← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 210

Sashe 138

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Baki dayansu suna shiga suka san akwai wani gagarumin sauyi dake shirin faruwa a rayuwar mustaphan,duk da basu fiya zuwa gidanshin ba kasancewar ko kadan su'adah bata mu'amala da matan abokanshi,a cewarta duka basu waye ba,ta raina ajinsu,bata qawance da diyoyin africa masu duhun kai,idan kika ga tana harka dake to matar wani hamshaqin ne wanda yake babban abokin kasuwancin kamfanin MM abaya,mazauni kowanne ya yiwa kansa a inda ya dace hamza naci gaba da takalar almustapha wanda ya daure gira acewarsa ya fita daga shirginsa,a mutunce abida ta gaidashi sannan tace
"Amaryar fa?"
"Barshi my wife,rowa zai mana halan" bugu ya kai masa da qafa sannan ya miqe yana tunanin inda zai samota,jin qarar kwanuka a kitchen ya sanyashi nufar can kai tsaye,tsaye take tana goge sink bayan ta kammala girkin ta zuba komai cikin kyakykyawan mazubi,hatta da kwanukan baki daya ta wankensu goge wajen kawai take.

       Atamfa ce a jikinta kasancewar tafi son sanyata,saidai baki daya dinkin na falle biyu ne,tana mutuwar son atamfar sanda ta ganta,falle biyu ta rage agun saidawar aka dinka mata,bata taba sanya kayan ba sai yau,hakan ya sanya dinkin ya mata dam,eight pieces ne skert din ya fidda shape din qugunta qwarai,rigar kuwa baki dayanta iya karta qasan cibiya,gashinta na fake tsakiyar kanta jelar na reto gadon bayanta,bata daura dankwali ba kasancewar tasan cewa ita daya ce a gidan,tana da yaqinin koda ya tashi baccin babu abinda zai kawoshi kitchen din,Allah Allah take ta kammala girkin taje ta cire kayan saboda sun takura mata,saidai ta barwa zainab ita zasu fi yiwa,tun jiya data ji labarin tafiyar take cikin fargaba,yaya zaman zai kasance musu?,wannan shi take yawaita tambayar kanta.

