← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 95

Sashe 62

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba ya ce "A'a, zuwa na yi dama na ganki, ni da ba a san da zuwana ba"

Jauhar ta ce "Dan Allah baba ka tsaya"

Ya ce "Gidanku ba zan tsaya ba, kira mini mijinki, zamu yi magana"

Ta tashi ta shiga É—akinsa, ta ce "Master, baba yana son ganinka".

Ya jinjina mata kai, ya tashi ya fito, ya samu wuri a ƙasa ya zauna.

Baba ya ce "Malam Aminu dan Allah alfarma zan nema, ka san jauhar ba ta kammala sakandare ba, an fara registration É—in WAEC ne, shi ne na ce ina neman alfarma, zan biya mata tayi registration ta yi jarrabawa dan Allah".

Aminu ya ce "Babu damuwa, Allah ya bada sa'a".

"Amin Aminullahi, Allah ya saka da alkhairi" Baba ya miƙe ya ce zai tafi.

Cikin rauni ta ce "Baba daga zuwanka sai tafiya kuma?".

"To Waliyiyya ba dai na ganki ba".

Kamar mara gaskiya, haka ta biyo bayan baba, a tsakar gida ya tsaya ya kalleta ya ce "Jauhar menene?" Ta girgiza masa kai alamar bakomai.

Ya juya zai buɗe gate, ta riƙe rigarsa ta fashe da kuka.

Ya ce "Subhanallah, gaya mini menene? Wani abun yake yi miki?" Girgiza masa kai ta sake yi.

Ta cukuikuye rigarsa, ta cigaba da sheshsheƙar kuka, shafa kanta ya dinga yi sai dai ya kasa hanata cigaba da kukan.

Sai ma hannu da ya sa, yana goge hawayen da suke ƙoƙarin zubo masa, ya san ba zata faɗa masa koma menene ba, amma yanayinta ya nuna masa tana da damuwa.

Dan kanta ta cika masa riga, ta goge hawayenta ta ce "Ka gaida gida baba, ka ce ina gaida su mama da Anty da kowa da kowa"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Za su ji in sha Allah, gashi ke ba waya ba, ranar talata ki je ki samu malam Hadi, a office É—in su, zaki yi thumb print, yayi miki registration"

Ta ce "To baba, na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" ya fita ta rufe gate É—in, ta jingina da jikin gate É—in, hawaye na cigaba da zuba daga idonta.

Duk yadda suka yi, Al'amin yana kallonsu ta window, ta goge hawayenta kafin ta dawo É—akin, ya bar falon. Haka ta koma bedroom É—in ta, ta kwanta tana ta tunani daban-daban a cikin zuciyarta.

****

'yan uwan Alhaji mu'azzam kuwa, ba su gaya masa cewar an aurar da jauhar ba, suka ce masa babanta ya ce yayi haƙuri idan ya dawo ayi auren, abun ya bashi mamaki, ga wata irin kewar yarinyar da yake yi, yana jin son ta sosai da sosai a ransa, ya din ga addu'a da fatan Allah ya sa ba wani abun ne zai faru ba, saboda jinkirin da ake samu ba.

Kusan kwanaki biyu kenan, jauhar bayan ta gama ciwon mara, ta koma zazzaɓi, gashi babu abincin kirki, kuɗin da take tarawa a kati, ba ta son ta je ta ce a bata, a fuskanci akwai matsala, hakan kamar tonon asiri ne ga mijinta, 'yan unguwa su samu abun faɗa.

Haka zata fita ya sayo gari, da gyaÉ—a ko suga babu ta sha, shi kuwa garujen ko a jikinsa, sai dai yana ankare da yanayin jikinta.

Al'amin na zaune a katafaren falon honorable Indabo, yana jiransa.

Babu jimawa ya iso falon, yana ganinsa yayi murmushi ya ce "Ango ka sha ƙamshi, da alama amarya ce ta ɓoye mana kai har haka"

Shiru yayi, ya saka babban yatsansa yana sosa girarsa.

