← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 95

Sashe 37

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta lura yana da mai aiki a gidan namiji, har girki da gyaran gidan shi ne yake yi masa su.

Ya kashingiÉ—a yana kallon tv, ita kuma tana gefensa a É—arare, sai mutsu-mustu take yi tana share hawaye.

Sahidar yatsunsa ya gani kwance a fuskarta, har ya ɗaga ya basar ya cigaba da kallonsa yana kaɗa ƙafa.

***
"Allah ya taimaki maigida"

"Menene labari?"

"Na samu kiran waya É—azu, wata yarinya ta je an kaita har ofishin secret files, an É—aukko mata file É—in viper ta duba"

"Wacece ita?"

"Yarinyar da ka ce ayi amfani da ita a kama Viper"

Da sauri ya ce "What? Ya aka yi ta san da file É—in ta je? Waye ya ce a bata?"

"Wallahi ban sani ba, amma an tabattar mini da ga sama su ma aka ba su umarnin ba ta"

"Sama ina, waye ya bayar da umarnin?"

"Ban sani ba wallahi, kuma da gaske lawyer ce, idan kuwa haka ne, za ta iya yiwuwa da gaske ta haÉ—u da Viper, Æ´ar jaridar nan raina mana hankali ta yi"

Indabo ya numfasa ya ce "Kar ku yi gaggawa, kar ta san mu na bibiyarta, ka bi ta hannun ƙawarta, ku samo me take son samu a kansa, idan ta ƙi, ku kamata ku azabtar da ita".

Ya amsa da "Ok sir".

Daga kotun, gida arfa ta tafi, tun daga shigarta, Sauda ta fara tsokanarta da faÉ—a, amma ba ta ita take ba, É—akinta tafi ta cigaba da tunani da lissafi.

Kamar wadda aka zungura, ta É—aukko wayarta ta kira Nasir.

Murya ƙasa-ƙasa ya ce "Arfa ya dai? Mun shiga meeting ne"

Kamar za ta yi kuka ta ce "Yaushe za ka dawo?"

"Zamu yi waya an jima, ki yi haƙuri"

"Kar ka kashe mana dan Allah, ni ina cikin damuwa magana nake son mu yi, wani abu zan baka"

Ya ce "Wani abu me?"

"Abu ne mai muhimmanci a kan viper, amma sai ka yi mini alƙawarin ba zaka yi mini faɗa ba ko ka gayawa abba ba"

Tattara nutsuwarsa ya yi ya ce "I hope, ba wata kasadar ki ka je ki ka aikata ba"

Ta girgiza kai ta ce "Ba wata kasada da na yi, ni dai ka yi ka dawo, kan na mutu"

A rikice ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, menene ki gaya mini"

"Ka kwantar da hankalinka, kawai dai ka yi ka dawo, abun yana da muhimmanci, na san yadda zaka same shi kai tsaye"

"Kin ga ba zan iya jira ba, gaya mini menene sai na aika su Mu'azzam, dama wanda aka kama ɗin nan ya ƙi magana"

"Sai ka dawo gaskiya" ta kashe wayar gaba ki É—aya, dan kar ya biyo ta, ta sake dafe kanta.

Sumayya na news room, tana jiran lokaci ya cika, ta gabatar aka turo ƙofar aka shigo. Sak tayi tana kallon mai shigowar.

Mutumin da honorable ya saka ya karɓi wayarta ne, ranar da ta je gidansa.

Ya ja kujera yana kallonta, ya ce "Ya dai, kin yi mamakin ganina ne? Mintuna goma sha biyar suka rage miki, kan ki fara karanta labaran, zaki yi mini aiki".

Ta zuba masa ido, amma ba ta ce uffan ba.

"Meyasa ki ke yi mana ƙarya a aikinmu? Da gaske ƙawarki ta haɗu da Viper?"

