← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 210

Sashe 83

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kyakkyawar budurwa ce tsaye a bakin qofar falon,farace mai matsakaicin tsaho,sanye take da yadin material plain mai santsi da kauri ruwan makuba(maroon)tayi rolling da mayafi ruwan hoda wanda ya sauka iya kafadunta,takalmin qafarta mara tudu(plate)ne shima ruwan hodar,fuskarta fayau babu kwalliya sai kwalli kawai,kallo daya zaka yi mata kasan cewa akwai hutu kwainane da boko zalla a gun,a qalla zasuyi sa'anni da sumayya,minal na tsaye gabanta tana ta tsalle,yayin da budurwar ke qoqarin budewa minal choculet data shigo mata da ita,daga kai tayi suka hada ido da sumayya,sai ta maida kanta ga minal,hakan ya sanya sumayyan itama dauke kanta don bata santa ba ta nufi matattakalar benen don ta haura sama,sai muryar anty dije dake saukowa ta dakatar da ita
"A'ah amira ya kike tsaye,samu gu ki zauna mana"
"Ba komai umman khalipha,sauri nake zamu fita ne da anty su'ad,sai malam alqasim yace min yaga dawowarku na shigo inga mutuniya ta" dariya anty dijen tayi tana qarasa saukowa
"Mutuniyarki kam ai gata nan,yasu maamaa"
"Maamaa lafiya tace in gaidaki"
"Ina amsawa,kice su'ad anzo kenan" dan murmushi tayi
"Eh wlh,bari na wuce umman khalipha"
"Af tsaya mana na baki saqo wajen maamaa"
"Umman khalipha sauri nake,amma may be idan mun dawo da wuri zan biyo na karba mata,banso ma akai su'ad na nan" ta fada a shagwabe kamar wata qaramar yarinya,dariya anty dije tayi don tasan dawar garin
"To shikenan,sai kun dawo"
"Tom" ta fada tana jan kumatun minal tana mata bye bye bayan ta dan sake duban sumayya dake danna wayar ta tana laluben mama don ta kira ma anty dije ita sannan ta miqa mata wayar,karba anty dije tayi tana fadin
"Kun gaisa ne da amira" kai kawai ta kada
"Kai amma dai baki kyauta ba,da na ganku tare ai na zaci kun gaisa sumayya"
"Bansanta ba anty,kuma ko da na fito bata min magana ba,hasalima dauke kanta tayi"
"Qaniyarki,ba gidanku tazo ba" dariya tayi cikin tsokana tana rufe baki
"Af,na manta gidanmu fa tazo afuwa umman khalipha" itama ta fada,sai ta baiwa anty dijen dariya,saboda kusan da wuya kaga sumayyan na zolaya ba al'adarta bace sai lokaci zuwa lokaci,daki ta juya ta shige tana fadin
"Idan kin gama anty ki bawa laila don Allah ta samun chargy"
"To" anty dijen ta amsa tana amsa kiran wayar.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽[1/7, 7:07 AM] ‪+234 807 885 3729‬: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣6⃣

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Wa wassainal insaana bi walidaini ihsaanaa*

*mun yiwa mutum dan adam wasiyya/umarni da kyautatawa iyaye(uwa/uba)kyautayawa(matuqar kyautatawa)*
________________________________

      Tana idar da sallar minal ta shigo dakin da gudu
"Anty kizo ana kiranki a waya"
"Waye yake kirana?" Bata amsa mata ba yarinyar sai jan hannunta da ta soma tana nuna qofa da yatsarta,murmushi tayi don tasan halin minal din,sai kawai ta miqe ta bita,tayi tsammanin wayarta dake gun anty dije ake kira,saidai bata tsaya ko ina ba sai kitchen,ta dangana da ita zuwa bakin wayar su ta landline
"A nan ake kiranki" cikin mamaki tace
"A nan kuma,ba wayarku bace ta gida,saidai ko anty ake kira ko?"
"A'ah sumayya suka ce" inji anty dije dake shigowa kitchen din,cikin shakka da ko kwanto ta daga bayan wayar ta sake sakin qararrawa.