Indabo ya zauna ya ce "Tun shekaranjiya na shigo, nake nemanka amma ka ƙi zuwa. Da farko dai ina yi maka murnar angwancewa da ka yi, ina Abuja aka sanar da ni an kama ka, ana gobe ɗaurin aure, na tura P.A . Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya"

"Amin" ya amsa a ciki kamar an yi masa dole.

"To yaya shirye-shirye? Ina fatan kana ƙara shirya mini yaranka, babban zaɓe yana gabatowa, idan aka yi nasara aka samu kujerar nan, Aminu zaku warwasa daga kai har yaranka, har da na kusa da ku ma, dan Allah kar ka bani kunya, duk da ba ka saba bani ɗin ba".

"To" ya amsa yana kallon wani wurin daban.

"Ka san meyasa na kira ka?"

"A'a"

"Akwai wani matashi, yana nan a social media, ba shi da wani aiki da ya wuce adawa da ni, da aibata mana jam'iyya,kuma hankalin matasa ya fara komawa kansa, na rasa yadda zan yi da yaron nan, duk wasu hanyoyi da zan bi a siyasance, na yi amma ya ƙi ganewa".

"Me ka ke so ayi?".

Ya jefowa Al'amin hoton matashin, an rubuta adress É—in sa a jiki.

Kallo É—aya ya yi wa hoton, ba tare da ya É—auka ba, ya ce "Me ka ke so ayi masa?"

"Ire-iren sa suna da yawa, amma sonake ayi musu misali a kansa. Ina son yayi ido biyu da Switzerland É—in ka, ka yi masa shaida alamar kun haÉ—u".

Wani irin murmushi ya yi, ya fito da dogon harshen sa, ya lashi laɓaɓɓansa na ƙasa da suka yi duhu ya ce "Switzerland. Kamar ka ce idan aka samu kujerar nan, zamu warwasa da yarana da na kusa da ni, alƙawari ne ko zance?"

"Wace irin magana ka ke haka ne, ba zance bane ba, da gaske nake yi mana".

Al'amin ya ce "In ɗauke shi a matsayin alƙawari dai"

Indabo ya yi turus, ya kasa bashi amsa.

"Ba zan tura mota, ta tashi a bule ni da hayaƙi ba, ba senator ba wallahi ko shugaban ƙasa ka zama, ba za a bule ni da hayaƙi ba, dan haka maganar nan a matsayin alƙawari na ɗauketa"

"Kai fa matsalarka kenan Aminu".

"Menene sallamar aikina?"

"Masu kauri ne, ga wannan ka fara rage ta" yayi maganar yana ajiye masa envelopes.

"Ka san dai in da ka tura ni ko? Wallahi idan ka bani abun da bai yi mini ba, ba zan yi ba"

Indabo yayi murmushi ya ce "Ai somin taɓi na baka, akwai ciko"

Ya miƙe tsaye ya ɗauki envelope ɗin sa ya fice.

Sai da ya je can dabar su, ya sallame su, sannan ya nufi gida.

Da ya je gidan a buɗe ya tarar da ƙofar gidan, kai tsaye ya shiga ya tarar duk ta cika igiya da kayansa, ta wanke masa su.
Mamakin jauhar yake, rashin sanin ciwon kai ne, ko me yake damunta, ta ce ba ta da lafiya, amma ta zage ta yi masa wanki, hatta É—akinsa da ya bari kaca-kaca ta gyara masa.

Ya samu wuri ya zauna a kan kujera, ya kunna sigari yana sha.

Sallamarta ya ji a tsakar gida, bai amsa ba ya cigaba da shan sigarinsa.

A hankali take takawa, ga yunwa ga ciwo, ta shigo hannunta riƙe da 'yar leda.