Cikin ɓacin rai Sumayya ta ce "Na gaji da amsa wannan tambayar, idan ba ku yadda da ni ba, ku nemeta ta amsa muku mana"

Ya shafi sajensa ya ce "Zamu gani ai, yau ta je court ɗin da aka yi wa Viper shari'a, ta karɓi secret file ɗin sa ta duba, zaki kira ta, ki ji dalilin zuwan ta, da kuma abun da za ta yi da file ɗin"

Sumayya ta girgiza kai ta ce "Nabila ba wani abu da za ta amfana muku, kawai na san Æ´ar rigima ce, so take ta yi suna ta É—aukaka ta taimakawa yayanta shikenan"

Yayi dariya ya ce "Za mu gani, daga yanzu zuwa azahar ɗin gobe, idan baki kawo rahoton dalilin bin diddigin shari'ar Viper da take yi ba, abun da ba kya zato zai faru" ya miƙe tsaye ya ce "lokaci ya cika, ki gabatar da aikinki"

Sumayya ta dafe kai cikin matsananciyar damuwa, tana tunanin wannan wace irin rayuwa ce.

Murtala ne ya shigo yana faÉ—in "Afuwan sisyna, mamager ya kira ni ne, na saita komai ki fara".

"Ba ka ga mutumin da ya fita yanzu ba?"

Ya kalli ƙofar ya ce "Ban ga kowa ba"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan mu fara".

***

Ƙaramar wayarta ce isheta da vibration a ƙasan pillow, ta ɗaga ta ce "Bacci fa nake ki ke ta kiran wayata".

"Haka dai, daga bacci sai kwalliya da cin abinci, ke har kin koma gida kin kwanta, ni tun 9 gani har 5 ban tashi ba"

Nabila ta ce "Ke ba na samun bacci a Æ´an kwankin nan wallahi"

"Meyasa?"

"Wallahi a tsorace nake, ba na iya bacci, gani nake kowane lokaci viper zai kashe ni, cewa yayi fa sai ya kashe ni, sonake Yaya ya dawo na danƙa masa wayar nan, na huta, wai da wayar wa ki ka kira ni ne?"

Sumayya ta ce "Wayata ce ta É—auke, ina ki ka je ne yau?"

"Wurin aiki mana, amma da labari sosai, mu haÉ—u gobe in Allah ya kaimu"

"Yakamata mu haÉ—u kam, dan na ga mutuniyarki bunkure, a gidan honorable Indabo"

Daga kan gadon da Nabila take ta miƙe tsaye ta ce "Amma ba ki gaya mini ba sai yau?"

"Na san halinki ne, uzzura mini zaki yi, ke bari na tafi gida ma yi magana"

Ta kashe wayar, ta kaiwa murtala wayarsa, dan ta fuskanci mutanen honorable na bibiyar kiran wayar da take yi.

Wuni guda ramma ba ta sake saka Abdul a idonta ba, sai dai kukunsa idan ya kammala girki, ya ƙwanƙwasa mata ƙofa ya ajiye mata abinci.

Tayi kuka har ta gaji, ta koma addu'a, tare da fatan Allah ya kuɓutar da ita daga sharrin zaluncin Abdul.

Tana zaune a ƙasan carfet, har wurin sha biyu na dare, ya shigo yana kokawa da ƙofar ɗakin, saboda a buge yake.

Ta tashi tsaye cikin tsoro, sai dai ba tare da ta yi masa laifin komai ba, ya hau ta duka, ya din ga ball da ita yana taka ta da ƙafarsa, tun tana kururwa har ta kasa sai ajiyar zuciya, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta iya yi.

Tamkar dabba haka ya afka mata, ba tare da la'akari da ƙarancin shekarunta ba, kodayeke ina tunani ga wanda hankalinsa ya gushe?.

Bai farka ba sai kusan tara na safe, yayi miƙa ya tashi yana kallon ɗakin, da sauri ya kalli gadon bai ganta ba, ya kalli jikinsa, ya tashi yana mayar da kayansa, kawai ya ga jini a gefensa, har zuwa banɗaki, cikin hanzari ya nufi banɗakin, ƙofar tana buɗe dan haka ya shiga, ya tarar da ita a zaune ta jingina da jikin bath jini yana ta zuba daga jikinta, ga jikinta duk a kumbure saboda duka, idonta a rufe.