       Safa(socks)din dake qafarsa ita ta hanata jin takunshi,idanuwansa na bisa bayanta tana ta goge goge abinta ba tare da kawo komai cikin ranta ba,zaj iya cewa bai taba ganin hips zaunannu jikin mace irin haka ba,da gaske matan africa sunfi matan kowacce shiyya structure ta jiki?,ya taba jin haka daga bakin hamza sanda yana kan ganiyar neman auren abida,wata kasala ta saukar masa sanda ta sake motsawa kadan ta gyara tsaiwarta,wanda hakan ya sake fitar da shape dinta,idanunshi ya dauke,sai ya tsaya cak yana tunanin yadda zai mata magana,kawai sai yaja ya tsaya gami da jingina da bango hannunsa cikin aljihunsa yayi crossing qafafunshi tare da maida idanunshi wani sashe daban,haka nan yaji yana son ya duba yaga ta gama,ta gama goge wajen,kwanukan take gogewa da tsaftataccen towel na kitchen tana jerasu a ma'ajiyarsu,dakin girkin na da tsaho da fadi hakan ya sanya zaiyi wuya kayi saurin ganin wulqawar mutum,sai yaci gaba da kallonta jikinsa na mutuwa,karon farko da ya taba ganinta a haka cikin rufin daki guda da 'yar qaramar tazarar dake tsakaninsu cikin muhalli guda,idanunsa ya lumshe yana son sake yiwa kansa shamaki da kallon nata,da hanzari ya tashi daga jikin ginin ganin bazai iya jira har ta ganshi ta kanta ba,freezer ya nufa ya bude wanda qarar taba tan ya sanyata juyowa a razane don tayi matuqar tsorata,hakan ya sanya plates din biyota suka fado suka tarwatse saman tiles din kitchen din,inda Allah ya taqaita na plastic ne da robobi,yadda ta tsoratan qwarai ya qawatar da shi,kamar wata qaramar yarinya,yana son mace mai tsoro wanda har ya manta akwai wannan halayyar wajen diya mace,su'ad nada dakiya da taurin zuciya irin ta wasu matan turawan,ba komai ke sanyata firgici ba tunda sun saba ganin bindiga da sauran makamai a banza,ruwan ya maida ya tako a hankali zuwa gabanta wanda taqin dake tsakaninsu bai da yawa,duqawa yayi ya soma tattare kwanukan tana tsaye jinkine da kantar hannayenta dafe ita tana maida numfashi cikin tsoro,ko bata fada ya tabbatar taji zafin yadda kwanukan suka zube mata saman qafa,sqi da ya gama tattarawar sannan ya tuna da kwalbar data taka itama jiya,ba zato taji ya daga qafar tata,ya sanya yatsanta guda daya yana shafa wajen data yanka din,idonta ta runtse tsam,yayin da ya kai ya kawo a gurin wajen sau biyar,da sauri ya saki qafar saboda tuna qafan wace a hannunshi da kuma wadanda ya bari a falo,tsaki yaja yana jin haushin kansa me ya zaunar da shi,bai bata umarnin ta fito ba kawai ya wuce,me ya kaishi tattare mata kwanuka bayan ita ta barar,me ye damuwarsa da ciwonta
"Saboda itama ta nuna kulawa da naka ciwon" ya amince da amsar,mutum ne mai nuna kulawa ga wanda ya kula da shi,miqewa yayi yaja da baya
"Me jiya na gaya miki game da wannan gashin dake kanki,bance ki cire ba?"ya tambaya cikin dakakkiyar murya da tsare gida,kai ta girgiza ba tare data iya duban idonshi ba saboda yadda yau yayi mata wani kwarjini
"ba saka nayi ba,nawa ne"hannu ya zura har qirjinsa yana gogar nata ya kama jelar da niyyar fincika,saidai lushi santsi da taushinsa kadai ya bashi amsar mallakinta ne tun kafin ya fincika din,da sauri ya saki saboda wani shock da yaji a jikinsa,haushin kanshi ya kamashi,me zaisanya jikinsu ya dinga haduwa haka?,da hanzari ya juya yana fadin
"kada ki bata musu lokaci"
"Amm,don Allah ka taimakamin da hijabi a daki?" Waiwayowar da yayi ya sanyata sunkui da kai,kallo ya qare mata tun daga qafarya har kanta,yayin da ya dawo ya tsaida idanunsa saman qirjinta wanda matsewar rigar ya takurasu suma,haka kawai yaji ya gamsu dari bisa dari da dauko hijabin,baice komai ba ya fice.

       Yanayin qamshin dakin daban yake da saura,komai na kintse a muhallinsa,kan gado ya hangi hijabin,saidai akwai littafi kan hijabin,hannu yasa ya dauki littafin yana jujjuyashi,littafine dake qunashe da qananun hadisai guda d'ari saboda hadda,maidashi yayi saman bedside drower din ya fito,daga bakin qofar ya cilla shi ya fito.

      "Haba malam,tsakani da Allah ka kyauta,ka barmu ni da madam daga kiran amarya saika tsaya yada manufa,ai ka bari mu baku waje ko?" Inji hamza dake fadi qasa qasa yadda abida ba zata ji ba,yatsunshi ya kama wanda saida hamzan yaji a jikinsa sannan ya sakar masa,bai damu ba tunda yasan shi ya tsokano.

       A nutse take takowa hannunta dauke da farantin wanda kansa ke dauke da lemukan kwali da kofuna sai kuma ruwa,sallama tayi musu hamza da abidan suka amsa,abida ta miqe ta rage mata wasu sumayyan na murmushi tace
"Kai,dama kin barshi"
"Babu komai,ai sunyi miki yawa"
"Ai kuwa da kin qyaleta,aikin wannan mutumin ne" inji hamza da bai daddara ba,da idanu mustapha yayi masa gargadi sannan ya sake tsare wuri.

       Bata zauna ba sai data jera dukkan wani abun ci da nasha wajen,lamo yayi cikin kujera ya wani lafe yana binta da kallo,abun yayi matuqar burgeshi,irin abinda yake gani gidan wasunsa kamar su hamza yau gashi gidansa,sai yake ji wani izza da girma na shigarshi
"Kai nifa abincin zan fara ci gaskiya hirar nan bata yiwuwa,my abida bismillah,sumayya sai kiji kema da angonki" kunya ta kama sumayyan sai ta saki murmushi tana sadda kanta,ya dan saci kallonta wanda zakayi tsammanin idanunshi a lumshe suke,tuni abida ta qarasa kusa da shi,wanda hakan ya tilastata miqewa,daura kadan da shi ta qarasa,wanda tana iya jin qamshin turarenshi kamar yadda yake iya shaqar humrarta,ta kiyaye tsarin cin abincinsa tsaf,qasa qasa gake dubanta yana mamakin yadda har ta iya gane ra'ayinshi da qa'idarsa,duk da sam baijin zai iya sanya komai a bakinsa,idanuwan hamza da abidan kawai ya sanyashi yayi shiru
"Barakallahu fiki" cewar hamza bayan ta gama zuba masa,kusan tare suka miqe sukayi dakin sumayyan don su basu waje.

