Sashe 51
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fitowa ya yi daga ɗaya ɗakin, hannunsa riƙe da baƙar leda, kallo ɗaya ta yi masa ta gane shi, ƙwala ihu ta yi, ta ruga da gudu ɗakin da gadonta yake, ta rufe ƙofar ɗakin.
Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Hanyar da ta bi ya bi da kallo, yana tunanin a ina ya taɓa ganin fuskarta.
A ransa ya ce "Mahaukaciya ce kenan, Shiyasa aka aura mini ita, haukana ya fi naki" ya fito daga falon ya saka takalmansa ya fice.
Jauhar kuwa durƙushewa tayi, ta ɗora hannunta a ka ta ce "Na shiga uku" a take ta fashe da kuka ta ce "Allah ka sanya mafarki ne ba gaske ba, Allah ka sa ba wannan ne mijin nawa ba? A gabana ya kashe wani, Allah Ubangiji ka rufa mini asiri ka dube ni, ya Allah ka dubi maraicina da ƙangin da na baro, ka sassauta mini a nan, ya Allah ka sa ba shi ne mijina ba". Ta cigaba da addu'ar tana kuka, ta kasa fitowa sai ma ƙara sakata da ta yi a ɗakin tana kuka.
A take komai ya dawo mata fes, yadda ta ganshi, ya yi kisan kai, hannunsa riƙe da mutum da wuƙa a gefen cikinsa.
"Na shiga uku, ko biyoni yayi ya kasheni, me na yi masa wallahi ban gayawa kowa yayi kisa ba" tayi maganar ƙasa-ƙasa tana kuka.
Ko da wasa ba ta yi yinƙurin, sake buɗe ƙofar nan, a banɗakik nan tayi alwalar magariba da ta isha'i, ta kasa addu'a komai, sai fatan Allah ya sa ba wannan ne mijinta ba.
Ba ta sake fitowa ba, har garin Allah ya waye.
Zaman ɗakin ya isheta, fitowa kuma ta gagareta, sai da ta leƙa ta ga babu kowa a falon, bakinta ɗauke da addu'a ta fito.
Ba kowa, ta leƙa tsakar gida, ya rufe mata ƙofar, babu taklmansa kuma a wurin.
Ta dawo falon, ya cinye taliya da man da da ta zuba masa tas, ya ajiye komai a wurin, hatta wadda ta ɗan zube a ƙasa bai kwashe ba, jug ɗin ma daban kofin jug ɗin daban.
Ta kwashe komai ta fitar tsakar gida, ga sauran kwanukan da ta fara wankewa ta bar su a wurin, komai yana nan.
Sai zuciyarta ta fara raya mata, ai ba shi ne mijin nata ba, ya shigo ne kawai ya tsorata ta, sai ta cigaba da addu'a Allah ya ƙara nesanta ta da shi.
Ta yi 'yan gyare-gyaren ta na gida, yaran da suke shigo mata, yau ba kowa duk sun tafi makaranta, ga tsakar gidan wasu irin manyan ƙadangaru suna bin bango, dan haka fitowa tsakar gidanma wahala yake bata, saboda tsoro.
Ta datse gidan, yadda babu wanda zai shigo sai ya bubbuga.
A jere ta sake jera kwana biyu ba ta sake saka shi a idonta ba, akwai ranar da bai kwana a gidan ba. Bai sake dawowa da rana ba, sai cikin daren nan, idan ya tarar da abinci ya zauna ya cinye abun sa, kafin ta tashi ya fice.
Abun ya fara damunta, ga tsoron gidan take ji, sosai da sosai.
Wajen la'asar ta ji ana buga ƙofa, ta din ga tambayar waye, amma ta ji shiru.
Har zata haƙura da buɗe ƙofar, ta zata ba kowa, aka kuma buga gate ɗin maimakon ƙofar da ƙarfin gaske.
