← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 95

Sashe 74

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ransa ya din ga maimaita ;idan ka sake ni, ka tozarta maraicina. Ita a tunaninta abun da ya faru ne ya sanya ya ce zai rabu da ita? Marainiya ce kenan? Ya tambayi kansa a lokaci É—aya ya bawa kansa amsa da no wonder.

Sai kuma jikinsa yayi sanyi, shi wannan wahalar da take sha, ya É—auka za ta yi murna da abun da ya ce, kawai ya basar ya kwanta.

Sosai ta din ga kuka, a ɗakinta, tana tunanin wane irin baƙin jini ne da ita haka? Duk yadda take haƙuri tana lallaɓa auren nan, amma ya yi mata wannan sakayyar, take ta fara tunanin wane irin zama zata koma ta yi a wannan gidan na su, da suke nuna mata ƙiyayyarsu a fili?

Da ƙyar ta shiga banɗaki ta gyara jikinta, ta fito zauna a ƙasa ta cigaba da kuka.

Bayan ya gama abun da yake yi, ya fice ya bar gidan.

Kanta ne ya fara ciwo, ga numfashinta da yake ta barazanar ɗaukewa, ga wani irin azababben ciwon mara da yazo mata da zazzaɓi duk a sanadin tashin hankalin maganganun Al'amin.

Yaya saifu kuwa tun da ya dinga bibiya, aka tabattar masa da an saki Al'amin, hankalinsa ya kwanta, ya so ya je gidan nata ya tabattar amma har ga Allah ba ya ƙaunar shi, duk da sau ɗaya ya taɓa ganinsa, ranar ɗaurin auren a masallaci, kawai a jikinsa yake jin azabatar da jauhar yake yi, dan ba zata faɗa bane kawai.

Al'amin kuwa, su walid suna ta hirar irin tashin hankalin da matarsa ta shiga, da aka kai shi prison, da irin aiken da ta din ga yi masa da kayan amfani yana prison.
Gaba daya sai ya tafi lissafin yanzu idan ya saketa, to abinci fa? Amma shi duk da haka gani yake hakan ne mafita, wannan tashin hankalin da take shiga idan ya shiga cakwakiya, sai ya ga kamar yana shiga hakkinta da yawa, kuma a idonta yake ganin damuwa idan ta ganshi a halin maye.

Da daddare da ya dawo, yadda ya fita ya bar kayan karin kumallo, haka ya dawo ya tarar da su, ba ta taɓa ba, sai yayi tunanin ko wani abun ta ci, dan haka ya ƙarasa hallake buredin da ƙwan, ya shige ɗakinsa ya cigaba da busa hayaƙi cikin nishaɗi.

Washegari ya din ga zaman jira, ya ga ta fito ta yi abun karyawa, amma shiru, gashi bayan sallar asuba ya yi shaye-shaye dan haka yunwa yake ji sosai.

Ganin har sha ɗaya ba ta fito ba, ya sanya ya fice, sai dai kuma yajin aiki ake yi, da ƙafarsa ya tafi unguwar su, wurin su Walid.

Yau ko tsintsiya jauhar bata É—auka ba, tana ta fama da kanta, da la'asar ya dawo, ya sake tarar da gidan yadda ya bar shi.

Gaba ɗaya sai gidan yayi masa wani iri, ya kwashe kwanukan da ya karya da su jiya, ya fara tunanin ko fushi tayi, shi ne ya sanya taƙi yin shara a gidan.

Yana tsaye yana kallon falon, ya É—aga kai ya ga ta fito daga É—akinta, kamar fuskarta ta kumbura.

Ya tsaya yana kallonta, ya ga tana ɗaga ƙafa da kyar a hankali.

Kawai ta yanke jiki ta faÉ—i a wurin, a sukwane ya yo kanta, ya É—agata.
ta motsa da ƙyar, hannu ya saka ya juyota jikinsa sosai, wani irin hucin zafi jikinta yake fitarwa, ta ɗaga idonta da ƙyar ta kalle shi, idanunta sun yi ja sosai da sosai ta mayar da su ta lumshe.

Hankali tashe ya ce "Menene?"

"Kaina ne zai fashe" tayi maganar hawaye na bin gefen fuskarta, kafin yayi magana, jikinta ya hau karkarwa, haƙoranta na karo da juna, idonta na neman juyewa saboda zafin zazzaɓi da matsanancin ciwon kai.

Ɗagota yayi sosai ya ce "Ki na ji na?" Ta ɗaga masa kai da ƙyar.

"Zan je in samo abun hawa, mu je asibiti"

"Yajin aiki ake yi, ka manta?" tayi maganar a galabaice.

Sai yanzu ya tuna, dan da ƙafa ya je yawonsa ya dawo, ƙungiyar ƙwadago na jagorantar yajin aiki da kuma zanga-zanga domin janyo hankalin gwamnati a kan wasu haƙƙoƙin 'yan ƙasa.

"Na sani, yanzu zan dawo"

Ba tare da ya san in da zai nufa ba, ya kwantar da ita kawai ya fita, a ransa yake jin idan ya bar yarinyar nan da ciwo, bai yi wa kansa adalci ba.

A titin unguwar, ya ga wani É—an adaidaita sahu, ya tsayar da shi ya ce "Malam mara lafiya zaka É—aukar mini"

Mai baburin ya ce "A'a yi haƙuri ba aiki na fito ba, ba ka san ana yajin aiki ba ne maigida?"

"Ana yajin aikin amma ka fito da babur?"

"Eh na yi wani uzuri ne, gida zan koma".

