← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 95

Sashe 54

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu lokutan sai su shafe kwana biyu ba su haɗu ba, gashi zai kwana a gidan, amma ba zai shigo ba sai ta yi bacci, duk da wataran ba ta baccin sai ta ji shigowarsa, asubar fari kuma sai ya fice, ranar da ya ga dama kuma, sai ya bari gari yayi haske, ko za ta bashi abinci, dan sai yanzu ya fuskanci abincin waje wasu lokutan ga ƙaurin hayaƙi gashi ba sa jin sinadaran ɗanɗano, nata kuwa har cikin kansa yake jin su.

Yau ma dawowa ya yi rana tsage-tsage, walid ya sayo musu abinci, yana fara ci ya ji babu daÉ—i, ya ajiye ya ce gida zai tafi.

Walid ya ce "Da ranar nan tsaka zaka fi gida?"

"Eh" ya amsa a taƙaice.

"Lallai, na fuskanci lamari yana ta daidaita to Allah ya sa mu ji alkhairi ya kawo zuriya É—ayyiba"

Ya haÉ—e rai ya ce "Mai laya"

Walid ya ce "Sorry maza, na kiyayi mai zamani" ya fice ya tafi gida.

Jauhar tana ta lissafin kuɗin hannunta, sun kusa ƙarewa, girkin ma duk da dabaru take yin sa, ga gogan babu ruwansa sai dai ta dafa ya lashe.

Da 'yan dabaru take yin É—an wake yau, ta aiki almajiri ya sayo mata kabeji da cucumber, tana jiran dawowarsa, Al'amin ya dawo, a duk lokacin da za ta ganshi sai ta razana, gashi ba sallama yake yi ba, ya hangota da tukunya a kan gas, ya yi ajiyar zuciya ya san zai ci abinci.

Ya shiga É—akinsa, ya tarar ta sake wanke masa kaya, ta gyara É—akin tsaf.

Tsaki yayi ya ce "Ita dai wannan an yi 'yar wahala"

Ya daidaici lokacin da ta gama girki, ya dawo falo ya zauna, aikuwa sai ga ta abinci bakinta É—auke da sallama.

Bai amsa na sai Alla-alla ta kawo ta ajiye, saboda yadda ƙamshin manjan, ya cika masa hanci.

Ta ajiye masa ya haÉ—a abun sa ya fara ci.

Ta zauna a gefensa, cikin fargaba ta ce "Yaya" shiru ya yi mata, yana haÉ—iye É—an wakensa da hurhuÉ—u biyar-biyar.

Ta sake cewa "Yaya magana nake dan Allah abu zan tambayeka".

"Malama sunana Aminu, kar ki sake ce mini wani Yaya" a ranta ta ce 'Ai na san a rina'

A zahiri kuma ta ce "Ai ba zan iya faÉ—ar sunanka ba, ya za ayi na faÉ—i sunan mijina kamar mara É—a'a" sai ya ji abun wani banbarakwai wai mijinta.

"To me zan din ga ce maka?" Ba ta jira amsar sa ba, dan ta san ba zai amsa ba, ita kuma zaman kuramen nan da suke yi ba son sa take yi ba, ace kana zaune a ƙarƙashin mutum, amma ba zai kulaka ba.

"Na ji abokanka suna ce maka boss, ni kuma sai na ce maka master, idan na ce master zaka amsa, ko nima boss zan ce? Tun da ba ka son yaya?" Ta tambaye shi tana murmushi ba tare da ta kalli in da yake ba, saboda kwarjinin da yake yi mata, yanzu haka ma ƙarfin hali kawai take da take yi masa magana.

Kallonta yayi, tana murmushi dimple É—in ta na side É—aya ya lotsa, ya gane dakiya kawai take yi, amma a tsorace take yi masa magana.

Duk da bai bata amsa ba, amma matsern da ta ce zata din ga kiransa da shi, ya so yayi murmushi, amma yaƙi ya sha kunu, yana suɗe kwanon ɗan wakensa.

