Sashe 42
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zakiyya ta dafe kai ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke ina jin labarinsa har a radio, dama shi ne, amma lokacin kina amarya kamar a nutse yake"
"Ke rabu da ni oho masa, ni sonake ya bar gidan nan, kar ya hana mini ƴaƴa auruwa, ko ya illata wani, dan Abba da ki ke gani ɓaras ya karya mini ɗa kamar kara.
Kina kallon halin da muke ciki, yanzu babu bushasha kamar da, ɗan abun da ta bari ya gada, ubansa ya fito da shi, ya ƙara jari, yaƙi wai ba zai taɓa masa kaya ba, kin ga da zai bar gida a neme shi a rasa ai ma samu mu ci, babu irin korar da ban saka ya yi masa ba, amma yaƙi tafiya".
Haka suka cigaba da hirarraki, wadda galibi a kan rayuwar makaranta da suka yi, sai na iyalinsu hirrar take.
Kusan sati biyu, da maganar da baba yayi, a kan wanda ya zo wurinsa a kan jauhar, yayi shiru da maganar kamar ta wuce, ya dawo da yamma, kasancewar juma'a ce, jauhar ta duƙufa tana ta shirin dutse. Kuɗinta da suka taru ba ta samu ta sai pad ba, sai ta sayo riɗi, ta ce zata soya ta juya kuɗin, idan suka taru ta saya da wuri.
A tsakar gida baba ya tsaya, ya ƙwala mata kira, ta amsa ta fito ta tsuguna.
Ya kalleta ya ce "Ki shirya, ki je ga baƙonki can a waje ya zo ku gaisa".
Ji tayi kamar ta fyalla da gudu, ta tsaya da saurayi, ya ce mata me, ko ta ce masa me?
Amma ta amsa masa, ta tashi ta shiga É—akinta, jikinta duk yayi sanyi.
Sajida ta shiga falo in da su surayya ke kallon Bollywood.
"Kai kuna nan kuna kallo, baba fa da gaske yake auren jauhar zai yi muna zaune"
Surayya ta ce "Kamar yaya?"
"Kamar yadda na gaya muku, wallahi wai wani ne wai yake son ta"
Hafsa ta ce "Da yardar Allah ba za ta yi aure ta barmu ba".
Jauhar kuwa turus ta yi, tana kallon ƙatuwar motar da ke ƙofar gate ɗin gidan an yi parking ɗin ta.
Zura kai ta yi tana lelleƙawa ta ga waye baƙon.
Ya buɗe ƙofar motar ya fito, yana murmushi.
Turus ta yi tana kallonsa, ya yi murmushi ya ƙaraso ya jingina da jikin motar, ya ce "Mayar da idon mana, kin yi mamakin ganina ko?"
Da sauri ta durƙusa ta ce "Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau Faɗimatul Jauhar"
Ya ɗan gyara tsayuwarsa ya ce "Na san dole zaki yi mamakin ganina, zuwa na yi na sake bayar da haƙuri, a kan incident ɗin da ya faru, na tsorata ki da na yi, na kusa buge ki da mota"
Jauhar ta ce "Ai bakomai ya wuce, na ma manta"
"Ai ni ban manta ba, dan sai da na koma wurin da muka haÉ—u, na tambayi ina ne gidanku, na samu baba muka yi magana, hankalina ba zai kwanta ba, har sai na aure ki, na kai ki gidana, na rarrasheki da kyau"
Jauhar ta sunkuyar da kanta, tana jin abun wani banbarakwai. Ita gaba É—aya ma ji take yi ya takurata.
"Jauhar"
"Na'am" ta amsa tana kallonsa da idanunta da suke farare tas, sai dai ba manya ne can ba.
"Me ki ka ce? Ni aurenki nake son na yi, kuma nan kusa wallahi ba da nisa ba, na yaba da tarbiyarki fiye da yadda ki ke tunani".
Kamar za ta yi kuka ta ce "Ai ban gama makaranta ba, ni yarinya ce kai kuma babba ne"
Dariya yayi ya ce "Wow, ashe shagwaɓaɓɓiya ce har haka? To dan ni babba ne ba za a aure ni ba? Kar ki ce haka, zaɓin Allah ake nema kin ji sweetheart, ki yi ta addu'a Allah ya tabattar mana da alkhairi. Ina da mata ɗaya da yara biyar kacal, yaro ne ni haryanzu" yayi mata maganar yana kashe mata ido ɗaya.
Ita kam gabanta ne ma ya faÉ—i, yara biyar ne kacal, ita duk wata harka da za ace kishiya, tsoronta take ji.
"Kar in cika ki da surutu, bani lambar wayarki, a hankali zamu saba, kin shiga raina sosai, zan yi iya ƙoƙarina na baki kulawa dai-dai iyawa ta, kuma karatunki, in sha Allah sai kin ce kin gaji dan kanki" yayi maganar yana miƙa mata wayar ta saka masa lambarta.
"Bani da waya ai"
Ya ce "Ohh, ashe fa ƴar baby ce, ba ta isa riƙe waya ba, zan kawo waya in sha Allah"
"A'a dan Allah kar ka kawo mini, ba ma za a bari na riƙe ba"
"To ikon Allah, to ta ina zan din ga jin muryarki? Amma shikenan bai kamata na karya dokar gidanku ba, zan san abun yi na nemi iznin baba na kawo wayar. Amma baki tambayi sunana ba"
Ita dai tayi shiru, tana mamakin yadda babban mutum kamar wannan, yake ta kashe mata murya.
