsil wutsil da qafafu da hannyensu,sakayau a yanzu take jinta kamar sun fita da duk wani ciwo dake damunta.

       Cikin mintuna qalilan nurses din suka soma gyara yaran,shi kuma ya gyara ta da kanshi a wani daki daban,komai ya kammala,aka maidata zuwa wani dakin ita da yaran baki daya.
Chapter 199 · 0% Book details