Sashe 68
Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun idar ya matso inda take,hannunsa ya sanya cikin nashi yana kallon qwayar idonta
"Sumayya,Allah ne kadai yasan yadda nake jin sonki a zuciyata" murmushi tayi tana girgiza kai."ya mukhtar,sai kace yau kasan sumayya,sai sake jaddada qaunarta kake bayan ta riga da tasan hakan"murmushin shima yayi
"Hakane fa ko sumayya,amma wannan karon wata qauna ta daban nakeji,sumayya,ina so ki kasance tare da ni har qarshen rayuwata"
"Na maka wannan alqawarin"
"Na gode"
Sai kuma shiru ya biyo baya har ya qosa taji me zai sake cewa,sai daga bisani yace
"Sumayya,zaki yimin alfarma na kasance tare da ke cikin wannan daren?"idanu ta daj fiddo
"Ya mukhtar,kwana hudu fa ya rage"
"Na sani sumayya,amma so nake kimim wannan alfarmar indai ban keta iyakar ubangiji ba"
"Na maka ya mukhtar" ta fada kanta tsaye
"Allah yayi miki albarka" ya fada yana janyota ta fada jikinsa kowannansu cuke da kewar dan uwansa,kada ma mukhtar yaji labari,ji yake kamar an masa bushara da aljanna.
Qarfe goma saura na dare ta fito daga bandaki,mukhtar tuni ya kammala shiryawa yana zaune yana jiran fitowarta,binta ya dinga yi da kallo,ji yake tamkar ya hadiyeta ya maidata ciki,har yanzu baiwar nan da ya santa da ita na tattare da ita,ganin ta kammala ta yafa mayafi tana saba jaka ya sashi saurin cewa
"A'ah,amarya guda bai kamata ace bata ci komai ba" sai ta saki murmushi cikin jin kunya
"Ya mukhtar yau ka manta da abdallahnmu?,munfa barshi a gida"miqewa yayi da sauri yana fadin
"Kai kai hakane fa,jikina ya bani ma fa ya farka" dariya ta saki
"Uhmmm,sannu masu 'ya'ya"
"Wallahi kuwa,d'a ba wasa bane" ya fada yana kama hannunta suka fice.
Ihu take so ta kwarara ko zataji sanyi a ranta amma zinatu ta hanata don kada ta tara musu mutane,wadda ita ta kawo mata labarin komawar auren sumayya da mukhtar,maimakon haka saita maida dubanta ga zinatu cikin daga murya
"Wallahi wallahi sai na aikata abinda na qudurta babu mai hanani aikatashi wallahi,mukhtar nawa ne,nawa ne ni kadai,bazan juri ganinsa da wata ba ba ni ba" ta fada kamar zararriya tana mai ficewa daga layin cikin qunar zuciya kamar zatayi aman zuciyar tata.
Ko da ya sauke ta ma sai da ya sake tsareta,kamar bazaya tafi ba har sai dayaga giftawar malam da alama ya shigo gida kenan sai da safe sannan sukayi sallama bayan ya cikata da kalamai masu tsayawa a zuciyar wanda ake so.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[2/19, 4:53 PM] +234 807 885 3729: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
4⃣8⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*kullu nafsin za'iqatul maut,summa ilaina turja'un*
*_DUKKAN RAI SAI TA DANDANI MUTUWA,SANNAN IZUWA GAREMU ZAKU KOMO_*
_________________________________
Tana shirin kwanciya wayarta ta dauki ruri,mukhtar ne sai ta kumahe idanu tana murmushi
"Na kasa bacci my sumy,ganinki nake kusa da ni".'yar qaramar dariya ya tasa tana fadin
" baban zumudi ka zama ya mukhtar ne?"shiru ya danyi sannan ya saki ajiyar zuciya
"Bakisan me nake ji ba game da ke sumayya". Hira suka kashe lokaci suna yi,a nan yake gaya mata ran rakota tare da yaya yahanasu za'a zo,har mamaki take idan taji yadda yaya yahasun ta sauya take nuna mata qauna,basu suka rabu ba sai daya na dare,ta dubi agogo tana zaro ido ganin lokacin da suka shafe tare,sai ta fita ta daura alwala tayi sallah raka'a biyu sannan ta kwanta.
