Sashe 26
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saidai kuma ina,maqaginsa ya riga ya QADDARA sai ya taka doron qasa,bayan wata bakwai ta haife yaronta namiji,ko yayeshi bata yi ba ta soma balle zawarci mai lasisi,a lokacin ta sake haduwa da qawaye kala kala idanunta suka bude,tasan duniya sosai har fiye da yadda uwarta ta sani ta koma dorata akai,hakan ya so tsorata maman har ta soma shirin hanata wasu abubuwan,amma ina.......maqeri ya riga mabada hali,tuni zainab din tasa aka rufe bakin maman da yayyenta maza biyu,duk wani abu da zata aiwatar bata laifi a idanunsu,musamman idan ta samo ta yaga musu.
Tun randa taga mukhtar zuciyarta ta yaba da shi,bata bata lokaci ba wajen bada sunanshi aka mata bincike a kansa,yadda takeso haka sakamakon yazo mata,mukhtar din yayi dai dai da ra'ayinta,saidai bata qaunar kishiya ko misqala zarratin,amma da ta samu labarin wace sumayya sai hankalinta ya kwanta,ta tabbatar ba matsala bace a gunta,aiki guda daya tak zata mata rana guda ta koreta daga gidan,duk da tana diyar malamai ai bata da maganin kirsa ko?.
*** *** ****
Hankalinta bai kwanta ba sai data gana da yaya yahanasu,wadda bata tunkareta ba sai data yi shiri sosai akanta,qwarai yaya yahansun taji wata qauna da aminta wa zainab,musamman data ji cewa ta taba haihuwar d'a namiji ma,nan zainab din ta zube mata alkhairai masu tarin yawa tare da tsara yadda zasu cimma nukhtar din duk da taimakon yaua yahansu wadda ke kiran kanta YAAYA kuma UWA a gunsa.
*** *** ***
Suna shirin cin abincin dare kiran yaya yahanasun ya baqunci wayarsa,dama ya tsammaci hakan saboda tun yammacin jiya da ya ziyarci gidan yaga gilmawar wata cikin layin nasu tamkar zainab din,zuciyarsa bata gasgata masa hakan ba tunda ya riga da ya sani bata san muhallinsu ba,amma duk da haka zuciyarsa bata samu nutsuwa ba har zuwa wannan lokaci.
"Kiyi haquri yaya,amma yanzu bazan samu damar fitowa ba" ya sanar da ita kai tsaye.
"La'ilaha illallahu,mukhtar yaushe kayi wannan riqar,akwai ranar dama da zata zo zan buqaci ganinka kaqi mukhtar" sai ta sa kuka
"Lallai ba shakka sumayya ta gama da mu,taci galaba akanmu ta sake cutar min da d'an uwa" sam baya son yaji kukan nata kamar yadda zuciyarsa ke quna idan yaji tana zagi aibata ko zargin sunayyarsa,hakan ya sanya ya amsa mata kan cewa yaba zuwa.
Wayar ya sauke yana duban sumayya
"Sumayya bana son fitar nan,ina zargin wani abu"ya fada idanunsa na sauya launi da alamun ransa ya fara motsuwa,kai ta kada
"Ka zargi alkhairi ya mukhtar,tunda kasan koma mene yaya jininka ba zata taba cutarka tana sane ba ko?" Shiru ya danyi sannan yace
"Na sani,amma matuqar abinda nake zaegi taje shirin aiwatarwa wannan karon wallahil azim sunayya ba zata kwashe mana da dadi ba,bazan yarda a ringa walagigi da rayuwarmu" duk da cewa a dunqule yayi maganar amma sai data haifar mata da matsanancin faduwar gaba wanda ta sanya har ta kasa tankawa, ya miqe ya shiga dakinsa ya dauki hularsa ya zura da muqullin babur dinsa don ya riga da ya ajjiye motarsa a inda take kwana ya fice daga gidan.
Kan kujera ta koma ta kwanta rigingine gabanta na ci gaba da lugude,a hankali ta dinga ambaton
"Ya rabbi yassir wala ta'asir" sabida neman gudun mawa da daukin wajen ubangiji.