A tsorace ta buɗe, aikuwa ya hankaɗo ƙofar, ta kuma kurma ihu, ta kwasa da gudu, ta shiga kitchen ta rufe ƙofa.
Sororo ya tsaya yana tunanin, ihun me take yi dan ta ganshi? Ya basar ya shiga ya yi abun da zai yi ya fice.
Sai a yanzu ta fara gazgata lallai wannan ne mai gidan, shi ne mijin da aka aura mata.
Cikin kuka ta ce "Allah komai ka yi dai-dai ne, Allah ka sanya shi ne mafi alkhairin da nake ta fata". Ta sanya wa zuciyarta za ta yi ƙoƙarin, danne tsoronsa da take ji, amma abun da ba ta gane na shi ne, ba iya abun da ya faru waccan ranar ne kawai yake ba ta tsoro ba, tsananin kwarjinin sa ne ke ƙara rikita ta.
Suna dabarsu, Al'amin yana ta shan sigari, Walid ya ce "Maza, gaskiya abun da ka ke yi baya dacewa, an kai maka mata, amma kullum kana nan kana cakewa, akwai matsala ne?".
Al'amin ya rausayar da kai ya ce "Yarinyar Mahaukaciya ce ashe"
Cikin rashin fahimta ya ce "Mahaukaciya kamar yaya?".
"Kamar yadda na gaya maka, ihu take yi itakaÉ—ai"
Walid ya ce "Ko dai tsorata ta ka ke yi? Ki tsaya kun yi magana kun gaisa?"
Aminu ya ce "Da wa?"
"Da amaryar mana" ya ja tsaki, yana mayar da sigari bakinsa.
"Wallahi Aminu da ni aka yi wa auren gatan da aka yi maka da na more, haba baka kyautawa gaskiya "
Yayi masa shiru, yaƙi ko kallonsa, dan ko zancen auren ba ya son ji, haka kurum ji yake yi kamar an yi masa dabaibayi.
Saifu kuwa yanzu ban da gaisuwa, babu abin da yake haÉ—a shi da da mama da Baba, dama Babar su hafsa Zakkyya ba shiri suke yi ba, ko kallo ba ta ishe shi ba.
Sai dai sun fara zancen a kawo 'yar aiki, dan duk yawan 'yan matan gidan nan, ba sa iya aikin gidan, girki sai dai a jagwalgwala, wani ya ciwu wani ba zai ciwu ba, gidan nan kuwa wasu lokutan kamar fadar mahaukaciya, dama jauhar ce ana ɓatawa tana gyarawa, yara na cire kaya suna zubarwa tana kwashewa, amma yanzu bata nan babu mai gyarawa.
Baba kuwa ƙasan zuciyarsa yana nadamar auren da ya yi wa jauhar, amma ba zai iya nuna hakan ba, ya duƙufa yana yi mata addu'ar samun kwanciyar hankali a gidan aurenta.
Cikin dare da ya dawo, ya ji gidan a rufe, bai tsaya jiran komai ba, ya kama katanga ya dira kamar ɓarawo.
Gaba ɗaya jauhar a zatonta, itakaɗai ta kwana a gidan, saboda ba ta ji bugun ƙofa ba, ta fito tana ta share-sharenta, ta ɗora ruwan zafin dafa makaroni, saboda su yaya saifu ya sayo mata, taliya makaroni, mai maggi sugar da sauransu.
Ta fara bin É—akunan tana gyarawa. Sai dai ta din ga jin warin taba, ta rasa daga ina take jin warin.
Kawai ta nufi É—akin da yake ciki, ba tare da ta san yana ciki ba, ta afka, a zatonta ita kaÉ—aice a gidan.
Yana kashingiɗe yana zaune yana kaɗa ƙafa yana shan tabarsa, ya zazzage kayansa a kan katifar ɗakin, ghana must go ɗin, ya cillar da ita a tsakar ɗakin. Har da takalma a kan katifar, soson wanka da brush duk suna kan katifar.
