← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 210

Sashe 111

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi tayi ganin yaron yayi saurin rufe bakinsa yana cewa
"Allah na tuba"
"To yanzu muje mu gwada inga alwalar kowa din,duk wanda yafi iyawa shi ya m....." Sai ta kasa qarasa sunan
"Wanda duk yafi iyawa shi aka fi so" ta sauya salon maganar tata,tsalle suke har suka isa gaban fanfon,tana tsaye tana kallon kowa daya bayan hannayenta harde a qirjinta,kamar yadda yake zaune saman kujera yan kurbar tea mai zafi yana kallonsu,sai da suka kammala tsaf,tabbas hibba ta fisu iyawa,amma ita dinma akwai gyare gyare,a hankali ta yaye yalwataccen mayafin data suturce jikinta da shu,wanda hakan ya bayyana shape dinta sosai kasancewar riga da skert ne a jikinta,tun bayan zuwanta abuja kayan suka dan kamata kasancewar ta murje ta cicciko,idanuwanshi ya lumshe saboda gujewa kallin haramun dinshi,sai ya kasa sake bude idanuwan mashi ya barsu a lumshe yana sauraron ta tana fadin
"Sai kuyu haka,yauwa haka,haka" bai bude ba har sai da yaji tana fadin
"Idan kayi haka,kayi alwala mai kyau" a hankali ya bude idanuwan nashi,wannan karon fuskarta tarwai take ta haske qwan lantarkin da ta tsaya saitinsa,ya dan qura mata idanuwa yana son tuna inda yasan fuskar
"Mai kuka a uk mall" qwaqwalwarsa ta birkito file dinta,qaramin murmushi ne ya subuce masa,wanda idan baka kula da kyau ba na zaka gane hakan ba,saboda cije leban qasan bakinsa da yayi
"Tana acting kamar wata babba" ya raya hakan a ransa.

Riqeta yaran suka sake yi,nurain daya daga cikin yaran yace
"Anty ki mana tatsuniya,baabaa lami mai aikin momi tana mana" murmushi ta saki,ta lura suma lallai yaran masu son mutane da sabo ne,saidai suna son riqeta gashi tana son tafiya gida ne
"Ban iya tatsuniya ba saidai na baki tarihi"
"Laaaah,irin wanda uncle man ya taba yi mana rannana?" Zaitun daya yarinyar ta ambata da salon tambaya,duk da bata sani ba amma sai ta daga kai
"Ita,amma yanzun inaso naje gida na gaida anty na,sai wani lokacin na muku ko?"
"Yaushe?" Inji hibban,kai ta girgiza qaramar dariya na son subuce mata,yaaraan akwai wayo,tana som tana yaro mai wayo da kaifin qwaqwalwa irin haka,ta tabbatar basirar da wayon bai tashi a banza,zai zama abu ne mai amfani a nan gaba
"Wataran in sha Allah".

A hankali ya janye idanuwanshi daga kansu jin qarar wayarshi,ya cirota daga aljihun black trouser din dake jikinsa yana duba mau kiran,su'ad ce,dan qaramin tsaki yaja,ba matsala yake so ta qara maishi ba,ya riga da ya yanke magana,ya gaji da auren asha ruwan tsuntsaye da sukeyi,ita tana kano shi yana daura,kusan tun jiya bayan isowarshi garin da yaje gidan hamza abun ke dawainiya da shi,kasancewar wanda amiran zata aura cousin suke da hamza,wata rayuwa ya gani ba irin tasu rayuwar ba,ba irin rayuwar gidanshi ba,yana iya tuna sanda hamza ya dagewa auren yarinyar suna ganin baikensa,ashe akwai abinda ya gano?.