Cikin falonta ya taddata wanda tun kafin ya kai ga shiga ya dinga jiyo dariya da hirarsu ita da yaran da alama cikin nishadi suke da walwala,sallamarsa ya katse hirar tasu,da daya da daya suka fice a dakin ya zama daga shi sai yaya yahanasun.
Suna kan gaisawa jamila ta shigo da jug guda biyu ruwa da lemo da kofuna ta dire masa,ya dauke kai ya dubi yaya yahansun yace
"Gani" sai ta dan murmusa
"Haba muntari,sai kace wanda ake gutsura,ko ruwa ai ka sha ko?" Sai yaga rashin dacewar yadda yazo matan,ko babu komai tsakaninsu ta bashi shekaru,saboda haka ya rusuna ya tsiyayi ruwan yayi kurba daya ya ajjiye kofin.
*** *** ***
Tana jin qarar babur dinsa ta miqe da hanzarinta,har ya shigo da shi ya kulle gidan ya qaraso falon tana tsaye,sam hankalinta ya gaza kwanciya a haka ya sameta a tsayen.
Saidai yanayin da taga fuskarsa ya zabge kaso mafi yawa na tashin hankalin da ta shiga,har ta saki bayyananniyar ajiyar zuciya ba tare da ta sani ba,'yar qaramar dariya ya saki yana fadin
"Me ya tsorataki haka?" Qwayar idanunta ta juya
"Kaine mana,hankalina ya qi kwanciya tunda ka fita"
"To ya kwanta,don babu komai sai alkhairi" duk da bata ji farinciki ko kadan ba yadda ta tsammata sai tace
"To Allah ya lamunce ya shige mana gaba" tayi maganar tana zama.
Ko kadan baiyi mata maganar komai ba,babu abinda yace mata kan hakan har bayan kwana biyu,a tsarinta mutum ce da bata shishshigi cikin lamuran da suka shafi rayuwar wani,hakanan ko da ga mukhtar din ne bata tambayarsa wasu lamura nashi na daban saidai idan shi yaga dama don rad'in kansa ya sanar mata,hakan ya sanya itama bata tambayeshi ba sai tayi zaton wani lamari ne da ya shafesu shi da 'yar uwar tasa.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
2⃣5⃣
____________________________
*wa tawakkal alal hayyul lazi la yamutu wasabbih bi hamdih*
_kayi tawakkali ka dogara da rayyayyen(Allah S W T)da baya mutuwa,kayi tasbihi/ka tsarkakeshi ka kuma gode masa_
____________________________
Guguwar dawowarta sumayya da taji ya sanyata daga kai ta bita da ido har ta shige dakinta.
Cikin mintinan da basu wuce biyu sumayyan ta fara jiyo qauri wanda yake da alama da wani abu aka sanya cikin garwashin wuta,data lura sosai sai ta fuskanci daga bangaren zainab ke fitowa,mai da kanta tayi taci gaba da kallonta,cikin sakanni qaurin ya buwayeta,hakan ya sanya ta koma dakinta ta dauko burner da turaren wuta ta fito falon wanda hakan yayi dai dai da sake ficewar fa'izan zuwa harabar gidan,jikin socket din dake daura da kayan kallon ta jona ta cikata da turaren wuta,mintina qalilan ya danne qaurin ya koma qamshi.
Tana zaune taji bude get din gidan da qarar motar mukhtar din,wanda hakan ke alamta dawowarsa,sai ta miqe ta koma daki ta sake feshe jikinta da turare sanna ta nufo harabar gidan.
Turus tayi ganin zainab gefan mukhtar tamkar zata shige jikinsa tana dubansa,hannunsa riqe da cup wanda ta cika masa da zobo wanda tuni ya fara kwankwada,yi tayi kamar ta juya saboda takaici sai kuna taga sam hakan baiyi tsari ba,zai kuma faranta ran zainab har taci karenta babu babbaka tunda ta riga da taga tsaiwarta.
