Sashe 62
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sumayya ce ta tashi ta isa bakin qofar dakin ta murza key din ta bude,karima ce tsaye bakin qofar rataye da jaka,shigowarta gidan kenan ta hangi motar lukman fake,ta tambayi mai gadi ya sanar mata kusan awanshi biyu da kenan da dawowa,dama tun tana gidan sunan taji hankalinta yayi gida,abun mamakin shine dukka yaranta na tsaye bayanta harta da qaramarsu,abinda ya sake daurewa sumayya kai kenan,nufinta a gabansu zata tijara babansu?,da yanayin da tazo mata taso itama ta tarbeta,amma ganin yaran ya sanya sumayyan murmushi
"A'ah,maman nuratu,kece kuma da yaran baki daya haka?"harara ta balla mata sannan tace
" munafukar Allah bake nake nema ba,babban magulmacin nake nema,matsamana mu shige"murmushi ta kuma yi tana gyada kai
"Mai zai hana na barki ki shiga,ke da dakin mijinki,amma bai kamata ku dunguma baki daya ba,saboda bakisan a yanayin da zaku ruskeshi ba" ta fadi maganar tata ta qarshe qasa qasa yadda kariman ce kawai zata iya ji
"Bismillah" sumayyan tace sa ita bayan ta janye mata jiki,sai data ja tsaki sannan ta wuce kamar zata bangajeta,yaran suka yunquro zasu shiga ta sha gabansu,ta dubi nuwaira wadda ta tabbatar itace mai hankalin cikinsu
"Nuwaira,maza ku tafi dakinku ku sauya kaya,mamanku na fitowa,kama hannun basma ku wuce ko?"
"To anty" ta fada tana kama amma da nuratu sukayi gaba,tsare sauran tayi da idanuwa tilas duk rashin kunyarsu suka bi bayan nuwaira daidai sanda maganganun karima cikin ihu suka soma tashi
"Na shiga uku na lalace,yanzu lukman sai da ka kwanta da matarnan,lallau namiji d'an kunama ne,wayyo Allah yau naga ta kaina" ta fada tana dora hannu a ka tare da qarewa gadon nasa kallo,tsaye sumayya tayi harde da hannayenta tana kallonta,wato badon ta kora yaran ba nufinta gabansu zatayi wannan tambelan?,gaskiya ne dole wasu matan su janyo a dinga kiran mata masu naqasun hankali,takawa tayi ta dafa kafadarta wanda ya sanya karima waiwayowa tana dubanta
"Meye na tashi hankali haka?,tun ranar farko kenan?,bakisan somin tabi bane yanzu aka soma?,ki godewa Allah ma da bakizo kin samu ana third round ba" ta fada tana kewayeta tare da komawa bangaran gadon ta soma gyara bedsheet din tana murmushi.
Ashar ta lailayo ta danqarawa sumayyan irin wadda bata taba jin irinta ba
"Wallahi kinyi qarya kin kwana da yunwa duk malantar ubanki baki isa ba,duk wanda yaci tuwo da ni miya ya sha,wallahi sai kin gane kurenki,saikin gane shayi ba komai bane face ruwa,sai na cusa miki baqinciki fiye da wanda kika cusa min" sai ta waiwaya inda lukman ke zaune,tayi tsammanin ganin tashin hankalinsa qarara yadda aka saba sai ta ganshi zaune ko gezau
"Kai kuma tashi mu wuce dakina" ta fada a tsawace
"Ba inda zanje" ya fada yana jin shakka shakka na tasowa can qasan ransa yana qoqarin danneta,idanuwa ta zaro,jikinta ya soma bari,ba shakka alqadarinta gab yake da karyewa,kasa magana ma tayi sai kallonsa da takeyi
"A'ah,ki wuce mana kije tunda dai shi din yace bashi zuwa" a fusace ta waiwayo ta tunkuda sumayyan wadda bata zata ba,hakan yayi sanadin da tayi taga taga zata fadi lukman din ya tareta,sai ta miqe daga jikinsa tana murmushi kamar ba ita aka yiwa ba
"Babu komai,duk cikin haushi ne" qwallar baqinciki ce ta fara qoqarin zubo mata,da hanzari ta juya ta fice a dakim saboda batason sumayya ta gani har ta gane ta soma samun rauni,qofar sumayyan tabi ta kulle sannan ta dawi ga lukman wanda ta lura hankalinsa ya soma tashi,sosai ta zauna gabansa tana karanta masa abubuwan da suka dace har ya soma daidaita,sannan suka tashi suka sake komawa duba jikin hajiya wadda mamaki ya sake kamata ganin sun sake dawowar duk da taji shigowar karima gidan.