A É—an hasale ya ce "Mara lafiya zaka É—aukar mini"

Shi ma a hasale mai baburin ya ce "Na ce ba zani ba, ana dole ne? Ka nemi wani mana"

A fusace ya daki tayar gaban adaidaita sahun, mai napep ya waro ido ya ce "Malam meye haka?"

Kawai ya shiga bayan adaidaita sahun, ya zare wuƙa ya ce "Bi cikin layin nan, ko na zaro hanjinka yanzun nan da russia" tsit mai ɗan sahun yayi, ya bi layin tare da yin sarandar ƙwace masa baburin ma zai yi.

A ƙofar gidan ya saka shi yayi parking, ya sauka ya ƙwace mukullin babur ɗin, ya shiga cikin gidan da shi.

Ya É—auko hijjabinta ya saka mata.

"Master"

Ya kalleta ba tare da ya amsa ba, ta ce "Yi haƙuri, na saka wahala"

"Ki yi mini shiru"

Ta ce "To" ya É—aukkota kamar matacciya, ya shiga da ita napep É—in.
Ya ciro mukullin ya miƙa wa mai baburin ya karɓa yana cunkusa fuska ya ce "Megida amma ka san yajin aiki ake yi, ina zan kai ku? asibitin gwamnati babu aiki".

Al'amin ya ce "Ko ma wane asibitin ne mu je"

Kamar wata 'yar kyanwa, haka ta kwanta luf a jikinsa, da suka hau kwalta, sai sanyin da take ji ya ƙaru, dan haka ta ƙara shigewa jikinsa, jikinta na ta rawa.

Wani Asibitin kuɗi ya kai su a gadon ƙaya, Al'amin ya cilla masa dubu ɗaya, ya rungumi jauhar ya shiga da ita.

Ba a taɓa ta ba, sai da ya biya kuɗin file da komai, sannan aka fara yi mata abun da yakamata.

suka shiga wurin likita, aka tambayi sunanta, ya manta surname É—in ta da ya gani a invitation É—in su, dan haka ya ce a saka mata Zahra Al'amin, shekaru ya ce bai sani ba, sai kintata akayi, aka tura su yin gwaje-gwaje.

Bayan sun dawo,ikitan da ya duba ta, yayi ta mita malaria tayi mata mummunan kamu, ga ulcer kuma ga jininta ya hau.

Al'amin ya ce "Malam ba lissafi ko masifa zaka yi mini ba, ayi mata abun da yakamata kawai" yanayin yadda yayi maganar, ya sanya likitan gane waye shi.

Sai dai Al'amin yayi mamakin jin an ce jininta ya hau.

Likitan ya ce "Tana da aure ne?".

"Eh"

Likitan ya ce "Ayi gwajin ciki, kar mu yi treatment da ka".

Al'amin ya ce "Babu ciki"

Likitan yayi saroro yana kallonsa.

"Malam ni ne mijinta, babu wani ciki, ka yi sauri a fara yi mata abun da yakamata, tana ta murƙususun ciwo. Ko ba ka yadda ba? Al'ada take yi, ko kuna ganin cikin kwana ɗaya ne ko biyu?"

Likitan ya ce "Ikon Allah"

Jauhar duk da tana fama da kanta, wata irin kunya ta rufeta, ya aka yi ya san tana period ma.

Tana ta yinƙurin amai, sai dai babu komai a cikinta, aka ce ya samo mata wani abun ta ci, kafin a fara treatment.

Ya fita ya sayo uwar gurasa mai nama, da ruwa ya kawo mata.

Ya zo ya tarar, an saka mata ruwa, da allurai.

Ya kalli fuskarta, bacci take yi sosai, tana iya ƙoƙarin ta a kan sauro, kar ya cije ta, ba ita ba har shi, da magariba ta yi za ta hau rufe ko ina tana kunna maganin sauro.
Abun da bai sani ba, tsananin damuwar da ta shiga bayan kama shi, da maganganun da ya gaya mata jiya ne suka haifar mata da ciwon.

Sai dai babbar damuwarsa, hawan jinin da aka ambata.

Sai wajejen magariba, ta É—an samu afuwa.

Wajen isha'i aka sallame su, suka yi mata wasu allauran, aka ce masa maza ya kaita gida, alluran suna kashe jiki.

Duk kuɗin jikinsa sai da suka ƙare, suna fitowa harabar asibitin, jikinta ya saki ta tafi zata faɗi, ya riƙeta da ƙyar suka fita, sai dai gaba ɗaya titin babu ababen hawa.

Ganin sai tangaɗi take yi, kuma bashi da wata dabara ya sanya, ya ɗaure ledar magungunan ta, ya ɗaga ta ya saɓa a bayansa, ya ɗauki takalmanta ya riƙe a hannunsa, ya zagaya ya bi lunguna.

A din ga yi ana sauke hakki, idan baki saya ba 0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Ayshercool
08081012143

🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955

A ƙalla ya kai awa ɗaya da mintuna talatin, yana tafiya da ƙafa, bayansa ɗauke da jauhar, wani wurin idan da mutane, ayi ta kallonsa, tun da sauran sahun mutane, har ya zama saura ɗai-ɗai.

A haka ya isa gida, ya buɗe gidan, ya shiga da ita ɗakinta ya kwantar da ita, zazzaɓin jikinta ya sauka, sai dai gaba ɗaya jikin nata ya saki.

Ya kunna fitilar wayarsa yana haskata.

Surutai take yi, wanda tun suna hanya take yi, sai dai ba ya gane me take faÉ—a sai yanzu.
Chapter 74 · 0% Book details