      Nemam wajen zama ta soma yi jin muryar namiji,gabanta ya yanke ya fadi tsoro ya kamata,ta tsani abinda zai hadata da namiji,ta amsa gaisuwar da ake mata sannan mamallakin muryar ya soma magana
"Nasan baki sanni ba duk da kin taba ganina sau daya,amma nasam zaki iya tunani,shekaran jiya na ganku a wani restaurant dake kaduna ke da qannenki da yayarki,so naso na tare ki na miki magana sai kuma kunyar idon mamanki ya hana,na lura akwai sanayya tsakaninku da masu wajen,gurinsu na amshi lambarku ta gida"
"To sai kuma akayi yaya?" Ta fada gabanta na faduwa tana neman wajen zama saboda sanyi da jikinta yayi,tana mai fatan alaqar ta yanke daga nan,murmushi yayi wanda har sai data jiyo
"Haba yi a hankali mana beauty,ni da nake so mai qulla dangantaka da alaqa mai kyau?"
"Me kake nufi?" Ta tambayeshi gabanta na faduwa
"Kin gane,tun ranar da na dora idanuwana a kanki Allah ya dora min qaunarki,duk duniya naji babu wata diya mace da zuciyata ke so da qauna sai ke,hakan ya sanya na kasa haquri da ke,ina kuma fatan zaki karbi maganar da hannu bibbiyu"
"Hmmmm,Allah sarki" tayi qarfin halin fada tare da kife kan wayar ta miqe ta fice daga kitchen din,baki daya jin zuciyarta tayi ta quntata,itakam duk yadda take qoqarin killace kanta bata tsira ba?.

       Kusan ragowar ranar baki daya a daki tayi ta,dadin abun ma suna tare da su laila,kwanakin qarshen mako ce,sai jibi litin zasu koma.

  *******   *******   *******

      Washe gari tana zaune falo ita da hafiz da minal suna kallo,hafiz kuma na goge musu uniform dinsu,da yake da kansu suke wankinsu saboda suna da inji wanki(washing machine),sumayya ke girkin dare suna ta murna yau zasu ci tuwo saboda haka hankalinta ta rabashi gida biyu,anty dije ce ta sauko daga sama laila na binta a baya hannunta riqe da turamen atamfofi guda biyar,har suka qaraso falon laila na wa anty dujin rakin kayan sun mata nauyi
"To hafiz guga yake muku da ya rakaki,khalipha kuma nasan idan ya bikin ba dawowa zaiyi da wuri ba,kuma aiki ne da shi zaiyi gyaran jakankunan makaranta,idan kinje bakin get baba haruna ya karba miki ku qarasa ciki"
"To" lailan ta fada tana nishi ta fice,dariya sumayya ta dinga yi mata tana tsokanarta wai taji kunya.

      Minti kusan ashirin shiru laila bata dawo ba har sumayyan ta kammala abincin dare,anty dije dake shirin shiga wanka ta sauko qasa tana duban sumayya
"Kinji lailan itama shiru kamar an aiki bawa garinsu?"
"Ko a tura khalipha ya ganota tunda har yanzu hafiz bai gama gugar ba?"
"A'ah,ai duk kanwar ja ce,sanya mayafinki don Allah ya rakaki ki gano min ita" fuska ta yamutsa
"Banson fita anty wlh"hararata tayi
"ke kam ko gajiya da zama a gida bakiyi,tun jiya da kika shigo ko waje baki leqa ba,to ba wani gu bane gidan Baabaa prof ne,gashinan yana kallon gidan nan" dan jim ta sake yi,haka kawai bata son shiga gidan,don tun daga qofar get din zaka ga banbamci qarara da sauran gidajen da ke dukka layin da kewayen unguwan,ba yadda ta iya ta shiga daki ta fiddo dogon hijabinta ta dora saman riga da skert na atamfa dake jikinta ta zura silifa ta fito khalipha ya biyo bayanta.