Qarfe goma da rabi suna dawowa daga wajen hajiya suka ratso ta falon,islam suka gani na matse hawaye ta tari gaban uban tana cewa
"Abba kaga kasa mamanmu ta hada kayanta ko ta tafi,kuma tace ba zata dawo ba" wani matsanancin faduwar gaba ya ziyarce ya zaro ido yana dubanta
"Tun yaushe?"
"Dazu,naje dakinka baka nan" duk sai sumayya taji babu dadi,kada dai abinda ya faru dazun ya sata bar musu gidan,sai ya kama hannun yarinyar yana fadin
"Ya isa,kada ki damu mamanku gobe zata dawo kinji,sumayya jeki da su suna dakinsu ina zato" amsa masa tayi,saidai qememe yarinyar taqi yarda ta kama hannuwanta haka suka tafi,koda ta shiga dakin suna zaune baki dayansu tsuru tsuru,duk sai taji tausayinsu ta dinga jin babu dadi,da fari duka qin sakin jikinsu sukayi da ita sai nuwaira kawai,amma ganin nuwairan ta saki jiki sai basma qaramar cikinsu itama ta ware,daga baya nuratu ta sake itama,sai islam kawai da tayi kicin kicin taqi shiga sabgarsu,ba ita ta barsu ba sai da taga sunyi bacci sannan ta musu addu'a ta bar dakin.
Sumayya na wucewa wayarsa ta dauki ruri,lambar karima ce hakan ya sanyashi dagawa cikin hanzari yana cewa
"Haba karima,haba karima,meye haka din da zaki bar yaranki ki kwashi kaya,yaji da girmanki da komai"
"Saurara ba wannan na kiraka ka gaya min ba,kiranka nayi na gaya ma ka sanar da wannan matar taka diyar malamai masu kwanan buzu cewa,ta bar murna karanta ya kama kura,babu inda zani ina nan dawowa,kuma dawowata ba zata yi mata dadi ba wallahi wallahi sai ta gwammace kida da karatu,don babu wata 'ya da zan bari ta shigarmin rayuwa ba tare da na nuna mata kuskurenta ba,kuma kada ka soma wahal da kanka kace zaka nemeni don ba samuna zaka yi ba,har sai randa na dawo da karan kaina,ina fata ka gane"qit ta datse kiran sai yabi wayar da kallo yana kada kai aljihu ya maidata yana amsa sallamar da sumayya tayi masa.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:45] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
4⃣4⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*innal laha la yazlimu misqala zarrah*
*_haqiqa Allah baya zalunci daidai da qwayar zarra(ko qasa ma da abinda yafi qwayar zarra qanqanta)*_
_______________________________
Gefansa ta zauna cikin rashin jin dadi,tana jin kamar ta raba yaran da mamansu ne,ta dubi lukman
"Ya kamata zuwa gobe kaje ka dawo da mamarsu islam,kada a ja abun yayi nisa don Allah,yaran na buqatar mamarsu" kai ya kada baison gaya mata wani abu da zai daga mata hankali,a yanzun da karima ta dan tura ta bar gidan sai yake jin kamar an zare masa wata qaya data tsaya masa a maqoshi
"To naji" kawai ya fada.
Kwana biyu tana masa mitar yaje ya dawo da karima arana ta uku yace kada ta sake masa maganar baiso,idan lokacin dawowa yayi zata dawo,ai ta saba ba yau farau ba,hakan ya sanya ta tsuke bakinta,hankalinta ya dan kwanta ganin yaran basu tada hankali sosai kan rashin dawowar mamansu ba.
