Sashe 102
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin hukuncin Allah suka isa qasar lafiya,tun daga airphort sumayya ta soma gane banbanci baro baro da tata qasar,haka tayi ta kalle kalle sanda taxi ke dauke da su zuwa masaukinsu,sai ta samu kanta da yiwa qasarta addu'a tare da fatan samun ci gaba kamar wannan qasar.
Da suka isa a gajiye suke,gida ne wanda ke dauke da falo guda daya,sai kitchen,bedroom uku,kowanne da manne da toilet,sallolinsu kawai suka rama kowa ya kama makwancinsa,kusan ita ce qarshen bacci a gidan,ta jima tana juyi kan gadon,hakanan take da tsananin baqunta,duk sanda ta sauya muhallin data saba da shi tana dadewa kafin bacci ya dauketa.
Tunda suka je uncle farouq bai zauna ba,yana ta zirga zirga kan abinda ya kawoshi tare da yi musu siyayyar abubuwan da zasu buqata na gida,sai da suka ci sati guda cur kafin komai ya daidaita,ya miqa laila da khalipha wata makaranta wadda ke nan cikin unguwar,yayin da ya samawa sumayya wata center ta manya dake karantar da su dukkan wasu karatuttuka irin na 'yan secondry tun daga matakin farko cikin shekara guda su baka certificate dinka,itama babu nisa tsakaninsu,ko a qafa zaka iya zuwa,idan kana da buqata kuma kana fita bus zata zo ta daukeka ta qarasa da kai,da fari sumayyan ta tsure,tsoro take ji,tana tunanin ta yadda zata dinga zuwa wajen ita daya,ta zauna cikin baqin fuska,fararen fata,wadanda akwai banbancin addini harshe da al'ada tsakaninsu,kamar tayi qwalla saboda tsoro,anty dije ta dinga tuntsira mata dariya
"To ko ni zan dinga rakaki?" Ta zolayeta
"Dole fa ki saki jikinki sumayya,nan qasar babu ruwan wani da wani ce,kowa abinda ya kawoshi shi yakeyi,ki zama mai budadden kai,so nake a kasa ganeki duk sanda muka koma gida" da irin wadan nan kalaman ta qarfafi gwiwarta.
Ranar farko gabanta na dukan uku uku haka taje,tayi tsurutsuru cikin ajin,sam bata fahimtar me suke fadi bata fahimtar turancinsu,a wani hade yake bare ta iya tsintar abinda zata iya tsinta din,tana nan zaune tsuru taji an dafa ta,ta waiwaya tana kallonta
"Sannu,ke baquwa ce ko?" Sai ta sake kallonta sosai,baqar fata ce 'yar uwarta wadda a qalla zasuyi shekaru daya,amsa mata tayi,fuskarta sake ta nemi wajen zama kusa da sumayyan tana gabatar mata da kanta,kusan ita tayata zama har aka tashi suka taho tare,ashe basu da nisa saboda haka ta samu abokiyar tafiya tare suka taho,sunanta zulaiha ta sanar mata,itama baquwa ce a qasar bata kai shekara guda da zuwa ba.
Cikin satittika suka soma sabawa da zulaihan,anan take gaya mata dan uwan mahaifiyarta ke ruqonta,mamanta na aure ne a kano qauyen sumaila,itace autarsu,tana da shekara sha takwas mahaifiyar tata ta rasu,babanta na son yi mata auren dole,yayan mamanta shi yaji labari yazo ya dauketa,ya taho nan da ita inda yake sana'ar drivern taxi,da yake qasa ce ta neman arziqi,jama'armu da yawa musamman daga qasashe na afirka kan tafi neman kudi irin wadan nan qasashe,idan zamanta ya karbeka duk sana'ar da kake sai kaga albarka cikin arziqinka,sam ba zaka ce yana tuqa taxi ba anan musamman idan yazo gida nijeria,matarsa daya dansu daya.
Akwai banbanci tsakanin sumayya da zulaiha,zulaihan ta fita wayewa da gogewa qwarai,idan ka ganta ba zakayi tsammanin ga daga inda ta fito ba,mutumce mai son jama'a da faran faran,hakan ya sanya take da qawaye sosai,sai a lokacinne sumayyan tasan alfanun qawa da dadinta,musamman idan ka hadu da mai kyakkyawar halayya irin ta zulaiha mai sonka da zuciya diya,da fari sumayyan ta fara tababa kan yadda zatayi shiga ta fita ba irin wadda ta saba ba,zulaihan ita ta karbi kudi wajen anty dije ta rakata ta siyo irin sutturun qasar,wanda zaki sanya basu fidda tsiraicinki ba,wadanda zaka dace da zamani ba kuma tare da ka fidda tsiraicinka ka sabawa al'adarka ba da addininka baki daya,sau tari idan ta shirya zata makaranta laila kan tsokaneta
"Wallahi anty sumy kin canza cikin watanni kadan,bakiga yadda kayan nan ke miki kyau ba,kamar ba sumyn malam ba,maman abdallah" anty dije na tayata
"Kin rigani a fili na rigaki a zuciya,ta koma wata qaramar baturiya,haskenki ne kadai ba qarasa nasu ba,inaga ma kafin mu koma fa kim saje da su,kayan sun amsheki" ita kanta ta sani amma sai ta saki dariya
"Ina wani kyau a kayan banasaren mutum anty,dadinta daya kawai basa fidda tsiraicin mutum" duk da haka bata bar hijabinta ba,don babu sutura mafi daraja a gunta irin hijabin,saidai duk sanda ta sanya kafin ta kai makarantar suna shan kallo ita fa zulaiha,har zulaihan kan ce
"Ke kuwa sumayya ki haqura mana"
"Babu abinda zai rabani da hijabi sai mutuwa,sai randa likkafani ya zama sutura ta ta qarshe" dariya zulaihan keyi
"Nima wasa nake miki".
