← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 95

Sashe 49

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta hau ta da zagi a gaban mutane, wai sai ta saka an ce aure dole za ayi mata, taƙi walwala ko wanka ba ta yi ta shirya ba.

Jiki babu ƙwari, jauhar ta yi wanka, aka yi mata kwalliya.

Tayi kyau sosai da sosai, dama dai-dai gwargwado tana da hasken fata da kyanta na fulani.

Baba ne ya fara dawowa gida, gaba É—aya jikinsa a sanyaye, ana ta yi masa Allah ya sanya alkhairi.

Ya saka aka kira masa jauhar, zuwa É—akinsa.

Cikin tsananin tashin hankali da damuwa, Saifu ya shigo gidan, yana ƙwalawa baba kira.

Mama ta ce "Saifu lafiyarka ka ke yi wa mahaifinka irin wannan kiran haka?"

Bai saurareta ba, ya shiga É—akin baban, mama da anty suka bi bayansa, 'yan biki kuma suka yi cirko-cirko.

"Baba wane irin miji ka aurawa jauhar? Tun a masallaci nake nemanka ban ganka ba"

Baba yayi shiru, ya ƙi bashi amsa.

"Baba magana nake yi fa kayi mini shiru yanzu zaka yi alfahari da wannan zaɓin da ka yi mata?marainiyar Allah, ka rasa wa zaka aura mata sai tantirin ɗan daba? Laifin me tayi maka har haka, mutumin arziki ya fito yana sonta, amma ka hana shi ka bawa mutumin banza, yanzu wane mutumin kirkin ne zai so haɗa zuriya da mai dogon zamani"

A gigice jauhar ta ɗago idonta, gabanta ya shiga faɗuwa, tana jin yadda sunansa ya karaɗe arear unguwannin, duk da ba ta taɓa ganinsa ba, amma ya shahara da rigima da 'yan unguwar su, da shi da madaki tana jin sunayensu, ta san dai madaki, tun da cikin unguwar su yake.

Cikin zafin rai saifu ya sake cewa "Baba ka yi mini bayani, menene dalilinka na yin haka?"

"Saifu, kai ma ka fara shaye-shayen ne? Uban naka ka ke gaya wa haka? Shi ka ke tuhuma? Ba 'yar sa ba ce? Zai zaɓa mata abun da zai cutar da ita ne?"

Ya ce "Zai yi mana mama, ke da wannan matar menene ba zaku iya aikatawa ba, kuma na san ku kuka ƙulla komai, akwai Allah"

Jauhar kuwa kuka ta fara, amma ta kasa magana, jikinta ya din ga tsuma, Hafsa kuwa fita tayi, ta kira yaya tijjani, wai ga saifu can yana yi wa baba rashin kunya.

Aikuwa ya shigo cikin gidan da sauri, zuwa ɗakin baba, sai faɗi in faɗa yake da mama, baba kuma ya ƙi magana.

Yana zuwa ya É—auke saifu da mari, sai dai yana sauke hannunsa shi ma ya rama, take dambe ya kaure, sai dai jin hayaniya a waje ne, ya sanya suka yi saroro.

Bushe-bushen 'yan tauri ne yake tashi daga ƙofar gidan, nan da nan warin wiwi ya din ga shigowa gidan, yaran Aminu sun cika layin, suka din ga busar 'yan tauri, suna yi wa Aminu kirari, sai dai babu shi a wurin.

Su maman ma waje suka yi, domin zuwa su ga abun da yake faruwa.

Nan 'yan biki suka dare, wasu kuma suka tafi kallo.