Ya ƙarasa ya durƙusa ya ɗaga hannunta ya saki, ya ga ya koma babu alamar numfashi a tare da ita, rigarsa dake jikinta, tayi sharkaf da jini.

Dafe kansa yayi yana tuna abun da ya faru jiya, kamar mafarki.
🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*

16

Shi gashi ko sunanta ma bai sani ba, ya sake ɗaga hannunta, amma hannun ya sake dawowa ƙasa.

Ya kai hannunsa hancinta, ya ji tana numfashi kaÉ—an-kaÉ—an.

Ya haÉ—a ruwa a bath É—in mai É—umi, ya cire rigar jikinta ya ajiye a gefe.

Ya ƙarewa jikinta kallo, ko ina shatin duka ne da ya yi mata, take wani abu mai kama da tausayinta ya ɗarsu a ransa, ya ɗaga ta, ya sakata a cikin bath ɗin, ga abun da ta yi ɓari nan daga cikinta a ƙarƙashin ta.

Duk da ƙyanƙyaminsa, da yadda ƙarnin jinin yake hawar masa ka, haka ya din ga tarar ruwa, yana kwarawa a banɗakin, ita kuma ya din ga canza ruwan da take ciki, saboda yadda yake ɓaci da jini.

Rigarta kuwa, wuri guda ya ware ta, dan kuwa yarwa zai yi, bai san yadda zai yi da ita ba.

Ya fita da sauri, ya kira mai aikinsa solomon, ya rubuta masa abubuwan da yake buƙata ya ce ya sayo masa.

Har solomon ya je ya dawo, yana ta ƙoƙarin ganin ya tsayar da jinin da take zubarwa.

Ya É—auke ta zuwa kan gado ya kwantar da ita kamar gawa, ya sake É—iban jininta, ya yi bawa solomon ya ce ya kai kowane lap ne, idan ya kai ya kira shi a waya.

Ya saka mata drip hannu biyu, ya sake su, yana yi yana duba vitals É—in ta.

Ƙofar ɗakin ake ta bubbugawa, ya tashi ya buɗe, ya ga saif a tsaye.

Saif ya kalleshi ya ce "Ya na ganka kamar mara gaskiya? Lafiya kuwa?"

Ya girgiza kai ya ce "Ina fa lafiya, yarinyar nan ce tayi miscarriage"

Saif ya ce "Shi ne me to? Dama ba haka kake so ba, na ga ma fa kasheta za ka yi ka bar ta"

Abdul ya ce "Haka ne, jiya daka sauke ni bayan ka tafi, ka san a buge nake, na dake ta sosai"

"Lallai Abdul, yau ka fara yi wa mata haka to?"

Ya girgiza kai ya ce "No, kawai su sauran su ne suke kawo mini kansu, shiyasa ban taɓa jin komai ba a kan abun da nake aikatawa, sai ta ji sauƙi sosai, zan kasheta na huta"

Saif ya ce "Well mu je in ga jikin nata"

Abdul ya tsaya a gaban ƙofar ya ce "No, ba zaka shiga ba"

Cikin mamaki ya kalli Abdul ya ce "Lafiyarka kuwa?"

"Ras nake, ba zaka shiga bane kawai"

"Ka kashetan kenan?"

"Idan na kasheta, zan kasa gaya maka ne, ko tsoronka nake ji?"

Suna haka solomon ya kira shi, ya haÉ—a su da masu lap, ya gaya musu gwaje-gwajen da yake so a yi wa jinin ramma da ya bayar aka kai.

Ya koma ɗakin da take, ya rufe ya saka mumulli, ta ciki, ya sake nufar gadon, ya hau yana tattaɓata ya ga ko ta na da rai.
Chapter 37 · 0% Book details