Sashe 95
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ta leƙa ta window falo ta hango shi, a cikin harabar gidan.
Ta ce "ÆŠago kanka sama ka ga" ya É—aga kai, ya hangota.
"To ka tafi, ba yau zan dawo gida ba, sai gobe"
"Wallahi idan ba ki fito ba, zan shigo har ciki"
"Kaikaikai, gidan mutanen za ka shigo?"
"Sai na shigo É—in tukuna kenan?"
Tayi dariya ta ce "A'a, rufa mini asiri, kar ka saka da ni da kai a zanemu, gani nan"
Hafsa ta yi ƙuri da ido, tana kallon jauhar, tana leƙen Al'amin kuma suna waya, tana ta dariya.
"Yaya hafsa, bari na tafi"
Hafsa ta tashi ta ce "Mu je na raka ki".
Suka fito harabar gidan tare, yanayin Al'amin a yanzu, akwai nutsuwa a tare da shi, ba kamar lokacin da ya je gidan su ya É—auki jauhar ba.
Hafsa ta ce masa "Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau" ya amsa idonsa a kan jauhar.
"Ya ka ke hararata ne, ba gani na fito ba"
Ya ce "Zaki yi bayani" motar Alhaji mu'azzam ce ta shigo gidan, yana hangen jauhar, ya ci wani irin wawan burki ya buÉ—e motar ya fito.
Ya ƙaraso ya kalli Jauhar ya ce "Jauhar, dama kina nan?"
Tayi murmushi ta ce masa "Eh, ina wuni?"
"Lafiya ƙalau jauhar, sai dawowa na yi aka ce mini kin yi aure, na ce ko wani laifin na yi miki? Hafsa ta ce mini dama akwai wanda ki ke so, shi ki ka aura, ni kuma baki gaya mini ba lokacin da nake neman aurenki"
Kallo É—aya jauhar ta yi wa Al'amin, ta ga ya murtuke fuska, idonsa ya fara kaÉ—awa zuwa ja.
Ta ce "Eh, gashi nan a gabanka mijin nawa, Allah dama ya ƙaddara yayata zaka aura. Yaya hafsa sai anjima".
Ya ce "Tsaya na baki na mota" ya saka hannu a aljihunsa ya ɗebo kuɗin da bai san yawan su ba, ya miƙa mata ta girgiza kai ta ce "A'a na gode"
Hafsa ta ce "Baby kawo ka ga" ta karɓi kuɗin ta turawa jauhar a jakarta, ta ce ba a mayar da kyautar manya, ku gaida gida. Tuni Al'amin ya juya ya fice, idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi wa Alhaji mu'azzam illa, da wuƙar da take cikin rigarsa a soke.
Tun da suka tafi hanya, bai ce mata uffan ba, hakan ya sanya ta cikin matsanancin tashin hankali.
Da ya ajiyeta a gidan ma, tafiyar sa yayi, bai ko shiga gidan ba.
Ta din ga addu'a Allah ya sanyaya masa zuciyarsa. Duk yadda ya so ya sarrafa kansa ya kasa, sai da yayi shaye-shaye, domin rage raÉ—aÉ—in abun da yake ji, dan zuciyarsa har wani tururi take yi.
Har sha biyun dare, idonta biyu tana zaune, tana jiran dawowarsa, ya koma mata Al'amin É—in sa, dan ko sallama bai yi ba ya shigo, ya wuceta ya tafi É—akinsa.
Cikin fargaba, tana addu'a, ta bi bayansa, warin wiwi duk ya cik wurin.
"Sannu da zuwa, nan zan kawo maka abincin?"
"Fita ki bani wuri, kafin na kakkaryaki na zubar. Idan ba kya son zama da ni, ba sai kin wulaƙanta ni, ta hanyar kai ni wurin tsohon saurayinki ba, shiyasa nake ta baki zaɓi tuntuni a kan zama da ni, ba dan na sarrafa zuciyata ba, sai na kashe mutumin nan har lahira yau, fita ki bani wuri, bana ƙaunar ganinki ma".
Ta marairaice ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, wallahi da na san zamu ganshi da ba mu je ba, ni saboda 'yar uwata na je".
"Saboda 'yar uwakki, ko kuma saboda ki ganshi?"
"Ya za ayi na je ganin wani, alhalin ina É—auke da igiyar aurenka a kaina"
"Ki daina wani kwantar da murya, na riga na gane abun da ki ke nufi, da in da ki ka dosa, if you still loves him zan iya sakin ki, ki iya koma wurinsa, tun kafin na illata ki, ba zan juri wannan cin fuskar ba, nan gaba ban san me zaki aikata ba"
Cikin tsananin ɓacin rai ta ce "Idan ka sake ni, hakan baya nufin rayuwata ta zo ƙarshe, jaririn da ya zo duniya ma Allah ya na iya karɓar rayuwar mahaifiyar sa, kuma ya raya mata shi. Ka yi mini duk hukuncin da ka ga shi ya dace ni" ta fice daga ɗakin, cikin tsananin ɓacin rai da damuwa.
Ransa yayi matuƙar ɓaci, jin yadda ta gaya masa maganganu, gashi dama a cake yake, ya nemi wata ƙwaya ya haɗiya ya kwanta, dan kar ayi ɓatacciya. Da asuba ya farka, ya saba ta zo tayi ta fama ta tashe shi, amma yau taƙi zuwa.
Yayi sallar asuba, gari yayi haske ya fito, amma ba ta fito ba, ya gaji da zama ya fita.
Da azahar ma, abincinsa ta ajiye masa ta yi zamanta a É—aki, idan yana falo tana É—akinta, idan yana É—aki sannan zata fito.
Ya shareta shi ma, yana jiran ta zo ta bashi haƙuri kamar yadda ta saba, amma taƙi, sai ya ji gidan yayi masa duhu babu daɗi. Kusan kwanaki uku, ba wanda yake shiga harkar wani.
Yau har ya cire kaya ya kwanta, ya tashi ya zauna yayi shiru yana tariyo maganganun da ya gaggaya mata, sai ya ji sun É—an yi nauyi da yawa.
Ya tashi ya tafi É—akinta, kasancewar babu wuta, ya kunna fitilar wayarsa, ya shiga.
Tana banÉ—aki tana wanka, ta jingina fitilarta a kan mudubi, tana haska mata cikin toilet É—in.
Ya ƙarasa gaban mudubin, ya ɗauki wayar ya kashe fitilar.
"Waye a nan?" Tayi maganar cikin tsoro, dan ba ta san ma ya dawo ba.
"Waye?" Yayi shiru bai yi magana ba.
Da sauri ta gama kwara ruwan a jikinta, ta fito sai dai É—akin yayi duhu, ba ta ganin komai.
"Wai waye ne?" Tayi maganar tana laluba hanya.
Direction É—in da yake ta nufo, cikin tsoro, kawai ta ji ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Cikin tsananin tsoro ta ware baki za ta yi ihu ya tsohe mata baki ya ce "Shhhhh, Al'min ne"
Ayshercool
08081012143