"Sunana Alhaji Mu'azzam. Ina dillancin kayan sawa, mussaman na mata, ina shigo da kaya daga ƙasashe daban-daban, kuma ni ɗan siyasa ne, yanzu haka ina da muƙmi a gwamanati, amma ba dai wannan ba, ni amincewarki nake nema, kar ki yi saurin rejecting ɗina ki yi mana addu'a kin ji zahrana"
Jauhar dai ta yi gum, ita wannan tsayuwar ma kawai, kunya take bata kamar ta falfala da gudu.
Haka ya gama surutansa, ba komai take fahimta ba, lissafi kawai take a zuciyarta, saura dozen nawa ta gama shirin dutse, ta kai ta karɓo kuɗin, ta cika ta soya riɗi.
Kuɗin da ya miƙo mata, ya sanya ta ja da baya, tana girgiza kai. Ya kaɗa ya raya, amma fafur ta ƙi karɓa, sai haƙura yayi.
Haka yayi mata sallama ya tafi, da sauri ta shiga gida, dan kuwa Alhaji mu'azzam duk ya cinye mata lokaci, ba ta ƙarasa shirinta ba, mugun kallon da ta tarar da ƴan matan gidan na yi mata a tsakar gida, ya sanya ta shan jinin jikinta, dan kuwa tuni yaran gidan suka kawo musu tsegumin irin motar da aka zo wurin Jauhar da ita.
Sai jikinta yayi sanyi, ta hau tunanin laifin me tayi? Jiki a sanyaye ta É—aukko aikinta ta cigaba.
Sai dai suka din ga zaginta babu dalili, hafsa ta saka ƙafa tayi fatali da ɗan plate ɗin jauhar da take zuba dusten.
Hankali a tashe ta É—aukko tsintsiya tana tattarewa, ba tare da ta damu da son sanin dalilin da ya sa hafsan tayi mata haka ba, domin kuwa idan da sabo ta saba.
Yaya saifu da ya fito daga banÉ—aki ne, ya É—urawa Hafsa ashar, saboda ya ga abun da ta yi hafsa.
Babarta ce ta fito tana yi masa masifa, tana kare hafsa, da mayar masa da zagin da yake yi mata.
Aikuwa mama ma ta fito ta haushi da bala'in menene ruwansa da shiga abun da babu ruwansa, nan faɗa ya harƙe, sum-sum jauhar ta ja jikinta ta koma ɗaki.
Da daddare bayan sallar isha'i, baba ya kira jauhar ɗakinsa, ya tambaye ta yaya suka yi da baƙonta, amma ta kasa magana, sai duƙunƙuna hannunta da ta din ga yi a hijjabi.
"Jauhar"
Kanta a sunkuye ta ce "Na'am baba".
"Ba zan yi miki dole ba, ban bawa mutumin nan damar zuwa wurinki ba, sai da na yi bincike a kansa, na san makarantar ki ke tunani, ina mai tabbatar miki ya tabattar mini zai bari ki cigaba. Bana jin daɗin irin rayuwar da ki ke yi a cikin gidan nan, babu yadda zan yi ne. Amma idan ba kya son sa, ba zan yi miki dole ba, ki bi komai a sannu, ki yi istikhara da addu'a, na san ke mai yawan addu'a ce, da miƙa lamuranta ga Allah, ki ƙara dagewa sosai da sosai, ki nemi zaɓin Allah"
"To Baba in sha Allah"
"Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya yi miki albarka, ya sa naga jikokina ƴan farare masu kyau kamar jauhar ɗina" rufe fuska tayi ta ƙunshe fuskarta tana murmushi.
Tun da ya shigo layin, wasu daga matasan layin ke darewa, suna ɓuya, ko a jikinsa, tafiyarsa yake yi cikin hanzari da ƙasaita, sumar sa ta cika masa kai, ya aske wani wurin ya bar wani, irin cikakken mara jin nan.
Kai tsaye ya buɗe ƙofar gidan, ya kunna kai cikin gidan.
Babu sallama ba komai, ya kutsa cikin falon in da suke zaune suna karyawa.
Abbu ya É—aga kai ya kalle shi, ya ce "Uban me ka zo yi mini gida? Me na gaya maka a kan zuwar mini gida?".
Ya sunkuyar da kai ya ce "Ganinka na zo na yi na gaisheka"
"Ba na buƙatar gaisuwarka Al'amin, ai tun da ka zaɓi watsewa a duniya, ka yi fatali da tarbiyarka nima na sallamaka, ka koma wurin abokanka ƴan wiwi da suka fi ni a wurinka. Kalli tsinannen askin da yake kanka, ka zo mini banda warin wiwi babu abun da ka ke yi, sanna ka ce ka zo gaishe ni? Ai ni na barwa duniya kai ka tashi ka bar mini gida"
Yayi shiru yaƙi tashi, kuma ya ƙi magana, sai murza zoben azurfar hannunsa da ƙarfi da yake yi, zuciyarsa na zafi.
Rahila ta ce "Dan Allah ka fita Aminu, wannan warin da ka ke yi, zan iya amai wallahi, kuma ni idan ina ganinka tsoro nake ji wallahi, tun da kullum a buge ka ke kar ka illatani ko yarana a banza" tamkar tana magana da dutse, haka yiyin gingirin gim, bai motsa ba.
"Ba magana ake yi maka ba?" Yayi masa maganar cikin tsawa.