Fuskarta ta fadada da fara'a,sannu a hankai ta soma takowa gun wanda takalmin qafarta duj da plate ne ya dinga bada sauti,hakan shi ya janye hankalin mukhtar ya zuba mata ido,ta masa kyau sosai,ji yake kamar ya tafi ya sureta ya daga sama yadfa suka saba,yau ta sauya masa sosai sumayyan,da wannan tunanin ta qaraso inda suke ta tsaya gabansa tana jifansa da murmushi,so yake take sumayyata kinyi kyau,so yake ya yaba mata,amma wani dunqulallen abun ya danne zuciyarsa,ya sake duban qwayar idanunta sai yaji wani bacin rai ya kamashi,murmushin da yakeson maida mata sai ya musanyashi da hade fusjarsa tsaf wanda hakan ya baiwa sumayyan mamaki,saidai duk da haka bata karaya ba ta miqa hannu ta amshi jakarsa tana masa sannu da zuwa.
Bai amsa ba don ji yayi ya gaza amsawar
"Wash" zainab ta fada wanda shi ya sanya su duja suka dubeta,baikai ga tambaya ba ta dora da nata jawabin
"Ka gani ko mukhtar,kaga abinda nake gaya maka ko?,yanzu fisabilillahi duk fadin gurin nan bai isheta ba sai ta takani saboda tsabar raini?" Mamaki fal zuciyar sumayya take dubanta,ya Allahu,nata salon kenan?matar da tazarar dake tsakaninsu ya isa tiqa tiqan mata biyu su tsaya shibe zata ce har ta taka ta?,tamkar dama neman abun fadan yake ya sake tunzura yana ji ana azqlzalar zuciyarsa,juyawa yayi yana jifan sumayyan da wani irin kallo
"Halayyar banzan da kike son koya kenan ko sumayya?,halayyar da ban sanki da ita ba?,to bari kiji ni bazan lamunta ba,bana son tashin hankali kin sani,har sau yaushe zan huta daga dawowata ko iskar gidan ban gama shaqa ba daga shigowarki zaki tada mana fitina?,to ki shiga hankalinki da ni idan ba haka ba zanyi mugun saba miki", bata data cewa,to me zata fada ma tunda ya riga ya yarda ya hau kai kuma ya zauna?,bata baki ne kawai tsayawa kare kai,saboda haka aladabce tace
" bansan na taka ta ba in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba kayi haquri ya mukhtar"sai da yaja fasali sannan yace
"Shikenan ta wuce"
"Au ni ba zaka ce ma ta ban haquri ba shikenan na gane matsayina wallahi" ta fada a zafafe tana fashewa da kukan kirsa sannan ta kwasa tayi cikin gidan da sauri,don sosai ta shaqa ba haka taso ya kasance ba,so tayi cikin biyu ayi daya,imma yace sumayyan ta durqusa ta bata haquri,ko kuma tayi qoqarin kare kanta ko ta masa turjiya ya jibgi banza a gabanta taci dariya ta more.
Da idanu sumayyan tabi mukhtar din ganin yadda ya diba shima ya bita cikin wani tashin hankali da yaji ya rikito masa sanda ya fara jiyo sautin kukanta,wanda babu qwalla ko daya sai tsabar ihu da iya manaqisa,kai sumayya ta kada zuciyarta ta karye,lallai babu shakka wani sabon SHAFIN QADDARAR TA NE YA SAKE BUDEWA CIKIN KUNDIN QADDARARTA,sau ta lallashi kanta kawai ta shige ciki da jakar tasa ta ratsa ta cikin falon nasu ta wuce sashen sa.
A qalla ta dauki kusan minti talatin zaune kafin ya shigo bangaren nasa,fuskarsa kadai zaka duba ta bayyana maka yanayin da yake ciki,kallonta yayi tana zaune gu guda,tausayinta nason masa tasiri amma wani abu mai qarfi na maye gurbin tausayin da jin haushi
"Na kai maka ruwan wankanka" tace da shi,bai amsa mata ba illa rage kayan jikinsa da yayi ya shiga wankan kawai.