Baba ya riƙo hannun jauhar, da take ta uban kuka, kamar shi ma zai fashe da kuka ya ce "Fatima, na yi miki laifi, ban san yaya aka yi wasu abubuwan suka faru ba, dan Allah ki yafe mini, in sha Allah ba zaki wulaƙanta ba, zaki yi alfahari da hakan, na san na daɗe ina zaluntar rayuwarki, ina cutar da ke, dan Allah ki yafewa baba jauhar, kar ki yi fushi da ni, in sha Allah sai auren nan ya zame miki alkhairi"

Ta share hawayenta ta jinjina masa kai ta ce "In sha Allah Baba"

"Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya yi miki albarka ya kare ki daga dukkanin sharri da abun ƙi, Allah ya kula mini da ke a duk in da ki ke.Na san dama ke mai haƙuri ce, zaki ci riba in sha Allah" ta jinjina masa kai tana ƙoƙarin haɗiye kukan da yake ƙoƙarin ciwota.

Ba a rabu da bukar ba an haifi habu, ta san wannan auren wani sabon ƙalubalen ne a rayuwarta.

Ƙawayenta tuni suka gudu gida, 'yan biki ma duk sun watse, ta samu wuri ta ƙule a ɗakinta, ta din ga kuka, tana neman agajin Ubangiji.

Kwatsam! Yaran madaki suma suka taho layin, da niyyar tarwatsa yaran Aminu, dan kuwa ba sa jituwar da za su bari su shigo musu layi, su yi musu wannan budurin.

Ba a jiyo komai, sai karafkiyar makamai, da zage-zage tamkar ana yaƙi.

Suna daga cikin gidan, suka jiyo ana cewa tun da aka aurar da ƴar gidan ga maƙiyinsu, idan ta bar unguwar ta bar ta kenan, idan suka kuma ganin ta, sai sun sassarata.

Mama ta ce "Zakiyya, kin ga wata tijara, ni fa hankalina ya tashi, ji kamar ana yaƙi".

"To ke ina ruwanki, da an kaita ba shikenan ba, can su je su ƙarata ba"

Suna cikin maganar, sai ga gwangwanin tiya gas, a tsakiyar cikin gidan Æ´an sanda sun sake dira, su tarwatsa su.

Jauhar ta ƙara takurewa tana kuka, saboda tsananin tsoro da tashin hankali, dan a kunnenta ta ji ana cewa, idan aka ƙara ganinta a unguwar ma, sai an sassarata.

Unguwar ba ta yi dai-dai ba, sai bayan sallar la'asar, hatta sallar la'asar a gida aka yi ta a unguwar, saboda tashin hankali.

Bayan Baba ya yi sallar la'asar, ya kira mama ya ce, ya shirya masa jauhar, ya kaita da kansa, tun kan yaran nan marasa ji su ce za su yi mata illa.

Idanun jauhar duk sun kumbura, sun jawur saboda azabar kukan da ta sha.

Mama tana dariya take cewa "Haba Jauhar, kowa da haka yake kafa nasa iyalin, da haka kowa ya saba"

Jauhar ta kalli mama, iya wannan tashin hankalin bai isa ya sanya su gane sun jefa rayuwarta a garari ba, amma take yi mata wannan surutan? Haka ta yi alwala ta yi sallar la'asar, sai dai ta kasa addu'a ma.

Ko kaya ba ta canza ba, mama ta É—aukko mayafi, ta ce tare za su kaita É—akin miji.

Sun fito waje, Saifu ya kawo kai, yayi turus ya ce "Baba, yanzu wannan tashin hankalin da aka yi a unguwar nan, duk a kan auren nan, bai sanya ka saduda ba, ka haƙura? Baba ya yi masa shiru, ya yi gaba hannunsa riƙe da na jauhar, ya buɗe mata mota ta shiga baya, suka ja suka tafi.

A can suka tarar da wasu daga danginsu Al'amin, a gidan suka din ga rangaÉ—a guÉ—a, da aka ce an kawo amarya, dan sun baro can gidan su Al'amin, a kan Abbu zai aika da motocin É—aukko amarya, sai dai suna ganin Baba suka nutsu suka yi shiru.