Ta zauna a kan carfet jiki a sanyaye ta ce "Ka yi haƙuri, baka nan ne ban tambayeka ba na fita, magani na je chemist ɗin bakin titi na sayo"

Sai da yayi wani munafukin tari, saboda tun ranar da mai chemist É—in nan yayi masa É—inki, ya din ga jan ta da hira, ya ji ya tsane shi, amma ya fuske yayi mata shiru.

"Kar ka ga ban yi girki ba tun jiya, kuɗin hannuna ne suka ƙare, amma ga gurasa na taho mana da ita daga titi" ƙara yawan hayaƙin da yake fitarwa daga bakinsa yayi, ba tare da ya ko kalleta ba.

Jin ba shi da niyyar kulata, ya sanya ta yinƙura za ta tashi, sai dai ta yi wani irin razanannen ihu, kallonta yayi da sauri, ya ga ihun me take yi, dan ya san ba zai wuce wani abun haushin ne ba, dan kamar gyare haka take da ihu.

Ashe ƙadangare ne a ƙarƙashin kujerar da ta zauna a gabanta, tun shigowarsa ya ganshi, amma bai damu ba, ƙadangaren na ta neman hanyar fita, jikinsa yayi baƙi sosai, kamar an ciro shi daga kwata, yayi ba kyan gani.

Tuni ta suma a wurin, dan kuwa hannunta ta É—ora a kansa ba ta sani ba.

Maimakon ya tashi, sai ya zuba mata ido, cikin takaici, abu kaÉ—an sai ta suma, ko ta hau ihu.

Kamar ba zai tashi ba, sai kuma ya miƙe.
Ya saka hannu ya ɗauketa ya kwantar da ita a kan kujera, sai dai jikinta ya yi zafi sosai, sai yanzu yake tunanin zazzaɓi take yi kenan?.

Ya duba ledar magungunan da ta sayo, maganin É—aya mai hoton sauro, É—aya kuma pcm ne.

Ya kama gefen hannunta, ya ji bugun zuciyar ta yana bugawa da sauri, ya saki hannun nata yana kallonta, ita a rayuwata komai ma tsoro yake ba ta kenan.

A hankali ta fara motsawa, ta yinƙura za ta tashi, ya ce "Koma ki kwanta" ta ɗaga idonta a hankali ta kalleshi.

"Tsoro nake ji" ta faÉ—a muryarta na rawa cikin tsoro.

Ya sake kama hannunta, yana jin bugun zuciyar ta, ya saki ya ce "Tashi" ta yinƙura ta tashi a hankali, kanta na sara mata ga jiri saboda yunwar da take ji.

Tana daga kan kujerar a kwance, ya ɗage ɗaya kujerar da ƙadangaren yake ƙarƙashin ta, kawai ya saka hannu ya danƙi ƙadangaren ya jefa shi waje.

"Na shiga uku master, ƙadangaren ka ke kamawa da hannunka"

Tsaki yayi, ya wuce É—akinsa, jikinta ya din ga rawa, tsigar jikinta ta din ga tashi. Ya dawo ya dire mata leda, ya ce "Ki ci ki sha magani" ya jefa mata wani kwali sannan ya fita.

Kwalin ne ya fara ɗaukar hankalinta, ta ɗauka da sauri tana dubawa, sabuwar mp ce kar 'yar ƙarama mai kyau.

Ba ta san lokacin da ta yi murmushi ba, ta hau kukkunata tana dubawa, sai da ta gama, ta ajiye ta buÉ—e ledar.

Irin meatpie ɗin nan ne oasis manya kusan biyar, da ƙatuwar robar fura da nono.

Kasancewar a yunwace take kuwa ta hau ci, ta ji babu daÉ—i kwana biyu tana ciwo, amma bai iya yi mata sannu ba, dama magani ba ta saka ran ya saya mata ba, mutumin da bai ba ta abinci ba wane magani zai bata, ashe yana sane, sannu ce ko ya jiki ba zai iya ce mata ba.
Sai dai da tuna yadda ya ɗauki ƙadangare da hannunsa, sai tsigar jikinta ta tashi.
Chapter 62 · 0% Book details