Cikin kwanakin da suka biyo bayan tafiyar karima baki daya gidan yayi dadi,kada ma lukman hajiya da nuwaira suji labari,da fari sumayya ta fara fuskantar matsala daga yaran saboda qarancin tarbiyya da suke da ita,amma sai ta jure tayi amfani da hikima irin tata,a hankali ta fara janye qananan,nuratu basma da syyada,islam ce kawai ta taqi biyuya,ta soma kwaso halin uwarta tsaf,hakan yasa ta tattarata ta watsar gefe,zasu hadu suci abinci tare,suyi karatu,ta basu labarai na annabawa da sahabbai,suna bala'in so ta basu tarihi,har rigima suke idan tace ta gaji,sosai ta shiga jikin yaran suka soma shaquwa da ita,ta koya musu abubuwa da dama wadanda ya kamata ace sun iya amma basu iya ba,kamar alwala,sallah,sallama idan zasu shiga guri,addu'ar sanya kanya,addu'ar bacci da tashi daga bacci,addu'ar shiga bandaki data fitowa,addu'ar fita daga gida da ta shigowa da yin bismillah da hamdala kafin da bayan gama cin abinci,su kansu yaran dadi sukeji,nuwaira tafi kowa murna takance
"Anty dama tuntuni kema 'yar gidan nan ce,ai da tuni nayi saukar qur'ani ko?" Dariya takanyi tace
"To ai yanzun ba gashi na zo ba?,kuma zakiyi ne in sha Allah",tarbiyya take basu sosai mai wuyar bari ko mantawa,tana musu ne bilhaqqi fisabilillahi,don har ga Allah tana son yaran,ko ba komai babansu da kakarsu na gwada mata qauna.
A hankali sai itama islam din ta fara biyuwa,ta shige cikinsu,idan kaga sumayya da yaran zakayi zaton qannenta ne,dama gata gwanar son yara,abun ya yiwa hajiya dadi,wani lokaci har takan tsinci kanta da addu'ar kada Allah yasa karima dawo,don ita kanta yanzu anan bangaren take wuni sai dare zata kwashi jikokinta suje su kwana tare da ita a can,a yanzu sumayya ta koya musu qaunarta da ganin girmanta,ta bangaren lukman kansa yana mamakin yadda hankalinsa yake a kwance,sau tari ma sai ya mance da wata karima,kwanciyar hankali da nutsuwa ya samu sosai irin wadda bai taba samun irinta ba tunda ya fara aure,ba shakka sumayya ta dabance,zai kuma yi fatan kasancewa da ita har qarshen rayuwarsa,hatta da mai gadi da mai aikin gidan sunga sauyi,sun kuma ga banbanci,suma sun samu 'yanci.
Kwanci tashi har aka kusa shafe wata biyu ba motsin karima,sam sun mance ma basa maganarta,banda yaran da wani lokaci zasu dan tada zancanta shikenan an wuce gun,ta maida qaunar dake tsakaninsu baki daya saboda haka nuwaira ta samu matsayinta na babba a gidan,a yanzu takan iya tsawatarwa dukkaninsu sabanin daa da bata isa ba,basma ma na iya dungurinta ta wuce,da tace musu abu babu kyau zasu daina saboda ta gaya musu wanda keyin abinda babu kyau Allah zai sashi a wuta,ta wassafa musu yadda wuta take dai dai da tunaninsu yadda zasu gane haka ma aljanna,don haka da tace abu da kyau tofa zasu shiga yi saboda sun san aljanna sun san wuta.
Da kanta ta nemi lukman kan ya sanya yaran islamiyya,saboda duk wanu ilimi da zai basu matuqar babu karatun addini aikin banza ne,ya yarje mata kan ta nema musu ya amince,da kanta ta duba islamiyar dake qarshen layinsu,ta gamsu da yanayin karatunsu saboda haka ta yankar musu foam,cikin kwanakin da basu wuce uku ba aka gama musu komai har dinkin unifoarm suka fara zuwa,su kansu yaran murna suke da fara zuwa makarantar,idan suka dawo tare suke bitar dukka karatuttukansu,wani dadi hajiya da lukman din ke ji,sai yanzu suka gane tabbas ashe da rayuwa suke cikin duhu sai da Allah ya kawo musu SUMAYYA HASKE.
*KUNDIN QADDARARTA*