Ba wannan ba kawai, har da ledoji da kwalayen taba, ga tokar maganin sauro ko ina.
Kamar mahaukaciya haka ta juya, ta ɗiba da gudu, sai dai a wannan karon, rufa mata baya ya yi, ya cimmata, tana ƙoƙarin rufe ƙofar ɗakin da ta shiga, ya hankaɗa ƙofar ta faɗi jikinta na wata irin tsuma.
Ya zuba mata ido, wanda ya haddasa mata tsuma da karkarwa cikin razani da matsanancin tsoro.
Bai ce mata komai ba, sai cigaba da kallonta da yake yi.
"Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ban gayawa kowa ka kashe shi ba, dan Allah ka yi haƙuri, ni matar aure ce, ka daina shigo mini gida" tayi maganar wani irin gumi na tsatstsafowa daga fuskarta.
Ya sunkuyo saitinta, warin sigarin da ya sha, tana dukan hancinta, sai a lokacin ya gane ta, ya gene a in da ya taɓa ganinta.
"Kin ganni na kashe shi?"
Ta jinjina kai alamar eh.
"Mahaukaciya ce ke? Ki na da taɓun hankali ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a, tana ja da baya.
"Idan ki ka kuma ganina, ki ka gudu kina ihu" ya zaro wuƙa a ƙugunsa, ya nuna mata. Sannan ya ce "Sai na yi miki abun da ki ka ga na yi wa wancan mutumin, wato in kashe ki"
Ta girgiza kai ta ce "In sha Allah ba zan sake ba" ya miƙe, ya mayar da wuƙarsa ya fita ya bar ta.
Wani irin numfashi ta din ga saukewa, cike da tsoro, ta ƙara gazgata cewar, shi ɗin ne dai mijinta ba wani ba.
Ta jima a wurin tana kuka, sannan ta tashi a hankali, ta sake komawa É—akin da ta gano shi.
ÆŠakin yana nan, kamar mahaukaciya ta buÉ—e dealer, ya watsar da komai, sai warin sigari É—akin yake yi.
Ta ɗaɗɗaga labulaye, ta zo ta durƙusa ta fara ware kayansa, wankakku da masu datti, ta kwashe takalmansa, ta jera masa a bayan ƙofa, wankakkun kayansa, ta shirya su a cikin wardrobe, marasa wankin ta fita da su, ta share ɗakin tsaf, ta ɗauki brush ɗin sa da toothpaste, ta kai masa banɗakin cikin ɗakin, da bokiti da buta.
Kayanta akwai turarukan wuta, da aka bata na gudunmuwa, sai dai ba ta da gawayi, dan haka ta kunna na tsinke, ta sassaka a ko ina, saboda korar warin sigarin nan. A cikin kayan sa ta ga wata Mp, ta É—auki mp ta kunna ta ji tana yi, ta kunna radion jiki, ta ji tana yi, ta fita tsakar gida da ita, tana ta aikace-aikace, da zummar kan ya dawo ta kashe ta ajiye masa, ta É—an É—ebe mata kewa, ta manta ko sallama baya yi kafin ya bayyana.
Gidan su jauhar, akwai maƙwabciyar su Anty lubabatu, tana tausayinta sosai, suna mutunci da juahar, dan idan ta haihu, jauhar ta yi ta zuwa gidanta, dan ta ɗauki yaranta, ita ce ta haɗata da 'yan gidan su, take karɓar shirin dutse tana yi.
Tun washegarin kai jauhar, ta shiga gidan ta ce wa su mama, a bata mutum É—aya ya rakata gidan jauhar, amma suka ce ba wanda ma ya san gidan.
Jauhar kuwa, ta gama aikinta tayi wanka, gidan babu komai na abinci, sai taliyar nan da macaroni da yaya saifu ya saya mata, gashi sun isheta, sai dai babban abun da yake yi mata daɗi, tana da damar ta dafa ta ci yadda take so, saɓanin idan a gida ta girka, sai ta gama wahalar a sanmata.