Rejecting call din nayi sannan ya maida kansa kan laptop dinshi da niyyar ci gaba da aikin da yakeyi,wani tsakin ya kuma ja ganin lokacin da ya bata yana kallon sha'anin da bai shafe shi ba,yayi asaran time dinsa a banza,saidai yadda take kiranshi a jejjere ya hanashi aiwatar da komai,wani wawan tsakin ya sake ja,a rayuwarshi ya tsani abinda zai takurashi,sai ya ciro wayar a fusace ya daga ya kara a kunnenshi,cikin shagwaba da karyar da murya ta soma fadin
"haba my man,please....please kada muyi haka da kai,ka duba fa ka gani duka duka shekara daya ya rage min na kasance tare da kai fa?"
"Keep quite su'adah please....na riga da na gama magana,idan zaki iya zama gu daya fine,idan ma ba zaki iya zama ba duk daya,amma kada ki zargeni nan gaba" ta tabbatar da cewa shi din kaifi daya ne,baha magana ya sauyata,mutum biyu ne tal a duniya ke sauya masa ra'ayi koda baiyi daidai da mizanin mashi ra'ayin ba,baabaa prof sai ummee,sanin baya qaunar kuka ko misqala zarratin,koda na qaramin yaro ne ya sanyata saka kuka har da sheshsheqa,sai ya lumshe idanuwansa yana sauraren sautin kukan nata,a hankali ya zame wayar daga kunnenshi sannan ya kasheta baki daya ya cillata aljihu,shutting down din system din yayi sannan ya miqe tsaye yana jira ta qarasa mutuwa,ya laluba aljihunsa yaji muqullansa na jiki,ya dauke system din sannan ya dinga takawa a hankali ya nufi inda yayi niyya,baki daya baya marmarin komawa bangaren bare taci gaba da jagula masa lissafi,saboda haka ya isa ga qarama cikin motocinsa ya bude ya ajjiye kayanshi ciki ya tada ta ya fice ba tare da ya nemi kowa ba.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[1/27, 12:44 AM] ‪+234 909 381 1661‬: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣0⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*

*HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL*
___________________________________

Mamaki ya kama anty dije ganin sumayya,dariya ta dinga yi tana cewa
"Maganinki,da kika qi dawowa ga mai gaba daya nan taje ta taho mana da ke ai" itama sumayya dariya take
"Hmmm,amira,amira rigima amira tabara,sai ganinta kawai nayi wallahi"
"Ina sane ban gaya miki ba ai" guri sumayyan ta samu ta zauna tana ci gaba da dariya.

Nan ta shantake suna ta hira da anty dijen,bata tashi farga ba sai taga har sha daya tayi,hakan ya sanya ta bude dakinta tayi kwanciyarta,anty dije je cewa
"Abdallah fa?"
"Barshi anty,babu lallai yayi rigima"

****** ****** *******

Qarfe goma na safe tayi wanka bayan ta gama hada breakfast ta barwa anty dije sauran aikin gidan,doguwar riga ta saka ta wani irin yadi mai talewa,hijabi ta zura wanda ya saukar mata har saman tafin qafarta,niqabinta ta daura sannan ta fita ta tadda anty dije na goge kayan kallo a falo
"Anty zan wuce,nasan amira tana can ta cika fam,fashewa kawai take jira tayi" ta fada tana qyalqyalewa da dariya,dariyar itama tayi
"Ato,yau mai rabaku sai Allah" tana dariya ta saki niqab din nata ta fice a gidan.

Ya kusan a qalla mintuna talatin zaune cikin corridor din dake saman benanshi,bata san sanda ya shigo ba,tun daren jiyan taje zaman jiran shigowarshi taji shiru,ta kira wayar babu adadi saidai duka amsa daya ce wayar a akashe take,tun tana kumbura har zuciyarta ta fara saukowa,ta sani cewa fushinsa bashi da dadi,tana shan wuya a duk lokacin da yayi fushi,hakan ya soma daga hankalinta,kusan ranar bata yi cikakken bacci ba,saidai duk da haka bata san shigowarshi cikin gidan ba.

Cikin qanqanin lokaci zuciyarsa tayi fes,fuskarsa ta soma washewa,yaran dake shawagi kan idanunshi a harabar gidan,yaro daya tak yake hangowa cikinsu wanda bai sanshi ba baquwar fuska ne,saidai a yadda wasan da yaran ke gudana duka ya fisu kuzari da wayo,motsin yaron ya dinga bi da kallo yana sakin murmushin gefan baki.