      Tuni hamza ya soma kaiwa cikinsa,ko ba'a fadi ba ya tabbatar ba'a qasa ta tsinci qwarewarta wajen girki ba,gyara zamansa yayi duk da yadda qamshin ya buwayi hancinsa,taba shi yayi
"Ya dai?,ko soyayya ta cika maka ciki?" Ya zolayeshi,miqewa yayi sosai ya zauna,wanda yanayin zamanshi kadai ya alamtawa hamza magana zasuyi mai muhimmanci,yana jin zuwa yanzu yana buqatar abikin shawara,wanda babu mutumin da yasan cikinsa irin hamzan,kasancewarsa mutum mai yawan zurfin ciki
"Hamzah"ya kira sunanshi da gaske
"Na'am"
"Hamza,bana jin yarinyar nan ta dace da ni,bana jin zamanmu zai yiwu,hamza komai namu ba iri daya bane,ban hangi abinda zai kawo dacewar zamanmu ba,amma na fuskanci tana qarqashin goyon bayan baba,kasan yanzu haka ya matsa sai mun wuce dubai tare?"
"Ka manta hausawa sunce duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau dala da gauron dutse bazai hangoshi ba?,akwai wani abun qyamata guda daya tak daka gani tattare da ita iya awannin da kuke tare?"
"Ta yaya zan gane?,bayan duka awananin da mukayin baifi ka qirgesu da yatsun hannunka ba,kawai ban son raini hamza kai ka sani"
"Duka macen data samu cikakken tarbiyya daga gidansu ba zata taba raina duk wani namiji da ya amsa sunan mijin aurenta ba,amma tunda haka ne kasan me yafi?" Kai kawai ya kada
"nisantarta duka bazai daidaita komai ba,ka zauna da ita,ka mu'amalanceta kamar mu'amalar yaya da qanwarsa,ta nan ne zaka karanceta,zaka gane halayyarta,,zaka dasa mata girman da kake so ta gani naka(yayi dariya cikin zuciyarsa shi yasan kan tsiyar shi yasa ya gaya masa haka)"shiru yayi ya koma ya lafe idanunsa a qulle yana nazarin maganganun hamza.

        Cikin 'yan awanni suka saba sosai da abida,tana da kirki da son jama'a,sunyi hira mai amfaji qwarai,wanda hakan ya sake sanyawa sumayya wasu mafarke mafarke da hange mai tsaho kan zamantakewar gidanta.sai da sukayi sallar magariba sannan suka wuce.

          Da daren ya shaida mata ta shirya da wuri gobe akwai inda zasu,bata san ina zasun ba har sai data gansu garin kano,murna da farinciki kamar zara yi me?kamar wadda ta shekara bata ga kowa ba,saidai bata samu ganin kowa ba,amma taga abdallahnta,don wunu sukayi tare,ta tabbatar abdallah ya samu iyaye fiye da nashi na asali,sauketa kawai yaayi suka wuce ahida driver,batasan ina yayi ba,bai shigo gidan ba sai da yammaci da zasu tafi,a lokacinne ya shigo suka gaisa da malam da mama,satar kallonshi take kawai,wato mutum me shi da yasan darajar iyaye koda ba nashi bane,sallama ya yiwa malam kan zasu wuce dubai,addu'a sosai malam din yayi musu.

      Cikin mota ta tsinci kanta tana kuka,a hankali ta dinga share hawayenta da gefan hijabinta,ji take kamar idan ta tafi ba zata dawo ba,waiwayowa yayi ya dubeta sai ya dauke kai yaci gaba da abinda yake,fata yake kada tayi mai sauti yadda zai dameshi,to kukan ma baiyi tsaho can ba sabida yadda ta tilastawa kanta yin haquri,tayi lamo tana tilawar nasihan mama.
Chapter 138 · 0% Book details