Cikin hikima ta ce "Da da sauran garin ɗan waken nan, da na dafa maka wani, ko na ƙaro maka?"

"A'a" ya ajiye kwanon, cikin sauri ta miƙa masa wani tsumma mai kyau, ta ce "Gashi ka goge hannunka, manjan yana da kamu, sai mu je waje na zuba maka omo ka wanke sosai" ya karɓa ya goge, ya koma ya kashingiɗa yana duba wayarsa mai madannai.

"Na ce, dan Allah sonake na shiga maƙwabta na yi musu sallama na tare, wai haka ake yi, ka ga mu bamu cewa kowa mun tare ba"

"Sauka lafiya" ya faÉ—a ba tare da ya kalleta ba.

"Yauwwa na gode sosai master, bari ayi la'asar, sai na je. Yauwwa mutumin ɗazu ya ce wai mai unguwa na nemank..... Ba ta ƙarasa ba ya tashi, dan surutunta ya fara isar sa.

Bayansa ta bi da kallo, 'Da sannu wataran zaka tanka mini ne, ni ba zan iya rayuwar zaman kurame ba' tayi maganar a hankali.

Huɗu da rabi, bayan ta yi la'asar, ta leƙa ɗakinsa ta ce masa za ta fita, ta tarar yana salla.

Wata irin ajiyar zuciya ta yi, tare da hamdala a zuciyarta, ba ta taɓa tsammanin yana kai goshinsa ƙasa ba.

Ta zauna a bakin ƙofar tana kallonsa, duk da shaf shaf yake yi, kuma azahar da la'asar ya haɗa a lokacin, amma ta ji dadin ganin yana salla.

"Master bari na je, idan ka idar ka sani a addu'a, Allah ya sa ka daina jin haushina, ban san me nayi maka ba" dama ta san ba amsawa zai yi ba ta fita.

Matasan 'yan mata ne su biyu a gaban rahila suna cin abinci, da alama daga makaranta suka dawo, domin kuwa bayansu jibga jibgan akwatuna ne, na 'yan makaranta.

"Umma, nifa haryanzu na kasa daina mamaki, wai yaya ne yayi aure? Wai dan Allah ya aka yi aka samu aka bashi 'ya a yadda yake? Kuma ba a bari mun dawo ba aka yi bikin?"

Rahila ta ce "Ke dallacan, waye ya ce miki abun na shiri ne shahida? Neman mafita nake ba shiri faka-faka na saka aka samo wata yarinya ya je can ya ƙarata, ya ƙara sako mini yaro a gaba, irin kallon da yake yi mini, tsaf zai halakka ni, cikin ikon Allah tun da aka yi auren, ban sake ganinsa a gidan nan ba, ya samu mace yayi luf"

Shahida ta ce 'Ni wallahi mai tsautsayin da aka aurawa nake jin tausyai, yaya za ta yi da shi dan Allah dan Annabi?"

Amira ta ce "Ke ina ruwanki ne shahida, ina ruwanki da ko ma wa ce ta aure shi, ba dai an samu ya tafi na, case close".

Shahida ta yi murmushi ta ce "Ina ne gidan nasa ne?"

"Yana can gidansa na ɗorayi, ba kuma cewa na yi ki je ba, kar abun da ya kai ki gidansa, balle ya lallaɓa ya dawo mana nan ya je can su ƙarke".

"Ahh haba umma, sai mu yanke alaƙa da shi duka kenan? Yayi aure muna school kuma mun dawo ba zamu ganshi ba?"

Amira ta ce "Wallahi a garin shishshigin nan da ki ke masa, zai kassara rayuwar ki, ki yi ta shige masa yana yarfaki"

"Wallahi ki ka je gidansa ma sai na ci ubanki shahida, na gaya miki, ke baki san sai ku kasa auruwa ba saboda mugun halinsa da mummunan tabon da yake da shi ba a unguwar nan?"