Har kan gado ya kaita ya zaunar da ita, ya riƙe hannunta, ya din ga yi mata addu'a, sannan ya sunkuya ya yi ƙasa da murya ya din ga yi mata nasiha, yana yi tana kuka, sai da ya gama ya din ga saka mata albarka ya ce mama ta wuce su tafi.

Angon kuwa yana can dabar su, ban da bushe-bushen sigari, babu abun da yake yi, hatta dambarwar da aka yi a gidan su amaryar bai sani ba, shi dai ya san Walid ya ce za su gayyato 'yan gangi da 'yan tauri, ayi nishaÉ—i.

Bai ma san a ina aka ya ba, balle ya san abun da ya faru.

Sai wajen ƙarfe takwas na dare, Walid ya dawo, ya din ga ba shi labarin, abubuwan da suka faru, da yadda suka yi da 'yan sanda. A ƙalla ya kai mintuna goma sha biyar yana zuba, yana bawa Al'amin labari, amma bai tanka ba.

Ya gaji ya ce "Maza, ka tashi mu shirya, mu raka ka gidan amarya".

Sai a yanzu ya É—ago ya kalleshi, amma ya yi tsaki ya koma ya kashingiÉ—a.

Walid ya ce "Wallahi ba ka isa ba, wai so ka ke sai Abbu ya yi fushi da kai? Dama na haɗa maka kayanka jiya, yau sai ka bar gidan nan, kai Allah ya ɗaga darajar ka, kana wasa da damar ka" walid ya cigaba da mita, yana ƙara haɗawa Al'amin kayansa a ghana must go, da masu dauɗa, da wankakku, har da takalma da brush, haka ya din ga danna su.

'yan uwan su Al'amin, babu yadda ba su yi ba, su ga fuskarta, amma fafur ta ƙi, ta din ga ƙudundunewa, suna nan tare da ita har tara na dare, suka gaji ga dare, masu zuwa ganin gida, duk suka gama, suka din ga tafiya, har ya rage saura itakaɗai aka bari.

Nan hankalinta ya fara tashi, daga ita sai farar fitila mai batir, tana ta addu'a a cikin zuciyarta cike da fargaba da tsoro. Tana ta tunanin kar 'yan daba su lallaɓo su zo su kasheta.

Ta gaji da zaman wuri ɗaya, ta ga ledar pure water, a ajiye a falo, da 'yan ganin gida suka zo da ita, ta ɗauka ta yi alwala, ta yi sallolin da suke kanta, ta zauna zaman dirshen tana tuna ƙalubalen rayuwa da ta haɗu da su kashi-kashi yanzu kuma ga ta kuma a wani mataki, mai hatsarin gaske.

Har bayan sha É—ayan dare, sai itakaÉ—ai a gidan.

Fargaba da tsoron da take ciki, ya ninku a zuciyarta. Kasancewar bacci ɓarawo ne, haka ya yi awon gaba da ita daga nan in da take a zaune kusa da gado.

Sai dai ba ta san adadin lokacin da ta shafe tana baccin ba, ta farka a razane, taga hasken wutar lantarki an kawo wuta. Ji ta yi kamar motsi a falon, ta lallaɓa ta leƙa cikin tsoro da tashin hankali bakinta ɗauke da addu'a.

Wani dogon mutum ta gani a kwance a kan doguwar kujera, ya juya bayansa, ya duƙunƙune da babbar riga, da alama sauro ne ya dame shi, ya lulluɓa.

Gabanta ya faɗi, ta koma ta zauna tana tunanin, wannan shi ne angon ko kuwa? Iya ƙoƙarinta ta dage kar ta kuma komawa bacci, saboda tsoron da take ciki.

Al'amin kuwa, Walid ne ya taso shi a gaba, ya kai shi har gidan, daga shi sai shi, da ƙullin kayansa a ghana must go wajen sha ɗaya da rabi na dare.

Suna tafe yana lallaɓa shi, sai da ya tabbatar ya shiga, sannan ya tafi.
Chapter 49 · 0% Book details