Wata baiwar qwaqwalwa Allah ya baiwa sumayyan,cikin wata biyu kacal harshenta ya fara juyewa,su kansu uncle farouq da anty dije mamaki suke,ganin tana ganewan ne ya sanya ya yanke shawarar sanyata wata makarantar dake training wa mata zamantakewar rayuwa,ciki harda nau'in girke girke na kowacce qasa,duk randa zakuyi girkin wata qasa tofa malamar 'yar asalin qasar ce,makarantar akwai tsada don ko ita anty dije ta burgeta,ba don tayi tsada da yawa ba itama taso shiga,amma tunda 'yarta ta samu tace ba komai ta dinga koya mata.
Watansu biyu da daddare uncle farouq ya kwashesu suka fice suga gari karon farko tun bayan zuwa,don sam bai da lokacin zama a gida,awa biyu kacal sukayi suka dawo saboda yana da aikin da zaiyi,suna gab da shiga gidan ya tuna dawowar qanin abokinsa wanda gidansa ke daura da nasu,sunje ganin gida ne shi da matarsa sai shekaran jiya suka dawo,baki dayansu suka nufi gidan don a gaisa,anty dije ta riga data sansu dama,mai gidan na girmama uncle farouq kasancewarsa abokin yayansa.
Gidane qarami kamar nasu,ga mamakin sumayya matar gida matashiya ce wadda kusan zasuyi sa'anni da ita,yaronta daya itama wanda ya kusa shekara hudu,nafisa asalin shuwa ce,tana aure da mijinta Dr auwal wanda qarin karatu ya kawoshi qasar,shekararsu biyu kenan,shekara biyu ya rage musu su koma gida,shekararsu hudu da aure,yaransu daya khalid wanda shima shekararsa hudun dai dai da shekarar aurensu,saidai har yanzu bata qara wata haihuwar ba,ita din ma karatu take,yanzu haka ta kusa hada degree dinta a fannin kasuwanci,abinda tafi sha'awa kenan tun tana yarinya,kusan gado tayi,sabida kasuwanci shine sana'ar mahafinta .
Ba qaramin dadi taji ba da ganin iyalan uncle farouq din,sai ta jita kamar a gida nijeria,nan kusa da su dama babu wani dan nijeria,duk a tsakiyar fararen fata 'yan asalin qasar take,tun kafin su tafi ganin sumayya sa'a take a gunta ta dinga fadin
"Na samu 'yar uwa"
"Lallai kam,wannan,ai sai kinyi da gaske nafisa,bata da son mutane,ga shegen qulafucin zaman gida,makaranta kadai ki fidda ta"
"Zamu saba ai ko sumayya,zaki zama qawata" ta fada tana kallonta,tashin farko taji sumayyan tayi mata,nutsuwarta ta burgeta,murmushi sumayyan tayi
"Insha Allah maman khalid"
"Kamar gaske" cewar anty dije
"Haba umman khalipha kada ki sage mana gwiwa mana" inji nafisan.
Sumayya kam ta gwada mata halinta,mutum ce mai yawan janye jiki ga baqin mutane,musamman wanda ta fuskanci rayuwa bata ajesu bigire guda ba,bata son sanya kanta inda zai zame mata matsala ko dana sani a gaba,ko kuma inda ya fi qarfinta,qwarya tabi qwarya haka nata ra'ayin yake,wanda ta gada ne daga wajen mahaifanta,mutane masu sanin daraja da qimar kansu,masu wadatar zuci da yakana,bata manta nasihan mama da kullum take gaya musu,kaso duniya mutane su qika,ka qi duniya mutane sai su soka,ka guji kwadayi,don shi din mabudin wahala ne,matuqar ka hau motar kwadayi to la shakka babu inda za'a saukeka sai tashar wulaqanci,mutunci yafi kudi,mutunci abu ne da idan ya zube qasa bai yiwuwa ka kwasheshi,mutunci abu ne da kudi ko wata isa basu iya siyanshi,ire iren wadan nan maganganu ke mata tasiri,takan zama mai tsantseni duk inda ta samu kanta,takan koma dora mutuncinta gaban komai nata.
Nafisa 'yar gata ce gaba da baya,itace auta a gidansu baya ga maza yayye da take da su guda hudu,ita daya ce diya mace qwal daya tilo da iyayenta suka haifa,hakan ya sanya take ganin gata,baya ga arziqi da Allah ya yiwa mahaifanta,nafisa irin mutanan nan ne masu son jama'a,sakin fuska da jan mutane a jiki,ko kadan ba zata taba yin wani aiki da zai nuna maka ga daga inda ta fito ba,saidai idan kai idanuwanka suka kai ka gani,tunda taga sumayya taji tayi mata,take jin ta samu 'yar uwar data rasa a baya,duk da cewa tana da tarin qawaye amma sai taji sumayyan ta zame mata daban.