Shahida ta ajiye cokalin hannunta ta ce "Umma, shi fa jini ya fi ruwa kauri, the only male brother i have, sai ki ce sai na yanke alaƙa da shi?"

"Au jayayya zaki yi da ni? Shi Abban uban meye idan ba yayanki ba?"

Ta tashi ta ce "Ai ba babanmu É—aya ba, Yaya Al'amin kuma babanmu É—aya, kowane ina son sa"

Rahila ta ce "La ila ha illalahu Shahida "

Amira ta ce "Dan Allah umma bar shashasha, za ta gane kurenta ne"

Rahila ta cigaba da salallami, a kan yadda ke adawa da ita wasu lokutan a kan Al'amin.

***
Juahar gidan malam lawan ta fara shiga, wato gidansu halimatu da walida, yaran da suke zuwa tayata hira, suka gaggaisa da maman, sannan su halimatun, suka rakata sauran gidajen maƙwabta, tayi musu sallama. Har wurin masu kayan miya, da masu shaguna suka nunnuna mata da wurin makarɗe.

A bayan gidan suka je har gidan wata tela, da har da yaranta, su na shigarwa jauhar, suka gaisa jauhar ta tarar da yaran suna stone work a jikin ɗinki, har ta karɓa tana taya su, saboda a rayuwarta tana son sana'oin hannu suna matuƙar burgeta.

Take cewa matar, idan an samu stone work ta din ga aika mata da shi tana yi mata.

Matar ta ce 'To nawa zan din ga baki, dan kuwa ina samun aikin su sosai da sosai"

Cikin tsananin murna, da jin cewa ta samu abun yi, ta cewa matar, ko nawa ne ta bata, tana son za ta din ga yi, nan hira ta ɓarke, take gaya wa matar, ta iya shirin dutse, har adon da ake yi da shi a jikin ɗinki, duk zata iya, suka yi yarjejeniyar matar zata din ga bata ta yi mata.

Ganin hadari ya fara haɗowa, ya sanya ta yi mata sallama, ta koma gida, sai dai tana komawa, ya zura takalmansa zai fice, ta ce masa kar ya fita, hadari ne a garin, amma ba ta gama rufe baki ba, ta ji ya buɗe ƙofa ya fice.

Ta kawar da abun da zata kawar, ta rurrufe ko ina, ta laluba ta ɗauki mp a in da ta ajiye, ta tarar ya ɗauke kayarsa, ta ce "Da sauƙi, tun da ba ka yi mini faɗa ba".

Ruwan sama aka yi, kamar da bakin ƙwarya, ga wata irin iska da ta jefa jauhar, cikin razani da tashin hankali, yadda kwanon yake ƙara ji take tamkar zai kwashe ne, saboda ƙarfin iskar da ruwan.

Ta takure wuri guda, tana ta addu'a, kasancewar lokacin da ake ruwan sama, lokaci ne na karɓar addu'a, mafi yawan addu'arta a kan Al'amin ne, da take masa fatan shiriya.

Ko da ruwan ya tsagaita, ta fito falonta, ruwa ya shigo sosai, ya jiƙe ɗakin, ta buɗe ƙofar falon, rashin kyakykyawan magudanan ruwa, ya sanya kwatocin layin yin ambaliya, duk suka shigo mata gida, gashi ba ga da rariyar kirki, sai ta banɗkuna, dan haka babu wurin da ruwan zai fita, tsakar gidan ya shafe da ruwan kwatami, falonta ma duk ruwan ya shigo, gashi idan aka yi ruwan, tsigar jikinta tayi ta tashi.

Haka ta samo kwano, ta din ga ɗibar ruwan tana zubarwa, ta naɗe carfet ɗin ta, ta jingine, sai zallar buhun da aka shimfiɗa a ƙasa, ta din ga kwarfe ruwa a falon nan.

Ta je ta yi sallar magariba, Allah ya sa ruwa bai shigar mata bedrooms ba.
Chapter 54 · 0% Book details