Sai data tsaya suka gaisa da baaba mai gadi kamar yadda suka saba sannan ta sanya kanta cikin gidan,tunda ta shiga gabanta ke wani irin faduwa,kusan yara sunfi yawa a harabar gidan suna wasanninsu,jifa jifa mutane na kai kawo,juyiwar da abdallah zaiyi ya hangota,duk da niqabin dake fuskarta da hijabinta hakan bai sanya ya kasa ganeta ba,da gudu ya tafi yana kiran
"Ammiiiii....amminaaaa" cak yaran suka tsaya suna kallonshi ganin suna tsaka da wasa ya bar gun.

Da idanuwa yabi yaron ganin yayi wani guri da gudu,hannayenta ta bude baki daya duk da har yanzu niqabin na kan fuskarta amma murmushi ne kan fuskarta,durqusawa tayi ta daga shi tana nishi saboda nauyin da abdallahn ya dan yi mata sannan ta dage niqaf din,fararen jerarrun haqoranta a waje
"Wai abdallah,na kusa fara kasa dagaka,me kaci yau ka qara nauyi?" Dariya ya saki irin ta quruciya sannan yace
"Ammi,wata ummi ce,na kwana a dakinta,ta yimin wanka ta bani chips da qwai ni kadai na cinye,harda tea da suger sosai" dariya ta kamata,har sai data dora tafin hannunta kan bakinta,kafin tace wani abu hibba tayo gaba da gudu itama sauran yaran suka biyota,bata ankara ba taji an ruqunqumeta ana fadin
"Anty,kin dawo zaki mana labarin?" Waiwayowa tayi tana dariya,ta sauke abdallah tana fadin
"Kin manta yau ana bikin anty ameeraa?,sai idan an gama zan muku,muje ku rakani inda anty amiran take" gaba tayi yaran na binta a baya wannan ya riqe hannunta wannan ya riqe hijabinta a haka suka tafi.

Baisan yana binsu da kallo ba sai da suka bacewa ganinsa,ya lumshe idanunsa sannan ya bude a hankali,abun ya burgeshi ya bashi sha'awa,yana son yara har cikin zuciyarsa,bayansa ya jinginar jikin kujerar yana fidda zazzafan huci daga bakinsa
"My man" yaji an ambata a tausashe,yasan ko wace hakan ya sanya yaqi waiwayawa,sannu a hankali ta tako gabanshi,sanye take cikin riga da wando,ire iren shigar da tasan yana muradi suna burgeshi qwarai idan tayi,jikinta na fidda wani irin qamshi mai dadi,duka hannayenta ta zuba a kafadarsa,cikin shagwaba salon da tasan yafiso tace
"My man,ka sanyani a damuwa jiya,kasan cewa ina buqatar ka,baki daya kwanakin da zamu kasance tare ba masu yawa bane,amma man ka qauracemin" ko kadan bai da buqatar maganarta,hakan ya sanya ya saka hannunshi ya sauke hannayenta dake kafadarsa sannan ya ture kujerar ya miqe tsaye ta juya yana shirin barin gun,ranta ne ya baci,hankalinta ya tashi,ta tabbatar cewa ya hau bigerin da shawo kansa zaiyi wuya,bata kuma isa ta sha gabanshi don hakan zai iya jawo mata wata matsalar,tilas ta janye jiki tana kallonshi ya wuceta,hannayenta ta saki zuciyarta na zafi,idanuwanta na neman tara qwalla,babu shakka idan banda mustapha mustapha ne da babu namijin da zata zauna a duniya yayi mata haka,saidai mustaphan na dabanne kamar yadda yake daban a zuciyarta,mafita daya gareta ta kaishu gaba inda za'a sashi tilas yayi mata abinda take so din,bama inda ta saba kaishi ba wannan karon na can zata kaishi ba,sai ta juya da dan sassarfa ta ratsa ta dakinsa zuwa falonsa ta sauko qasa ta nemi hanyar ficewa ba tare data damu da sauya kaya ko daukar babban mayani ta suturta jikinta ba ko don girman wanda zata gurinsa.
Chapter 111 · 0% Book details