Khalipha na gaba tana biye da shi har bakin tamqamemen get din gidan,qwanqwasawa ya shiga yi a hankali,daga ciki taji ance cikin wata dattijuwar murya
"Kai,waye a nan"
"Khalipha ne"
"A'ah,khalipha khalipha 'yan kano" taji ana fadi kafin taji motsin bude qofar,dattijo ne wanda a qalla zaiyi shekaru sittin tsaye a gabansu hannunsa riqe da buta yana murmushi
"Ina wuni baba halliru"
"Lafiya qalau khalipopi,dazu naga laila ta wuce ai tana tafiya da qyar da kaya a hannu,sai haruna ne ya qarasa mata da su" baban ya fada yana basu hanya su wuce,russunawa rayi cikin girmamawa kamar yadda halayyarta take ta gaidashi amsawa yayi cikin fara'a,khalipha uban 'yan surutu yayi caraf yace
"Yayarmu ce baba daga kano muka taho da ita"
"Sannu da zuwa" baban yace ta amsa da yauwa sannan ta ja khalipha suka wuce ciki.

A darare taki bin bayan khaliphan wanda yayi gaba abinsa da alamun sabo da gidan a tattare da shi,girma da kyawun gida ya ratsata tare da bata mamaki,zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba ganin gida kwatankwacinsa ba,ko ina ka kalla qasan gidan a shimfide yake da grass carfet,babban gida ne wanda aka tsara gininsa,sannan aka baje fasaha aka fidda sassa sassa a gidan a zamanance masu kyau da kama da juna,gidan na dauke da sassa biyu manya,kowanne sashe akwai sasanni a cikinsa guda uku masu yalwa da tsari kuma kowanne ma dauke da bene,babban sashin dake hannun dama sashi ne na mai gidan da matansa guda biyu,daya sashen kuma sashe ne da tun usuli yake mallakar yaransa maza su uku tun zamanin samartakarsu har ya zuwa yanzu da dukkansu sukayi aure mallakarsu ne suna amfani da shi lokaci zuwa lokaci,kallo daya zaka yiwa gidan ya burgeka saboda tsarinsa da yanayinsa,komai luf luf a tsaftace a killace,kama daga wajen hutawa dake gefe guda,gun ajiyar motoci wajej wasannin motsa jiki da lambun dake daga bayan gidan.

Sashen dake hannun dama khalipha ya dosa,ganin sun tunkari wata qofa ya sanya sumayya riqeshi
"Kai,wai ina zamu?" Dariya yayi
"Kiran anty laila mana"
"A wanne guri?"
"Gun ummee ko gun anty maamaa" sakinsa tayi tana kokwanto kafin daga bisani ta bishi.

Shi ya tura qofar falon da sallama kafin itama tayi tata,saka kanta kawai ya sanar mata akwai sauyin yanayi sosai tattare da gun,falo ne na alfarma wanda ya ginu ya kuma tsaru abun burgewa da sha'awa ga idanuwa,tsit falon yake babu kowa sai tafkekiyar t.v plasma dake barazanar mamaye bango dake manne tana aikinta a tashar sunna t.v,carfet ne mamaye da falon duk girmansa a maimakon tiles,labulaye da kujeru na alfarma kalar carfet din mai azabar taushi,flower vase ce masu kyau qirar qasar chaina a sakaye a kowacce kusurwa ta falon,sai tarin kayan turaren wuta da humra dake ajjiye cikin tsari gu guda,da qananun centre table dake tsakanin kujeru don ajjiyewa baqo abin sha,ba wani tarkacen qyale qyale bane a falon amma ya tsaru,hakanan duk abinda ke cikinsa mai kyau ne da tsada,qamshi da sanyin da falon ke bayarwa kadai ya ishi zuciya samun nutsuwa.

Sallama ta qarayi tana wuwwurga idanuwa cikin falon jin shuru ba motsin mutane duk da tana iya jiyo qamshin girki dake tasowa bisa dukkan alamu kitchen din na cikin falon duk da bata iya gano qofar da kitchen din yake,jin still shiru yasa ta juya ta dubi khalipha
"Wai ina ka kawo mu nan ne khalipha,kasan dai nan babu alamun laila,inda tana nan da tuni ka jiyo ka......." Qarar takalmi da ta jiyo alamun ana saukowa daga saman benen ya sanyata yin shuru ba tare da ta qarasa fadar abinda takeson fadin ba
"Ha'an,khalipha ne?" Taji ana fada wanda hakan ya sanyata daga kai.
Chapter 83 · 0% Book details