****** ******** *******
Shirye shiryen tariya sun kankama sosai,tayi gyaran jiki hadi da qunshi da kitso,kayanta baki daya ta kammalesu.
Ranar alhamis ana ya gobe zata koma,da azahar suna falo ita da halima da zainab suna hira ita kuma tana gugar ragowar kayan abdallah da bata gama shiryawa ba,sai anty salma qanwar mama wadda anam zata kwana,wayarta dake daki ta soma burari,abdallah ne ya miqe da gudunsa ya dauko ya miqa mata,anty salma ta talle masa qeya tana cewa
" kaji dan jakar uba wai yasan kayan uwarsa,sai kace wani yace zai dauki wayar ne"dariya sukayi dukansu halima tace
"Indai Abdallah ne kadan kika gani anty" ita kuwa sumayya miqewa tayi ganin lambar mukhtar ce ta fita ta koma dakinta
"Lafiya abban abdallah naji muryarka can qasa?"murmushi ya saki sannan yace
" lafiya qalau,a yanzu ma ina gida kwance ina hutawa,babu abinda nayi amma wata gajiya nakeji sosai a jikina,kewarki nake sumayya goben nan kamar ba zata zo ba"tamkar yasan abinda take ji jikinta itama kenam,sai ta saki ajiyar zuciya tana masa murmushi
"Au dariya ma kike min?,naji na gode,amma da zaki taimaka min da kinzo na ganki kinji my sumy" sai ta kasa musa masa,dama suna da agender fita karbo dinkunan sumayya gidan wata mata bayan sallar la'asar ita da anty salma
"Babu damuwa ya mukhtar,amma sai bayan la'asar"cikin zumudi yace
"Da gaske sumayya ta?,kada fa ki shirgani"dariya ta qyalqyale masa da ita
" da gaske nake mana abban abdallah,ka jirayeni,amma fa gobe ba za'a rakoni da wuri ba tunda yau ka sake gani na"
"Babu komai,ai goben ta Allah ce,Allah yayi miki albarka sumayya ta" tana jin dadi ya sanya mata albarka don haka da sauri ta amsa da amin.
A gidan mai dinki ta bar anty salma tace zata je ta dawo,ta riga da tasan inda zata din saboda haka tayi tayi abdallah ya zauna qememe yaqi har da kukansa ammi zai bi tace madallah yayi ta binta din sai sun dawo.
A qofar gidan mai adaidaita sahu ya sauketa,ji tayi ana malam ga kudinka,tana waiwayowa sai taga mukhtar ne,cikin mamaki take tambayarsa
"Ya akayi kasan na qaraso"
"Jikina ne ya bani" ya bata amsa yana amsar abdallah daga hannunta yana masa cakulkuli suna qyalqyala dariya tana biye da su har zuwa falon gidan,kallon gidan take ya sauya komai kamar wanda zai kawo budurwa,komai fes gwanin sha'awa,zubewa sukayi kan kujera mukhtar na biyewa abdallah suna ta wasanninsu yayin da sumayyan ke zaune gefe guda
"Wai nikam 'yar kallo kuka maidani ne,nazo amma ba'a tani,bayan nemana akayi" ta fada tana murguda baki,dariya mukhtar din ya saki yana duban abdallah."lah,abdallah kaga mamanka na kishi da kai"sai ya kada kai kawai yaron don bai fahimci me yace ba,juyawa yayi gunta
"Dama taimaka mana kika yi kika dafa mana wani abun madam"
"Kamar me?" Ta tambayeshi
"Abinci mai sauqi da dadi"
"An gama" ta fada tana miqewa
"Ammm,madam,amma da kin taimaka kin cire wannan hijabin tunda gaban mijinki kike ko?" Dariya ma ya bata yadda yayi maganar a dake,bata ce komai ba ta cire din,sai ta miqawa abdallah hannu
"Muje kayi fitsari sai ka dawo ko?" Lafewa yayi jikin mukhtar din qememe yaqi yarda da ita
"Barmin yaro na ana dole ne,yayi fitsarinsa babu komai cinyar babanshi ce".don haka ta juya zuwa kitchen ta barsu nan.
Tana tsaka da girkin mukhtar ya shigo goye da abdallah,saura qiris ta dona hannunta cikin gas garin dariya
" ka ganka kuwa da goyon nan,don Allah tsaya na maka hoto"shi din ma dariya yake,
"To ya zanyi,yaqi yarda na kwantar da shi kwata kwata"hoto ta musu wajen kala biyar ta nuna masa suka dinga sheqa dariya,tex din da ya shigo wayarta ya katseta,anty salma ce ke gaya mata ta wuce gida uta kam sai ta taho,tana niyyar kiranta tace ta jirata tana tahowa mukhtar ya riqe hannunta
" qyaletq ni da kaina zan maidaki".qarshe tare suka gama girkin wajen sallar magariba sannan ta karbi abdallah da qyar zata kwantar,sai ya farka ya riqe mukhtar gam gam yana sakin kuka,tilas yace ta qyaleshi suka dauro alwala sukayi jam'in sallar magariba tare sannan ta gabatar masa da abincin.
Tare suke ci baki dayansu,saidai duk daga kan da zatayi idanuwansa na kanta,saidai ya sakar mata murmushi ta maida masa martani,sake hada idanuwa sukayi karo na barkatai,sai ya kauda kallonsa ya maida kan abdallah
"Na godewa Allah da ya sake gwadamin wannan lokaci cikin rayuwata,lokacin da zan zauna ni da matata abar sona da kuma diyan cikina,ina fata Allah ya rayamin kai" ya fada yana shafa kan abdallah,sai yaron ya dago kai yana kallonsa kamar yasan ma'anar abinda yake cewa
"Ina da buri kanka abdallah" ya sakw fadi,sai ya dubi sumayya
"Ki taimaka min wajen tarbiyyar abdallah don Allah" murmushi ta saki zuciyarta na bugawa kadan kadan
"Banda abinka ya mukhtar ai saidai mu taimaki juna tunda tare zamuyi tarbiyyarsa" girarsa daya ya dage
"Haka ne fa,to Allah ya bamu aron rai"
"Amin ya Allah" ta fada tana ci gaba da cin abincin,sai daga bisani ta lura ba wani cin abincin sosai mukhtar din keyi ba sai aukin kallonsu
"Ai bama cin abincin kake ba fa yaya,wannan kallon duka na meye?"
Murmushi ya kuma saki."kallon so da qauna nake muku"dariya ya bata sosai
"Naga alama sai na maka dura" ta fadi tana debo abincin da spoon tana bashi,qarshe ita ta qarasa basu abincin dukansu sannan ta gyara gun,kayan wasa taga yana ta hadawa abdallah sannan ya janye ta bedroom yace zata tayashi wani aiki,bata fahimci wayo yayi mata ba sai da labari ya soma shan banban.
Daf da kammaluwar komai sai ta tsinci hawaye na diga idanunsa,tasa hannu ta shafo sai taji itama nata idanun na fidda ruwan qwallar da batasan dalili ba
"Ya mukhtar ko na yi ma laifi ne?" Ta tambayeshi cikin sanyin jiki,sai ya sake qanqameta yana sakin ajiyar zuciya tare da murmushi
"Babu abinda kika yimin,tsakani na da ke sai fatan alheri,Allah ya haskaka rayuwarki,qwallar farinciki nake musamman idan na tuna gobe zamu sake sabon zama sumayya" dariya tayi tana kwantar da kanta a qirjinsa
"Na gode ya mukhtar"
"Nine da godiya sumayya,ina so ki sake yafemin ki dauka tamkar babu abinda ya taba faruwa tsakaninmu mara dadi" cikin shagwaba tace
"Ni na manta ma fa ya mukhtar,ni babu abinda ya taba faruwa tsakanina da kai,kai fa uban 'ya'ya na ne".
Da qyar ya yarda zai maidata gida,da sdrd yayi tayi zamanta meye marabar yau da goben,ko a motar ma sai da ya gama yawo da su guri guri ya loda uban siyayya sannan ya kaisu gida,riqe hannunta yayi sanda take shirin fita ya sumbaci bayan hannun nata,itama sai ta maida masa martani,ta jima tsaye a soronsu tana leqensa ganin ya tsaya bai tafi ba,sai daga bisani taga ya ja motar ya tafi.
*JUMA'A*